Ticker

6/recent/ticker-posts

Muzambilu Ga Sako

(1) Ya ka Muzambilu ga saƙo,
Zo ka iyar saƙon ɗan ƙis.

(2) Na ji su na turo saƙo,
Su na jaje wai na yi laƙwas.

(3) Ce su ina nan da lafiya,
Alhamdullahi ina nan ras.

(4) Tarwai nake gani dimirmir gau,
Tafiyata ma tinƙis-tinƙis.

(5) Shi lamari ko da lafiya,
Akwai ƙudurar Allah mai ƙas.

(6) Kace masu komai iko ne,
A haƙƙin Allah zaka khalas.

(7) Idan ya so ni da in shirya,
Na yo shi'ira ba wani cikas.

(8) Akwai tarin ɗangwaye him,
Da ke rugugi kaina cunkus.

(9) Su na buzaci da fusata,
Da tamɓele sun yo mankas.

(10) Da tsirin tsere tsarin tsari,
Tsururutar su tsiro reras.

(11) Su na fasa kansu suna rugi,
Sa-toka-sa-katsin kaciɓis.

(12) Cane su sani mun ɗau aniya,
Fa bamu bari har mui warwas.

(13) Da farko tun a zanin gunya,
Izuwa ga lifafi babu ribas.

(14) Fa babu gudu kuma ba yakwaci,
Ba ƙonƙona ma raina fes.

(15) Fa za na luguiguito lugga,
Lagonta na yo lugudansa lilis.

(16) Na lallauya ta cikin layi,
In lelaye kanta lumi da lalas.

(17) Fa koyaushe na saɓo ta tazo,
Ba ƙemagadede babu ribas.

(18) Ɗauki Muhammadu ga saƙo,
A gare su ka miƙa can takanas.

(19) Kace su su yo haƙuri fa kaso-
Awalaja ne wannan (adibas).

(20) Su bini da bashi sui haƙuri,
Wataran zan daina in je ƙas.

(21) Domin tuni Imru'u yayi gaba,
Su Zuhairu Farasdaƙu sun je ƙas.

(22) Hassanu da Ka'abu fa sun shuɗe,
Alfazazi Mutanabbi ƙas.

(23) Malam Mudinmu Sipikin ma,
Aliyu Aƙilu fa na can ƙas.

(24) Mu'azu Hadejiya ya kwanta,
Da Alu ƊanSidi maso mai Fas.

(25) Haka nan wataran nima bani,
Don zana gushe ku sani tilas.

(26) Kui min adu'a Allahu ya ban,
Na ringa ɗiga muku ko da ɗis.

USMAN NAGADO (II)
22 ga Afrilu, 2024.

Muzambilu

Post a Comment

0 Comments