FISKA TA FARKO:
Mushrikan farko suna shirka ma Allah ne a halin sauki kawai ban da halin kunci da tsanani, amma mutanen yanzu suna shirka ma Allah ne a halin sauki da halin kunci duka, a halin zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma halin wahala da tsanani da tashin hankali. In mutum zai fadi, ko ya fada rijiya, ko motarsu tana tangal – tangal za ta fadi, ko wani yanayi na wahala sai ka ji yana cewa: Shehu, Shehu, Shehu….., suna kiran wanin Allah suna yi masa shirka, amma su kuma Mushrikan farko Allah kawai suke kira a irin wannan hali.
Allah ya ce:
فإذا
ركبوا في الفلك دعوا الله مخلصين له الدين فلما نجاهم إلى البر إذا هم يشركون
"Idan Mushrikan Larabawa sun
hau jirgin ruwa (a cikin kogi), sai su kira Allah (a kan ya taimakesu), suna
masu tsarkake Addini gare shi, amma idan Allah ya tsiratar da su zuwa tudu
(doron kasa) sai su zama suna masu yi masa shirka".
Abin lura:
Wannan shi yake nuna cewa; ashe
shirkan mutanen wannan zamanin ya fi muni a kan shirkan Mushrikan farko, wanda
Al- Qur'ani ya sauka a zamaninsu.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.