Ticker

6/recent/ticker-posts

A Yau Mun Fi Bukatar Dabi'un Ilimi Fiye Da Komai

Daga cikin ginshikan Ilimin Shari'a akwai siffantuwa da halaye da dabi'un Ilimi, da kiyaye su a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.

Malamai sun kasance suna bayanin dabi'un Ilimi a lokacin da suke bayanin hakkokinsa da wajibansa da hanyar nemansa. Amma a yau idan ka duba dabi'u da halayen ma'abota ilimi cikin Malamai da Dalibai za ka ga da yawa sun rasa dabi'un ilimi, alhali wadannan dabi'u suna cikin manyan wajiban Shari'a.

Dabi'un da yawa daga cikin Malamai da Daliban ilimi ba dabi'un ilimi ba ne, dabi'u ne irin na jahilci, wadanda ya wajaba gama gari cikin mutane su nisance su balle kuma ma'abota ilimi.

Kar fa mu manta, hakikanin ilimin Shari'a shi ne tsoron Allah. Kamar yadda Allah ya nuna mana cewa; masu tsoron Allah su ne masu ilimi.

Malamai magada Annabawa ne, don haka dabi'un Annabawa su ne dabi'un Malamai, musamman Annabinmu Muhammad (saw). Shi kuma dabi'unsa gaba daya Alkur'ani ne.

Don haka wajibi ne ma'abota ilimin Shari'a su siffantu da dabi'un ilimi:

1- Ikhlasi: wato yi don Allah da neman yardarsa,   a lokacin neman ilimin, da lokacin kararantar da shi. Da nisantar neman ilimin don wani abu na Duniya, sawa'un neman yabo ko suna da daukaka a wajen mutane, ko samun wata dukiya ko matsayi da mulki.

2- Taqwa: wato jin tsoron Allah da kiyaye iyakokin Shari'a.

3- Tawali'u ma Allah, da tawali'u wa bayin Allah da nisantar girman kai wa mutane.

4- Tsantseni: ta hanyar nisantar duk wata shubuha a mas'alolin ilimi da kuma shubuhohi a rayuwa, wadanda suke tsakanin halal da haram, da nisantar duk abin da zai kai ga shiga hakkin mutane.

5- Gaskiya: fadin gaskiya cikin zance yana daga cikin manyan halayen Muminai, kamar yadda karya take cikin manyan halayen Munafukai.

6- Rikon amana: musamman a dukiyoyin mutane da hakkokinsu, sifa ce ta Mumina, cin amana kuma sifa ce ta Munafukai.

7- Hakuri: yana daga cikin manyan siffofin Annabawan Allah, an cutar da su musamman a halin suna da'awa, amma sai suka yi hakuri, sai Allah ya kara musu daraja da daukaka. Wannan ya sa hakuri a kan wautar wawaye a halin da'awa, da kuma cutarwarsu a halin rayuwa babban wajibi ne a Shari'a.

Da sauran halayen Annabi (saw).

Allah ya azurta mu da siffantuwa da halaye da dabi'un ilimi.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments