Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka'idojin Rubutun Hausa - Darasi Na Hudu

👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏

💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍

https://www.youtube.com/@AmsoshiTV

Idan aka samu samu jumlar da take ɗauke da aikatau, sannan aikin da aka gudanar da a cikin jumlar ya faɗa kan wakilin suna, to wannan wakilin sunan da aikin ya faɗa wa shi ake kira “wakilin suna karɓau.” Haka kuma, ana kiran sa da suna “wakilin suna sha-wuya.” Dalili kuwa shi ne, saboda mai wannan wakilin sunan shi ne ya sha wuyan aikin da aka gudanar a cikin jumlar – domin aikin ya faɗa a kansa ne.

Misali, a jumlar “Audu ya kama akayu,” ana iya maye gurbin “akuya” da wakilin suna. Jumlar za ta koma kamar haka: “Audu ya kama ta.” A nan za a ga cewa aikin “kamawa” wanda Audu ya yi, ya faɗa ne kan “akuya.” Ke nan ita ce sha-wuya (kuma karɓau) a cikin jimlar.

Duk inda aikatau ya zo kafin kalmar wakilin suna karɓau, to a rabe ake rubuta su ba a haɗe ba. Aikatau ɗin yana iya kasancewa mai gaɓa ɗaya ko ɗaurarren aikatau ko kuma mai gaɓa biyu, da sauransu.

A wannan bidiyon, an yi ƙoƙarin yin bayani dangane da wannan ƙa’idar rubutu tare da misalai a cikin jumloli.

Verb and Object Pronoun (Wakilin Suna Karɓau / Wakilin Suna Sha-Wuya)

When a sentence contains a verb, and the action of that verb falls upon a pronoun, that pronoun is called “wakilin suna karɓau or “wakilin suna sha-wuya (object pronoun). The second name, sha-wuya (“the one who bears the burden”), comes from the fact that this pronoun is the receiver of the action in the sentence.

For example, in the sentence “Audu ya kama akuya” (“Audu caught a goat”), the word ‘akuya (“goat”) can be replaced with a pronoun. The sentence would then read: “Audu ya kama ta” (“Audu caught it”). Here, the action of catching performed by Audu falls on the goat (akuya), making it the object pronoun (karɓau / sha-wuya) in the sentence.

In Hausa orthography, whenever a verb is followed by an object pronoun, they are written separately, not joined together. This rule applies whether the verb is a single-syllable verb, a ‘ɗaurarren aikatau’ (closed-syllable verb), or a two-syllable verb, among others.

In this video, we explain this important writing rule with practical examples in full sentences.

Post a Comment

0 Comments