Ticker

6/recent/ticker-posts

Hakuri A Kan Da'a Ma Allah Shi Ya Fi Falala Da Soyuwa Ga Allah Fiye Da Hakuri A Kan Masifa Da Bala'i

Hakuri shi ne ka hana ranka yin abin da take so da ya saba ma abin da Allah yake so.

Hakuri ya kasu kashi biyu:

1- Hakuri a kan da'a ma Allah.

2- Hakuri a kan kaddarar Allah.

Kowannensu ya kasu kashi biyu:

Hakuri a kan da'a ma Allah ya kasu zuwa:

1- Hakuri a kan bin umurnin Allah.

2- Hakuri a kan nisantar sabon Allah.

Hakuri a kan kaddarar Allah ya kasu zuwa:

1- Hakuri a kan masifa da bala'i kai tsaye daga Allah.

2- Hakuri a kan cutarwa daga mutane.

A duka wadannan halaye ana so bawa ya yi hakuri, ya danne zuciyarsa ya bi abin da Allah yake so a cikin kowane hali da ya samu kansa a ciki, kar ya bi abin da ransa yake so matukar ya saba ma abin da mahaliccinsa yake so.

Amma kuma duk da haka hakuri na kashi na farko ya fi falala da girma a wajen Allah, wato hakuri a kan da'a ma Allah.

Hakuri a kan nisanar sabon Allah ya fi falala fiye da hakuri a kan masifa da bala'i da zai samu mutum, sawa'un a kan kansa ne ko kan dukiyarsa ko wani abu nasa.

Wannan ya sa hakurin da Annabi Yusuf (as) ya yi a kan nisantar aikata alfasha da matar Sarkin Misra ya fi falala fiye da hakuri da ya yi a kan cutarwa da 'yan uwansa suka yi masa, suka jefa shi a rijiya, aka dauke shi aka sayar da shi a can Kasar Misra a matsayin bawa. Saboda a wannan hali, babu yadda mutum zai yi dole sai hakurin.

Amma hakurin da ya yi a kan aikata alfashafa kuwa, wannan hakuri ne na jin tsoron Allah da jin kunyarsa, da yakar zuciya, saboda da ya ga dama da ya bi son ransa ya biya sha'awar farjinsa. Musamman saboda dukkan abubuwa da za su taimaka masa ya yi alfashan sun gama haduwa:

1- Shi matashi ne yana tsakiyar kaifin sha'awar saduwa da mace.

2- Kuma gauro ne, ba shi da matar da za ta biya masa wannar sha'awa.

3- Kuma bako ne a garin, bako kuwa ba ya jin kunyar aikata mummuna a garin bakunta, garin da ba a san shi ba balle ya ji kunya.

4- Kuma bawa ne, bawa ba ya jin kunya da kare mutunci kamar yadda 'Da yake kare mutuncinsa.

5- Sa'annan matar da ta neme shi kyakkyawa ce ta gaske.

6- Kuma matar sarki ce, tana da matsayi da daukaka.

7- Kuma ita ce uwar dakinsa, da umurninta yake aiki.

8- Kuma su biyu ne kawai a dakin, babu mai kallonsu cikin mutane.

9- Kuma ita ta neme shi da alfashan, kawai shi take jira.

10- Kuma tana tsananin kwadayin ya yi wannan aiki da ita.

11- Kuma har ta yi masa barazana da dauri a kurkuku da wulakantarwa in bai aikata ba.

Amma duk da haka ya ki aikata abin da take so, ya ji tsoron Allah, ya ji kunyar Allah, ya fifita lada a wajen Allah a kan jin dadin lokaci guda, sai ya gabatar da abin da masoyinsa Allah yake so a kan abin da shi yake so, ransa yake sha'awa.

Don haka ta yaya za ka hada tsakanin wannan hakurin da ya yi da wancan hakurin dole da ya yi a kan jefa shi rijiya da 'yan uwansa suka yi???

Shi ya sa Allah ya siffanta shi da cewa:

{إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُخْلَصِينَ } [يوسف: 24]

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments