Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangane Da Muhimmancin Rubuta Darussan Hausa Da Islamic Studies a Jarabawar SSCE Da UTME - Kashi Na Biyu

Daga

Dr. Jibril Yusuf

Batun wayar da kan ɗalibai dangane da muhimmancin rubuta darussan Hausa da Islamic Studies a jarabawar SSCE abu wanda ba wai ya kamata ne kaɗai ba, a'a, ya ma zama wajibi ne duba da muhimmancin da hakan yake da shi ga ci gaban ilimin 'ya'yanmu masu tasowa.

Duk da cewa ɗaliban su ne suka fi buƙatar wayar da kai sosai don su fahimci amfani da muhimmancin waɗannan darussan a gare su, sai dai a ɗaya ɓangaren, iyayen yara ma suna buƙatar wayar da kai na musamman a kan wannan batun.

Iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen cusa wa 'ya'yansu ra'ayin abin da suke don zama a rayuwarsu. Wannan ya sa wasu iyayen sukan cusa wa 'ya'yansu ra'ayi kan fannin da suke so su karanta a jami'a, wanda hakan yana da tasiri wajen zaɓen darussan da za su fi mayar da hankali a kansu

Mafi yawa daga cikin iyayen, dukan yi amfani da tunaninsu ne kawai ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a kan harkar ilimi ba. Wanda hakan yakan haifar da kurakurai da dama a cikin zaɓin da yaran kan yi.

Dangane da batun zaɓin darasin Hausa da na addinin Musulunci (Islamic Studies) kuwa, a ganina abin kunya ne a ce Bahaushe bai zaɓi darussan guda biyu a jarabawar kammala sakandire ba. Ko bai zaɓa don yana ganin ya kamata ya zaɓa domin samun ƙarin maki ba, ya kamata ya zaɓe su don kishin kansa da addininsa.

Alal misali, idan aka dubi hotunan da suke ƙasa, za a ga cewa misali ne na yadda ƙabilun kudancin ƙasar nan suke girmama harshensu, kuma suka ɗauke shi da muhimmanci saɓanin yadda mu muke wa namu harshen riƙon sakainar kashi. Dubi yadda ɗaliba 'yar ƙabilar Ibo daga Jihar Enugu ta rubuta darasin Ibo a jarabawar NECO (a hoto na farko), ita kuwa Bahaushiya daga jihar Sokoto ta ƙi zaɓar darasin Hausa. Abin mamaki kuma shi ne, dukkansu daliban fannin kimiyya (science) ne.

Na tattauna da mutane da dama da suka bayyana cewa, bai a lokacin da suka rubuta jarabawarsu ta SSCE sun rubuta darussan Hausa da Islamic Studies ba tare da la'akari da ɓangaren da dalibi yake ba.

Don haka, ya rage namu, mu rungumi waɗannan darussan da muhimmanci domin ƙara mana samun damar samun gurbin karatu a jami'o'i, ko kuma mu ci gaba da watsi da su mu ci gaba da rasa damar shiga jami'a saboda ƙarancin makin da ake buƙata domin samun gurbi (admission).

Jibril Yusuf Dokan Lere, Ph.D.

18/9/2025

Sakamakon Jarabawar Wata Ɗaliba
Sakamakon Jarabawar Wata Ɗaliba Bahaushiya

Sakamakon Jarabawar Wata Ɗaliba
Sakamakon Jarabawar Wata Ɗaliba Igbo

Post a Comment

0 Comments