Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka'idojin Rubutun Hausa: Darasi Na Shida

👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏

💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍

https://www.youtube.com/@AmsoshiTV

Dokokin mallaka iri biyu ne a rubutun Hausa. Akwai gajeruwar mallaka, akwai kuma doguwar mallaka. Gajeruwar mallaka ita ce wadda ake kawo sunan abin da aka mallaka, sai kuma a kawo kalmar da take fayyace wanda ya mallaki abin ko wadda ta mallaka ko waɗanda suka mallaka. Misali “rigarsa”. A nan an kawo suna (riga) da mafayyaciya ko wakilin sunan wanda ya mallaki rigar (sa).

A doguwar mallaka kuwa, ana yin ƙarin “na” ga jinsin namiji sannan a yi ƙarin “ta” ga jinsin mace yayin kawo mafayyaciya ko wakilin sunan wanda ya yi mallaka. Misali, “rigar tasa”. A nan, an kawo sunan abin da aka mallaka “riga” sannan aka kawo “ta” haɗe da wakilin sunan wanda ya yi mallaka “sa”. “Ta” ta zo ne kasancewar “riga” jinsin mace ce. Idan abin da aka mallaka jinsin namiji ne, ana amfani da “na”. Misali, “gidan nasa”.

A wannan darasi, an kawo bayanai game da “doguwar mallaka” tare da misalai a cikin jumloli.

Hausa Orthography Rules: Long Possession

In Hausa writing, there are two types of possession: short possession and long possession.

Short possession is when the possessed item is mentioned first, followed directly by the pronoun or marker of the owner.

Example: “rigarsa (“his shirt”). Here, “riga (“shirt”) is the possessed item, and “sa (“his”) shows the owner.

Long possession involves adding “na for masculine nouns and “ta for feminine nouns before attaching the pronoun or marker of the owner.

Example: “rigar tasa (“his shirt”). Here, “riga (“shirt”) is the possessed item, and “ta is used because “riga is a feminine noun, followed by “sa (“his”).

If the possessed item is masculine, “na is used.

Example: “gidan nasa (“his house”).

In this lesson, we focus on explaining long possession with detailed examples in full sentences.

Post a Comment

0 Comments