Cite this article as: Isah Z. (2024). Mahangar Mawaƙan Zamani a kan Siyasa da Tsaro: Nazari daga wasu Waƙoƙin Farfaganda na Hausa. Proceedings of International Conference on Rethinking Security through the lens of Humanities for Sustainable National Development Interdisciplinary Perspectives. Pp. 386-396.
MAHANGAR MAWAƘAN ZAMANI
A KAN SIYASA DA TSARO: NAZARI DAGA WASU WAƘOƘIN FARFAGANDA NA HAUSA
Na
Zainab Isah, PhD
Sashen Koyar Da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Tsakure: Mawaƙa suna daga cikin rukunin jama’a da suke ba da
gudunmawa wajen haɓaka siyasar Nijeriya. Don waƙa tana ɗaya daga cikin hanyoyin
yaɗa manufofi cikin sauri. Wasu mawaƙan sukan duba yanayin siyasar Nijeriya da
tsaro, sannan su bayyana su cikin waƙoƙinsu ta hanyar nuna rashin jin daɗi da
goyon baya a kan yadda ake tafiyar da tsarin mulki. Manufar wannan bincike ita
ce, a nazarci hoton siyasar Nijeriya da tsaro kamar yadda suka bayyana a cikin
wasu waƙoƙi. Har wa yau, binciken ya ayyana matsalolin da Nijeriya take
fuskanta dangane da siyasa da tsaro maslahan da mawaƙan suka kawo a cikin
waƙoƙinsu. Domin ‘yan Nijeriya su farga, kuma wasu waƙoƙin suka kawo mafita. An
zaɓi waƙar ‘Baubawan Burmi’ da ‘Bubukuwa’ da ‘Ɗaurin Gwarmai’ dukkansu na Aminu
Ladan Abubakar (ALA) da waƙar ‘Mafarkin Mulki I da II’ na Jibrin Muhammad
Jalatu. Dalilin binciken shi ne, don a bayyana halin da ‘yan Nijeriya suke ciki
ta fuskar harkar tsaro da siyasa, musamman na Arewacin Nijeriya da nufin kawo
mafita ga al’umma. Binciken yana da muhimmanci, don zai fito da matsayi da
muhimmancin waƙa wajen haɓaka mulkin dimokraɗiyya.
Muhimman Kalmomi: Waƙa da Mawaƙa da Siyasa da Tsaro da Farfaganda
1.0 Gabatarwa
Tun lokacin da Hausawa
suka fara yin amfani da kayan kiɗa na zamani wajen aiwatar da waƙoƙin Hausa,
suka fara bayyana damuwarsu a kan yanayin tsarin mulkin da yake gudana a
Nijeriya. Mulkin kamar yadda suke bayyanawa ana aiwatar da shi ne, ba bisa
tsarin da ya dace ba. A cikin waƙoƙin nasu, sukan hango makomar Arewa da
Nijeriya a kan yanayin tattalin arziƙi da tsaro da sauran abubuwan da suka
shafi tsarin zamantakewa. Har ya zuwa yanzu, mawaƙan suna ci gaba da jawo
hankalin al’umma da mahukunta a cikin irin waɗannan waƙoƙi. Mawaƙan sun mayar
da hankali wajen faɗakarwa, suna yaɗa manufofinsu da zummar jan hankali. Haka
kuma, waƙoƙin sun yi fice a ƙasar Hausa ta irin saƙon da suke isarwa, har a kan
sanya su a gidajen rediyo domin yaɗa manufa ta farfaganda.
Haka kuma, manazarta sun
tofa albarkacin bakinsu dangane da waƙoƙin da ake yi na zamani; waɗannan
manazarta sun haɗa da: Musa (2007) da Baba (2007) da Gusau (2008) da Ɗan’asabe
da Wasu (2008) da Imran (2008) da Bello (2009 da 2011) da sauransu. Waɗannan ayyuka
sun yi magana a kan waƙoƙin nan da ake yayi, inda wasu daga cikinsu suka ɗauki
marubuta waƙoƙin suka yi nazarin a kansu da kuma ayyukansu. Wasu kuwa, waƙoƙin
kaɗai suka ɗauka don ƙwanƙwancewa. Yayin da wasu zambo da yabo suka duba.
Daga cikin waƙoƙin da
ake yi yanzu, an sami waɗanda suke yin kira ga ‘yan Arewa da ma Nijeriya gaba
ɗaya, suna faɗakar da su kan yanayin yadda Nijeriyar take tafiya. Waƙoƙin na
nuna kishin kai irin na mazan jiya don suna kira ga ‘yan Nijeriya da ma ‘yan Arewa
suna ilmantar da su cewa su tashi tsaye, su farka daga barcin da suke yi, su
duba halin da al’umma suke ciki, wanda bai kamata a ce hakan ake yi ba. Don
kuwa, mawaƙan sukan ɗora alhakin taɓarɓarewar komai ga shuwagabanni. Waƙoƙin na
faɗakarwa don samun cigaban Nijeriya da al’ummarta. Mawaƙan suna maganar
matsalolin da ‘yan Nijeriya suke fuskanta, suna nuna yadda abin yake yi masu
ciwo. A don haka, manufar wannan maƙala, kamar yadda takenta ya nuna shi ne,
fito da irin gagarumar gudunmuwa da mawaƙan Hausa na zamani suke bayarwa wajen
ci gaban Arewa ta fuskar siyasa da tsaro, kamar yadda suka bayyana a cikin
waƙoƙin. Wasu mawaƙan sukan yi waƙoƙin ne kacokan a kan Arewa kawai, yayin da
wasu kuma a baitocinsu suke bayyana rashin jin daɗinsu. An zaɓi waƙar ‘Baubawan
Burmi’ da ‘Bubukuwa’ da ‘Ɗaurin Gwarmai’ na
Aminu Ladan Abubakar (Ala) da waƙar ‘Mafarkin Mulki I da II’ na
Jibrin Muhammad Jalatu. …………
2.0 Siyasa
Manazarta da masu yin
sharhi a kan waƙoƙin siyasa sun ta bayyana ra’ayoyinsu a mahanga daban-daban.
Shi ya sa aka jima ana yin amfani da ita wajen isar da saƙo da kuma yaɗa
manufofin siyasa da harkokinta a ƙasar Hausa. Waƙa musamman rubutatta ta samu
ne a sanadiyar yaɗa manufa ta addinin Musulunci. Funtua (2011) ya bayyana cewa,
su kuwa Ɗangambo (2007) da Yahaya (1988) sun jaddada cewa, waƙoƙin siyasa na
Hausa sun fara samuwa tun lokacin jihadin Shehu Usman ƊanFodiyo, misali idan
aka dubi waƙar ‘Murnar Cin Birnin Alƙalawa’ da waƙar ‘Yaƙin
Kalambaina’ na Abdullahi Fodiyo. Baya ga waɗannan, akwai waƙar ‘Tsarin
Mulkin Musulunci’ ta Abdullahi Bn Fodio, ita waƙa ce ta siyasa da ta
warware komai dangane da yadda tsarin mulkin Musulunci yake.
Bayan haka, an samu
waƙoƙin ƙarni na sha tara (Ƙ19), a ƙarni a ashirin (Ƙ20) ma an yi wasu. Kafin
haka, akwai waƙar ‘Zuwan Annasara Ƙasar Hausa’ ta sarkin Musulmi
Attahiru Amadu, wadda ya yi a farkon ƙarni na ashirin. Har wasu malamai na
kiran ta da kadarkon waƙoƙin ƙarni na sha tara da ƙarni na ashirin (Ƙ19) da
(Ƙ20). Ita ma waƙa ce da aka yi da nufin canza tunanin jama’a, don jawo hankalin
mabiya kada a amince da zuwan Nasara ƙasar Hausa.
A lokacin Turawan mulkin mallaka, an yi
farfaganda sosai, don a cimma wasu manufofi. A jaridu an rubuta waƙoƙi na
farfaganda don a nuna muhimmancin noman gyaɗa, da haƙar kuza, don a lokacin
babu maganar fetur. An ci gaba da hidimomin siyasa, an kakkafa jam’iyyun siyasa
wanda aka riƙa gudanarwa yadda ya kamata. A ƙoƙarin tabbatar da haka, an yi
waƙoƙin farfaganda ana isar da wasu manufofi kala-kala da al’ummar ƙasa,
musammam a lokacin yaƙin neman ‘yancin kai. A lokacin an rubuta waƙoƙi ana
wayar da kan mutane kan irin nau’in mulkin da ya kamata a yi. Su ne waƙoƙin su
Sa’adu Zungur, kamar waƙar ‘Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya’. Wasu
waƙoƙin an yi su ne a kan zuwan Turawa da abin da suka zo da shi. Wasu waƙoƙin
suna nuna a guje wa Turawa. Wasu waƙoƙin kuma na’am suka yi da sabon sauyin da
aka samu. Haka dai aka ci gaba da rubuce-rubuce na waƙoƙin farfaganda a kan
jam’iyyun siyasa da sauran manufofi iri-iri.
A ƙasar Hausa, waƙa wata hanya ce ta isar da
saƙo, don Hausawa sun riƙe ta tun zamani mai tsawo, suna amfani da ita, suna
isar da manufofinsu da saƙonninsu ga jama’a. Har ya zuwa yanzu, wato lokacin
nan da aka kaɗa kugen siyasa, waƙa abar yabo ce domin an lura cewa siyasa ba ta
armashi, sai an haɗa ta da waƙa. Wato dai a ce waƙa wata makamashi ce ta
siyasa. Wasu mawaƙan siyasar sukan rubuta waƙoƙin ne domin tallata jam’iyya da
kwarzanta ɗan takara, yayin da wasu zambo da habaici kan zama jigogin waƙoƙin
nasu. Wasu kuwa, yanayin da ake gudanar da mulkin ne bai gamshe su ba, sai su
rubuta waƙoƙi na farfaganda suna ilmantar da mutane da kuma faɗakar da su a kan
yadda ake gudanar da mulki.
2.1 Tsaro
Tun lokacin da tsarin
zaman jama’a a ƙasar Hausa da Arewa gaba ɗaya ya fara shiga halin matsi na
rashin tsaro, jama’a suka fara nuna rashin jin daɗinsu ta hanyar ayyukan adabi
musamman waƙa. A irin wannan lokacin ne masana da manazarta suka duƙufa wajen rubuce-rubuce
don ganin an shawo kan wannan matsala. Akwai ayyuka irin na su Ƙanƙara (2016)
da Katsina da Wasu (2022) da Bunza (2017) da Aliyu (2018 da 2024). Aliyu (2024)
ya nuna yadda manazarta suka ba da ma’anar tsaro da nufin kare wani mutum ko
wani muhimmin abu ta hanyar tsayawa kusa da kuma kulawa da shi. Tsaro hanya ce
ta kulawa da wani abu domin kada wani abu ya same shi. Akan yi tsaro domin
gudun faruwar wani abu. Haka kuma, tsaro shi ne ɗaukar mataki ko tsayawa domin
bayar da kariya ga rayukan mutane ko muhallinsu ko daga hari ko wani haɗari.
Tsaro garkuwa ne domin kare kai da kaya. Bisa ga abin da ya gabata, a iya cewa
tsaro shi ne kulawa ko kare wani mutum ko wasu abubuwa daga faɗawa wani haɗari.
Ba mutum kaɗai ake tsarewa ba, har da dukiyoyi da wasu abubuwa masu amfani ga
ɗan’adam. Irin wannan tsaron ne, Nijeriya musammam yankin Arewa suka gagara
samu. Rashin irin wannan tsaron ne, rayuka da dukiyoyin mutane suka salwanta,
An ɗauki lokaci mai tsawo hakan tana faruwa, abin har ya kai halin ha’ula’i.
Sai neman agaji daga Allah.
2.2 Farfaganda
Zainab (2013) ta bayyana
yadda su Dambo (1999) da Jumare (2007) da Hassan (2011) da Mannura (2008) sun
yi ayyuka kan farfaganda. Zainab (2013) ta nuna yadda bakin masana irin su Doob
(1948) da Lasswell (1977) da Ellul (1965/1973) da Barlett da Goebbel, ya haɗu a
kan cewa, farfaganda wani ƙoƙari ne na canza tunani da manufofin mutane zuwa da
wani abu da ake son su gane. Kalmar farfaganda ta samo asali daga kalmar
aikatau ta harshen Latin propagare, to propagate a
Ingilishi ma’ana, a yaɗa. Farfaganda tana nufin a isar daga wani
zuwa wani. A lokacin da Hausawa suka aro ta, suka fara mu’amala da wannan kalma
ta ‘Farfaganda’, kalma ce ta Allah da Annabi, wato faɗakarwa zuwa ga wani abu
marar kyau ko nuna amfanin abu. Daga baya kalmar ta samu yawan ma’ana. Yawan
ma’ana na faruwa a harsunan duniya, wanda shi ma harshen Hausa yakan ci karo da
irin waɗannan sauye-sauye, inda ake samun kalma ɗaya tak da yawan ma’anoni a
jikinta dangane da muhallin da aka yi amfani da ita, Wurma (2008). Sannan akwai
dalilai da ke sa a sami kalma mai yawan ma’ana, kamar juyin zamani, yalwar
harshe da sauransu. Don haka, ana kyautata zaton irin haka ne ya samu wannan
kalmar da aka aro zuwa Hausa.
Farfaganda kamar yadda
aka bayyana a baya, tana nufin duk wani ƙoƙari don yaɗa wata manufa a fuskoki
daban-daban ko wasu labarai ko dabaru da ake yaɗawa cikin hikima. Farfaganda
tana nufin keɓaɓɓun bayanai domin haɓɓaƙa wata aƙida, ra’ayi ko ɗabi’a da duk
wani ƙoƙari na jan hankali. Haka kuma, tana nufin yaɗa wata manufa ko bayani ko
ƙarya ko wani ra’ayi da nufin canza tunanin mutane ko faɗakar da al’umma don
kawo wani sauyi ga duk wani yunƙuri na yaɗa wata manufa. Farfaganda tana nufin
yaɗa labarai na gaskiya ko ƙarya don a samu tasiri ga tunanin mutane.
Haka kuma, Zainab (2013)
ta bayyana yadda su Dambo (1999) da Jumare (2007) da Hassan (2011) da Mannura
(2008) suka kalli farfaganda. Dambo (1999) ya nuna yadda kalmar ta samo asali
daga Ingilishi. A cikin ƙamusun Encyclopedia Britannica (1966:390)’,
Kalmar tana nuna cewa, wata hanya ce ta baza labari, wannan labari na iya
tabbata gaskiya ko abin taƙaddama ko jita-jita, ko mai alamun ƙamshin gaskiya
ko ya zamana ƙarya ce tsabarta domin jawo hankula ko ra’ayin jama’a. Dambo
(1999) ya ci gaba da cewa, “Amma ƙamus na ‘International Encyclopedia of Social
Sciences (1968:583)’ an nuna ma’anar kalmar farfaganda da cewa, sassauƙar hanya
ce ta yin amfani da wasu fitattun alamomi, wato kamar irin maganganun bebaye ko
tuta ko mutum-mutumi na wani abu ko kaɗe-kaɗe ko waƙe-waƙe da sauransu. A nasa
ra’ayin cewa ya yi, farfaganda hanya ce ta baza ra’ayi domin lallashi da jawo
hankalin jama’a da nufin isar da wani sabon tunani zuwa ga wani ra’ayi ko
tunani nata, da a da ta riga ta runguma, kuma ake son yanzu a karɓi sabon abin
da aka zo da shi. Jumare (2007) ya nuna farfaganda da cewa, “Hanya ce ta jawo
hankalin jama’a domin yin na’am da wani sabon abu ko kuma samun ƙarin karɓuwa
ga wani abu da dama can aka sani ko kuma nuna ƙyama ga wani abu.” Hassan (2011)
kuwa cewa ya yi, “Farfaganda tana nufin yaɗa manufofi ko tallata haja da
muradin wata al’umma ko ƙasa ko tsari na siyasa ko tattalin arziƙi ko tallata
wata haja da nufin sauya tunanin al’umma ko karkato da hankalinsu zuwa ga abin
da ake yaɗawa ko tallatawa.”
3.1 Yanayin Siyasa da
Tsaro a Cikin Wasu Waƙoƙin Farfaganda
Siyasa tana ɗaya daga cikin sha’anonin da mutane
suke yi wa hidima sosai. Domin kuwa, tana da matsayi da muhimmancin gaske ga
rayuwar al’umma. Siyasa tana da matsayi mai girma ga kowace al’umma, saboda
irin wannan matsayi nata, sai mutane suka riƙa yi mata hidima iri-iri. Daga
cikin hidimomin da ake yi wa siyasa a ƙasar Hausa akwai waƙa, wadda za a iya
cewa, ta fi yin tasiri ga jama’a, ganin yadda take ɗauke da manufofi kala-kala.
Waƙa tana da muhimmanci sosai a fagen siyasa, don alfanunta da tasirinta ba zai
misaltu ba, domin wata hanya ce ta isar da saƙo cikin sauƙi, mutane sukan zaɓe
ta domin cimma burinsu na ilmantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa da sauran
makamantansu. Bayan haka, mawaƙan sukan yi ƙoƙarin jawo hankalin jama’a ta
hanyar yin amfani da ɓangaranci, wani lokacin ma da addini domin cimma buƙata
ta farfaganda. Kusan za a iya cewa, waƙoƙin kacokan don ‘yan Arewa aka yi su,
duk da kasancewa mawaƙan kansu ‘yan Arewa ne, akwai gugguɓin manufar nuna
ɓangaranci a waƙoƙin da nuna kishin kai. Kusan duk abin da mawaƙan suke faɗa,
Arewa suka fi shafa, a Arewa aka fi yin su ko ma a ce ‘yan Arewa ake yi wa su.
A wannan bagire, an yi nazarin irin waɗannan
waƙoƙi ne, don a ji ta bakin mawaƙa a kan yanayin siyasa da tsaro da Arewa da
ma Nijeriya gaba ɗaya suke ciki. An zaɓi mawaƙa guda biyu, Aminu Ladan Abubakar
(Alan Waƙa) da Jibrin Jalatu. An zaɓi waƙoƙin Aminu ALA guda uku ‘Baubawan
Burmi’ da ‘Bubukuwa’ da ‘Ɗaurin Gwarmai’. An zaɓi
waƙoƙin Jibrin Jalatu guda biyu. Wato waƙar ‘Mafarkin Mulki I’ da ‘Mafarkin
Mulki II’.
Waƙar ‘Baubawan Burmi’ ta
Aminu ALA, tana daga cikin waƙoƙin siyasa na farfaganda, don waƙa ce da aka yi
da nufin yaɗa wata manufa zuwa ga al’umma kan yanayin yadda ake aiwatar da
mulki, wato ana mulki ba a kan tsarin da ya dace ba. Waƙar ta yi ƙoƙarin
faɗakar da jama’a illolin shuwagabannin da suka zaɓa, tare da fito da aibu da
sauran halayyar mahukunta a yayin gudanar da mulki. Waƙar ‘Bubukuwa’
ita Aminu ALA ya yi ta. Kuma waƙa ce ta farfaganda da ke bayyana wa
al’umma abubuwan da ke faruwa a cikin ƙasa. Waƙar ta fito da hoton siyasar
Nijeriya, da nuna yadda shuwagabanni ba su aiki yadda ya dace. Kuma ya taɓo
dukkan rukunonin al’umma, tun daga shuwagabanni, malamai, attajirai da
sauransu, ya nuna manufarsa, da nufin cewa, idan sun gyara, sauran al’umma za
ta gyaru. Ya yi ƙoƙarin baza ra’ayinsa ga al’umma maza da mata, yara da manya
da sauran waɗanda abin ya shafa kan sha’anin mulkin dimokraɗiyyar da ake yi a
Nijeriya. Waƙar ‘Ɗaurin Gwarmai’ ta Aminu ALA, ita ma waƙa ce ta
farfaganda da aka yi da nufin sauya tunanin jama’a don su zama masu kishin
kansu, kuma su zama masu tunani idan sun tashi zaɓen shugaba. Wanda rashin
shuwagabanni adalai ya saka ‘yan Nijeriya halin da ake ciki a yanzu, shi ne ya
siffanta halin da ake ciki da ɗaurin gwarmai. Ya yi farfaganda ƙwarai, yana mai
baza hikimominsa da nufin jan hankalin al’umma baki ɗaya.
Waƙar ‘Mafarkin Mulki
I’ ta Jibrin Jalatu, wannan waƙa tana ɗaya daga cikin waƙoƙin
farfaganda ta siyasa da aka yi a zamanin nan. Mawaƙin ya suranta yanayin
shuwagabanni da yadda suke tafiyar da mulkin jama’a. Ya bayyana abubuwan da ke
faruwa na rashin adalci da zalunci. Ya suranta mulkin Nijeriya tun daga lokacin
samun mulkin, har zuwa lokacin da zai ƙare. Ya kuma zayyana abin da ke gudana
tsakanin mahukuntan da mabiyansu, da kuma abin da ke wakana tsakanin mahukuntan
da sauran muƙarrabansu. Ya jaddada yadda mahukunta suke cin karensu babu
babbaka, da sauran abin da ya shafi siyasar ƙasa na zahiri.
Waƙar ‘Mafarkin Mulki
II’ ta Jibrin Jalatu, kamar waƙar da ta gabata, a wannan ma, mawaƙin
ya yi nazarin siyasar Nijeriya gaba ɗaya, inda ya bayyana shi a cikin waƙar.
Kamar yadda ya nuna, wannan waƙar, ci gaba ne daga cikin waƙar ‘Mafarkin
Mulki I’. Ke nan, ya suranta siyasar Nijeriya da yadda ake
aiwatar da zango-zango na mulki, wato zango na ɗaya da na biyu. A cikinta ya
ayyana matsalolin da ‘yan Nijeriya suke fuskanta, tare da bayyana manyan
buƙatun da suke mafarkin samu, domin kuwa, kowane shugaba ya hau, da irin yadda
yake tafiyar da jagorancin al’umma. Ya zayyana halin ko-in-kula da mahukunta
syke nunawa a kan dukkan sha’anin mulki. Bayana haka, a cikin waƙar ‘Baubawan
Burmi’ ta Aminu ALA kuwa, mawaƙin ya yi maganar siyasar Nijeriya
dangane da yadda ake gudanar da ita, shi ne ya nuna cewa, ai gara ma lokacin
mulkin mallaka, da irin nau’in mulkin da ke wakana a yanzu. Tun da a wancan
lokacin, jama’a ba su jigata ba, kamar yanzu. Domin kuwa, yanzu talauci ya yi
wa jama’a katutu, abin dai ba a cewa komai. Da ma can, Hausawa sun ce ‘Kowat
tuna bara, bai ji daɗin bana ba’.
“Dangi a duba mini hanya,
Da can da muna a mulkin mallaka.”
“Wahala dai aka ba bawa,
Amma duk tsiya abinci a ba ka.”
“Yanzu ko gadonmu talauci,
Ai kuɗarsa ta fi dukanka da gora.”
A waƙarsa ta ‘Bubukuwa’ kuwa,
sai ya nuna cewa duk yanayin da Nijeriya da mutanenta suke ciki, mahukunta suka
haddasa hakan. Ƙasa ta rikice, komai a yamutse, babu cikakken tsaro, sata a
ko’ina yin ta ake yi, babu wani tsari na a zo a gani a Nijeriya. Su
shuwagabannin ba su da tausayi, aljihunsu kawai suka sani, sai wanda suke so.
Talauci ya yi yawa, babu aikin yi, irin haka ne yake haddasa gurɓacewar al’ada.
“Ɓarayinmu a kan ƙasa, Atifishiyal muka
ƙirƙiro,
‘Yan dabarmu a ko’ina, Atifishiyal muka
ƙirƙiro,
Masu 419 Arewa, na ƙirƙira aka ƙirƙiro,
Wahalar da muke ciki, ita tas sa suka bijjiro,
Na rashin shuwagabanni Adalai, da rashin
tsaro,
Rayukanmu kamar kiyashi, fagen kulawa ba
tsaro,
Rabbi Kai Ne, Rahimi, tsare ƙasar Nijeriya.”
Haka kuma, Aminu ALA, a
waƙar ‘Ɗaurin Gwarmai’, ya kai kokensa zuwa ga Allah SWT a kan abin da
yake gudana a ƙasa, da nufin Allah ya amsa, Ya kuma kawo canji mai amfani.
Mawaƙan zamani suna ƙoƙari ta amfani da ayyukansu na adabi wajen ganin an samu
sauyi a siyasar Nijeriya. Shi ya sa waƙa take zama wani makami na canza
al’amuran yau da kullum.
“Ubangiji har kullum Kai nake kai wa kukana,
Mai yaye haddi, gambi na taho da buƙatuna,
Abin da ake a ƙasar nan ya ɗugunzuma
tunanina,
Zan faɗi da baɗala, an ce da ni na iya
bakina.”
ALA ya ci gaba da kiran
Ubangiji, yana nuna halin da ake ciki, abin na buƙatar taimako. Yana suranta
halin da mutanen Nijeriya suke ciki, da kuma yadda ake tafiyar da mulkinsu bisa
gadara.
“Allah mun yi zaman dirshan,
Tamkar fitila a lokon alkuki”.
“Sai a kaɗa mu a raurayar,
Allah namu na buƙatar jagora, iye-iye”.
Shi kuwa Jibrin Jalatu a
waƙarsa mai suna Mafarkin Mulki I, ya yi magana zuwa ga muƙarraban
ƙasa da sauran sarakuna da makamantansu, yana nuna yadda ake ba su cin hanci,
idan ana so su bi wani tsari na musamman wanda gwamnati take so, su amsa, su yi
shiru. Sai ya nuna wani lokaci a kan tilasta su, da su yi hakan.
“Manya
iyayen ƙasa, su ma na ɓata lamarinsu,
Su za su
zo gabana, a da fa ni za ni je gabansu,
Ina faɗi,
ina tashi, har ina Allah taimake su,
Sai na
sakwarkwata su, na karya ƙwarin da ke gurinsu,
Idan na
zo da tsari suka ƙi bi, zan gina asusu,
Baho-bahon
kuɗi zan tattara in kai gabansu,
Wallahi
za su bi ni, daga ƙarshe su shiga uƙuba.”
Aminu ALA a waƙarsa ta ‘Baubawan Burmi’,
ya ƙara bayyana irin halin da mutanen Nijeriya suke ciki, ya nuna cewa talauci
ya yi yawa, babu wadatar kirki, jama’a a ƙuntace suke, a kuma wahalce. Wato
dai, an zama mabarata a wajen shuwagabanni.
“Talauci
shi muka gado,
Jahilci
ko ya zamanto rigarmu.”
“Ba mu da ikon yin mulki,
Balle mu
ciro masharin kukanmu.”
“Mun ɗore da tumasanci,
Mabarata muke a hannun jagora.”
Bai gushe ba, sai da ya
siffanta nau’in mulkin Nijeriya, da wata siffa ta rashin adalci, zalunci da
ƙuntatawa na danne haƙƙin talaka, tare da nuna cewa mahukuntan dai kansu kawai
suka sani.
“Allah wanga kashin mulki,
Ya yi kama guda kashin dankali.”
“Na sama ya danne na ƙasa,
Idan ya so numfashi babu dalili.”
“Jin daɗinsu kawunansu,
Alfarmarsu iyalensu suna kibra.”
Shi kuwa Jibrin Jalatu a
waƙarsa mai suna Mafarkin Mulki I, ya yi magana zuwa ga muƙarraban
ƙasa da sauran sarakuna da makamantansu, yana nuna yadda ake ba su cin hanci,
idan ana so su bi wani tsari na musamman wanda gwamnati ke so, su amsa, su yi
shiru. Sai ya nuna wani lokaci a kan tilasta su, da su yi hakan.
“Manya
iyayen ƙasa, su ma na ɓata lamarinsu,
Su za su
zo gabana, a da fa ni za ni je gabansu,
Ina faɗi,
ina tashi, har ina Allah taimake su,
Sai na
sakwarkwata su, na karya ƙwarin da ke gurinsu,
Idan na
zo da tsari suka ƙi bi, zan gina asusu,
Baho-bahon
kuɗi zan tattara in kai gabansu,
Wallahi
za su bi ni, daga ƙarshe su shiga uƙuba.”
A waƙar Mafarkin
Mulki II ta Jibrin Jalatu, ya ragargaji siyasar Nijeriya, ya kawo
buƙatun da ‘yan Nijeriya suke fatan su ga sun samu, kamar adalci, a kyautata
tsaro da sauran abin da ya shafi rayuwar jama’a, sai matsaloli wanɗanda rashin
adalci da rashin gaskiya suke haddasawa.
“Suka ce gaskiya, na ce ba zan ba,
Suka ce taimako, na ce ku tafi gaba,
Suka ce yunwa, na ce ba ku mutu ba,
Suka ce tsaro, na ce ba ku gaji ba,
Kama-karya na sanya a gaba,
Kama-karya na sanya a gaba,
Ba ku wanda za ya ture ni a kan mulki.”
A waƙar Mafarkin
Mulki I, Jibrin Jalatu ya yi magana a kan matsalar tsaro da kuma bayyana
halin mahukuntan Nijeriya, ya nuna cewa, ba su dai yin daidai, wato ba a
tafiyar da mulkin yadda ya dace. Sannan ya fito da hali na zalunci da kwaɗayi
na shuwagabanni. Ya bayyana yadda suke sha’ani da matan banza, da yadda ake ci
wa ƙasa bashin da ya fi ƙarfinta, kuma ba a damu da haƙƙin jama’a ba.
“Tsaro a zamanina a kashe kowa a kan abinshi,
Ni na ci, na yi ɗaɗin, na kwanta ina ta nishi,
Saboda taƙamata, ba mai cewa da ni ka tashi,
Ka ji wahalallu, wai in wa ƙasarmu kishi,
Wata karuwa ta ce ban kurɗi in gyara gashi,
Ko ɗan ten miliyan of dolas, ku kuna uƙuba.”
Daga nan, sai ya karkata
zuwa ga shuwagabannin addinai, na Musulmai da na Kiristan duka, ya nuna yadda
suka shiga siyasa dumu-dumu, da kuma nuna yadda ake amfani da su ana cutar
talaka, wato yadda suke fakewa a inuwar addini, su yi yadda bai kamata ba. Ya
bayyana yadda ake ba su cin hanci don toshiyar baki.
“Casa’in cikin ɗari na shugaban addinai na
riƙe su,
Ya kamata shuwagabannin addinai a je gida a gan
su,
Yanzu
wasu shuwagabannin addinai kwaɗayi gare su,
Idan ka kama mulki na zamani, yanzu za ka gan
su,
Talaka na ta ihu, wai me za na taimake su,
Ina da iyayen ƙasa, da mahukunta da ke wurinsu,
Babu yadda za ku yi, ƙarshe ku shiga azaba.”
Mawaƙin ya ci gaba da farfagandarsa, yana
bayyana dalilan da suka sa ya rubuta wannan waƙa, wato ya duba ya ga
shuwagabanni ba su tafiyar da mulkin yadda ya kamata, wato sun kauce hanya, sun
bi son zuciya, inda ya zayyano irin waɗannan shugabanni, kamar Kansila,
Gwamnoni, Kwamishinoni, Ciyamomi da sauransu. Da haka ne ma, ya nuna cewa, ai
ɓarayi iri-iri ne, sata ma ana yin ta, ta kowace hanya.
“Abin da ya sa ni tunzuri, na ɗora tsuwa cikin
dare,
Na kasa bacci cikin dare, ina wasi-wasi na
fanɗare,
Batun hukunci nai nazari, da shi ya ka ƙagi
falken dare,
Masu mulki daga Kansila, ‘Yan-majalisa sun
fanɗare,
Kwamishinoni, Ciyamomi, ga Gwamnoni sun
fanɗare,
In suka saci haƙƙin jama’a, babu hukunci
gare-gare,
Lallai ɓarayi suna suka tara, an yi gudu da ba
wurin zuwa.”
Jibrin Jalatu, a waƙarsa
mai suna Mafarkin Mulki II, ya bayyana irin yadda mahukunta
suke ƙoƙarin lalata mulkin ƙasa gaba ɗaya, dukiyar ba a tafi da ita yadda ya
dace, sai dai su kwashe, su wadata kansu, da wanda suke so. Wato, fito da yadda
suke ƙoƙarin ɓata komai, da ma kashe ƙasar baki ɗaya. Ya zayyana ƙuncin da ‘yan
Nijeriya ke fuskanta, don rashin adalai.
“Nai masu tarnaƙin baƙar wahalata,
Duka ƙasa na barbazo matsalata,
Ƙadarar ‘yan ƙasarmu na sace ta,
Makarantun ƙasarmu na lalata,
Burina kawai ƙasa na kashe ta,
Burina kawai ƙasa na kashe ta,
Sai mai cuta da zamba, zan ba mulki.”
Sai ya ci gaba da Magana
a kan buƙatun ‘yan Nijeriya na neman shugabanni nagari, adalai, masu gaskiya da
riƙon amana, waɗanda za su yi kishin ƙasa, su kuma kamanta adalci, amma hakan
ba ta samu ba. Sai waɗanda ba su cancanta ba, su ne su ke mulkin jama’a.
“Suka ce tausayi, na ce ba mu gamu ba,
Suka ce jinƙai, na ce ba mu haɗu ba,
Kuma kishin ƙasa, ba za ai ba,
Mulkin gaskiya, na ce ba zan ba,
Kuma mai gaskiya, ba zai hau ba,
Kuma mai gaskiya, ba zai hau ba,
Sai marar gaskiya nake miƙa wa mulki.”
A waƙar Mafarkin
Mulki I, ya zayyana yadda shuwagabannin suke damawa, ta yadda duk wani
muƙami ko wani mataki na mulki su ke zaɓar wanda suke so, su ba shi ko da kuwa
bai cancanta ba. Sukan yi hakan kuwa domin jin daɗinsu da kuma samun damar
handama da babakere. Duk wanda suka bai wa wani muƙami, ba zai ƙi bin ra’ayinsu
ba, idan ma ya saɓa, sai a karɓe daga hannunsa a bai wa wani. Don haka, duk
wani mai faɗa-a-ji da ke riƙe da wani babban muƙami, za a tarar akwai ra’ayin
gwamnati a ciki. Watau dai a nan, an nuna yadda ake kashe-mu-raba tsakanin
shuwagabanni da mataimakansu.
“Na zamo kamar ɗakin kura sai dai na jikina,
Ministan tsaro, ni zan naɗa da kaina,
Ministan ilmi da lafiya, zan sa na wurina,
Ministan kuɗi, ni ne zan naɗa abuna,
Ministan sufurin jiragen sama, yana wurina,
Ministan ruwa shi ma, ni zan naɗa da kaina,
Idan na sanya doka, kowanensu kar ya saɓa.”
4.0 Kammalawa
Mawaƙan zamani suna duba
da yanayin zamani sai su rera waƙoƙinsu masu cike da hikima da jan hankali, har
ma da daɗin sauraro. Adiban sukan baje hikimominsu da kaifin tunani su tsara
waƙoƙi a kan matsalolin al’ummar da suke zagaye da su. Waƙoƙin suna nufin sauya
salon tsarin mulkin da ake gudanarwa zuwa tsarin da ya dace da al’umma. Shi ya
sa waƙa ta zama wani makami na canza ɗabi’un jama’a. An ji yadda mawaƙan suka
bayyana matsalar siyasa da tsaro a ƙasa.
Manazarta
Abba, A. (2000). The Significance of The
Northern Element Progressiɓe Union, (NEPU) in the Politics of Nigeria:
1950-1960. PhD Dessertation. Department of History, Ahmadu Bello University,
Zaria.
Aliyu, S. (2018). Hanyoyin Tsaro na Gargajiya da
Zamani a Jihar Katsina. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya.
Jami’ar Umaru Musa Yaradua, Katsina.
Aliyu, S. (2024). Gargajiyar Tsaro A Hausa:
Nazari a kan Muhimmancin da Illolon Ƙungiyoyi Tsaro na Sa-Kai a Wasu Sassa na
Jihar Katsina. Takardar Neman Amincewa Domin Gudanar Da Bincike Don Samun
Digiri Na Uku. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,, Jamia’r Umaru Musa Yaradua,
Katsina, Katsina.
Amin, M.L. (1992). Poetry and Political
Ideology: A Glimpse at Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya of Sa’adu Zungur. A Seminar
Paper Presented at Nigerian and African Languages. Ahmadu Bello University,
Zaria.
Amin, M. L. (1993). Ra’ayin Sauyi a Waƙoƙin
Sa’adu Zungur. Dandalin Hikima 2 Mujallar Ƙungiyar Marubuta da
Manazarta Waƙoƙin Hausa Ta Tarayya.
Amin, M. L. (2001). The
Political Ideology of Sa’adu Zungur as Potrayed in Arewa Jumhuriya
Ko Mulukiya. Nigerian Educational Forum
Journal of The Institute of Education. No 1, Vol. 17. Ahmadu
Bello University, Zaria.
Amin, M. L. (2004). Radicalism In the Poetry of
Sa’adu Zungur. Journal of Arts and Humanities. No 1, Vol.1.
International Research and Development Institute.
Auta, A.L. (2008). Rubutattun Waƙoƙin Hausa na
Faɗakarwa a Ƙarni na Ashirin. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Baba, H. (2007). “Haruna Aliyu Ningi da
Waƙoƙinsa” Kundin Digiri na Ɗaya. Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Baban Zara, M. H. (2010). Short Biographies of
Selected Hausa Political Poets. FAIS Journal
of Humanities. No.1. Vol.4. Bayero University, Kano.
Bunza, A.M. (2017).
Ƙunar Baƙin Wake: Ƙalubalen Tsaron Ƙarninmu: Duba Cikin Tunanin
Bahaushe. Nigeria In Search of Stability,
Relevance, Language and Religion. Faculty of Arts and Islamic Studies. Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto.
Bello, A.S. (2009). Nazarin Waƙar Baubawan Burmi
ta Aminu Ladan Abubakar (ALA). Takarda da Aka Gabatar A Wurin Taron Ƙarawa Juna
Ilmi na Tsangayar Harsuna. Kwalejin Ilmi ta Tarayya, Zaria.
Bello, A.S. (2011). Gudunmuwar Adabin Hausa A
Fagen Cigaban Siyasa Da Tabbatar da Dimokraɗiyya a Najeriya: Nazarin Waƙar
‘Dimokraɗiyya Ta Aminu Ala. Takardar da Aka Gabatar A Taron Ƙarawa Juna Ilmi Na
Tsangayar Harsuna. Kwalejin Ilmi Ta Tarayya, Zaria.
Binta Salma, S. M. (1997). The Language of
Poetry: A Stylistic Study of Selected Poems Of
Soyinka and Osundare. M.A Thesis. Department Of
English and European Languages, Bayero University, Kano.
Birniwa, A. H. (1987).
Conservatism and Dissent: A Comparative Study of NPC/NPN and
NEPU/PRP Hausa Political Verse from Circa
1946-1983. Kundin Digiri na Uku. Jami’ar Usman Ɗanfodio, Sokoto.
Dambo, J. B. (1999). Farfaganda A Cikin
Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Hausa Studies. No.1, Vol.1. Department Of
Nigerian Languages, Usman Ɗanfodio, University, Sokoto.
Ɗangambo, A.
(2008). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari). Amana
Publishers Limited,
Zaria.
Ɗangulbi, A. R. (2003)
Siyasa A Nijeriya: Gudunmuwar Marubuta Waƙoƙin Siyasa Na Hausa
Ga Kafa Dimokraɗiyya a Jumhuriya ta Huɗu Zango
na Farko. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman
Ɗanfodio, Sokoto.
Ɗan’illela, A. (2010).
Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Nazari A Kan Jihohin Sakkwato Da Kebbi da Kuma
Zamfara. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman
Ɗanfodio, Sokoto.
Ɗan’asabe, K.M da Wasu,
(2008). Muhimmancin Mawaƙa Ga Cigaban Siyasar Nijeriya:
Tasirin Waƙar “Ba Mu Yarda Ta Zarce Ba”. Zaria
Journal of Linguistics and Literary Studies. No.1 Vol .2.
Zaria.
Ɗanƙwari, M. L. (2000).
Ethics In Hausa Poetic Tradition: A Historical Survey. Kundin Digiri
Na Biyu. Sashen
Harsunan Nijeriya da Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Funtua, A. I. (2003). Waƙoƙin Siyasa Na Hausa a
Jumhuriya ta Uku: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Funtua, A.I. (2011). Manufar Waƙa a Siyasa:
Ire-Iren Jigogin Waƙoƙin Siyasa na Hausa.
Algaita Journal of Current Research In Hausa
Studies Vol. 2 No. 1. Sashen Harsunan Nijeriya.
Jami’ar Bayero, Kano.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A
Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited,
Kano.
Imran, A.L. (2008). Jigo Da Salon Waƙoƙin Aminu
ALA. Kundin Digiri Na Ɗaya. Sashen Harunan Nijeriya Da Afirka, Jami’ar Ahmadu
Bello, Zaria.
Jumare, M. S. (2007). Tasirin Farfaganda A
Tallar ‘Yan Siyasa. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya Da Afirka,
Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Katsina, Et al (2022). Arming The Unarmed for
Security in Katsina State: A Study into The
Vigilante Group of Nigeria (VGN). A Paper
Presnted at the Conference on Security Organised to Celebrate the Turbaning of
Ahmad Rufa’i as the Sardaunan Katsina, Katsina.
Ƙanƙara, I.S. (2016). Impedements to Nigerian
Democracy: Anbivalent Role Vigilante Group in Maintaining Security in the wake
of the Boko Haram Insurgence in Northern Nigeria 2009-2015. A Seminar Paper
Presented at The Department of History and Security Studies. Faculty of
Humanities, Umaru Musa Yaradua Unuiversity, Katsina.
Lasswell, H.D. (1977). On Political
Sociology. University of Chicago Press, Chicago.
Lubabatu, M. (2007). Waƙoƙin Siyasa Na ANPP’.
Kundin Digiri Na Ɗaya. Sashen Harsunan NjieriyA Da Afirka, Jami’ar Ahmadu
Bello, Zaria.
Mannura, U. (2008). Farfaganda A Wasan
Kwaikwayon Rediyo. Kundin Digiri Na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya Da Afirka,
Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Mashi, M. B. (1986). Waƙoƙin Baka Na Siyasa:
Dalilinsu Da Tasirinsu Ga Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Koyar
Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Muhammad, D. Y. (2003). Ginuwar Salo A Waƙoƙin
Musulunci Na Hausa Daga Ƙarni Na 17 Zuwa Na 20. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Musa, I. I. (2007). Nazarin Yabo Da Zambo A
Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Na Haruna Aliyu Ningi. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Tsoho, M.Y. (2013) Adabi Da Harkokin Siyasa:
Bijirewa A Waƙar Shegiyar-Uwa Mai Kashe ‘Ya’Yanta PDP Ta Haruna Aliyu Ningi.
Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Ƙasa Na Farko Kan Harshe da Adabi da Al’adu.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Wurma, A. G. (1999). Waƙa Rubutacciya: Muhimman
Hanyoyin Nazarinta da Abubuwan da ke Ɓata ta. Jakadiya: A Journal of
Researches in African Languages and Literature No.1 Vol.1 Department
of Nigerian and African Languages. Ahmadu Bello University, Zaria.
Wurma, A. G. (2008) Kalma Ɗaya Ma’ana
Tuli. Algaita: Journal of Current Researches in Hausa Studies. Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero, Kano.
Yahaya, (2000). Sharhi A Kan Rubutattun Waƙoƙin
PDP. Kundin Digiri Na Ɗaya. Jami’ar
Ahmadu Bello, Zaria.
Yahaya, I.Y. (1988). Hausa
A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC, Zaria.
Zainab, I. (2013) Gudunmuwar Mawaƙan Hausa ga
Cigaban Arewacin Nijeriya: Nazarin Waƙar ‘Ajanda’ ta Haruna Aliyu Ningi. Muƙala
da aka Gabatar a Taron Ƙasa na Farko a kan Harshe, Adabi da Al’ada. Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Zainab, I. (2013). Farfaganda A Waƙoƙin Fiyano
Na Hausa 2003-2013. Kudin Digiri na Biyu.
Sashen Harsuna Nijeriya da Afirka. Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.