Ticker

6/recent/ticker-posts

Tauhidi a Wasu Wakokin Siyasar Zamani: Nazarin Habaici-Sakayau Domin Kafa Shugabanci Nagari

Cite this article as: Ɗangulbi A. R. & Kurawa H. M. (2024). Tauhidi a Wasu Waƙoƙin Siyasar Zamani: Nazarin Habaici-Sakayau Domin Kafa Shugabanci Nagari. Proceedings of International Conference on Rethinking Security through the lens of Humanities for Sustainable National Development Interdisciplinary Perspectives. Pp. 379-385.

TAUHIDI A WASU WAƘOƘIN SIYASAR ZAMANI: NAZARIN HABAICI-SAKAYAU DOMIN KAFA SHUGABANCI NAGARI

Na

Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, (Ph.D)
Sashen Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau

Da

Halima Mansur Kurawa
Sashen Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau

Tsakure: Kodayaushe aka yi maganar shugabanci nagari, abin da zai zo a zukatan masu karatu ko sauraro, shi ne, wane ne shugaba nagari? Shugaba nagari shi ne, mutum mai tsoron Allah da tausayin na ƙasa da shi da nuna gaskiya da riƙon amana ga shugabancin al’umma da aka ɗora masa. Idan waɗannnan abubuwa suka haɗu ga mutum, to ana kyautata masa zaton ya kasance shugaba nagari, wanda zai yi shugabanci cikin adalci da ke haifar da zaman lafiya da haɓaka tsaro. Wannan muƙala mai suna, ‘Tauhidi a Wasu Waƙoƙin Siyasar Zamani: Nazarin Habaici-Sakayau Domin Kafa Shugabanci nagari’ ta yi bayani ne a kan rawar da ‘habaici-sakayau’, yake takawa wajen faɗakar da ‘yan siyasa domin su kyautata ɗabi’unsu da halayensu kuma su zama masu tsoron Allah da yarda da ƙaddara ta alheri ko sharri kasancewar su ne tushen samar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma. An yi amfani da wasu waƙoƙin siyasar zamani kamar waƙar “Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya, Baba Buhari kai muke so Nijeriya” ta Ibrahim Yala Hayin Banki da waƙar “‘Yan Nijeriya mu fito mu yi P.D.P. ta gyara ƙasata” ta Shu’aibu ‘Yan Medi Ƙaraye da kuma waƙar Ɗan takarar kujerar Gwamna a jihar Neja Mu’azu Bawa Rijau ta Kabiru Yahaya Kilasik, da ta “Munafuccin Karen Ruwa” ta Garba Gashuwa Kano, wajen isar da saƙon wannan muƙala tare da hira da masu ruwa-da-tsaki a wannan fanni. Haka kuma, Muƙalar ta fito da sakamakon da ke yin nuni ga illar da tsafe-tsafe da zuwa wurin bokaye da ‘yan bori da malaman tsibbu suke yi wajen neman biyan wata buƙata ta siyasa ko wani shugabanci na al’umma. Yin haka ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci da aƙidar tauhidi. Saboda haka, mawaƙan siyasar zamani suna amfani da habaici-sakayau wajen faɗakar da ‘yan siyasa da sauran al’umma a kan illolin da ke tattare da bin ƙazamun hanyoyi wajen neman muƙaman siyasa da sauransu.

Muhimman Kalmomi: Tauhidi, Waƙa, Habaici, Sakayau, Siyasa, Shugabanci, Tushe, Kafa

1.0 Gabatarwa

Wannan muƙala wata faɗakarwa ce da ke jawo hankalin ‘yan siyasa da sauran mutane da duk wani mai neman biyan wata buƙata ta duniya, ya neme ta wurin Allah Mahaliccin kowa, mai kowa mai komai, maimakon bin ƙazamun hanyoyin tsafe-tsafe da bokaye da ‘yan bori da malaman tsibbu. Mutane, musamman ‘yan siyasa da masu neman kuɗi da mulki kowane iri suna zuwa wurin bokaye da masu tsafe-tsafe da ‘yan bori da bin sauran hanyoyin da ba su dace da shari’a ba a lokacin da suke son tsayawa takarar wata kujera ta siyasa ko kuɗi ko wata sarauta ta gargajiya. Waɗannan mutane suna yin imani da bin irin waɗannan hanyoyi bisa ga yarda da cewa, idan har suka bi irin waɗannan hanyoyi, buƙatunsu za su biya. Tauhidi shi ne dogara ga Allah ga dukkan al’amuran rayuwa wajen gudanar da harkokin yau-da-kullum. Wannan tauhidi yana taimaka wa mutum ya ƙara yarda da Allah, da imani da ƙaddara ta alheri da ta sharri; domin kuwa, su ne tushen samar da shugabanni nagari masu gaskiya da riƙon amana a tsarin shugabanci na sarautar gargajiya da mulkin siyasa da ake magana a kansa. Mawaƙan siyasa na zamani malamai ne masu hikima da hangen nesa wajen yin amfani da basirarsu wajen jawo hankalin mutane cikin waƙoƙinsu ta hanyar amfani da habaici-sakayau domin su ji, kuma su gyara kurakuransu. Duk wanda ya nemi biyan wata buƙata ta duniya ta hanyar tsafi ko bokaye da saurnsu, babu shakka ya saɓa wa aƙidar tauhidi da addinin Musulunci ya yarda da shi. Saboda haka ne ya sa mawaƙan siyasa suke jawo hankalin ‘yan siyasa da su koma ga hanyar gaskiya ta yarda da ƙaddara ta alheri da akasin haka, domin su zama shugabannin al’umma da za a iya alfahari da su. Habaici kuwa, wata magana ce mai ɓoyayyar ma’ana wadda idan mutum bai san dalilin yin ta ba, ba zai fahimci inda maganar ta nufa ba. Mawaƙan siyasa suna amfani da habaici-sakayau su yi wa al’umma kashedi ko gargaɗi ga barin aikata wani abin da bai dace ba, ko wanda ya saɓa wa tunani da hankalin ɗan Adam. Habaici-sakayau nan, shi ne wanda mawaƙi ke furtawa ta hanyar amfani da kalmomin lamirin sakaya zance, kamar su ‘wani,’ wata’, wane, wance da su wane, domin sakaya sunan wanda yake yi wa habaicin a zukatan al’umma.

1.2 Habaici

Habaici wata magana ce da ake furtawa zuwa ga wani mutum ko wasu mutane a matsayin hannunka-mai–sanda ko shaguɓe ko gugar-zana don wanda aka yi wa, ya ji kuma ya gyara halayensa ba tare da an ambaci sunansa ba. Masana da manazarta sun yi bayanai daban-daban dangane da ma’anar habaici. Bergery (1934:431) da Ɗangambo (1984:41) da Ɗangulbi (2013:95) da Malumfashi da wasu (2014: 24), sai Umar (1987) da Koko (1989) da Swift ed (2023) da kuma Yahya (1997), dukkansu sun yi ittifaƙi a kan cewa, “habaici magana ce mai ɓoyayyar manufa”. Watau akan yi magana ce gajeruwa da nufin isar da wani saƙo ko wani abu ga wanda aka yi maganar domin sa.Wato akan yi habaici a cikin sigar karin magana don a gargaɗi wani mutum ko a yi masa hannunka-mai-sanda ko shaguɓe ga wani abu maras kyau da yake aikatawa domin ya ji, ya daina, kuma ya yi ƙoƙarin gyara ɗabi’unsa da ake zargin sa da su. Dangulbi (2013:95) ya ce, “habaici wani kalami ne da ake furtawa a taƙaice a matsayin wanka-da–jirwaye, ko gugar-zana domin a musguna wa wani mutum ko a faɗakar da shi a kan wani ko wasu miyagun ayyuka ko ɗabi’u da yake aikatawa waɗanda suka saɓa wa buƙatar al’ummar Hausawa da yake zaune tare da su.” Ya ƙara da cewa, ana amfani da karin magana a gina habaici don a gargaɗi mutum ya gyara halayensa. Wannan ya nuna cewa, ita karin magana ana amfani da ita a gargaɗi masu aikata munanan halaye, musamman shugabannin siyasa ko wasu masu riƙe da muƙaman sarauta ko neman wani matsayi na siyasa. Haka kuma, ana amfani da kalmomin lamirin suna kamar, ni, kai, ke, ku, su, mu, wani, wata, wasu, wanda, wadda, waɗanda domin a yi wa mutum ko mutane shaguɓe ko hannunka-mai-sanda. Sannan ana yin amfani da lamiran suna na gama-gari kamar kowa, kowanne, kowace, waɗanda ake magana a kansa ko a kansu da sauransu. Har wa yau, akwai kalmomin tsigalau kamar ɗan, ‘yar da ‘yan waɗanda ake gina habaici da su domin a bayyana wani hali ko ɗabi’a ko sifa ta wanda ake yi wa habaicin. Bugu da ƙari, akwai kalmomi kamar: ‘o’o, ‘a’, ‘an’, ‘in,’mai’ ‘masu’ da sauransu. Duk waɗannan kalmomi da mawaƙan Hausa sukan yi amfani da su suna gina habaici cikin waƙoƙinsu domin su gargaɗi ko wayar wa ‘yan siyasa da sauran masu sauraron su kai. Waɗannan kalmomin lamirai sun taka muhimmiyar rawa a fagen isar da saƙo na gyara ɗabi’un ‘yan siyasar Nijeriya.

1.3 Habaici-Sakayau

A wannan nau’in habaici-sakayau, akan yi amfani da kalmomin sakaya magana ta hanyar ɓoye sunan wanda ake yi wa habaici, a bar mutane su yanke wa kansu hukunci wajen ƙoƙarin gano wanda ake yi wa habaicin. Galadanci (1976) da (Bagari 1986) sun ce, ana amfani da kalmomin mafayyaci kaikaitau da wakilin suna kaikaitau kamar haka: Wani, wata, wasu, waanѐ, wancѐ, ko waɗansu, domin a gina habaici zuwa ga shugabanni ko ‘yan siyasa ko jam’iyyar siyasa ko ɗan adawa wanda ba a son a ambaci sunansa ƙarara domin a kauce wa tashin hankali tsakanin masu saurare da ‘ya’yan jam’iyyar wanda ake yi wa habaici. Siyasa abu ce mai tafiya da ra’ayi da kuma zamani, saboda haka, kowane ɗan siyasa yana ƙoƙari ya ga cewa, tafiyarsa ta yi daidai da zamanin da ake ciki ta hanyar yin abubuwan da zamani da mutanen zamani suke buƙata. Habaici yakan iya sa masoyan ɗan takara ko ɗan siyasa su ƙaurace wa zaɓen wanda ɗabi’unsa da halayensa suka saɓa wa aƙidar addini da tauhidi da kuma manufar jam’iyyarsu ko al’ummarsu. Sannan sukan dubi matsayin shugaba ko ɗan siyasar da ya kasa aiwatar da mulki daidai da tafiyar zamani saboda rashin ilimi ko ƙwarewa ga hulɗa da jama’a, ko rashin ɗaukar ƙaddara wajen neman muƙami, sai su jefe shi da habaici da ya yi daidai da halayensa da ɗabi’unsa a bayyane domin ya ji, kuma ya gyara.

Misali, Ibrahim Yala yana cewa:

Duk wani wanda ba ya jin tsoran Rabbana,

To mun daina girmama shi ya cuta mana,

Mai rawani da jiniya Allah isar mana,

  Za mu buga da ku bana faɗin Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Waƙar APP/ANPP 2003).

Tsoron Allah da yarda da ƙaddara ta alheri ko sharri ɗabi’a ce mai kyau da ke tabbatar da mutunci da kyawawan ɗabi’un ɗan siyasa ko shugaba. Idan shugaba ya kasance yana da irin waɗannan halaye, to za a same shi mutum mai gaskiya da adalci, waɗanda su ne tushen samar da shugabanci nagari. Idan aka samu shugaba wanda ba ya da imani da tsoron Allah, to talakawansa za su bijire masa, komai kwarjininsa a kujerar mulki. Saboda haka ne ya sa mawaƙan siyasa sukan yi amfani da habaici-sakayau su jawo hankalin talakawa da su ƙaurace wa irin wannan shugaba da ba ya da tsoron Allah wajen jagorancin jama’a. Yana da wuya a sami shugaba maras tsoron Allah ya zama mai adalci, domin yakan kasance mai danne ko take haƙƙin jama’arsa. Sannan kuma, ya tursasa wa jama’arsa su aikata abin da ba daidai ba ta hanyar amfani da ƙarfin mulki. Wannan dalilin ne yakan taimaka wajen zaburar da talakawa su bijire wa shugabanni tare da nuna rashin girmawa a gare su.

1.4 Bin Bokaye da Malaman Tsibbu

Wannan ɗabi’a ta yarda da bokaye da malaman tsibbu ta zama ruwan dare game-duniya a tsakanin ‘yan siyasa da masu neman muƙaman siyasa ko sarautun gargajiya a wannan zamani. Lokuta da dama za ka sami gidajen bokaye da malaman tsibbu da ‘yan bori sun cika da mutane masu neman a taimaka masu su ci zaɓe ko su sami nasarar karya abokan hamayyarsu. Bokaye da malaman tsibbu suna amfani da wannan dama su cusa aƙidar imani da sihirce-sihirce da tsafe-tsafe a zukatan ‘yan siyasa ko masu neman muƙami, domin su saka su mugunyar hanya ta barin Ubangijinsu lokacin da suke neman biyan wata buƙata.’Yan siyasa suna zaton bin wannan ƙazamar hanya ita ce ta fi saurin biya masu da buƙatunsu. Wannan aƙida ta saɓa wa tauhidi, domin Allah shi kaɗai Yake biya wa kowa buƙatarsa bisa ga ƙudirar ƙarfin ikonsa. Saboda haka, ya wajaba ‘yan siyasa su sani cewa, duk lokacin da suka buƙaci tsayawa wata takara ta siyasa, to su nemi biyan buƙata ga Allah don shi kaɗai ne Yake iya biya masu dukan wata buƙata ba bokaye ko malaman tsibbu ko ‘yan bori ba. Bisa ga wannan dalili ne ya sa mawaƙan siyasa suke sukar ‘yan siyasa da ba su da tauhidi domin su jawo hankalinsu su gane kuskurensu, sannan su dawo ga hanyar gaskiya domin su tsira da imaninsu da mutuncinsu a idon duniya. Misali, Shu’aibu ‘Yar Medi Ƙaraye ya yi wa wani ɗan takarar kujerar gwamna habaici, wanda ya tafi wurin bokaye da malaman tsibbu don su taimaka masa ya ci zaɓe. Mawaƙin yana cewa:

Wani ɗan takarar wasu ya saɓa laya ba a kada shi,

Wai sai dole ya yi Gwamna wataƙil boka ya duba shi,

Ba sa’a gare shi ba PDP ce za ta kada shi,

Ran zaɓe mu ɗau inuwar lema domin a gyara ƙasata.

(Shu’aibu ‘Yar Medi: Waƙar PDP).

Al’adar zuwa wurin bokaye ko malaman tsibbu ta yi ƙamari a zukatan ‘yan siyasa. Saboda haka, a duk lokacin da siyasa ta kunno kai za ka taras masu neman a tsayar da su takara suna ta kai-kawo wajen bokaye da malaman tsibbu domin neman sa’a ga buƙatar da suka sanya a gaba. Wannan kuwa, ɗabi’a ce ta rashin tauhidi, wato maguzanci da Hausawa ‘yan siyasa suka rungume ta hannu bi-biyu domin samun biyan buƙatunsu na siyasa.Wato, ba su yarda da cewa, Allah shi Yake ba da mulki ga wanda yake so, kuma Ya karɓe mulki ga wanda yake so ba. Irin waɗannan ‘yan siyasa ne mawaƙan siyasar zamani suke suka ta hanyar amfani da habaici don su jawo hankalinsu su koma ga Allah a duk lokacin da suke neman wata buƙata. Wannan ɗabi’a ta zuwa wurin bokaye da malaman tsibbu ta sanya wani ɗan takarar kujerar Gwamna ya tafi neman sa’a, sai aka ba shi laya da nufin shi zai kada abokin takararsa. Amma hakan bai sa ya sami nasara ba. Duba da wannan rashin tawakkali da rashin tauhidi da wannan ɗan takara ya nuna wajen neman kujerar Gwamna ta hanyar zuwa ga bokaye don neman sa’a ya sa wannan mawaƙin ya soki ɗan takarar Gwamnan da habaici kamar yadda ya gabata a sama. Wato inda yake cewa, wani ɗan takarar wasu ya saɓa laya ba a kada shi, amma mawaƙin ya nuna masa cewa, ƙarya ne Jam’iyyar PDP ce za ta kada shi. Haka kuma, abin ya kasance a lokacin da aka yi zaɓe a jihar Kano lokacin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.

Haka shi ma da yake yi wa wani ɗan takara habaici dangane da rashin yarda da Allah shi kaɗai Yake ba da mulki ga wanda ya so, a lokacin da ya so, mawaƙi Garba Gashuwa, ya yi habaici ga wasu ‘yan siyasa waɗanda suka zama azzalumai da rashin yarda da koyarwar addinin musulunci suka rungumi hanyar bokaye wajen neman muƙami idan suka hau mulki sai su sa zalunci a gaba. Ga abin da yake cewa:

Wasu ba su tsoron zalunci,

Ba sa gudun keta mutunci

Da rashin sani ga bambanci,

Ko kuma su shirya munafunci

Da rusa hanyar addini

(Garba Gashuwa: Waƙar APP, ‘munafuccin karen ruwa’).

A nan mawaƙin ya yi amfani da azancin magana na habaici ga wasu ‘yan takara na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, inda ya alaƙanta su da zalunci a lamarin tafiyar da mulki ga al’umma. Haka kuma, ya siffanta su da masu keta mutuncin mutane ta hanyoyi daban-daban domin cimma manufofinsu na siyasa. Bugu da ƙari, mawaƙi ya ƙara siffanta abokan adawar jam’iyyarsa da rashin sani (Jahilci) da kuma zuwa ga bokaye da nuna bambanci waɗanda duk gazawa ce ga mai mulki. Bayan waɗannan misalai a ɗango na huɗu da na biyar, mawaƙin ya bayyana cewa, su waɗannan abokan hamayyar suna shirya munafunci da kuma rusa koyarwar addinin musulunci ta hanyar zuwa wurin bokaye don neman buƙata. Yana isar da saƙon shi ne ga Hausawa musulmi don su ƙyamaci jam’iyyar PDP, su zaɓi jam’iyyarsa ta APP, kamar yadda mawaƙin ya bayyana cewa, su waɗancan ‘yan siyasa ba nagartattun mutane ne ba.

Mawaƙin yana gargaɗin mai neman muƙami ta hanar bin bokaye da malaman tsibbu da ya bari ya dawo wa hanyar Allah domin ya rabauta daga shiga wutar jahannama. Sakin hanyar Allah wajen neman buƙata ya saɓa wa tauhidi, shi ya sa Garba Gashuwa yake jan hankalin ‘yan siyasa da su bar bin hanyar bokaye, domin bin bokaye barin hanyar ni’ima ce, wato hanyar shiga aljanna. Daga ƙarshe, ya rufe da baitinsa, inda yake gargaɗin ‘yan siyasa da su tambayi tarihin magabata, waɗanda suka saɓa wa hanyar tauhidi suka bi hanyar bokaye, yaya ƙarshensu ya kasance? Wuta ce makomarsu saboda sun saɓa wa tauhidi, sun bar Allah, wanda shi ne Yake ba da mulki ga wanda ya so, suka shiga hanyar tsafi kuma suka halaka.

1.5 Tsafe-Tsafe da shiga Ƙungiyoyin Asiri

Tsafi yana nufin yi wa iskoki ko rafanai hidima domin neman yardarsu su biya wa wanda yake hulɗa da su buƙatarsa. Bunza (2009) ya bayyana tsafi da cewa, “yi wa wani abu da ba Allah ba hidima domin neman biyan buƙata ta duniya”. Ya ƙara da cewa, yanke-yanke da watsa wani abinci a gidan Tururuwa ko a mararrabar hanya ko gindin wani icce ko bishiya wani salo ne na hulɗa da aljannu domin su taimaka wa wanda ya nemi biyan buƙata daga gare su. Bergery (1933/34) akwai dalilai da dama da sukan sa mutane su riƙa bin hanyoyin tsafe-tsafe don neman biyan wata buƙata ta duniya. Misali:

1.5.1 Jahilci

Jahilci yana nufin rashin ilimi na yadda abubuwa suke gudana na harkokin rayuwar yau-da-kullum. Wato, duk mutumin da ba shi da ilimin addini da na zamani ana kiran sa jahili. Shi ma da yake jefa habaici ga wani ɗan takarar kujerar Gwamna a jihar Neja, wanda ya saki hanyar Allah don ya sami nasarar lashe zaɓe, amma ba shi da ilimin addini da na boko. Sai Kabiru Kilasik ya jefe shi da kalmar habaici-sakayau inda yake cewa:

Ga wani na son Gwamnan Neja, amma an ce bai da boko,

Ba Arabiya ba ya da boko sai girman kai nan na iko,

Ya ce lallai sai ya yi Gwamna, shi tafiyatai babu tsaiko,

Lallai ka ebo ta da faɗi, wane da kai nai zai yi raki.

(Kabiru Kilasik: Waƙar ‘Neja ga mafita’).

Babu shakka rashin ilimi yana daga cikin dalilan da ke haifar da girman kai ga kowane mutum, balle ma wanda yake neman wani muhimmin matsayi a cikin al’umma. Rashin ilimi shi ke haifar da dogon tunanin faɗawa cikin hanyar da ba ta dace ba wajen neman wani matsayi na siyasa ko na sarauta. Mai ilimi yakan tsaya ya auna ya ga amfani ko illar abin da yake so kafin ya tsunduma gadan-gadan wajen neman abin, sannan ya dogara ga Allah lokacin da yake neman sa ta hanyar halal domin ya tsira da imaninsa. Haka nan ma Kabiru Yahaya Kilasik yana cewa:

Wane buku ne ko kwaɗɗo don na gan shi yana ta ciccika,

Haka nan yake tun can farko da shi da matatai dakan-ɗaka,

Mulki dodon bango ne sai ka rage izza da ɓaɓɓaka,

Wata rana da ranka kana nan sai wani Gwamna ake yi wa jiniya.

(Kabiru Kilasik: Waƙar Neja ga mafita).

Ciccika da izza da ɓaɓɓaka kalmomi ne masu nuna ji-ji-da-kai, wanda aka fi samun sa ga mutane jahilai marasa ilmi na addini da na boko. Mawaƙin ya siffanta wani ɗan takarar kujerar Gwamnan Neja da wasu halittu na ruwa, wato buku da kwaɗɗo waɗanda ya ce su ne suke nuna ƙasaita da izza. Wato, mawaƙin ya dabbantar da wannan ɗan takara domin ya jawo hankalin mutane su lura da cewa, waɗannan halittu suna da halaye na girman kai ko saurin fushi idan aka taɓa su. Saboda haka, shi wannan ɗan takara bai san cewa mulki dodon bango ne ba, wata rana sai an yi kamar ba a yi ba. Ya yi masa habaici ta hanyar sakaya sunansa ta hanyar amfani da kalmar ‘wani’ domin ka da mutane su gane wanda ake yi wa habaicin, sai dai idan sun san halaye da ɗabi’un wannan mutum. Ba komai ya jawo masa girman kai ba, illa rashin ilimi da rashin sanin ya kamata. Mawaƙin ya nuna wa wannan ɗan takara cewa, ko da an zaɓe shi ya yi mulki, to, ya sani da izzarsa da ji-ji da kansa wata rana sai labari; domin zai sauka mulki ya koma tare da jama’ar da suka zaɓe shi ya zauna, ya girbi abin da ya shuka na alheri ko akasin haka. Haka shi ma da yake sukar wani shugaba maras ilimi da aka zaɓa, sai ya kasa iya tarbar baƙinsa da suka zo daga ƙasashen Turai saboda ba ya jin harshen Turanci. Misali, inda Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yake cewa:

Wani ya hau mulki ba ilimi,

Ya ruɗe an mashi Turanci.

(Kamilu: Runhu an furen banza).

Rashin ilimi matsala ce mai girma ga wanda yake neman matsayi na jagorancin jama’a. Domin duk mutumin da ba shi da ilimi ba zai san abin da mutane ke so ba, balle ya yi masu abin da ya dace. Ilimi shi ne tushen samar da kyakkyawar hulɗa tsakanin shugaba da waɗanda yake shugabanta, ko waɗanda suka zo domin su yi hulɗa da shi ko da ƙasarsa da yake shugabanta. A baitin da aka kawo a sama, mawaƙin ya bayyana irin illar da rashin ilimi take da shi ga shugaba domin yakan kasa aiwatar da kyakkyawar hulɗa sakaninsa da waɗanda yake da wata hulɗa ta siyasa ko cinikayya ko makamanta haka da su. Yin magana da wani harshe na daban da ya bambanta da harshen ƙasa, dole sai an koye shi, sannan a iya magana da masu jin wannan harshe. Wannan dalili ne, ya sa mawaƙin ya yi wa wani shugaba habaici saboda rashin iya ko jin harshen Turanci. Rashin jin harshen Turanci babbar illa ce ga shugaba, musamman a ƙasar da harshen Turanci shi ne harshen gudanar da hulɗa tsakanin ƙasar da wata ƙasa. Domin ba zai iya jawo hankalin mutane su fahimci abin da gwamnatinsa take so ba. Saboda haka, wannan illar zaɓen mutumin da ba shi da ilimi a kowane irin muƙamin gwamnati, ta jawo hankalin mawaƙan siyasa su riƙa amfani da habaici wajen ƙasƙanta shugabanni ko ‘yan siyasa a bainar ko idon jama’a. Mulkin siyasa yana buƙatar mutum mai ilimi da ƙwarewa a harshen Turanci da sha’anin mulki domin ya kasance ba ya jin shakkun zuwan baƙi idan sun zo masa daga ko’ina.

1.5.2 Son Kuɗi ko Mulki

Son kuɗi ko mulki wata buƙata ce ta zuciya, wadda take zame wa mutane alaƙaƙai a zukatansu. Wannan buƙata takan jefa mutane su riƙa bin hanyoyi na tsafe-tsafe da bokaye da malaman tsibbu domin neman biyan buƙatunsu. Wannan ɗabi’a tana daga cikin abubuwan da ke saka mutane su zama marasa tausayi da rashin jinƙai idan sun sami mulki ko sun mallaki dukiya. Duk wanda ya nemi biyan wata buƙata ta ƙazamar hanya za a taras ba yakan kula da bai wa talakawa haƙƙinsu su ba, wanda hakan kan jefa mutane cikin tunanin aikata kowane irin abu na ta’addanci domin su sami sauƙin rayuwa. Saboda haka, sai mawaƙan siyasa su riƙa amfani da habaici-sakayau da manufar gargaɗin ‘yan siyasa su daina amfani da matasa wajen neman biyan buƙatunsu na siyasa domin samun al’umma ta gari da shugabanci nagari. Domin shugabanci nagari shi ne tushen samar da adalci da zaman lafiya da tsaro a ƙasa, musamman a yankin Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

1.6 Habaici-Sakayau Ga Jam’iyya

Jam’iyya wata ƙungiya ce ta jama’a masu ra’ayi iri ɗaya suka taru suka kafa ta domin cimma wata manufa ta siyasa. Kowace jam’iyya tana alfahari da yawan magoya bayan da take da su. Idan jam’iyya ta kasa samun magoya baya da za su taimaka mata ta kai ga ci, to takan samu matsala da za ta kai ta ga rushewa. Duba da irin kwarjini da jam’iyyar APC take da shi a duk faɗin Nijeriya ya sa Kamilu ya yi wa wata jam’iyya habaici domin ya soki tafiyar ta da ta magoya bayanta.Ya yi amfani da harshen Turanci, ya kira jam’iyya da ‘Fati’ (party), wanda hakan ya sa ya ba ta sunan namiji. Misali, Murtala Mamsa yana cewa;

Wani fati ya mutu mun gano,

An je zaɓen duka gwamnoni.

(Murtala Mamsa:Waƙar A.P.C.).

A ɗan waƙa na farko mawaƙin ya yi amfani da habaici-sakayau don ya muzanta wata jam’iyyar adawa da magoya bayanta bisa ƙaryar da suka yi wa al’umma na taimaka masu ga samun abubuwan more rayuwa da ayyukan cigaban ƙasa, amma suka kasa. Sannan ya nuna cewa, saboda ƙarya da suka yi wa jama’a shi ya sa fatin ya mutu. Sannan ya aibata su da cewa, sun yi ƙarya da suka ce, sun ga ɗiyan bishiyar ƙarya. Kowa ya san Hausawa suna cewa, ‘ƙarya fure take yi ba ta ‘ya’ya’. Saboda haka, wannan habaici da mawaƙin ya yi, yana yi wa ‘yan jam’iyya mai mulki shaguɓe ne ko hannunka-mai-sanda domin su sauya salon tafiyarsu ga al’amarin siyasa ko da za su samu fatinsu ko jam’iyyarsu ta dawo da darajarta.

Mawaƙin ya yi amfani da aron kalmar Turanci a inda ya kira jam’iyya da sunan ‘Fati’ shi ne ya sa ya gina habaici-sakayau da cewa, ‘wani Fati’ domin ya ƙasƙanta jam’iyyar da yake yi wa habaicin. Kamar yadda aka sani ba a gane kwarjinin jam’iyya sai ran da aka je wajen jefa ƙuri’a. Wannan jam’iyya da ke tinƙaho cewa, tana da mutane, ashe duk kurari ne kawai. Ba a tabbatar da haka ba sai a lokacin jefa ƙuri’a sai ga shi jam’iyyar ta sha kaye. Wato, ba a zaɓe ta ba. A duk lokacin da fati bai yi nasarar lashe zaɓe ba, to babu tabbas da cewa, zai cigaba da bunƙasa. A dalilin haka ne ya sa mawaƙin ya jefe shi da habaici yana cewa, ‘wani Fati ya mutu mun gano, an je zaɓen duka gwamnoni’. Saboda haka, martabar Fati ko jam’iyya ita ce, a zaɓe ta domin ta kafa gwamnati, idan ba haka ba, to za ta mutu. Irin wannan yanayi ne da jam’iyyun siyasa suke shiga ya sa, Muhammadu Awwalu Isah Bunguɗu yake yi wa jam’iyyar NPN habaici-sakyau domin ya kambama tasa jamiyyar PRP, inda ya nuna cewa:

Ga wata tunkiya da ba ta da tsoron tsara,

Ta kashe damisa da zilla balle kura,

Mai tsoron tsiya ƙazama mai kai ƙara,

Mun kore ta dole ta yi gudu ta tsira,

Balle kai biri da kai zure kai gwaiwa.

(Muhammadu Awwalu Isah Bunguɗu: Waƙar ‘PRP mu gode Allah’).

1.7 Kammalawa

 Mafi yawan mawaƙan siyasar zamani suna alfahari da yin amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin ‘yan siyasa da masu sauraro su fahimci saƙonnin da suke isarwa gare su tare da samar masu nishaɗi. Muƙalar ta gano cewa, mafi yawan ‘yan siyasa da ke bin hanyar bori da tsafe-tsafe da malaman tsibbu wajen neman biyan buƙatarsu ta siyasa, marasa ilimin addini ne, da na zamani. Wasu kuma suna da ilimin amma saboda son jin daɗin duniya ne yake jefa su cikin wannan hali ido rufe. Mawaƙan siyasa suna ƙoƙari matuƙa wajen jawo hankalin ‘yan siyasa don su fahimci cewa, Allah shi kaɗai Yake ba da mulki ga wanda Ya so, a lokacin da Ya so. Saboda haka, suke kira ga ‘yan siyasa da su guji yin tsafe-tsafe da shirka wajen neman mulkin duniya da ba ta da tabbas. Idan kuwa aka samu haka a tsakanin masu neman mulki, suka dogara ga Allah, to za a sami shugabanni nagari masu tsoron Allah da gaskiya da riƙon amana waɗanda za su yi shugabanci cikin adalci. Kowa ya dogara ga Allah, ya nemi Allah ya yi masa zaɓi, zai sami nasarar cimma gurinsa ta hanyar da ta dace. Sannan a sami shugabanni nagari waɗanda za su kawo wa ƙasa zaman lafiya da tsaro da cigaban tattalin arzikin ƙasa.

Manazarta

Abdullahi, S. U. (1987). Gaskiya dokin Ƙarfe. Kano, Triumph Publishing Company.

Bagari, D. (1986). Bayani Hausa:Jagora ga mai Koyon Ilimin Bayanin Harshe. Rabat-Moroc, Imeremerie El- Maarif Al-Jadida.

Bergery, G.P. (1993). Hausa-Enlish and English-Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.

Dangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Dangulbi, A. R. (1996). Habaici da Zambo a cikin Waƙoƙin Baka na Hausa. Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato.

Encyclopedia Britannica Updated Feb. 11,2023. An article History.

Koko, H. S. (1989). Jagoran Naarin Tatsuniyoyi. Sakkwato: College of Education.

Mawaƙa

Dauda Adamu Kahutu Rarara: Waƙar Muhammadu Buhari ta APC.

Kabiru Yahaya Kilasik (2015). Waƙar Neja ga Mafita ta Muhammadu Bawa Rijau ɗan takarar Gwamnan Neja.

Muhammmadu Awwalu Isah Bunguɗu (1983). Waƙar PRP.

Garba Gashuwa, ( 1999). Waƙar APP, Mnafuccin Karen Ruwa

Malumfashi I. da Nahuche I. (2014). Ƙamusun Karin Magana,

Martan Websters {10th Edition Dictionary}

Mudassir Kasimu Kano: Waƙar APC

Murtala Mamsa Jos: Waƙar Jam’iyyar APC.

Ibrahim Yala Hayin Banki: Waƙar Muhammadu Buhari

Tauhidi a Wasu Wakokin Siyasar Zamani: Nazarin Habaici-Sakayau Domin Kafa Shugabanci Nagari

Post a Comment

0 Comments