Article Citation: Ibrahim, A.A. (2025). Rowa a Bakin Makaɗan Fada na Hausa. Zauren Waƙa, 4(2), 60-61. www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.007.
ROWA A BAKIN MAKAƊAN FADA NA HAUSA
Aminu Alhaji Ibrahim
Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari Sakkwato
TEL: 08062716148
Email: aminuibrahim7@gmail.com
Tsakure
Hausawa kan ce “Roƙi roƙaƙƙe ka ga baƙar
rowa” Rowa wata ɗabi’a ce mummuna da ke haifar da hasada da ƙiyayya da rashin jin ƙai a cikin al’umma. Wannan maƙala za ta dubi irin kallon hadarin Kaji da mawaƙa kan yi wa marowata, da ɗabi’un
da suke tantance marowata a yayin aiwatar da sana’arsu ta waƙa. Haka kuma maƙalar za ta yi tsokaci kan martanin da mawaƙan kan mayar wa marowata waɗanda
suke ganin tamkar ‘yan hana ruwa gudu ne. Daga ƙarshe za a ɗauraye da irin sakamakon da rowa ke
haifarwa.
1.0 Shimfiɗa
Makaɗan baka na Hausa tamkar Alƙalai
ne a tsarin zaman jama’a, ana yin amfani da waƙoƙinsu wajen yi wa al’umma gargaɗi, ko hani, ko
horo, bisa wannan akan sami waƙoƙin baka na Hausa da yawa, da suka yi ruwa suka yi tsaki,
wajen yabon al’umma da kyawawan ɗabi’unsu. A ɗayan ɓangaren kuwa, waƙoƙin baka na Hausa suna cike da zambo, da habaici, don
tsawatarwa, koi gargaɗi, ko hannunka mai sanda ga mutanen da suke bisa tafarki
na mummunar ɗabi’u
kamar ƙarya, da hasada da kuma rowa, da makamantansu. A cikin
wannan maƙala, an dubi yadda makaɗan fada suke kallon
marowaci da irin raddin da suke yi masa a cikin waƙoƙinsu. A cikin wannan maƙalar
za a dubi ire-iren rowa da kuma tubalan da suak gina rowa kamar da farmama.
Haka kuma duk cikin wannan maƙala an kawo
sakamakon yin rowa wanda idan ɗan sarki ya yi wa makaɗa rowa ga abin da
ke biyo wa baya na zambo da habaici. Daga ƙarshe,
za a fito da irin illolin da rowa take haddasawa a cikin tsarin zmaantakewan
al’umma.
1.1 Ma’anar Rowa
Bisa ga ra’ayoyin masana, ana iya cewa rowa na nufin
rashin yin kyauta da wani ɓangare, na abin da Allah ya hore wa mutum, na kɗi, ko abinci, ko
sutura, ko wani abin amfani (CNHN 2006). Bisa ga wannan ra’ayin za a iya gane
cewa duk wanda bai iya ɗibar wani abu cikin dukiyarsa ya yi kyauta da shi ya zama
marowaci.
Makaɗan baka ma sun bayyana rowa da wadda ke kallon ma’anata,
makaɗa
Alh. Musa Ɗankwairo Maradun ya bayyana muna ma’anar rowa cikin waƙar da ya yi wa Turakin Kano in da yake cewa:
Zaman duniya dadai haka yake
Ga wani ya ce bai buƙatarka
Bai iya ‘yamma abinai,
Ga wani can na murna ko za ya ganka,
Don ya sami abin da ya yi ma,
(Ɗankwairo: Turaki Ɗan
Hashim Jikan Dabo).
A nan idan aka dubi wannan ma’ana da makaɗa Musa Ɗankwairo ya bayyana, za a gano cewa, rowa dai, tana nufin ƙin ɗibar abin da Allah ya hore wa mutum, ya yi kyauta da shi.
Domin makaɗa
Ɗankwairo cewa ya yi wani ne wanda bai buƙatar ganinsa domin kada ya ɗan ɗibi wani abu daga
cikin aljihunsa ya bashi.
2.0 Ire-iren Rowa
Kamar kowane abu da ake yi ta hanyoyi daban-daban, ita ma
rowa ana yinta ta hanyoyi da dama daga cikinsu akwai rowar da ake yi kai tsaye,
akwai kuma wadda ake yi a faƙaice. Don haka idan
aka lura wannan maƙala za ta raba rowa gida biyu watoi rowa
kai tsaye da rowa a faƙaice kuma za a yi bayaninsu ɗaya bayan ɗaya.
2.1 Rowa Kai Tsaye
Rowa kai tsaye wani nau’in rowa ne da mutum kan roƙi wani mutum wani abin buƙata
wanda ya shafi kuɗi,
abinci ko kuma sutura ko ma wani abu da ake iya biyan buƙata
da shi, domin kuma sai wannan mutum da aka roƙa
sai ya ƙi bayar da abin da aka roƙe
shi kai tsaye ya ce baya bayarwa wannan rowar kai tsaye ce.
2.2 Rowa a Faƙaice
Rowa a faƙaice
rowa ce da mutum da ke yin ta, ba zai iya cewa wanda ya roƙe
shi wani abu ba zai bayar ba, sai dai ya ce masa ya je sai lokaci kaza kuma
idan lokacin ya yi ba zai gan shi ba, har ma in ya gan shi sai ya koma sanya
masa wani lokaci wanda ba zai same shi ba har dai wanda ya yi roƙon ya gaji da wannan jeka-da-dawo ya ƙyale
shi wannan nau’in rowar ita ce rowa a faƙaice.
3.0 Tubalan Ginin Nazarin Rowa
Masana sun bayyana tubali da
cewa wani curin ƙasa ne da ake yi ya
bushe don a yi gini da shi (CNHN Kano, 2006:440). Gusau (`999/2003:30) ya
bayyana tubali a cikin waƙar baka na nufin wasu
maganganu ne da aka ƙuƙƙula waƙa da su don ta ƙara tsawo amma ba su ne babbar manufar waƙa ba.
Ta
la’akari da waɗannan ma’anoni za a gano cewa, tubali curarriyar ƙasa ce karfi da ake yin gini da ita. Wato komai za a gina
dole sai an sami tubalin gini, wannan abin ya fara daga gini na gida. Da wannan
ake amfani da tubali wajen gina abubuwa da dama domin idan ba tubali to ba a
gini komai. Kuma duk wani abu da mutum zai yi sai ya nemi tubalin yinsa, domin
ya gina abin da yake son ginawa.
A
fagen nazarin waƙa, tubali na nufin ƙananan saƙonni
waɗanda za su yi nuni da a gano babban saƙon da waƙa
take ɗauke da su, domin isar da saƙon ga jama’a. Daga cikin tubalan da ake gina turken yabo sun
haɗa da ambaton addini da nasaba, iya mulki kyauta jarunta da
sauransu.
3.1 Ƙarya
Masana
sun bayyana ƙarya da cewa, duk
wata magana da mutum zai faɗa amma kuma ba yana nufin
gaskiya ba, to wannan ƙarya ce. Wato duk
wata magana ko aiki wanda mutum zai faɗa ko
zai aikata amma bayana nufin gaskiya da shi ba, to wannan ya zama ƙarya (CNHN, 2006:278).
Makaɗan
fada sukan bayyana wanda ya yi ƙarya
a cikin waƙoƙinsu, misali Alhaji Musa Ɗankwairo
a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin
Daura Muhammadu Bashar inda yake cewa:
Ɗan sarkin ga ya ɓakalce,
Ku ji yawo ya kai da ƙara.
(Ɗankwairo: Babban jigo Nayai Tura Haushi).
Idan
aka dubi wannan ɗan waƙa, za a ga cewa nakaɗa ya
bayyana wani ɗan sarkin Daura da yake yawo yana ta yin ƙarya duk in da ya zauna wanda kuma bai dace ɗan
sarki yana yin ƙarya ba, domin idan
ya sami sarauta da me za a dube shi da zamansa maƙaryaci, ko da zamansa na ɗan
sarki. Wannan ya nuna cewa, wannan ɗan
sarkin da makaɗa ya kawo cikin
wannan ɗan waƙa, ya yi masa rowa ne shi ne yasa
ya mai da shi maƙaryaci. A ƙarshen wannan ɗan waƙa makaɗa ya yi nasa nasiha da ya bar yin ƙarya.
Haka kuma makaɗa Ibrahim Narambaɗa, ya bayyana ƙarya, da kuma matsayin da
mutumin da ya kai, ya kamata mutum ya barta. A
cikin waƙar da ya yiwa Sarkin Gobir na Isa Alhaji Amadu Bawa Na II inda ya ke cewa:
Na wuce ƙarya ko ma kiɗi,
Na bar ƙarya ko ma kiɗi,
Nai sitin saba’in nika faɗa,
Mai saba’in yai ƙarya,
Ana fa zunɗe nai,
Ko yaran da ag garai,
Sun warwatse masa duka.
(Narambaɗa: Ka ci maza ya kwan yana shiri).
Idan aka
dubi wannan ɗan waƙa, za a ga makaɗa yana bayyana munin ƙarya ga mutum kamili wanda ya mallaki hankalinsa da iyalansa, wanda za
a iya sanya shi ya zamo jagora cikin kowane irin lamari. Amma idan yana yin ƙarya sai kaga mutanen Unguwarsu suna ƙyamar labarinsa sai
don a yi dariya kawai.
Hasalima ko gaskiya ya faɗa za a yi shakun wannan labarin da ya bayar. A cikin wata
waƙa kuma yana cewa:
Ka ga ɗan Sarki da kunnuwa da hwaɗi,
Ga ya da ƙarya ga shi da rowa,
Ko ka girmamashi ba ya sarki.
(Narambaɗa: Masu gari mazan gabas Tsayayye).
A nan makaɗa ya bayyana ɗan sarki mai rowa baya yin sarauta wato baya zama sarki, saboda ya faye
yin ƙarya kuma makaryaci baya da ƙima gun jama, don haka ko an naɗa shi jama’a za su
kyamace shi,ba don komai ba sai don rowarsa.
3.2. Fankama
Masana sun bayyana ma’anar fankama da cewa cika-baki da mutum ke yi wajen
magana, da nuna shi babba
ne ko kuma girman kai wanda mai yin waɗannan halayen yana tare da yin dana-sani cikin al’amarinsa. (CNHN 2006:133).
Makaɗan fada na amfani, da wanan kalma domin su bayyana wa
jama’a ɗan
sarki, ko fadawan sarki ko wani mai riƙe da wani mukami
cikin gidan sarauta cewa, marowaci ne sai taƙamar
banza da yake yi. Makaɗa Salihu Jankiɗi ya kawo irin wannan ɗan waƙa, cikin waƙar da ya yiwa
sarkin Musulmi Abubakar na Uku inda yake cewa:
Kutun-kusheri
a bas son zati,
Ga takama ba ko sisin kwabo,
Kadangaren hantsi ɗai za shi sha.
(Jankiɗi: Bubakar Ɗanshehu Bakadire).
Idan aka dubi wannan ɗlan waƙa, za a gano makaɗa ya
na magana a kan wani muturn wanda
ke yi musu taƙamar banza, ya nuna
shi mai wadata ne amma kuma baya da ko sisin
kwabo. A nan kuma yana ta
nuna shi wani babban mutum mai wadata ne, amma kuma ba ya iya baiwa kowa komi saboda rowar da yake dai ta.
Mai kama da ƙari mun gane,
Bamu san heshi ga fankama,
Wanda ya yi shifka
bisa kan fako,
Baya samun
komi kun sani,
Waɗanga aikin banza na
sukai
(Kankiɗi: Bubakar Ɗanshe Baƙadire).
A nan makaɗa Salihu Jankiɗi ya ƙara kawo muna wani misali, inda bayyana mutum mai fankama, wanda ke
nuna shi mai samu ne, amma kuma ba samun, ko kuma ba ta iya yin kyauta da abinsa, sai ya zamo bai da abin ko kuma
baya iya yin kyauta ko sisin kwabo. Haka makaɗa ya ƙara bamu misali da mutumin da ya shibka bisa dutsi wanda
zai wahala wurin yin noman amma kuma ba zai sami wani abin kwarai ba. Domin
murin da ya yi shabkar ba wurind shibke
ko jin daɗi ba ne.
Alhaji Musa Ɗankwairo ya kawo irin wannan
ɗan waƙa cikin waƙar da ya yi wa ‘yan
Doton Tsafe in da yake cewa:
Ganin hanya ab baida un hwani,
In ka zo garai baka more mai,
Na rna burodi mai kumburin banza,
Na saye na gani bai yi abki ba,
Burodi mun gane cikinka iska ne.
(Ɗanƙwairo: shirya kayan faɗa mai gida Tsafe).
A cikin wannan ɗan waƙa, makaɗa Musa
Ɗanƙwairo
yana ƙoƙarin ya bayyana wa al’umma cewa, ganin mutum daga nesa ba zai sa ka iya gano mai kyauta ne, ko kuma marowaci ne. wannan ta sa makaɗa ya bayyana ganin
mutum ga hanya ba zaka
iya gane halinsa sai ka zauna da shi, sa’annan za ka gano halinsa. Makaɗa ya kamanta mutum mai fankama da burodi wanda za ka saya yana kato amma da ka matse shi zai koma ɗan tsino. Don haka girmansa
ya zamo na banza.
A wani wuri kuma duk cikin wannan waƙa makaɗa ya ƙara mana wani misali inda ya ke cewa:
Gawani ɗan sarki da bakar rowa
Ko ka kwana salatil-fatih,
Ba ka hidda taro ga hannunai.
(Ɗankwairo: shirya kayan faɗa).
A nan makaɗa ya
bayyan rowar da wani ɗan sarkin ƙasar Tsafe ya yi masa kuma ta kai maƙura. Duk yadda mutum ya yi ba zai iya samun komai ba gunsa.
4.0 Sakamakon Rowa
Idan ana maganar sakamako na rowa gun su makaɗa abu ne, wanda za su iya
faɗin maganganu masu
muni ga wanda ya yi musu rowa. Don haka wanan maƙalar
ta yi nazarin sakamakon rowar da ake yi wa makaɗa musamman makaɗan fada wanɗanda su ne ke ganin
ya dace mutumin da ke kusa ga sarki ya yi musu kyauta amma kuma ya ƙi yi musu kyautar don haka sai su saka masa da wasu
kalmomi masu muni kalmomin zambo da habaici bisa ga nazarin da wannan maƙalar ta yi tana ganin sakamakon rowa ne aka sami zambo da
habaici.
4.1. Zambo
Masana irin su Gusau (1988) da Dumfawa (2005) sun bayyana
ma’anar zambo da cewa, aibanta wani mutum ko wani abu dangane da siffarsa ko aƙidarsa ta yin amfani da wasu laffuzza na aibantawa
ko muzantawa ko munanawa.
Shi kuma Yahya (1997) cewa ya yi, Zambo kishiyar yabo ne
kuma akaikace yabo ne ga gwarzon waƙar da ake yi. Ta
la’akari da waɗannan
ma’anoni ana iya cewa zambo shi ne, aibanta mutum da wasu kalmomin da ke da
muni domin ko aibanta shi ga jama’a.
A wannan maƙalar ana ganin ba abin da ya jawo wannan in ba rowa ba. Saboda idan mutum ya yi wa makaɗi rowa to zai bi
hanyar da zai
bi, domin ya muzanta shi domin ya ji ciyo, kamar yadda shi ya ji ciyon rowar da
ya yi masa.
Sarkin taushin sarkin Musulmi Salihu Jankiɗi, ya
kawo irin wannan misali cikin waƙar da ya yi wa sarkin Katsina Gusau Rabakaya inda yake
cewa:
Su wane ba a da kyauta,
Sai rowa sai ƙarya,
Sai batun kwazaba,
In an sauka a sha gara,
Abin da munka sani,
Mun lura da shi sai hira.
(Jankiɗi: Ɗan Nagwamace Kigo).
A cikin wanann waƙa nakaɗa ya yi wa wani dan sarkin wanda ya nemi sarauta tare da
sarkin Katsinan Gusau Muhammadu
Rabakaya. Kuma ya yi wa makaɗa rowa, don
haka ya fara da ce masa ba ya kyauta duk wanda bai kyauta matsolo ne. Kuma zai iya ɓata lokacinsa ya yi
ta hira da mutum har sai mutumin ya gaji ya tafiyarsa da kansa ba tare da ya bashi
wani abu ba.
Alhaji Musa Ɗankwairo ya bayyana
irin wannan misali a
cikin waƙar da ya yi wa ‘Yan Doton Tsafe in da yake cewa:
Ni na ci na kwana da mamaki,
Na ga ɗan sarki mai baƙar rowa,
Ko kace Allah ya yi mai rabo,
Sai ya gintse maka baya tankawa,
Wanga aikin kaba ne hita zamba,
Wanga aikin kaba bai sarauta ba.
(Ɗankwairo: shirya kayan faɗa magida tsahe).
A cikin wannan ɗan waƙa, makaɗa ya bayyana
wani daga cikin ɗiyan sarautar Tsafe
mai baƙar rowa wanda ba ya iya yiwa
kowa kyauta, kuma ko da ka yi
masa roƙon Allah ya nufa ya zama sarki ba za yi maka magana ba,
ballantana har ya ɗauki wani abu ya baka kyauta. Makaɗa ya kira shi da ya bar irin wannan hali don ba halin kwarai ba ne. Makaɗa ya yi masa wannan zambo saboda rowarsa ta jawo masa
zambo ba.
Shi kuwa makaɗa Jankiɗi ya yiwa
wani ɗan sarki zambo a
cikin waƙar da ya yiwa sarkin Musulmi in da yake cewa:
Wane ya tsinkan bisa hanya,
Shina ta ɓoyo ban zo
gunka ba,
Mai idon jakkai rowa shi kai.
(Jankiɗi: Bubakar Ɗanshehu Baƙadire).
A nan makaɗa ya bayyana wani ɗan sarki wanda baya son ya gan shi domin ba ya iya yi masa kyauta, sanadiyar wannan rowar da ya yi masa sai ya yi masa zambo inda ya kwatanta idanuwansa
dana jakkai wanda idan yana bisa hanya yana tafiya to idanunsa hanyar kawai suke kallo, basa kallon ko’ina. Don haka shi
wannan ɗan
sarkin hanya kawai yake duba domin idan ya ga wanda ke roƙo
ne sai ya ɓoya,
in kuma wanda za su yi labari ne, ba ya amsar komi gare shi sai ya zauna su
yi.hira har agaji a tashi.
4.2 Habaici
Hausawa kan ce: “Abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa” Masana da
manazarta a lokata daban-daban sun tofa abarkacin bakinsu a kan ma’anar habaici
misali: masana irin su Gusau (1988) da Bunza (2009). Sun bayyana habaici da
cewa:
“Habaici magana ce da ake faɗi a faƙaice don musgunawa wani a cikin hikima da jera tunanin
cikin ‘yan kalmomi kaɗan masu rikitarwa”
Dunfawa (2005) ya bayyana
habaici da cewa:
Faɗawa wani ko wasu wani abu da suka yi ko suke yi a faƙaice ba tare da ambaton suna ko sifanta wanda ake yiwa ba”
Ta ala’akari
da waɗanan ma’anoni za a iya cewa Habaici, wata magana ne da ake yi wa wani domin a shammaceshi, ba tare da bayyana wanda ake yi da shi
ba. Don haka mafi yawan masanan sun yi ittifaƙin
cewa habaici yana da rufin asiri bisa ga zambo, domin ba kowa ke gane wanda aka
yiwa shi ba.
Da yake makaɗan fada kan yi zambo da habaici ga ‘ya’yan sarakuna waɗanda suka yi masu
rowa, kuma suka ruwa, suka yi tsaki wajen neman sarauta da waɗanda suka ƙi yin mubayi’a bayan an naɗa sarki. Haka kuma a
wani lokaci habaici kan faɗa wa fadawan sarki waɗanda ake zargi ƙull wani makirci waɗanda sarki bai san da su ba. Misali
Ibrahim Narambaɗa Tubali ya kawo wani ɗan waƙa inda yake cewa:
Amadu miƙe ƙahwakka,
Domin waɗanga ‘yan sarki,
Da ka dambe da rashi,
Ba mai kowa,
Ba mai kwabo ga hannu,
Su duka ɗiɗɗimin su kai,
(Narambaɗa: yaci maza ya kwan yana shiri).
A cikinwanann ɗan waƙa, makaɗa ya ambato wasu ‘yan sarauta da suka nemi sarauta da
cewa ba su da arzikin da za su nemi sarauta dukansu talakawa ne, hasali ma ba su da cikakkiyar lafiya. Idan aka duba da
kyau za a ga cewa makaɗa ya musu habaici domin ya muzantasu ba wata ƙima ke garesu ba. A
cikin wata waƙa ya kawo wani misali in da ya ke cewa:
Haba basu amana,
Bassu da Allah,
Komi suka
yi ya sani,
Munahukkai ku bi sannu,
Kar yaka gani.
(Narambaɗa: Ibrahim na guraguri).
A cikin wannan ɗan waƙa makaɗa yana yi wa
wasu ‘yan sarki hannunka mai sanda ne domin su sani an san halin da suke ciki. Sai dai kawai sarki ya kyalesu ne ya bar su da Allah. Don haka su yi hankali. Amma kuma a cikin habaici ne yake gaya musu wannnan
maganar.
Shi kuwa makaɗfa Sa’idu Faru ya kawo wani misali a cikin waƙar da ya yi wa sarkin Banga inda yake cewa:
Ga wani yai kokuwa da wani ƙarfinai,
Ya faɗi ya kare,
Tun ba a tantance ba,
Shina nishi sun kaishi sun baro,
(Sa’idu Faru: Gwabron giw uban Galadima Ɗansambo ginshimi)
A cikin wannan ɗan waƙa, makaɗa ya yi wa
wani ɗan sarkin Banga
wanda ya ja da sarki aka ɗauke shi aka buge, wato bai sami sarautar ba, kuma ba ya ga kuɗinsa da ya kashe don haka sai a koma nishin rashin sa’a.
Makaɗa Alh. Musa Ɗankwairo ya kawo wani misali cikin waƙar ‘Yantodon
Tsafe in da ya ke cewa:
Ɗan sarki in yay yi sittin,
Bai gadi gidansu ba, ta ɓare mai,
Sai biɗar jalli a sami nashan dawo,
Ka a lalace.
(Ɗankwairo: shirya kayan faɗa maigida tsahe).
A cikin wannan ɗan waƙa, makaɗa ya yi habaici ga wani ɗan sarki wanda ya
kwashe shekaru masu yawa har shekara sittin (60), bai sami
sarauta ba. To makaɗa ya bashi shawara ya je ya nemo jalli (Jari) na yin
sana’a, wanda zai sami kuɗin biyan bukatunsa na yau da kullum. Domin kada ya zauna
jiran sarauta ya lalace ga banza, wato ya yi biyu babu, ba a ga tsuntsu ba a ga tarko.
5.1. Kammalawa
Wannan maƙala ta yi tsokaci a kan rowa da wasu abubuwan da ta ke ganin su ne suka zamo tubalan da sukan sanya makaɗan fada yin zambo da habaici ga ‘ya’yan sarakunan su kan ƙonawa ‘yan sarki rai da yi masu zambo ko
kuwa su yi masu habiaci. Maƙalar ta kawo ɗiyan waƙoƙin da ke ɗauke da waɗannan misalai.
Haka wannan maƙalata ta kawo wasu misalai na hadisin Annabin Rahama
Sallahu Alaihi Wasallam. In da aka yi bayani da zaman rowa ɗabi’a ce mummuna
har inda aka bayyana Annabi ya yi wa duk mutumin dake yin kyauta addu’a. Inda
yake cewa:
“Allah ka bai wa duk mai cisuwa mamayi” wanda bai ciyarwa
kuma aka roka masa halaka”.
Manazarta
Abba M. da Zulyadaini B. (2000). Nazarin
kan waƙar Baka ta Hausa Gaski:ya Corperation limited Zaria.
Bello G. (1976). “Yabo zuga Da zambo a waƙoƙin sarauta” a cikin Nijeriya, 6.21-34.
Bunza A.M. (2009). Narambaɗa Ibarahim Islamic publication canter Ltd. Sulwere-Lagos.
CNHN. (2006). Ƙunusun Hausa na Jama‘ar Bayero Kano. Ahmadu Bello
Univercity press
Ltd Zaria.
Ɗunfawa A.A (2004). Habaici a cikin waƙoƙin
Hausa. A cikin Ɗundaye journal of Hausa Studies Vol-I-no-I
Gusau S. M. (1980). Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi. Bechmack Ltd Kano.
Gusau (2009). Diwanin Mawaƙa Zaɓaɓɓun Mafanoni na Waƙoƙin Baka
na Hausa. Centrary Peresh and
Publishing Ltd. Kano
Ibrahim A.A (205).
“Kyauta Ma’aunin Yabo a waƙoƙin Fada na Hausa” kundin digiri a biyu Jami’ar Umanu Ɗanfdiyo Sakkwato.
Junaidu I. da ‘Yar aduwa
TM (2007). Harshe Da Adabin Hausa
A Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare. Spectan Book Ltd. Ibadan.
Muharnmad M.S. (2014). “Rowa (hali wayau ko ciwo)” Takadar da aka gabatar a taron talàfawa marayu a garin Kaduna. Jahar Kaduna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.