Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’aziyyar Sambo Wali Gidadawa

Article Citation: Bunza, M.B. (2025). Ta’aziyyar Sambo Wali Giɗaɗawa. Zauren Waƙa, 4(2), 66-68.

TA’AZIYYAR SAMBO WALI GIƊAƊAWA

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Gabatarwa

Alhaji Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa fitaccen malami ne, fitaccen marubuci, kuma masanin tarihin ƙasar Hausa da Daular Sakkwato. A cikin Ƙungiyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa su ne dattawan marubuta. Ya yi koyarwa a firamare da ɓangaren Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Ya yi wa Gidan Rediyon Rima Sakkwato gudummuwa gawurtacciya da ko’ina an ji ta. A fannin wasanni da faɗakarwa, Malam Sambo ya yi gudunmuwa sosai. A ɗan nawa bincike, cikin manazartan zamaninmu babu wanda ya kai Malam Sambo sanin tarihin ƙasar Hausa ta Gobir da Daular Sakkwato. Don haka nake ganin ko bayan rasuwarsa, ya kamata Jami’ar Sakkwato ta ba shi yabo da digirin Girmamawa (Dr.). Allah ya gafarta wa Malam Sambo Wali Giɗɗawa. Amin.

Ta’aziyyar Sambo Wali Giɗaɗawa

1. Bismillahi Allah Gwani mai ƙaddarowa

2. Mahalicci maƙagi da ba wani mai hanawa

3. Kai ka yi duniya halittun ciki ba musawa,

4. Kay yo annabawa da saƙon don isarwa,

5. Komai sun ka ce, Kai ka ce haka tabbatarwa

6. Kai ka yi duniyar maus rai kafin macewa,

7. In mutuwa ta riske mu duk ƙasa za mu yowa,

8. Ko a rufe mu, ko dunƙulewa sai ruɓewa,

9. Kowa nashi lokaci yaz zo bai wucewa,

10. Ko tsufa walau ƙaddaron ciwon tuƙewa.

11. Ko wata ƙaddara wadda ba bagiren laɓewa.

12. Allah ka jarabce mu mun yi rashin rasawa,

13. Sambo Wali masoyinmu Malam mai kulawa,

14. Dattijon Giɗaɗawa mai ƙwazon kulawa

15. Da maƙwabta da yanuwa Sambo yake ganewa.

16. Manya, yara in yai kira ba mai ƙiyawa,

17. Muryatai ka jawo taro ba a wucewa,

18. Wanda yake kusan Sambo ko ba mai ɗagawa,

19. Zai yi shiru ya soke kai nai ba ya ɗagawa

20. Wani waƙaci kamar hawayenmu su so fitowa.

21. Kan a jima haƙorannmu su ke ƙyalƙyacewa,

22. A yi kuka, a yo dariya a yi marmashewa,

23. Matuƙar ya isar da saƙonsa na tsawatarwa,

24. Dole ido ja zukata na ɗunguzowa,

25. Rai ya langaɓe tunanin ranar haɗewa,

26. Muryar Sambo tausai haƙiƙa da tsoratarwa.

27. Ya Allah Ka gafarci Sambo Waliyi nawa,

28. Sa shi cikin WaliyyanKa ya mai tausayawa,

29. Yafe kurakuran Sambo kaɗai ke iyawa.

30. Mun roƙe Ka Allah Gwani mai ƙaddarowa,

31. Sa muna Sambo Aljanna ɗakin wartsacewa,

32. Shi ji daɗin da kwancin da kwana bai tahowa,

33. Ya zamo saurayi babu harshe mai cirewa,

34. Dole ƙafarsa mai ɗingishi taka murmujewa

35. Ya fito tangaram ga tsawo ga girgijewa.

36. Roƙo ne mukai Jalla sarkin agazawa

37. Kai kac ce a roƙe Ka mun yi muna daɗawa

38. Ta’aziyya ta kowanmu ce ba mai ƙiyawa.

39. Malami Sambo sha’iri yai sa’ar macewa,

40. Ga tsufa ta kirki da shekarun ƙwarewa,

41. Kuma masani cikin malamai ba mai musawa

42. Sambo Bagimbanen ƙwarai ga ƙabilar Arewa,

43. Tanzanko sukai da yin adu’a ba gazawa.

44. Allah Kai ka yi, Kai ka yi, ba mai hanawa,

45. Kai ke gafara Kai ka ceto ba musawa,

46. Kai ke yafe duk zununbban da muke zubawa.

47. Sambo Wali muke son Ka ba bagirin shigewa,

48. Can Aljanna Firdausi mai daɗi daɗawa.

49. Ka yi mai ɗaukaka da’iman ciki bai fitowa.

50. Waƙoƙin Wali Taala shi ka ambatowa.

51. Daga nan sai salati ga Manzo sai daɗawa.

52. Ga sahabbai da Malamai don tsananin kulawa,

53. Yau ko Sambo an kai ga ƙarshe ba tsayawa

54. Wada yawwa gabacinmu yo mishi ba gazawa.

55. Ya Allah Ka ceci Sambo Gwani mai iyawa.

56. Ba shakka gado na ceto Kai ke azawa

57. In kac ceto Sambo bawa duk bai hanawa.

58. Allah ba shi Aljanna Firdausin tuƙewa.

59. Sa shi cikin mutanenKa masu yawan kulawa.

60. Nan Ɗanbunza zai tsaya taaziyyar cikawa

61. Sambo Wali Uban sha’irai ba mai hanawa.

62. Sunana Aliyu kai mai son bincikawa.

63. Babana Muhammad idan ka son cikawa.

64. Birnin Bunza Ungwar Malammai daɗawa.

65. Nan Birnin Masar nay yi ta’aziyyar cikawa.

Aliyu Muhammadu Bunza

A Birnin Masar, Ƙasar Egypt
7 ga watan Yuli, 2025

Post a Comment

0 Comments