Ticker

6/recent/ticker-posts

Karancin Daliban Hausa a Manyan Makarantun Kasar Nan, Laifin Malaman Hausa Kadai: Ba Gaskiya Ba Ne!

ƘARANCIN ƊALIBAN HAUSA A MANYAN MAKARANTUN ƘASAR NAN, LAIFIN MALAMAN HAUSA KAƊAI: BA GASKIYA BA NE!

Daga

Dr. Isah Abdullahi Muhammad

1. Ƙarancin ɗalibai matsala ce da take addabar kwasa-kwasai da dama, ba ga Hausa kawai ba ne. Ya faru ne saboda buɗe Jami'o'i barkatai, akwai ɗaiɗaikun kwalejoji da suke yin digiri da ma masu zaman kansu. Ga zirga-zirga ta yi wuya, ba tsaro ga matsatsin tattalin arziki. Duk suna daga ciki.

2. Cewa Malaman Hausa kashi 70 ba su tafiya da zamani a yanzu, shi ma abin tambaya ne. Da waɗanne alƙalumma ne aka kai ga wannan adadi? A bayyana shi kowa ya gani, kuma a binciki sahihancinsu. In ba haka ba to wannan adadin shaci-faɗi ne kawai, kowa zai iya yi. Sannan 'Kimiyya' (Science) da Fasaha (Technology) fannoni ne masu cin gashin kansu. Gwama su da nazarin Hauy, abu ne mai buƙatar haɗaka tsakanin waɗannan fannoni, abu ne da yake buƙatar tallafi kuɗi masu tsoka musamman ta fuskar fassara. Wa zai ba taimaka da wannan Malami? Ko Gwamnati? Ko Hausawa? Malami dai ba zai iya ba, ɗan albashin da ake ba shi bai taka karya ya karya ba! Kuma shi ne da laifi dai, saboda a Nijeriya an raina malami ko? A ciki an bayyana malaman Hausa ba su cika yin bincike cikin Ingilishi ba ko Larabci ko Faransanci? Ke nan yin nazari cikin Hausa ƙauyanci ne, nazarin Hausa cikin Larabci ko Faransanci shi ne daidai ko? Anya dai? Malaman Hausa ba su ansar sabon abu, hujjarsu ba su san shi ba! Wannan ƙarya ne! In ba haka ba, a kawo misalin inda malaman Hausa suka yi musun wani abu sabon abu, haka kawai ba wani dalili, sai don kawai ba su san shi ba.

3. Rashin iya Amfani da Kayan Na Zamani. Kaso 90 na malaman Hausa, ina aka samo wannan kididdiga ko shi ma na fatar baki ne? Dangane da 'Language Laboratory' duk manya karantu ƙasar nan suna da shi, ba gaskiya ba ne! Ga ƙa'ida ba za ka je ka yi amfani sai an horar da kai, yadda ake amfani da shi, wace Jami'a ce a ƙasar nan, ta horar da malamai yadda za a yi amfani da suka ƙi? Babu, hasali ma, wasu dodon bango ne ba sa aiki. Wataƙila, sai waɗanda suka sami gatan tsallakawa zuwa waje, za su fahimcin sirrin. Nan ƙasar nan, kam! Ilimi a yanzu bai kai a yi masa wannan gata ba. Ko a fagen tsintsar kimiyya suna fama da ƙarancin Laboratories balle sashen Hausa. Abin da Asuu take fama da shi har a yanzu, abin ya faskara. To kuma sai a ce laifin malamin Hausa ne, bai je ya koya ɗalibansa ba, alhali ko aiki ba su yi. Haba, an yi wa malaman Hausa adalci.

4. Rashin tsayayyiyar ƙungiya ta ƙasa, wannan gaskiya na yarda da akwai wannan matsalar, ya kamata a gyara ta. Magabata su shige gaba, mu ƙanana, mu biyo baya.

5. A P.G. Malaman Hausa Ba su faɗaɗa bincike. Wannan maganar ba, babu hujja, ba a tattaro ayyukan da aka yi ba, ƙiyasi ɗai aka yi. Shi ma wannan shaci-faɗi ne kawai. Ya kamata ya fahinci har gobe nazarin 'Jigo' da 'Salo' da 'Zubi', matakai ne da aka yi amfani a da kuma har yanzu suna da muhimmanci aikin bai ƙare ba. Duk inda ake buƙatar a yi amfani da su, za a ɗauko su a yi da su, ba za a raina su ba. Bai hana a kalle su ta fuskoki daban- daban. Wataƙila, Dr. Abdurrahman, bai zagaya wuraren da ake gabatar da ƙudurorin bincike (Proposals) an sami sauyi sosai, ana samun cigaba

6. Rashin bayar da ƙwarin gwuiwa. To a nan, akwai buƙatar Malamai a duk inda suke su ƙara ƙwazo, to amma wani hanzari ba gudu ba, tuni halayyar da gwamnati take nunawa ilimi gaba ɗaya, ya sa akasari sana'ar koyarwa ta rage tagomashi ba ga Malaman Hausa kawai ba, ai abin ruwan dare ne..

Dr. Isah Abdullahi Muhammad

Karancin Daliban Hausa a Manya Makarantun Kasar Nan: Laifin Malaman Hausa Ne

Post a Comment

0 Comments