Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka'idojin Rubutun Hausa (Darashi Na Biyar): Kalmomin Dirka

👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏

💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍

https://www.youtube.com/@AmsoshiTV

Ƙa’idojin Rubutun Hausa: Kalmomin Dirka

Kalmomin dirka guda biyu ne a Hausa. Su ne “ce” da kuma “ne”. “ce” tana nuni ne ga jinsin mace. Don haka, duk inda ta fito, to dole ne ta kasance tana nuni ga lamirin mace. Ita kuwa kalmar “ne”, tana nuni ne ga lamirin namiji. Duk inda ta fito, dole ne ta kasance tana nuni ga lamirin namiji. Yayin da aka samu jam’i, nan ma akan yi amfani da “ne”.

Kalmomin dirka sun faɗo cikin dokokin rubutun Hausa na raba rubutu. A duk inda aka ci karo da su a cikin rubutu, dole ne a rubuta su a matsayin masu cin gashin kansu. Ba a haɗe su da kowace kalma.

A wannan darasi, an kawo misalan kalmomin dirka a cikin jumla domin fahimtar yadda dokar take.

Hausa Orthography Rules: The Dirka Particles

There are two ‘dirka’ particles in Hausa: ‘ce and ‘ne.’

a. The particle ‘ce is used to mark the feminine. Wherever it appears, it must refer to a feminine subject.

b. The particle ‘ne is used to mark the masculine, and wherever it appears, it must refer to a masculine subject.

c. In the case of plurals, ‘ne is also used.

In Hausa orthography, dirka particles fall under the rules of word separation. This means that whenever they occur in writing, they must always be written as independent words, never joined to any other word.

In this lesson, we provide examples of dirka particles in full sentences to illustrate how this rule works in practice.

Post a Comment

0 Comments