Akwai batattu da yawa masu kyakkyawar manufa, wadanda suka bata a dalilin mummunar fahimta ga Addini da Guluwwi a cikinsa, har suka kauce hanya, suka saba Shari'a, suka afka cikin barna, alhali ba tare da mummunan nufin saba ma Shari'ar ba.
Khawarijawan farko, sun yi nufin
su bi Alkur'ani ne, su yi aiki da Shari'arsa, har suka ce: Dole a kadaita Allah
wajen hukunci "Hakimiyya", amma da yake suna da Guluwwi a Addini, da
mummunar fahimta game da Addinin sai suka bata, suka saba ma Shari'a, suka dace
da wa'eedin da Annabi (saw) ya yi a kansu, duk da cewa: suna zaton Allah suke
bi, Addini suke yi, aikin Allah suke yi, gaskiya suke bi, kyakkyawan aiki suke
yi. Shi ya sa Sayyidina Aliyu (ra) yake fadi a kansu, da aka tambaye shi kamar haka:
((عن أبي
الطفيل عامر بن واثلة قال: سمعت عليا رضي الله عنه، قام فقال سلوني قبل أن تفقدوني،
ولن تسألوا بعدي مثلي، فقام ابن الكواء فقال: من الذين بدلوا نعمة الله كفرا وأحلوا
قومهم دار البوار؟ قال: منافقوا قريش قال: فمن الذين ضل سعيهم في الحياة الدنيا وهم
يحسبون أنهم يحسنون صنعا؟ قال: منهم أهل حروراء)).
المستدرك
على الصحيحين للحاكم (2/ 383) جامع البيان ط هجر (15/ 426 - 427)
((Abu al-Dufail (ra) ya ce: Na ji
Aliyu (ra) ya tashi yana cewa: "Ku tambaye ni kafin ku rasa ni (mutuwa), a
bayana ba za ku samu wanda za ku tambaya kamata ba".
Sai Ibnu Kawwa'u ya tashi ya ce:
Su wanene wadanda suka canza ni'imar Allah da kafirci, suka janyo wa mutanensu
shiga gidan halaka?
Sai Aliyu (ra) ya ce:
"Munafukan Quraishawa".
Sai ya ce: Su waye wadanda
aikinsu ya bace a rayuwar Duniya, alhali suna zaton suna kyautata aiki ne?
Sai Aliyu (ra) ya ce: "A
cikinsu akwai mutanen Haraura'u (Khawarijawa)")).
Saboda haka a kullum, a kowane
zamani, ana samun irin wadannan mutane, saboda mummunar fahimta ga Addini, da
Guluwwi a cikinsa, sai su zo da barna a cikin Addini, su zo da ra'ayoyi da suke
kai wa ga kafirta al'ummar Musulmi da zubar da jinanensu, amma duk da haka su
suna zaton kyakkyawan aiki suka yi. Ma'ana; ba da mummunar manufa suka yi hakan
ba. Wannan shi ne irin abin da al-Maududiy da Sayyid Qutub suka yi a wannan
zamani. Kafirta al'umma da suka yi, bisa "Hakimiyya", bisa fassara
Addini a ma'ana ta Siyasa, irin yadda Khawarijawan farko suka yi, shi ya shiga
tunanin Kungiyoyin Gwagwarmayan zamani, har daga karshe suka zo suna kashe
Musulmai, suna barin Kafirai da sunan Jihadi.
Dr. Muh'd Imarah, yana magana a
kan al-Maududiy sai ya ce:
((ولقد
يدهش كثيرون – من أنصار المودودي وخصومه – إذا علموا أن الرجل قد ذهب إلى أن
"تيار الجاهلية الجارف" قد وجد سبيله ثانية إلى النظام الإسلامي منذ عهد
الخليفة الراشد عثمان بن عفان! وأن النظام الإسلامي – في الحكم والسلطة – "قد
قام على قواعد الجاهلية بدلا من قواعد الإسلام" منذ الانقلاب الأموي على الخلافة
الراشدة!...
قد يدهش
الكثيرون لهذا التقييم الذي بلبلت نصوصه جماعات إسلامية معاصرة، وقادت كتّابا إسلاميين
إلى الحكم بكفر الأمة وجاهلية المجتمعات الإسلامية منذ قرون وقرون))
قال في
الحاشية: ((سيد قطب: معالم في الطريق (ص: 8، 39، 101، 103، 173) طبعة القاهرة سنة
(1980))
أبو الأعلى
المودودي والصحوة الإسلامية (ص: 67)
((Hakika mutane da yawa – cikin
mabiya Maududiy da abokan husumarsa – idan suka san da cewa; mutumin yana da
ra'ayin cewa; "ambaliyar Jahiliyya da ta kwashe al'umma gaba dayanta"
ta samo hanyar shigowa cikin al'umma ne a karo na biyu, zuwa ga tsarin Muslunci
tun lokacin Khalifa Usman bn Affan (ra). Kuma tsarin Muslunci - a Mulki da
shugabanci - "ya tsayu ne a kan ginshikan Jahiliyya a maimakon Ginshikan
Muslunci", tun daga lokacin da Banu Umayya suka yi juyin Mulki wa
Khalifanci na shiriya…
Hakika mutane masu yawa za su
rude game da wannan hukunci da Maududiy ya yi, wanda maganganunsa suka janyo
bala'i da rudani a cikin Kungiyoyin Gwagwarmayan Muslunci na zamani, kuma suka
ja marubuta Musulmai zuwa ga yin HUKUNCI DA KAFIRCI GA AL'UMMA, DA HUKUNCI DA
JAHILIYYA GA AL'UMOMIN MUSULMAI TUN KARNONIN BAYA CAN)).
A can kasa (hashiya) sai Dr.
Imarah ya ambaci littafin Sayyid Qutub "معالم
في الطريق" da shafuka na misalan irin maganganun kafirta al'umma da
suke cikin littafin.
A nan sai ya nuna irin fitinar da
Fikirorin Maududiy suka haifar a cikin Kungiyoyin Gwagwarmaya, da kuma yadda
suka yi tasiri a kan Marubuta, har ya yi ishara zuwa ga Littafin Sayyid Qutub
"معالم في الطريق" (Milestones), a
matsayin misali na irin wannan tasiri.
Abin nufi shi ne irin su Maududiy
da Sayyid Qutub, da kyakkyawar manufa, bisa mummunar fahimta suka haifar ma
al'umma babban sharri mai girma, suka gadar mata ta'addanci da kashe Musulmai
ba bisa hakki ba.
Kuma a hakan ake samun wadanda
suke ruduwa, kyakkyawar manufar wadannan mutane take rufe musu ido, ba sa iya
kallon mummunan sharri da suka haifar ma al'ummar Musulmi, don a yi maganin
matsalar.
Saboda haka kyakyawar manufar
mutum ba za ta taba gyara wani mummunan aikinsa ba. Ibnu Mas'ud (ra) ya ce:
«وكم من
مريد للخير لن يصيبه»
سنن الدارمي
(1/ 287)
((Mutum nawa ne masu nufin alheri
amma ba su dace da alherin ba?)).
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.