Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane Aiki ne Mafi Muhimmanci da ya Dace a yi wa Karatun Hausa a Yau?

👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏

💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍

https://www.youtube.com/@AmsoshiTV

Ya zuwa yau, akwai rubuce-rubuce masu tarin yawa da aka yi a cikin harshen Hausa, tun daga kan kundayen digiri na uku da na biyu da na ɗaya, har zuwa kan littattafai da maƙalu da sauransu. Wasu rubuce-rubucen kuwa masana da manazarta harshen Hausa sun gudanar da su ne a cikin wasu harsuna na daban (misali Ingilishi da Larabci da Faransanci da sauransu), duk da sun shafi harshe da adabi da al'adun Hausawa ne. A cibiyoyin binciken Hausa da sashe-sashe na Hausa a jami'o'i da kwalejojin ilimi akwai tarin waɗannan rubuce-rubuce.

Sai dai kash... duk da yawaitarsu, akwai matuƙar ƙarancin rubutun Hausa a kan intanet. Abin takaici, har an ayyana Hausa a matsayin ɗaya daga cikin harsuna masu ƙarancin bayanai a kan intanet (low-resource language). Kwatakwata bai dace a ce Hausa tana cikin wannan rukuni ba. Dalilin kawai shi ne, ba a riga da aka ɗora waɗannan tarin bayanai da ɗimbin ilimi a kan intanet ba.

A wannan tattaunawa, an kawo muhimmancin ɗora bayanai a kan intanet guda goma sha biyu (12) tare da bayar da shawarwari kan yadda za a samar da ingantattun bayanai game da Hausa da Hausawa a kan intanet.

Muna maraba da shawarwari da tsokacinku.

Post a Comment

0 Comments