Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhawara Da Ake Yi Game Da Daidaitar Zatin Allah

In an fadi abin da Allah da Manzonsa (saw) suka fada, cewa: "Allah yana sama, ya daukaka a saman Al-arshinsa", sai 'Yan Bidi'a su ce:

Subhanallahi!

Ai ya yi wa Allah guri, ya sanya makani ga Allah. Allah ba shi da guri, ba shi da makani.

Haba Malam!

To wa ya ce maka Allah ba shi da guri, ba shi da makani?!

Mu dai a iya saninmu babu inda Allah ya ce ba shi da guri da makani, haka Annabinsa (saw) bai kore masa guri da makani ba. Amma Allah da Manzon nasa (saw) sun ce: Allah yana sama, ya daukaka a saman Al-arshinsa.

To in wannan kake nufi da guri, to Allah ya tabbatar ma kansa wannan din, amma bai kira shi da guri ko makani ba.

Saboda haka wannar shubuha ce maras ma'ana.

Imam Ibnu Abdilbarr Al-Malikiy ya ce:

وأما احتجاجهم لو كان في مكان لأشبه المخلوقات لأن ما أحاطت به الأمكنة واحتوته مخلوق فشيء لا يلزم ولا معنى له لأنه عز وجل ليس كمثله شيء من خلقه ولا يقاس بشيء من بريته لا يدرك بقياس ولا يقاس بالناس لا إله إلا هو كان قبل كل شيء ثم خلق الأمكنة والسموات والأرض وما بينهما وهو الباقي بعد كل شيء وخالق كل شيء لا شريك له وقد قال المسلمون وكل ذي عقل أنه لا يعقل كائن لا في مكان منا وما ليس في مكان فهو عدم

التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (7/ 135)

"Amma kafa hujja da 'Yan Bidi'a suke yi da cewa; da a ce Allah a wani guri yake da ya yi kama da halittu, saboda duk abin da gurare suka kewaye shi kuma suka kunshe shi to shi abin halitta ne, to wannan ba dole ba ne, kuma wannar magana ba ta da wata ma'ana, saboda shi Allah babu wani abu da yake kama da shi a cikin halittarsa, kuma ba a auna shi da wani abu na halittunsa, shi ba a saninsa ta hanyar aunawa (Qiyasi da kwatance), ba a auna shi da mutane, babu abin bauta bisa cancanta sai shi kadai, ya kasance tun kafin komai, sa'annan ya halicci guraren da sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, kuma shi ne mai wanzuwa bayan komai, kuma shi ne mahaliccin komai, ba shi da abokin tarayya. Kuma Musulmai da dukkan wani mai hankali ya san cewa; hankali bai san wani abu da ya kasance ba a wani guri ba daga cikinmu, kuma duk abin da ba ya wani guri to babu shi".

Saboda haka, kokarin kore daukakar Allah a saman dukkan halittunsa da saman Al-arshinsa kokari ne na nuna cewa; babu Allah. Saboda a hankalce ba zai yuwu a ce Allah yana ko'ina ba, kamar yadda ba zai yiwu a ce Allah ba ya ko'ina ba. Allah yana sama, ya daukaka a saman Al'arshinsa saman dukkan halittunsa.

~ Dr. Aliyu Muh'd Sani

   30 July, 2018

Allah ya saukar da Alkur'ani ne a matsayin littafi mai bayani kuma shiriya ga mutane, kuma littafin da ya kunshi ilimin sanin Allah da siffofinsa da sanin girmansa da kamalarsa, da bayanin Addininsa da Shari'arsa, shi ya sa ya zama littafi ne:

 القرآن الذي هو حجة الله على عباده والذي هو خير الكلام وأصدقه وأحسنه وأفصحه وهو الذي هدى الله به عباده وجعله شفاء لما في الصدور وهدى ورحمة للمؤمنين ولم ينزل كتاب من السماء أهدى منه ولا أحسن ولا أكمل

الصواعق المرسلة في الرد على الجهمية والمعطلة (1/ 239)

"Alkur'ani wanda shi ne hujjar Allah a kan bayinsa, wanda shi ne mafi alherin magana kuma mafi gaskiyarta, kuma mafi kyaunta mafi fasaharta, kuma shi ne wanda Allah ya shiryar da bayinsa da shi, ya sanya shi waraka ga abin da ke cikin zukata, kuma shiriya da rahama ga Muminai. Allah bai saukar da littafi daga sama da ya kai shi shiriya da kyau da kamala kamarsa ba".

Shi ya sa Alkur'ani ya sanar da mu cewa:

1- Allah yana sama, ya daukaka a saman Al'arshinsa.

2- Kuma yana da fiska.

3- Yana da hanaye biyu.

4- Yana magana.

5- Yana fushi.

A Sunna kuma:

6- Allah yana da kafa.

7- Yana dariya.

Da sauran siffofin Allah na kamala, sawa'un na zati ne ko na aiki, siffofi da suka dace da girmansa, kuma ba shi da makamanci a cikinsu, kuma shi ya san kamanninsu.

Amma abin mamaki sai ga 'Yan Bidi'a suna siffanta Ahlus Sunna mabiya Salaf da cewa; su MUSHABBIHA ne, -wai- suna TASHBIHI suna siffanta Allah da siffofin mutum, don kawai suna tabbatar da siffofin da Allah ya tabattar ma kansa a cikin Alkur'ani, ko Annabinsa (saw) ya tabbatar masa a cikin Sunna. Don kawai su suna kore su, saboda sun saba ma ra'ayinsu.

Duk da cewa; su ma a tsakaninsu kowace kungiya tana kiran 'yar uwarta da sunan "Mushabbiha" din.

'Yan Falsafa da yake ba sa tabbatar da hakikanin samuwar Allah, suna kiran Mu'utazilawa da sunan "Mushabbiha", don suna tabbatar ma Allah sifar "Al-qidam".

Mu'utazilawa kuma suna kiran Asha'ira da Maturidiyya da sunan "Mushabbiha" da yake suna tabbatar da siffofi 7 ko 8.

Su kuma Asha'ira suna kiran Ahlus Sunna mabiya Salaf da sunan "Mushabbiha" saboda Salaf suna tabbatar da dukkan siffofin da Allah ya tabbatar ma kansa a Alkur'ani, ko Manzonsa ya tabbatar masa a cikin Hadisai tabbatattu.

To wasu daga cikinsu Hadisan kawai suke jefawa a bola, su yi Tawilin Alkur'ani, amma abin mamaki har sai da ya kai ga wasu daga cikinsu sun yi magana ta zindiqanci inda wani ya ce:

الأخذ بظواهر الكتاب والسنة من أصول الكفر

حاشية الصاوي على تفسير الجلالين (3/ 9)

"Riko da zahirin Alkur'ani da Sunna yana cikin ginshikan kafirci".

Haka wani ma ya ce:

إن أصول الكفر ستة... التمسك في أصول العقائد بمجرد ظواهر الكتاب والسنة من غير عَرْضٍ على البراهين العقلية والقواطع الشرعية

حاشيه الدسوقي على أم البراهين (ص: 252)

"Lallai ginshikan kafirci guda shida ne... (na shida) riko da zahirin Alkur'ani da Sunna a Babin Aqeeda ba tare da auna su a kan hankali -wai- da dalilan Shari'a ba".

Don haka ka ga su wadannan hatta Alkur'anin ma kafirci yake koyarwa a ganinsu. Ba don komai suka fadi haka ba sai don su ba za su iya bin Alkur'anin ba, hankula da ra'ayoyinsu kawai za su bi, don haka duk abin da ya saba ma hankulansu a cikin Alkur'ani kafirci ne.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments