Ticker

6/recent/ticker-posts

Sukar Hadisan Annabi (SAW) A Jiya Da Yau

Ba yau aka fara samun masu sukar Hadisan Annabi (saw) ba, a'a, tun zamanin magabata an samu masu yakar Hadisan Annabi (saw) bisa manufofi daban-daban, ta bangaren Munafukai masu yakar Muslunci, haka kuma ta bangaren wasu Musulmai gafalallu da aka yaudara da sunan ba da kariya ga Sunna, da sunan ware Hadisan da suka saba hankali ko suka saba waqi'i ko suka saba Alkur'ani, da sauran munanan manufofi da aka yi musu ado da kyawawan sunaye.

Don haka aka samu masu yakar Sunnar ta hanyar jefa shakku a zakutan Musulmai game da Hadisan Annabi, da kira ga riko da Alkur'ani kadai ban da Sunna.

Da kuma masu sukar maruwaitan Hadisan -har Sahabbai- da sukar hanyar da aka ruwaito su.

Da masu gindaya wasu sharuda da ba su da asali, kamar cewa; ba a daukar Aqida daga Hadisi "Ahaad" saboda zato ne, ko ba a kafa hujja da Hadisi in ya saba hankali, ko ya saba Alkur'ani, d.s.

Tun zamanin Sahabbai aka samu irin wadannan mutane, shi ya sa a lokacin da wani ya zo wajen Sahabin Annabi (saw) Imrana bn Huswain (ra) ya ce masa:

"Ya kai Baban Nujaid, kuna karantar da mu wasu Hadisan da ba su da asali a cikin Alkur'ani. Sai Imran ya fusata ya ce masa:

{Shin ka karanta Alkur'ani?} Sai ya ce: Eh.

{Shin a cikin Alkur'ani ka ga inda aka ce Sallar Isha'i raka'a hudu ce, Magriba uku, Asubah biyu, Azahar da La'asar hudu?}. Sai ya ce: A'ah.

Sai ya ce: {To a wajen wa kuka samu hakan, shin ba daga gare mu kuka samu ba, mu kuma mun samo daga Annabi (saw)?".

To kun ga kenan, idan ka ce za ka jefar da wani Hadisi da ya tabbata daga Annabi (saw) to sai ka watsar da Sallolin da kake yi, saboda babu bayanin adadin raka'o'insu a Alkur'ani Mai girma.

Haka aka samu wani mutum ya ce wa Mudarrif bn Abdillah: Kar ku karanta mana komai sai abin da ke cikin Alkur'ani kadai. Sai Mudarrif ya ce masa:

{Mu ma ba ma bukatar canjin Alkur'ani, amma muna bukatar bayanin wanda ya fi mu sanin Alkur'anin (wato Manzon Allah)".

Haka nan aka yi ta samun masu inkarin Hadisan Manzon Allah (saw), da sunan bin Alkur'ani, ko da sunan ya saba ma hankali da sauransu. Aka samu 'Yan Jahamiyya da Mu'utazila da sauran kungiyoyi masu yakar Sunna, suka yi ta inkarin Hadisan da suka saba munanan Aqidunsu da son zuciyoyinsu.

Malaman Muslunci kuwa ba su gushe ba suna yi musu raddi suna tona musu asiri, irin su Imamu Shafi'iy cikin littafinsa "Jima'ul Ilm", da Imam Ibnu Qutaiba cikin littafinsa "Ta'awilu Mukhtalafil Hadeeth".

Haka abin ya cigaba da tafiya har ya iso wannan zamani, ta yadda ya zama duk wani Dan Bidi'a ko Mai son zuciya za ka samu yana yakar Hadisan da suka saba ma Bidi'arsa da son zuciyarsa, yana sukarsu yana karyata su, kawai don sun saba son zuciyarsa.

A takaice, bacin wannan mummunan tafarki a fili yake, saboda in har da gaske ka yi imani da Alkur'ani, to a cikinsa Allah ya yi umurni da bin Allah da bin Manzonsa (saw), alhali babu yadda za ka bi Allah sai ta hanyar bin Alkur'ani, kamar yadda babu yadda za ka bi Annabi sai ta hanyar bin Hadisansa tabbatattu.

Kuma babu tabbataccen Hadisin da yake cin karo da Alkur'ani ko lafiyayyen hankali. Matukar Hadisi ya tabbata, amma sai ka ga ya saba hankalinka, to ka tuhumi hankalin naka, hankalin naka ne ya samu tabuwa ba Hadisin ne bai tabbata ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments