Amru bn Salama al-Hamdaniy ya ce:
((Mun kasance muna zama a kofar gidan Abdullahi bn Mas'ud (ra) kafin Sallar Asubah, idan ya fito sai mu tafi Masallaci tare da shi. Sai Abu Musa al-Ash'ariy (ra) ya zo ya same mu, sai ya ce: "Shin Abu Abdirrahman ya fito?"
Sai muka ce: A'a, bai fito ba
tukun.
Sai ya zauna tare da mu, har sai
da ya fito. Yayin da ya fito gaba dayanmu sai muka tashi muka tafi wajensa. Sai
Abu Musa (ra) ya ce masa:
"Ya Baban Abdirrahman,
lallai dazu na ga wani abu a Masallaci wanda ban san shi ba, amma - Alhamdu
lillah - ban ga komai ba sai alheri".
Sai ya ce: "Miye shi?".
Sai ya ce: "Idan muna raye
wata rana za ka gani". Sai ya ce:
"Na ga wasu mutane a
Masallaci suna zaune sun yi da'ira, suna jiran Sallah. A kowace da'ira akwai
mutum daya a tsakiya, suna rike da tsakuwa a hanayensu, sai ya ce musu: ku yi
kabbara 100, sai su yi, sai ya ce: Ku yi Hailala 100, sai su yi. Sai ya ce: Ku
yi Tasbihi 100, sai su yi".
Sai Ibnu Mas'ud ya ce: "To
me ka ce musu?".
Sai ya ce: "Ban ce musu
komai ba, ina jiran ra'ayinka da umurninka".
Sai ya ce: "Ba za ka umurce
su su kirga munanan aiyukansu ba? Na lamunce musu kyawawan aiyukansu ba za su
bata ba".
Sa'annan sai ya wuce muka tafi,
har sai da ya je da'ira daya daga cikin wadannan halkoki sai ya tsaya a kansu,
sai ya ce:
"Menene wannan abin da na ga
kuna yi?".
Sai suka ce: ya kai Baban
Abdirrahman, tsakuwa ne muke kirga kabbarori da Hailala da Tasbihi.
Sai ya ce: "Ku kirga munanan
aiyukanku, na lamunce muku babu wani abu na kyawawan aiyukanku da zai bata.
Kaiconku ya ku al'ummar Annabi,
Na yi mamakin saurin halakarku! Wadannan Sahabban Annabinku ne (saw) suna nan a
cike, ga nan tufafinsa ba su rube ba, ga nan kwaryayen da yake amfani da su ba
a fasa ba. Na rantse da wanda raina yake hanunsa, lallai imma kuna kan hanya
wacce ta fi hanyar Annabi (saw) shiriya, ko kuma ku masu bude kofar bata
ne!".
Sai suka ce: Ya Baban
Abdirrahman, Wallahi ba mu nufi komai ba sai alheri!
Sai ya ce: "To mutum nawa
suke nufin alheri amma ba za su dace da shi ba?!".
Lallai Manzon Allah (saw) ya ba
mu labari:
((Lallai wasu mutane suna karanta
Alkur'ani amma ba ya wuce makoshinsu)). Na rantse da Allah, ban sani ba la'alla
mafi yawansu daga cikinku suke)).
Sa'annan ya juya ya tafi.
Amru bn Salama ya ce: Mun ga da
yawan wadancan halkoki suna sukarmu da masu a ranar yakin Nahrawan, suna tare
da Khawarijawa)).
Duba:
سنن الدارمي
(1/ 286 - 287)
A yau idan ka samu 'Yan Maulidi
ka ce: Me kuke yi?
Sai su ce: Babu abin da muke yi a
cikin Maulidi face Karatun Alkur'ani, da Zikiri, da Salatin Annabi (saw), da
Karanta Tarihinsa, da rera wakokin yabon Manzon Allah (saw), don nuna soyayya
ga Annabi (saw) da murnan zagayowar ranar haifuwarsa.
Sai ka ba su amsa da maganar Ibnu
Mas'ud (ra) inda ya ce:
"Lallai imma kuna kan hanya
wacce ta fi hanyar Annabi (saw) shiriya ko kuma ku masu bude kofar bata
ne!".
Idan suka ce: Wallahi mu ba mu
nufi komai ba sai alheri!
Sai ka fada musu maganar Ibnu
Mas'ud (ra) ya ce: "To mutum nawa suke nufin alheri amma ba za su dace da
shi ba?!".
Bidi'a shu'uma ce, aikin Ibada,
bisa kyakkyawar niyya, amma saboda ba ta cikin Shari'ar da Annabi (saw) ya zo
da ita sai ta zama sharri a maimakon alheri.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.