Ticker

6/recent/ticker-posts

Sabon Salon Bude Wakoki a Karni Na Ishirin Da Daya

Article Citation: Baffa, A.S. & Ibrahim, O.M. (2025). Sabon Salon Buɗe Waƙoƙi a Ƙarni Na Ishirin Da Ɗaya. Zauren Waƙa, 4(2), 50-59. www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.006.

SABON SALON BUƊE WAƘOƘI A ƘARNI NA ISHIRIN DA ƊAYA

Na

Ahmed Sulaiman Baffa
Department of African Languages & Linguistics
Yobe State University
Damaturu, Nigeria
Email: ahamadsulaimanbaffa 4455@. Com
GSM: 07068946160

Da

Ogah Muhammed Ibrahim
Department of General Studies & Pre-ND
Isa Mustapha Agwai 1 Polytechnic, Lafia

Tsakure

Al’umma ta lura da cewa waƙa aba ce mai saurin kama zuaciya da isar da saƙo cikin ƙanƙanin lokaci, wannan ya sa masana da manazarta suka ba da lokutansu musamman don nazartar waƙoƙin. Tun a ƙarni na shabakwai aka fara samun rubutattun waƙoƙi a ƙasar Hausa masu mabuɗi da marufi. Haka abin ya ci gaba har ya gangaro ƙarni na 18, da 19 da na 20. Sai dai ana samun bambance-bambance dangane da matakai da ake bi wajen buɗe waƙoƙin a kowane ƙarni. Wannan ya sa aka dubi matakan buɗe waƙoƙi a ƙarni na 21 inda aka samu matakai shida da mawaƙan ƙarni na 21 ke amfani da su wajen buɗe waƙoƙinsu, waɗanda suka samu sakamakon samuwar sigogin waƙar baka da na rubutacciyar waƙa a waƙoƙin waɗanda suka haifar da samuwar waɗannan sababbin matakai na buɗe waƙa. Matakan sun haɗa da; take wato kiɗa da amshi da sharar fage da ambaton Allah da yin addu’o’i da ambaton Annabi (SAW) da kuma rashin amfani da mabuɗi. Sanin waɗannan matakai zai taimaka wa manazarta da ɗalibai wajen nazari, kuma zai bayyana tasirin baƙin al’adu a kan na Hausawa. Sannan an kawo bayanin kammalawa.

1.0 Gabatawa

An lura da cewa waƙa aba ce mai saurin kama zuciya wajen sauya wa al’umma tunani da kawo saƙonni masu muhimmanci ga jama’a. wannan ya sa masana da manazarta suka duƙufa wajen nazarinta. Tun ƙarni na sha bakwai aka fara samun ɓirɓishin rubutattun waƙoƙi irin su; ‘Waƙar Daliyya’ da, ‘Nuniyya’ ta Wali Ɗanmarina. Sha’anin waƙa ya ci gaba da wanzuwa har ƙarni na sha takwas lokacin da aka samu malamai irin su; Malam Muhammadu Na Birnin Gwari wanda ya yi waƙoƙi da dama, waɗanda suka haɗa da; “Ma’akusa” da, “Jawahiru” da, “Billahi Arumu”. Haka Malam Shi’itu ɗan Abdurra’uf ya yi waƙoƙi da dama kamar; “Fassarar Arshada” da “Waƙar Tuba”. A ƙarni na sha tara kuma aka samu mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo a (1754-1817) da almajiransa sun yi waƙoƙi da dama masu manufofi na addini kamar su; “Waƙar Cin Birnin Alƙalawa” da “Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci” ta Abdullahi Fodiyo da sauransu (Yahaya, 2002:37-59). A ƙarni na ashirin al’amarin waƙa ya zama muhimmin al’amari, jigoginta suka faɗaɗa daga manufofi na addini suka haɗa da al’amuran rayuwar duniya, an yi waƙoƙi da dama kamar “Waƙar Zambon Ƙazama” ta Aliyu Namangi da “Waƙar ‘Yar Gagara” ta Aƙilu Aliyu da sauransu. Kamar yadda masu iya magana ke cewa: “Idan kiɗa ya sauya dole rawa ma ta sauya”. Wannan sauyi shi ne za a iya cewa abin da ya faru da tsarin mabuɗan waƙoƙin Hausa a ƙarni na ishirin da ɗaya. Sauyin lokaci da cuɗanya da baƙin al’adu ya yi tasiri kan tsari da sigogin waƙoƙin Hausa a ƙarni na ashirin da ɗaya musamman mabuɗan waƙoƙi. An samu sauye-sauye dangane da mabuɗan waƙoƙi a ƙarni na 21 ta fuskoki daban-daban. waɗanda ba a samu irinsu a waƙoƙin ƙarni na 17-20 ba.

Wannan ya sa aka dubi sabbin tsarin matakai na mabuɗan waƙoƙin Hausa na ƙarni na ishirin da ɗaya don fito da sababbin matakan buɗe waƙoƙi da mawaƙan ke amfani da su yayin buɗe waƙoƙinsu. Wannan takarda ta yi bayanin matakai shida da mawaƙan ke amfani da su yayin buɗe waƙoƙinsu. Matakan sun haɗa da; take wanda ya ƙunshi kiɗa da amshi da sharar fage wanda ya ƙunshi sunan mawaƙi da sunan wanda aka yi wa waƙa da wanda ya ɗauki nauyin waƙa da lambar waya da gabatar da sallama. Sannan ambaton Allah wanda ya ƙunshi gaskata shi da yabon sa da girmama shi da yi masa kirari da sauransu. An dubi addu’a da ta haɗa da nema ƙarin basirar tsara waƙa da ƙarin ilmi da neman tsari da sauransu. An kawo ambaton Annabi wanda ya haɗa da yi masa salati da yabo da kamun ƙafa da shi da ambaton iyalansa da sahabbansa da sauran Annabawa.

1.1 Waƙoƙi A Waƙoƙin Ƙarni Na 21

Waƙoƙin da suka shahara a yau waƙoƙi ne da ba zai yiwu a kira su kai tsaye da rubutattu ko waƙoƙin baka ba. Duba da yadda waƙoƙin suka haɗa sigogi daban-daban na waƙar da baka da kuma na rubutacciyar waƙa. Hakan ya sa masana da dama suka yi ƙoƙarin samar musu suna wanda zai dace da su. Daga ciki akwai Dumfawa (2014) ya kisu da Makaɗan Zamani, Atowa da Dono (2014) sun kira su da Hausa Poems in The 21ts Century, shi kuma Usman (2018) ya kira su da Ruwa-biyu. Wasu masan kuma su kira su da Jemagu, wasu kuma da waƙoƙin fiyano

Idan aka iya la’akari da waɗannan sunaye da masana suka bayar ga cewa akwai abin dubawa kamar haka:

a.      Jingina su ga zamani, idan zamanin ya wuce da me za kira su?

b.      Kiransu da ruwa biyu, shima ba zai yiwu ba saboda ba sigogin waƙar baka dana rubutacciyar waƙa ba ne kaɗai a cikinsu, suma sun zo sabin abubuwa nasu daban. Haka bayanin yake idan aka kira su jemagu.

Don haka na zaɓi na kira su da waƙoƙin ƙarna na 21, saboda sun haɗa sigogin rubutacciyar waƙa kamar mabuɗi da marifi da amsa-amo da tsarin layuka da baiti da kari, da kuma sigogin waƙar baka kamar sanƙiranci da amshi da kiɗa da da gaza da sauransu, waɗanda su uka haifar da samawar waɗannan sabin salailai na mabuɗan waƙa. Bayan haka kuma waƙoƙin sunzo da sabin abubuwa da babu su a waƙoƙin da suka gabace su, kamar jagorancin mace da namiji da sauransu. Waɗannan dalilai ya sa aka kira su waƙoƙi ƙarni na 21.

2.0 Sharhin Tubalan Take

A lokutan da suka shuɗe mawaƙa na amfani da wasu hanyoyi wajen buɗe waƙoƙinsu, waɗannan hanyoyi kuwa wasu lafuzza ne da aka san marubuta waƙoƙi na amfani da su yayin bude waƙoƙin su. Mabuɗin waƙa yakan ƙunshi duk wasu lafuzza da mawaƙa ke amfani da su a yayin buɗe waƙa.

2.1 Mabuɗin Waƙa

Sa’id (1978), ya ce waƙoƙin Hausa da suka samu kafin ƙarni na ishirin duka sun bi tsarin farawa da rufewa da ambato da salati ga Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da addu’a.

Omar (2013), ta bayyana cewa mabuɗi salo ne da ke nuni da cewa an fara waƙa. Ta kuma ƙara da cewa abu ne da ya ɗau salo na musamman tun asalin tarihin rubutattun waƙoƙin Hausa har zuwa lokacin da take rubuta takardarta.

2.2 Mabuɗin Waƙa Kafin Ƙarni Na 21

Omar (2013), ta bayyana cewa marubuta waƙoƙi sun fara amfani da mabuɗi da marufi a waƙoƙinsu tun daga ƙarni na 17 har zuwa ƙarni na 20. Hanyoyin da marubuta waƙoƙin ƙarni na 19 da na 20 ke bi don yin amfani da mabuɗi a yayin buɗe waƙoƙinsu sun rabu gida huɗu kamar haka:

a.      Ambaton Allah ta hanyar gaskata shi da yabon sa da girmama shi da yi masa kirari da sauransu.

b.      Ambaton Annabi Muhammadu (Mai tsira da amincin Allah) ta hanyar yi masa salati da yabonsa da kamun ƙafa gare shi da ambaton alayensa da sahabbansa da sauran annabawan Allah.

c.       Yin addu’a ta hanyar roƙon Allah wani abun buƙata, masamman basira ta tsara waƙa, ko neman buɗi na ilimi ko neman tsira da sauransu,

d.     Rashin amfani da mabuɗi da marufi wato, rashin amfani da hanyoyin da aka zayyana a sama.

Mabuɗin Waƙa a Ƙarni na Ishirin da Ɗaya

Ta la’akari da yadda matakan buɗe waƙoƙi suke a lokutan da suka gabata za a iya cewa, wasu daga cikin mawaƙan ƙarni na 21, sun ɗau sahun magabata wajen amfani da mabuɗi a yayin aiwatar da waƙoƙinsu, duk da cewa ba su taƙaita a kan hanyoyin da magabatan suka yi amfani da su ba. Sun zo da sababbin tsari da wasu matakai da suke amfani da su wajen buɗe waƙoƙinsu.

3.1 Matakan Buɗe Waƙoƙi a Ƙarni na Ishirin da Ɗaya (21)

A nan an bayyana matakan da mawaƙan ƙarni na 21 ke amfani da su wajen buɗe waƙoƙinsu, saboda sun bambanta da na magabatansu. Mawaƙan ƙarni na 21 na amfani da matakai har guda shida a yayin buɗe waƙoƙinsu kamar haka:

3.1.1 Take: kiɗa da amshi

Wannan shi ne matakin farko kuma abin da ke fara shiga kunnen mai sauraro, kuma wannan ya zama tamkar wajibi a waƙoƙin Hausa a yau. Wannan ya ƙunshi abu biyu kamar haka:

a.      Kiɗa

b.      Amshi

Da yawa daga cikin waƙoƙin ƙarni na 21, abun da ake fara ji a cikinsu shi ne kiɗa da amshi ko kiɗa sannan amshi ko amshin ya riga kiɗan. Misali: Waƙar Amina Buni Yadi ta Dokta Yarima Ngama ta fara da kiɗa da amshi kamar haka:

An samu kiɗa:------------------------ Sannan amshi.

Amshi: Minista Dokta Yarima Lawan gwanin talakawa mai nasara,

Magauta dole su ƙyale ka ka kawo gyara PDP.

(Amina Buni Yadi: Waƙar Dokta Yarima Ngama)

Idan aka saurari waƙar Amina Buni Yadi da ta yi wa Dokta Yarima Ngama abin da aka fara ji kiɗa ne, sannan amshi kamar yadda aka gani cikin misalin da ya gabata.

Haka waƙar Kamilu Hussaini Nguru wadda ya yi wa Atiku Bagudu, ita ma abun da aka fara ji shi ne kiɗa da amshi kamar kaha:

Kiɗa: ------------------------------- Sannan Amshi.

 

Amshi: Waƙe na jihar Kebbi na koma, gwarzo Bagudu ne gwamna,

Abin da kake mana na gaskiya, Bello ne ya faɗa mana halinka.

(Kamilu Husaini Nguru: Waƙar Atiku Bagudu)

Idan aka lura da wannan misali, za a ga cewa Kamilu Husaini Nguru ya fara amfani da kiɗa sannan amshi a waƙarsa da ya yi wa Atiku Bagudu, Hakan ya nuna cewa kiɗa da amshi su ne mataki na farko da mawaƙan ƙarni na ishirin da ɗaya ke amfani da shi wajen buɗe waƙoƙinsu.

3.1.2 Sharar fage:

Wannan shi ne gabatar da wasu kalmomi kafin fara waƙa waɗan da suka ƙunshi abubuwa kamar haka:

       Ambaton sunan mawaƙi

       Ambaton sunan wanda za a yi wa waƙa

       Ambaton sunan waƙa.

       Ambaton sunan wanda ya ɗauki nauyin waƙa

       Ambaton lambar wayaA

       Yin sallama ga masu sauraro

Wasu waƙoƙin wannan ƙarni na 21 akan yi sharar fage kafin ko bayan kiɗa da amshi wanda yakan ƙunshi abubuwan da aka lissafo gaba ɗaya a ƙarƙashin sharar fage a wasu lokuta, a wasu lokutan kuma sharar fagen takan shafi wasu ne daga cikin abubuwan da aka zayyan a ƙarƙashin sharar fagen. Misali: Waƙar Kabiru Kilasik da ya yi wa Cigarin Mafara.

07036650441, 08123225152

Assalamu alaikum mai sauraro,

Kabiru Classic ne ke ɗauke da sabuwar waƙa,

Cigarin Mafara Barista Mainasara Mika’ilu Tafida,

Wanda aka fi sani da suna Hasken Cigarin Mafara.

A yi sauraro lafiya.

(Kabiru Kilasik: Waƙar Cigarin Mafara)

A wannan waƙar ta Kabiru Kilasik da ya yi wa Cigarin Mafara, an samu sharar fage da ya ƙunshi lambar waya da sallama da sunan mawaƙi da kuma sunan wanda aka yi wa waƙa.

Haka waƙar Yahaya Sauwa da ya yi wa Ciroman Kebbi mai taken “Alheri” ta zo da sharar fage kamar haka:

Assalamu alaikum al’ummar jihar Kebbi baki ɗaya,

Ga Yahaya Bala Sama’ila Sanwa ɗauke da sabuwar waƙa,

Mai suna Wutar kara izar masu ɗiya,

Ya yi wannan waƙa ne ga Alhaji Muhammadu Mera,

Mai neman tsayawa takarar kujerar jihar Kebbi,

Mai neman ƙarin bayani sai ya ƙira lambar waya kamar haka,

08068070503. Ayi saurare lafiya.

(Yahaya Sauwa: Waƙar Alheri ta Ciroman Kebbi)

Wannan misali ya bayyana yadda sharar fagen ya ƙunshi sallama da ambaton sunan mawaƙi da sunan wanda aka yi wa waƙar da lambar waya.

Assalamu alaikum.

Za ku saurari waƙa daga bakin ni Amina Buni Yadi,

Wadda aka yi wa maigidanmu Yarima Ngama,

Ƙarƙashin jagorancin Alƙali B.A. Don neman

Ƙarin bayani za a iya nemanmu ta lambar waya kamar haka,

08062931262 A yi saurare lafiya.

Jagora: Na gode tabara sarkin kyauta Tabara mai baiwa da yawa,

Almaliku mai yanayin sanyi Tabara kai ke ba mu ruwa,

Ka ninka salati ba adadi ga Annabi mai kyawon tsayuwa,

Na sanya sahabbai musu son zaman lumana ba sa son rigima,

(Amina Buni Yadi: Waƙar Dokta Yarima Ngama)

Ta la’akari da wannan misalin za ga cewa an samu sharar fage da ya ƙunshi sallama ga masu saurare da sunan mawaƙiya da sunan wanda aka yi wa waƙa da wanda aka gudanar da waƙar a ƙarƙashin jagorancinsa, sannan aka kawo lambar waya a ƙarshe.

3.1.3Ambaton Allah:

Wannan hanya ta haɗa abubuwa da dama kamar haka:

a.      Gaskata shi

b.      Yabon sa

c.       Girmama shi

d.     Yi masa kirari

Mawaƙan ƙarni na 21, na amfani da salon buɗewa na ambaton Allah ta hanyar yabon sa ko girmama shi ko yi masa kirari ko gaskata shi.

Misali: Kamilu Husaini Nguru a waƙarsa ta Atiku Bagudu ya yi amfani da ambaton Allah wajen buɗe waƙarsa inda yake cewa:

Jagora; Sarki buwayi gwani Allah, ka san shi ne masanin mulki,

Shi ne ya yi yo jaki na gida cikin iko nasa yai doki,

Shi ne ya yi yo mutumin banza, sannan ya yiyo mutumin kirki,

Haka nan ya yiyo ɓauna a dawa sannan Allah haka yai zaki,

Mu yi nema na halal jalla shi ya hana mu je sata.

(Kamilu Husaini Nguru: Waƙar Atiku Bagudu)

Wannan misali bayyana yadda Kamilu Husaini Nguru ya yi amfani da ambaton Allah a yayin buɗe waƙarsa. Kuma ambaton ya zo ta hanyar kirari da girmama Allah (SWT) inda mawaƙin ya nuna buwaya da gwanintar Ubangiji wajen halitta.

Haka Amina Buni Yadi ita ma ta zo da irin wannan salo a mabuɗin waƙarta da ta yi wa Dokta Yarima Ngama kamar haka:

Jagora: Na gode Tabara sarkin kyauta Tabara mai baiwa da yawa,

Almaliku mai yanayin sanyi tabara kai ke ba mu ruwa,

Ka ninka salati ba adadi ga Annabi mai kyawon tsayuwa,

Na sanya sahabbai musu son zaman lumana bas a son rigima.

(Amina Buni Yadi: Waƙar Dokta Yarima Ngama)

Wannan misali ya nuna yadda Amina Buni Yadi ta yi amfani da ambaton Allah a mabuɗin waƙarta da ta yi wa Dokta Yarima Ngama. Ambaton Allah (SWT) ya zo ta hanyar godiya da yabo a gare shi bisa kyautar da ke yi wa bayinsa ta hanyar kawo ruwa da sanyi da sauran ni’imominsa

Shi ma Ali Mega a waƙarsa ta “To A Yi Dai Mu Gani”, ya yi amfani da irin wannan salo wajen buɗe waƙarsa misali:

 Jagora: To da fari Tabara gwani shi ne wanda ya ƙagi wuta da ruwa,

Mahaliccin saman bakwai da ƙassai ga mu cikin matsuwa,

Taimaka mana rabbi guguwar canji ta fara hawa

Mulkin kama-karya ‘yan Yobe muna faman taɓuwa,

Allah sarkin haƙuri canja mana wanda ba za su ci ba.

 

Jagora: To Rabbi sarki gatanmu ƙara mana son manzoka fari,

Ɗan Amina rasulullahi kowa ya riƙa ya yo katari,

Jalla har da sahabbansa da sahabbai gida haƙuri,

Allah kai za ka yi, kai kake mana ba wani ɗan zina ba.

(Ali Mega: Waƙar To A Yi Dai Mu Gani)

Wannan misali ya nuna yadda Ali Mega ya yi amfani da ambaton Allah (SWT) a yayin buɗe waƙarsa mai taken “To A Yi Dai Mu Gani”.Ambaton ya zo ta fuska kirari ta hanyar nuna gwanintarsa kan halittar wuta da ruwa da sammai bakwai da ƙassai bakwai.

3.1.4 Yin addu’a

Wannan hanya da mawaƙi ke bi roƙon Allah wata buƙata, kamar su:

a.      Neman basira ta tsara waƙa

b.      Neman buɗi na ilimi

c.       Neman tsira da sauransu.

Mawaƙan ƙarni na 21, ba a bar su a baya ba wajen yin addu’a a cikin mabuɗin waƙoƙinsu. Ga wani Misali:

Ali Mega a waƙarsa ta “To A Yi Dai Mu Gani” ya yi amfani da addu’a inda yake cewa:

Jagora: To Rabbi sarki gatanmu ƙara mana son manzoka fari,

Ɗan Amina rasulullahi kowa ya riƙa ya yo katari,

Jalla har da sahabbansa da sahabbai gida haƙuri,

Allah kai za ka yi, kai kake mana ba wani ɗan zina ba.

(Ali Mega: Waƙar To A Yi Dai Mu Gani)

Ta la’akari da yadda mawaƙin ya tsara mabuɗin wannan waƙar, za a ga cewa, an yi amfani da addu’a inda mawaƙin ke neman Allah ya ƙara mana son manzo da sabbansa.

Sai kuma waƙar Ɗahiru Na Maikwari, wanda ya yi wa Abu Magaji, ita ta zo da irin wannan salo kamar haka:

 Jagora: Abu Magaji Allahu ka ƙara ɗaukaka,

Abu Magaji ka yi mana Allahu yai maka,

Abu Magaji dan manzo ɗaha mai Maka

Kariya ya yo maka kowa ba shi yo maka,

Shatima Bature giwa ba a far maka,

Kura ki ƙara haushi zaki ya far miki,

(Ɗahiru Na Maikwari: Waƙar Abu Magaji)

A wanna misali za a ga yadda Ɗahiru na Maikwari ya yi amfani da addu’a wajen buɗe waƙarsa, inda yake fatar Allah ya ƙara wa maigidansa Abu Magaji ɗaukaka.

3.1.5 Ambaton Annabi Muhammadu ( Mai tsira da amincin Allah):

Wannan hanya ce da ake bi wajen yi masa abubuwa kamar haka:

a.      Salati

b.      Yabonsa

c.       Kamun ƙafa gare shi

d.     Ambaton Alayensa

e.      Ambaton Sahabbansa

f.        Sauran Annabawan Allah.

A ƙarni na 21, wasu mawaƙa kan yi amfani da wannan salo wajen buɗe waƙoƙinsu wato ambaton Annabi. Mawaƙan sukan yi hakan ne ta hanyar salati ko yabo ko kamun ƙafa ko ambaton alaye ko sahabbansa. Misali:

Muhammadu Barnin Magaji a waƙarsa ta Salisu Tafida ya yi amfani da irin wannan salon wajen buɗe waƙar kamar haka:

Jagora: Rayuwata ta nutsu kullum ni so nake in ga Muhammadu,*2

Cikin dare ban bacci kullum ka gan ni na koma can Kudu,

Ban da aikin yi sai sallah na riƙi Allah in ga Muhammadu,

Na yi Gabas na yi Yamma na dawo Arewa kai har na koma kudu,

Tsaya tsakiya cak ni dai farin cikina in ga Muhammadu,

Allah idan ka haɗa ni da manzonka na sani na ƙare lafiya.

(Mahammadu Birnin Magaji: Waƙar Salisu Tafida)

Wannan misali ya nuna yadda Muhammadu Birnin Magaji ya yi amfani da begen Annabi wajen buɗe waƙarsa ta Salisu Tafida. Ta hanyar fatarsa ita ce kullum ya ga Annabi Muhammadu.

Haka shi ma Yahaya Sauwa a waƙarsa ta “Alkairi ta Ciroman Kebbi”, ya yi amfani da irin wannan salo ga abin da ya ce:

Jagora: Annabinmu ɗan gatan Allah wanda ba ya zalunci,

Mai isar cika wajen Allah mai hali da karamci,

Rayuwa da ba ta begenka ba ta hurce ƙasƙanci,

Kai muka biya ɗan Abdallah kai ɗai ka ceto mu.

(Yahaya Sauwa: Alkairi ta Ciroman Kebbi)

A nan an ambaci Annabi ta hanyar yi masa yabo, inda mawaƙin ya bayyana halinsa na karamci, ya kuma nuna rashin begen Annabi zai jawo ƙasƙanci. Sannan ƙarshe ya yi kamun ƙafa gare shi, don neman ceto.

Shi ma Kabiru Kilasik ya zo da irin wannan misali na salon buɗe waƙa a waƙarsa ta Cigarin Mafara kamar haka:

Jagora: Manzo ƙaunarka nake, ni kan zaɗin ka nake,

Manzo Allah mai hana ƙarya, Ilahi ƙaunarka nake,

Manzona ma’asumi bayin Allah, sarkinmu kake,

Kowa ya yarda da manzona, a ƙiyama za ya sam tsira.

(Kabiru Kilasik: Waƙar Cigarin Mafara)

A wannan misali mawaƙin ya ambaci Annabi (SAW) ta hanyar nuna masa ƙauna, sannan kuma ya yabe shi.

3.1.6 Rashin Mabuɗi

Wannan wata hanya ce da mawaƙi ke bi yayin fara waƙarsa inda ba zai yi amfani da kowace hanya ba daga cikin hanyoyin da aka ambata a sama sai dai hanya ta farko kaɗai wato, ba amfani da kiɗa ko amshi. Galibi mawaƙa a wannan ƙarnin sun fi amfani da wannan hanya, musamman a waƙoƙin soyayya. A taƙaice ana iya cewa babu wata takamammiyar hanya ko wani salo na musamman da suke amfani da shi a yayin buɗe waƙoƙinsu. Sai dai galibi mawaƙi yakan fara ne da wasu abubuwa kamar haka:

Bayar da umarni ga masu yi masa kiɗa ko amshi, inda zai nemi su ba shi kiɗa, ko wani abu mai kama da haka. Misali;

Umar M. Sharif shi ma ya yi amfani da maimaita amshin waƙarsa wajen buɗe waƙar kamar haka:

Amshi: Hafiz kai nake so a zuciya, tsaya ka saurare ni,

Hafiz ka daɗe a zuciya, kar ka kore ni.

(Umar M. Sharif: Waƙar Hafiz Kai Nake So)

A nan an ga misalign yadda Umar M. Sharif ya fara waƙa ba tare da bin ɗaya daga cikin matakan da aka zayyana a sama ba. Sai dai ya yi amfani da wasu kalmomi na soyayya ne wajen fara waƙar.

Nura M. Inuwa a waƙarsa ta Hussuna da Huzzuna ya buɗe waƙar da amshi wanda ke ɗauke da wasu kalaman soyayya, kamar haka:

Amshi: Huzzina na yi tuntuɓe, nai gam-da-katar da dinshina,

Idanu dole yai rufewa, ba nisa garin masoyi.

(Nura M. Inuwa: Waƙar Hussina da Huzzina)

Wannan misali ya nuna yadda Nura M. Inuwa ya fara waƙarsa ta Hussina da Huzzina ba tare da bin matakan buɗe waƙa da aka kawo a sama ba. Sai dai ya yi amfani amshi mai bayyana sunan masoyiyarsa.

Waƙar Hauwa ‘Yar Filani ta Yankari ba ta da mabuɗi, ta fara waƙar ta hanyar nuna mamakinta ga dajin Yankari kamar haka:

Jagora: Yankari ƙudura ta Allah daji na al’ajab,

Sansani na ahalil dabbobi,

Giwa zaki Burungu ga Ɓauna saniyar sake

Nau’i nau’i cikin cikn dabbobi.

(Hauwa ‘Yar Fulani: Waƙar Yankari)

Wannan misali ya bayyana yadda Hauwa ‘Yar Fulani ta fara waƙarta ta “Yankari” ba tare da bin matakan buɗe waƙa da aka ambata a sama ba. Sai dai ta fara waƙar ne kai tsaye da mamakin ikon Allah (SWT) game da sha’anin dajin Yankari.

Haka Dauda Kahutu Rarara ya yi a waƙarsa ta “Mai Malafa Ya Karya Ta Ƙure”, ita ma ba mabuɗi ya fara waƙar yana cewa:

 Mai malafa ƙarya ta ƙure,

Ku faɗi ko kar ku faɗi, sama,

Mai malafa ƙarya ta ƙure

PDP ta mutu an gama.

(Dauda Kahutu Rarara: Waƙar Mai Malafa Ƙarya ta Ƙure)

Idan aka dubi wannan misali za a ga cewa Dauda Kahutu Rarara bai yi amfani da matakan buɗe waƙa da aka zayyana a sama ba. Sai dai ya buɗe waƙar ne da amshi mai ɗauke da taken waƙar, inda yake nuna gazawar abokin takarar maigidansa.

4.0 Kammalawa

Wannan takarda ta dubi muhimmancin waƙa ga al’umma da taƙaitaccen tarihin samuwarta tun daga ƙarni na 17 har zuwa na 20 da ma’anar waƙa da hanyoyi da magabata suka bi wajen amfani da mabuɗi a waƙoƙinsu. Sannan aka shiga zuciyar takardar wato, tsarin mabuɗin waƙoƙin ƙarni na ishirin da ɗaya, inda aka kawo matakai shida da mawaƙan ƙarni na 21 ke amfani da su yayin buɗe waƙoƙinsu. Matakan sun haɗa da; take wanda ya ƙunshi kiɗa da amshi da sharar fage wanda ya ƙunshi sunan mawaƙi da sunan wanda aka yi wa waƙa da wanda ya ɗauki nauyin waƙa da lambar wayar mai waƙa da gabatar da sallama ga masu sauraro. Sai kuma ambaton Allah wanda ya ƙunshi gaskata maganarsa da yabonsa da girmama shi da ya masa kirari. An dubi addu’a da mawaƙan ke yi kamar nema ƙarin basira ta tsara waƙa da ƙarin ilmi da neman tsari da sauransu. An kawo ambaton Annabi wanda ya haɗa da; salati da yabo da kamun ƙafa a gareshi da ambaton iyalansa da sahabbansa da sauran Annabawa. Sannan aka dubi rashin mabuɗi. Misalan da aka kawo sun tabbatar da samuwar waɗannan matakai na buɗe waƙoƙi a wannan ƙarni na 21. Kana daga ƙarshe aka kawo jawabin kammalawa.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

Atuwo, A. A. da Bunza, D. B. (2014). “Transformation of Hausa Poems in the 21 Century” Taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa. Sashen Nazarin Harsunan Najerya, Jami’ar Bayero, Kano.

Auta, A. L. (1986). “Gudumawar Waƙoƙin Makaɗan Baka Dangane da Adana Tarihi Kundin Digiri na biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bunza, D. B. (2015). Aron Murya Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa A cikin Yobe Journal of Language, Literature and Culture.Yobe; Department of African Languages Linguistics.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

Ɗanjuma, S. (1992). “Rabe-Raben Waƙoƙin Hausa da Tasirinsu ga Rayuwar Hausawa”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.

Dunfawa, A. A. (2002). “Waƙa A Tunanin Yara”. Kundin Digiri na uku, Sokkwato: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Dunfawa, A. A. (2014). “Makaɗan Zamani: Wani Ƙarin Kaso na Rukunin Makaɗa”. Takarda da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa, ƙarni na 21, a Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S. M. (2002). “Salo a Waƙoƙin Baka: Tsokaci Kan Turke da Rabe-Rabensa”. A Cikin Nazari a Kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausa, Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Gusau, S. M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publisher Limited.

Gusau, S. M. (2011). Adabin Hausa A Sauƙaƙe. Kano: Century Research and Publishers Limited.

Isah, Z. (2013). “Farfaganda A Waƙoƙin Fiyano Na Hausa Daga 2003-2013”. Kundin Digri na Biyu, Zariya: Department of African Languages and Cultures Ahmadu Bello University, Zariya.

Jamilu, A. (2019). “Siyasa Aƙida:Nazarin Jigon Aƙida A Waƙoƙin Kabiru Yahaya Kilasik”. Kundin Digri na Biyu, Sokkwato: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Omar S. (2013). Mabuɗi da Marufi a Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja A cikin Ɗunɗaye Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Sa’id, B. (2002). “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin a Jahohin Sokoto da Kabi da Zamfara: Nazari a Kan Bunƙasarsu Da Hikimomin da ke cikinsu”. Kundin Digiri na Uku, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Usman B.B. (2018). Ruwa Biyu: Sabon Zubin Waƙoƙin Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya A cikin Yobe Journal of Language, Literature and Culture.Yobe; Department of African Languages and Linguistics.

Yahya, A. B. (1995). “Ƙawancen Jigo Tsakanin Waƙoƙin Sarauta na Baka da Rubutattu’’. Takarda Wadda aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yahya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yahaya, I. Y. (1988). Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Kamfanin Buga Littattafai Na Arewa.

Sabon Salon Bude Wakoki a Karni Na Ishirin Da Daya

Post a Comment

0 Comments