Kalmomin mene, wane, wacce, wanne, da waɗanne suna daga cikin kalmomin tambaya a Hausa. Wani lokaci akan kira su da suna “tambayau.” Ana amfani da su wajen yin tambaya ko neman bayani game da wani ko wani abu ko wani zaɓi.
mene – what
wane – which (namiji, tilo)
wacce – which (mace, tilo)
wanne – which (gama-gari)
waɗanne – which (jam’i)
A rubutu, ana rubuta kowannensu a haɗe, ba a rabe ba. Rubuta su a rabe kuskure ne.
A wannan bidiyo, an yi bayanin yadda ake amfani da kalmomin tare da misalai a cikin jumloli.
English Version
The words mene, wane, wacce, wanne, and waɗanne are question words in Hausa. They are used to ask about things, people, or choices.
mene – what
wane – which (masculine singular)
wacce – which (feminine singular)
wanne – which (general/singular)
waɗanne – which (plural)
Each of them should be written as one word, not separated. Writing them apart is incorrect.
In this video, we explain their correct usage with examples in sentences.
Ƙa'idojin Rubutun Hausa (Kashi Na
Ashirin Da Ɗaya): Kalmomin Tambaya Tambayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.