Ticker

6/recent/ticker-posts

Littatafan Da Ake Koyon Tafarkin Salafiyya A Cikinsu

Bin Salafiyya shi ne bin fahimtar Salaf Magabata a dukkan babukan Addini.

Abin nufi da fahimtar Salaf shi ne fassarar da Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut tabi'eena da Limaman Addini suka yi wa Nassoshin Shari'a; Nassoshin Alkur'ani da Hadisi, da yadda suka yi aiki da su a babin Aqeeda da Fiqhu da Mu'amala.

Fahimtar Salaf a fassarar Alkur'ani yana kunshe cikin littatafan Tafsirai kamar haka:

1- Tafsirin Dabariy.

2- Tafsirin Ibnu Abi Hatim.

3- Tafsirin Sa'eed bn Mansur.

4- Tafsirin Ibnul Jauziy "Zadul Maseer".

5- Tafsirin Ibnu Kathir.

6- Tafsirin Suyudiy "Al- Durr".

Sai kuma fahimar Salaf a babin Aqeeda ana samunsa ne cikin littatafan Aqeeda da aka ruwaito da Isnadi, kamar su:

1- Al- Sunna na Abdullahi bn Ahmad bn Hanbal.

2- Al- Sunna na Khallal.

3- Al- Sunna na Ibnu Abi Asweem.

4- Al- Ibana na Ibnu Batta.

5- Al- Shari'a na Ajurriy.

6- Sharhu Usuli 'itiqadi Ahlis Sunnati wal Jama'a na Lalaka'iy.

Da makamantansu, suna nan da yawa.

Sai kuma littatafan da aka hakaito Aqeedar Salaf a jumlace, kamar su:

1- Aqeedar Dahawiyya.

2- Aqeedar Salaf ta Isma'iliy.

3- Aqeedar Salaf ta Sabuniy.

Da makamantansu.

Haka fahimtar Salaf a ma'anonin Hadisai kuwa, musamman a babin Fiqhu, ana samunsa ne cikin littatafan "Athaar" kamar su:

1- Muwadda ta Malik.

2- Musannafu Ibnu Abi Shaibah.

3- Musannafu Abdirrazzaq.

4- Sunanu Sa'eed bn Mansur.

Da makamantansu.

A cikin wadannan littatafai da ire-irensu ake samun fahimtar Salaf ga Nassoshin Alkur'ani da Hadisi da kuma bayanin Ijma'insu a kan mas'alolin Addini.

Saboda haka wannan raddi ne ga wadanda suke raya cewa; Fiqhun Salaf shi ne bin Littatafan Fiqhun Mazhabobi.

Kamar yadda yake raddi ga wadanda suka mayar da Salafiyya ita ce "Jarhi da Ta'adeeli", wanda muhallinsa shi ne littatafan tarjamar maruwaitan Hadisai.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments