Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhawarar Malamai Da Masana Tarihi Dangane Da Asalin Kasar Hausa

Kasar Hausa, wadda aka fi sani da Kasar Hausa a Harshenmu, wani yanki ne na tarihi a yammacin Afirka da Hausawa ke zaune tun tsawon ƙarnuka. Yankin ya haɗa da arewacin Najeriya da kudancin Nijar. Hausawa na daga cikin manyan kabilu a Afirka, masu ɗimbin tarihi na kasuwanci, shugabanci, ƙere-ƙere, da ilimi. Mafi yawan Hausawa musulmai ne da suke musulunci tun sama da shekara dubu, a cikin Hausawa kuma Akwai mabiya addinin kiristanci da mabiya addinin gargajiya wanda su ke yi tun kafin zuwan Addinan Ibrinayanci (Judaism, kiristanci da  musulunci).

Kasar Hausa

Asalin Hausawa ya kasance batun muhawara a tsakanin masana tarihi. Wasu masana sun yi imanin cewa Hausawa sun fito ne daga yankunan Habasha, Nubiya, da Masar ta Dauri (Ancient Egypt) bayan ƙaruwar hamada, suka matsa zuwa kudu don kafa sababbin garuruwa. Wani ra’ayi kuma yana danganta Hausawa da gaɓar yammacin tafkin Chadi, inda sauyin yanayi ya tilasta musu bazuwa zuwa yamma, wanda hakan ya haifar da kafuwar Kasar Hausa. Shaidu na binciken tarihi, musamman wani jirgin ruwa na Dufuna  da aka gano a Jihar Yobe, wanda aka kiyasta yana da sama da shekaru 8000, na tallafawa wannan ra’ayi na cewa Hausawa sun yi kaura daga inda su ke ta amfani da wannan jirgi kasancewar a zamanin Ruwa ya fi yawa a duniya.

Wani ra’ayi kuma na cewa Hausawa ’yan asalin yankin ƙasar Hausa ne tun bayan saukar jirgin Annabi Nuhu (AS), a nan su ke zaune inda ba su da wani labarin ƙaura daga Wani waje. Labarun baka ma ya nuna cewa wasu kabilu na Afirka, ciki har da ’yan tsohuwar Masar, su ne suka fita daga Kasar Hausa, ba wai Hausawa ne  suka shigo ba. Binciken Sule Garba, wani masanin kimiyyar Masar daga Nijar ya ƙara ƙarfafa masu wannan tunani, inda masanin ya gabatar da hujjoji masu ƙarfi game da dangantakar tarihi tsakanin Hausawa da tsohuwar Masar. Shaidarsa ta haɗa da tsohuwar Dala (Pyramid ) na ɗan baƙi da ke Damagaram, Nijar, wanda ya fi na tsohuwar Masar tsufa.

Tarihin Hausawa da wayewar su na daga cikin daɗaɗɗu a yammacin Afirka tun  (kimanin 1000 K.H. – 300 M.), wanda ya sanya su cikin ƙabilu mafi tsoffin wayewa Afirka ta yamma da Afrika baki ɗaya tare da al’ummar Nok da ta shahara wajen sarrafa ƙarfe da fasahar tukwane. 

Daura ta kasance cibiyar farko da ke da tsarin mulkin Hausawa, inda sarautar mata ta mamaye ƙasar tsawon ƙarnuka ma su yawa  har zuwa ƙarni na 9.  Kabarai ko Magajiya kamar  sarauniya Kufuru, Ginu, Wanzamu, Yanbamu, Daurama I, Fatatuma, Ja_mata, Ha_mata,Sai-Da-Mata, Daurama II da sauran su, sun shugabanci Kasar Hausa na Tsawon lokaci cikin hikima da Tsari kafin a samu sauyi. Tsarin mulkin ya  zuwa tsarin sarauta ta maza, inda zuriyar Daurama II ta ci gaba da mulki a manyan biranen ƙasar Hausa har zuwa ƙarni na 19th.

A ƙarni na 11, biranen Hausa sun bunƙasa zuwa manyan cibiyoyin kasuwanci da al’adu. Kowanne birni yana da Sarki, tare da Galadima da majalisar dattijai masu ba da shawara. Tsarin zamantakewa ya kasu gida-gida; akwai sarakuna, malamai, ’yan kasuwa, masu sana’a, manoma, da bayi. A karkara ana yin noma da kiwo da sauran sana'o'in Hausawa irin su kira,saƙa,jima, suu (kamun kifi), Farauta, Dss amma daga baya ikon mallakar kasar noma da gini ya dawo ƙarƙashin masu mulki inda Sarki ke kula da harkokin siya da siyar da ƙasa. Bayi sun taka muhimmiyar rawa a harkokin noma, yaƙi, da cinikayya a wancan zamani.

Kasar Hausa ta zama cibiyar kasuwanci a yankin Afrika, wadda ta haɗa Yammacin Afirka, Arewacin Afrika da Gabas ta Tsakiya. Hausawa sun kan yi  cinikayya ta zinariya, fata, gishiri, kayan rini, kayan ƙarfe, bayi, kayan ado, goro, da kayan abinci. Kano da Rano sun shahara da masana’antun saƙa da Rini , Katsina da Daura sun ƙware a harkar fatauci, yayin da Zariya ta bunƙasa wajen noma da kasuwancin bayi. Gobir da Haɗeja sun fi kowa ƙarfin soja da iya kare ƙasar Hausa. Sana’o’in Hausawa, musamman Jima, kere-kere kamar zoben azurfa, da zane-zanen kaya kala kala wato rini, sun shahara har zuwa Turai da Gabas ta Tsakiya.

Gine-ginen Hausa sun nuna kwarewar Su da al’adu da kuma kula da  bukatar tsaro. Garuruwa an zagaye su da katanga (Ganuwa/Badala) saboda yawan yaƙe-yaƙe a wancan loto. Gidaje ana yi da tubalin laka, ana kawata su da zane-zane masu ban sha’awa, kuma ana rufewa da rufi na musamman da suka zama alamar Hausawa har yau.

Addinin Musulunci ya shigo Kasar Hausa ta hanyar cinikayya a ƙarni na 11, ta hannun ’yan kasuwa Larabawa da malamai Wangara daga Mali. Masu mulki da mutanen birane sun rungumi Musulunci tun da wuri, yayin da karkara suka ɗauki lokaci kafin su ma suka karɓa. Bayan jihadin Sultan Ali Yaji Ɗan Tsamiya, Musulunci ya zama addinin masarautar sa. A Katsina kuma, Sarki Muhammadu Korau ya yi irin wannan sauyi. Daga cikin gine-ginen tarihi da ke nuna jimawar Musulunci a cikin Hausawa sun haɗa da Hasumiyar  Gobarau a Katsina yana daga cikin tsofaffin gine-gine da suke a Najeriya kuma bene na farko a tarihin ƙasar, an gina shi a ƙarni na 15. Haka kuma, Sarki Muhammadu Rumfa na Kano ya gina Babban Masallacin Kano da fadar sarkin kano a ƙarni na 15.

Kano ta zama shugabar Kasar Hausa a ƙarni na 15 musamman a zamanin Muhammadu Rumfa, inda ta girmama gami da tunɓatsa wajen kasuwanci, ilimi, da shari’ar Musulunci, inda take  gogayya da Katsina. Duk da haka, rikice-rikicen siyasa na cikin gida da ’yancin gashin kai ga kowacce Masarauta sun hana Hausawa haɗuwa a ƙarƙashin sarki ɗaya. Wannan rashin haɗin kai ya sa Kasar Hausa ta zama ta samu  rauni, fiye da sauran Dauloli dake kewaye da ita, hakan kuma ya ba Fulani damar  suka karɓe masarautun ta hanyar  jihadin 1804, wanda ya sauya tsarin mulkin masarautun suka zama mallakar Fulani karkashin Daular Sakkwato.

A yau, ina kira ga Hausawa da su hade kansu domin cimma abin da kakanninsu ba su iya cimma ba – haɗin kai da zama ɗaya. Ta hanyar haɗin kai, Hausawa za su iya cimma duk abin da suka sa a gaba.

Kasar Hausa na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin cibiyoyin ilimi, kasuwanci, da shugabanci mafi dadewa a Afirka. Duk da mulkin baƙi, jihadin Fulani, da mulkin mallaka na Turawa, Hausawa sun cigaba da tsare harshe, al’ada, da addininsu, suna ci gaba da zama masu tasiri har zuwa yau.

Post a Comment

0 Comments