Ticker

6/recent/ticker-posts

Shawarwari Game Da Kalubalen Da Karatun Hausa Yake Fuskanta a Yau

SHAWARWARI GAME DA ƘALUBALEN DA KARATUN HAUSA YAKE FUSKANTA A YAU

Daga

Mal. Yunusa Ibrahim Adamu

Assalamualaikum.

A yanzu na samu lokacin tofa albarkacin bakina a bayanan da aka tattauna jiya. Kuma sai da na bibiyi yawancin abubuwan da aka tattauna wanda suka ba ni haske.

Da farko dai, ina yi wa Allah godiya da aka zunguro wannan ɓangaren duba da cewa abu ne da ya daɗe yana damuna ƙwarai da gaske. Sai dai a ganina, bai dace idan ana neman hanyar gyara ba, kuma a ɓuge da ɗorawa wasu musamman malamai laifi. Domin su ne suka ɗora mu a hanya, kuma har yanzu mu ke kwankwaɗa daga maɓuɓɓugar ilimin da suke ba mu. Don haka, haryar da Malam @www.amsoshi.com ya kawo su ne hanyoyin da suka dace a bi domin a samu gyara. Allah ya saka masa da alheri. Haka shima Ɗan'uwa Dr. Isah Muhammad ya kawo wasu shawarwari da matuƙar aka bi su, za a samu nasara.

Ga wasu shawarwari kamar haka:

1: Tun daga tushe (matakin Primary da Secondary) ya kamata a samu 'Yan uwa malamai su riƙa yin amfani da dabarun koyarwa na zamani a wajen inganta harkar koyo da koyarwar yara masu sha'awar karatun Hausa. Irin waɗannan hanyoyi sun haɗar da bayar da kulawa ta fannin ƙirƙira a fannin harshen Hausa da Adabi da kuma al'adun mutanen Afirka ba lallai sai Hausawa ba. Domin takaita tunani a ƙasar Hausa kan jawo ƙwaƙwalwar yaran ta tsaya nan kusa, a kan abubuwan da suke iya gani yau da kullum.

2: Iyaye suna da rawar da za su taka, wajen saita tunanin yaransu wajen ganin sun ginu a kan wani tunani na rayuwar yau da kullum, ba wai a riƙa daƙile tunanin yara, ya zuwa wani ɓangare da aka saba gani yau da kullum ba. Misali: Iyaye ne malaman farko, da yakamata su riƙa fahimtar da yaran muhimmancin al'ummar mu, tun daga tushe da irin nisan da aka yi mana a fannoni da dama, da kuma yadda kowa zai iya taimakawa a inganta hanyar koyo da koyarwar.

3: Gwamnati musamman masu riƙe da muƙamai a nan arewa, da su daure su riƙa bibiyar yadda lamura ke kasancewa a makarantun mu na Gwamnati da masu zaman kansu, domin ana yi wa yaranmu illar da sai nan gaba ne za a gano hakan. Sabo da ana gurɓata musu tunani da ƙyamar ƙasarsu da yankinsu. Wanda hakan ke ƙara ta'azzara komai.

Dole ne Gwamnonin jihohin arewa su mayar da harshen Hausa ya zama harshen koyarwa tun daga matakin Primary ta yadda za a fassara Litattafan kowanne fannin da za a koyar da harshen Hausa. Hakan zai bunƙasa tunanin Dalibai da ƙara musu fahimtar abubuwan da ake koya musu. Idan ya so, sai shi ma Ingilishi ya sama wani darasi da ɗalibi zai koye shi kamar dai yadda ake koyon Jogirafi.

4: Malaman harshen Hausa kuwa, su ne kan-kat! Wato su ne a sahun gaba, wajen ganin komai ya daidaita ta hanyar yaye Ɗalibai masu hikima da basira da kuma daurin fahimtar inda duniya ta dosa. Da sauya tunani daga hanyar gargajiya ya zuwa hanyoyin zamani ta hanyar kutsawa cikin duniya ta shafukan sada zumunta da leƙawa duk wani dandali da ake magana da Hausa domin kawo gyara da saita abubuwa da kuma ƙarawa mabiya himma da sanin darajar harshen Hausa. Kamar dai yadda manyan Malamanmu na wannan zauren kamar Prof. A. B. Yahya da Prof. A.M. Bunza da Prof S.A. Yakasai da Prof. B.B. Usman da Prof. Aliya Adamu da Dr. Yahaya Idris da sauransu da yawa da su ke kashe lokacinsu wajen ganin sun bayar da duk gudunmuwar da ake buƙata. Wannan yana ƙarawa daliban ilimi ƙarfin gwiwa wajen sake zage damtse.

5: Kowa sai ya zama jakadan dawo da martabar harshen Hausa a tsakanin al'umma. Tun daga gidajenmu da unguwanninmu da ƙauyukanmu da duk inda mu ke zuwa kasuwa ko aiki, da nufin faɗaɗa tunanin mutane a kan cewa harshen Hausa ba harshen arewa ba ne, harshe ne na duniya. Kuma muna sa rai nan gaba sai ya mamaye duniya baki ɗaya. Duba da yadda yake samun tagomashi daga wasu al'ummu a faɗin duniya.

Allah ya taimaki harshen Hausa da Hausawa da masu amfani da harshen Hausa. Amin.

A yi haƙuri 

Ɗalibi ne.

Yunusa Ibrahim Adamu

Shawarwari Game Da Kalubalen Da Karatun Hausa Yake Fuskanta a Yau

Post a Comment

0 Comments