Daga
Dr. Jibril Yusuf
Dokan Lere
Abu ne sananne cewa ana la'akari da yawan maki ne wajen samun gurbin karatu a jami'o'i. Haka kuma fahimtar da yaro zai yi wa darasin Hausa ko Islamic Studies ya bambanta da yadda zai fahimci sauran darussa. Dalili kuwa shi ne, dangane da Hausa, duk abin da aka koya maka da harshenka sai ka fi fahimtarsa ko da ba darasin Hausa ne ba. Haka kuma Islamic Studies akwai abubuwa da dama waɗanda ko ba a makarantar boko ba za ka fahimce su domin ya shafi addini.
Idan ɗalibin da ba na Sciences ba zai rubuta
jarabawar neman gurbin karatu a jami'a, misali zai nemi fannin shari'a (law)
zai iya sanya Hausa ko Islamic a cikin darussan da zai rubuta, kuma fahimtarsa
da waɗannan darussan
guda biyu zai sa ya iya samun maki mai gwaɓi
(sakamako mai kyau). Hakan zai kara masa damar samun gurbin karatun, kasancewar
ya ci jarabawar da kyau.
Kuma ba zai ɗauki darasi ya rubuta a
jarabawar UTME ba har sai yana da shi a cikin SSCE ɗin sa.
To idan kuwa ya raina waɗannan darussan, kuma yaƙi
rubuta su a SSCE, maimakon haka ya ɗauki
waɗanda bai fahimce su
sosai ba saboda wataƙila matsalar harshe ko mu'amalar yau da kullum, sai a samu naƙasu
wajen samun sakamakon da ake buƙata.
Wannan ya sa nake ganin cewa,
inda yara 'yan sakandire musamman waɗanda
suke fannin 'arts' za su gane, da sai su riƙa rubututa waɗannan darussan a SSCE da UTME domin zai ƙara
masu yawan maki da kuma damar samun admission a jami'o'i.
Da yawa cikin darussan da za a
karanta a jami'a, musamman na fannin 'arts' wajen yin rajista a UTME sukan ce a
zaɓi darasin Ingilishi
da wasu darussa uku na fannin 'arts' ko 'social science'. Kuma ai Hausa da
Islamic suna cikinsu, kuma suna da sauƙin samun maki a cikinsu idan an rubuta.
Yawan maki kuma da shi ake amfani wajen samun gurbin karatu.
Wannan yana buƙatar
wayar wa da al'umma kai, domin fahimtar da su cewa ƙarin dama ce wajen samun
gurbin karatu.
Jibril Yusuf Dokan Lere, Ph.D.
11-09-2025
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.