Ticker

6/recent/ticker-posts

Za a Gudanar da Ranar Marubuta Hausa ta Duniya a Dutse, Jihar Jigawa

Shirye-shirye sun kankama na gudanar da Ranar Marubuta Hausa ta Duniya a wannan shekara 2025 karo na uku a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa. Taron zai gudana a ƙarƙashin taken: “Marubuta a Karni na 21: Kalubalen Tsaro da Tattalin Arziki”.

Taron na bana zai kasance wata babbar dama ga marubuta daga sassan duniya daban-daban domin tattauna rawar da adabin Hausa ke takawa wajen fuskantar manyan ƙalubale na tsaro da tattalin arziki da ke addabar ƙasashe da al’ummomi.

Kuma zai ƙarfafa haɗin guiwa tsakanin marubuta da gwamnati, da ƙungiyoyi wajen samar da mafita ga matsalolin tsaro da tattalin arziƙi. Zai bai wa marubuta, musamman matasa, damar musayar ilimi da dabaru na amfani da rubutu a matsayin makamin ci gaban ƙasa. Zai taimaka wajen ɗaukaka harshen Hausa da al’adunsa a idon duniya.

Domin tabbatar da tasirin taron, an gayyato ƙwararru daga fannoni daban-daban musamman fasahar zamani (AI), tsaro da tattalin arziki domin gabatar da bita. Wanda zai taimaka wajen samar da sabbin fahimta ga marubuta kan yadda za su yi amfani da AI wajen rubuce-rubuce da faɗakarwa.

Sannan za a wayar da kan marubuta kan tasirin tsaro da yadda za su bayar da gudummawa wajen gina zaman lafiya.

Koyar da marubuta dabarun tattalin arziki da dogaro da kai domin su zama ginshiƙan ci gaban ƙasa na daga cikin abinda taron na bana zai maida hankali.

Kamar yadda aka sani ne marubuta tun tarihi suna taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma. Misalai a Afirka ta Kudu, rubuce-rubucen marubuta sun taimaka wajen wayar da kai kan ’yanci da adalci. A Indiya, marubuta irin su Tagore sun yi tasiri wajen tabbatar da ’yancin kai. A Nijeriya kuma, marubuta a shekarun baya sun kasance muryar jama’a wajen ilmantarwa da nishadantarwa, da faɗakarwa.

Kwamitin shirya taron na kira ga gwamnati a matakai daban-daban da hukumomi da NGOs, da kamfanoni da su mara wa taron baya domin nasararsa. Nasarar taron ba wai ta marubuta kaɗai ba ce, nasara ce ta al’umma baki ɗaya.

Ranar Marubuta Hausa ta Duniya a Dutse za ta kasance tarihi wajen ƙara ɗaukaka harshen Hausa da kuma tabbatar da cewa marubuta suna daga cikin ginshiƙan magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.

Abdulrahman Aliyu Ph.D
Sakataren kwamitin shirya taron

Marubuta

Post a Comment

0 Comments