Ticker

6/recent/ticker-posts

Kukana Game Da Lamuran Karatun Hausa a Yau

Daga

Yusuf. M. Kazaure

IDAN NA YI KUSKURE DAMAN NI ƊALIBI NE A GAFARCE NI SANNAN A YI MINI GYARA.

Tsokaci: Ni ɗalibi ne mai neman sani a koyaushe da maraba da gyara, idan na yi kuskure a gafarce ne ko na yi mummunar fahimta a fahimtar da ni.

Ni ɗalibi ne kuma mai neman sani a cikinku, na san maganar taku ce ta manya, wadda bai kamata mu ce wani abu ba, saboda haka a gafarce ni a bisa wannan kuskuren.

A batun gaskiya www.amsoshi.com ya taɓo mana ciyon da ya daɗe yana sosa mana rai, sannan ya bayar da ingantattu kuma sahihan misalai, da hanyoyin da ya kamata a bi domin gyara da ci gaba a zamanance.

 Haƙiƙa ni kaina na taso da burin nazartar harshen Hausa, bisa wasu muhimman dalilai, wanda hakan tasa a yanzu haka ina da Digirin farko a fannin B.A Hausa, sai dai kash! Wallahi a yanzu sam an cire muni sha'awar ci gaba da nazarin wannan harshe bisa wasu dalilai, wanda a yanzu haka ina tunanin a fannin da zan yi PGD (postgraduate Diploma), in saura sheƙa.

Kaɗan daga cikin dalilan da suka sanya ni son nazarin harshen Hausa sun haɗa da:

A- ina son wallafa litattafai, ta yadda ko bana raye ayyukana zasu ci gaba da bayyana a doron ƙasa, kamar yadda a yau ake tunawa da su; Alh. Abubakar Imam, da su Ahmadu Ingawa, su Bello Kagara da sauran su.

Wlh tun a firamare na ji ina son zama irin su, yadda suka bayyana basira da hikimarsu ta hanyar rubuta litattafan da suka haɗa da; Magana jari ce, da Ruwan Bagaja, da su Iliya Ɗan Maiƙarfi da sauran su.

b- Ina son na san wane ne ni, ma'ana waye cikakken Bahaushe?

c- Ina son a fannin Hausa ni ma ya kasance ana damawa da ni nan gaba idan lokacin mu ya zo.

d- Da sauran dalilai sun fi a ƙirga wlh.

Amma a yanzu sam an cire min wannan sha'awar gaba ɗaya. Bisa dalilan nan da suka haɗa da:

a- Alokacin da muke koyan darasi na koyi darasi da dama, dangane da malaman shashen mu da na sauran sashe musamman a fannin Science couses, har da tambayar miyasa a Hausa, History, Arabic ba a fiye fita da sakamako mafi daraja ba (first Class) saɓanin Science courses?

1- Daliban da suke nazarin waɗannan fannonin ba su da ilimin cin hakan ko kuwa?

Mukan yi iya bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mun ci A ko B, a kwas amma cikin nufin Ubangiji sai hakan ta gagara, wanda ba wai ba a cin makin da ya kai a ba mutum A ko B, bane a'a sam-sam ba haka bane, amma dai a biyo ni bashin wannan......

Amma a bin mamaki a sauran kwasa-kwasai musamman na gidan sayins basu fiye.... maki ba, akan samu A ko B, kuma akan samu masu sakamako mafi daraja da yawa a kowace shekara a ɓangarorinsu da dama, sosai-sosai matuƙar ɗaliban sun yi abinda ya dace.

Amma za a daɗe ba a ji irin wannan abin ba a fannonin Hausa, Arabic, ko History, domin tunda nake ban taɓa jin wanda ya fita da (First Class) a History ba.

1- Ko har yanzu ba a samu haziƙin ɗalibin da zai iya ci bane?

 Waɗanda wannan batu ya ɓatawa rai, a gafarce ni wataƙila kuskuren fahimta ta ne yasa nake ganin hakan, fahimta ta bai zama wajibi ta zama gaskiya ba.

 b- A lokacin da zan rubuta kundin bincike na kammala Digirin farko, na zaɓi " matanin" da zan yi bincike a kai, inda na zaɓi taken bincike mai alaƙa kai tsaye da tarihin mahaifa ta, domin nima na fara bayar da tawa gudummawar a mahaifa ta, ta binciko muhimman abubuwa game ta ita, amma kash ! Na fuskanci ƙalubale da dama na rashin bani lokaci da yimin bayanin tambayoyina ga masanan, a matsayina na ɗalibi mai neman sani, ba alfahari ba, ban da na saka naci da ƙwawa wlh da binciken ba zai kammalu ba.

Hakan yasa na ƙara cire tsammani, saboda rashin ɗaukar mutum da muhimmanci balle a ba shi gudummawar da ta dace.

c- A yanzu kana ji kana gani ko a makarantu masu zaman kansu (private school), ba ma manyan kamfanoni ba, za a nemi masu karatu na fannoni daban-daban amma kash sai ka ji an ce babu masu irin karatunka.

A kwai yayana wlh har M.A Hausa yake da ita, kuma malami ne a makarantar gwabnati amma cemun ya yi "A kwai sanda a makarantar da yake koyarwa, sai da aka tura kowane malami semina, amma ban da shi kaɗai, da ya yi magana aka ce masa wai ai ban da malamim Hausa"

Abin tambayar a nan miyasa aka ware Hausa?

a- Ba a ɗauke ta da muhimmanci bane ko kuwa?

b- Su waye suka ware malaman Hausar, sannan ina manyan malaman Hausar da ba su bibiyi dalili ba?

c- shin hakan ba zai sanya ɗaliban su raina kwas ɗin ba, balle har su yi sha'awar nazarin?

d- Anya hakan ba zai sanya wasu malaman su raina Malamin Hausar ba, ganin yadda ta faru ba?

Bayan haka ina da tarin tambayoyi da misalai wanda rubutn zai yi tsayi idan kawo su za mu yi.

Allah ya sakawa malaman mu, irin su www.amsoshi.com, duk da Allah bai halicce mu kai ɗaya ba, da a ce malaman Hausa na koyi da irin ayyukansa na bunƙasa harshen Hausa da wallahi da yanzu ba wannan batun ake ba.

Na san a wannan zaure akwai malamai na da abokanan karatu, amma dan Allah ina fatan za su fahimci zancena ta hannun dama, ba ta hannun hagu ba domin ita fahimta fuska ce, kowa da irin tasa fahimtar, amma ni fatana a yi mini adalci wajen fahimtar manufata.

Idan a kwai wani matani da mutum bai fahimta, kafin yanke hukumci zai iya tuntuɓa ta domin ya ji, miye manufata sannan ya san inda na nufa.

Muna fatan Allah ya zaɓa mana abinda ya fi alheri amin.

Kukana Game Da Lamuran Karatun Hausa a Yau

Post a Comment

0 Comments