Ticker

6/recent/ticker-posts

Waye Margayi Farfesa Hafizu Miko Yakasai?

Daga

Abubakar S. Sabiu
(Sarki)

5 Satumber, 2025

Tarihinsa da Gudunmawarsa....

Farfesa Hafizu Miko Yakasai, fitaccen masanin ilimin harshe daga Jami'ar Bayero, Kano (BUK), wanda ya taka muhimmiyar rawa a fannin ilimin harsuna, musamman Hausa.

Ya fara Digiri na Farko (B.A.) a Hausa Jami'ar Bayero, Kano.

Digiri na Biyu (M.A.) a Hausa Jami'ar Bayero, Kano.

Digiri na Uku (Ph.D.) a Jami'ar Warsaw (University of Warsaw) Poland

Farfesa Yakasai ya yi aiki a Sashen Harsuna da Harsunan Waje (Linguistics and Foreign Languages) na Jami'ar Bayero, Kano. Ya rike mukamai da dama, ciki har da kasancewa shugaban farko na Kwalejin Harsuna da Al'adu (College of Humanities) da aka kafa a jami'ar.

Gudunmawarasa a Fagen Harshe...

Margayi Farfesa Yakasai ya wallafa maƙaloli da litattafai da dama a fannin ilimin harshe, kamar haka:

Mechanisms of Adjustment in English–Hausa Translation: A Case Study of Semantic and Structural Adjustments” (1990) – B.A. Dissertation.

Figurative Language in English–Hausa Translation: A Communicative Approach” (1994) – M.A. Dissertation.

Ga wasu daga cikin muhimman litattafan da Farfesa Hafizu Miko Yakasai ya wallafa ko ya taka rawa wajen shirya su, waɗanda suka shafi fannin ilimin harshe, musamman Hausa.

Figurative Language in English–Hausa Translation: A Communicative Approach (1994) 

Wannan littafi yana nazarin yadda ake fassara kalmomin misali daga Turanci zuwa Hausa ta hanyar amfani da dabarun sadarwa. Ya kasance aikin digiri na biyu (M.A.) da ya gabatar a Jami'ar Bayero, Kano.

Hausa Reduplication in the Process of Grammaticalization and Lexicalization* (2006) 

Aikin digiri na uku (Ph.D.) da ya gabatar a Jami'ar Warsaw, wanda ya mayar da hankali kan yadda ake maimaita kalmomi a Hausa wajen ƙirƙirar sabbin ma'anoni da tsarin nahawu.

Incantation in Hausa Culture: An Example of Syntactic Reduplication* (2010) 

Wannan bincike ya bayyana yadda ake amfani da maimaita jimloli a cikin addu'o'i da tsafi a al'adun Hausa, tare da nazarin tasirinsu a nahawun harshe.

📚 Litattafan da Ya Taka Rawa Wajen Shirya Su:

Language, Literature and Culture in a Multilingual Society: A Festschrift for Abubakar Rasheed (2016)

Faresa Ya kasai ya rasu a ranar 4 ga watan Satumber, 2025, a asibitin koyarwa Aminu Kano. An kuma binne shi  a ranar Juma'a 5 ga watan Satumba, 2025.

Tuni Malamai da ɗalibai daga sassa daban-daban na cike da wajen Kano suka fara miƙa saƙon ta'aziyyarsa a shafukan sada zumunta.

Tuni wasu daga cikin ɗalibansa suka fara nuna alhinin rasuwarsu, inda suke bayyana shi a matsayin malami abun koyi da haƙuri.

Dr. Yusuf Ahmad Gwarzo Malami a Jami'ar North West da ke Kano,  ɗaya ne daga cikin ɗaliban margayin, ya bayyana shi a matsayin wanda ya ɗauke shi darasi a lokacin da yake Degree ɗinsa na farko a tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2010. Gwarzo ya kara da cewar ''Yakasai shi ne wanda ya duba ni a lokacin yake Degree  na Uku (Phd) a Jamilar Bayero. Ya suffanta margayin da abin koyinsa da kuma lakcarsa ba karatu kaɗai take koyarwa ba har da koyar da ladabi, in ji Gwarzo.

Shi kuwa Dr. Muhammad Sulaiman ya bayyana margayin da cewar '' malami ne mai ƙwazo a wajen aiki da nutsuwa, mai yawan murmushi da sunkuyar da kai a yayin da ake magana da shi.

Sauran wanda suka nuna alhinin su, sun haɗa da Dr. Saifullahi Dahiriu da Jibril Yusuf Dokan Lere da kuma Kabir Garba Ingawa.

Muna roƙon Allah Ya gafartawa Yakasai ya kyautata makwancinsa amin.

Farfesa Hafizu Miko Yakasai

Post a Comment

0 Comments