Article Citation: Baffa, A.S. & Ibrahim, O.M. (2025). Harshe Makamin Yaƙi: Taƙaddama Cikin Soyayyar Zamani a Waƙoƙin Ƙarni na Ashirin da Ɗaya. Zauren Waƙa, 4(2), 41-49. www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.005.
HARSHE
MAKAMIN YAƘI: TAƘADDAMA CIKIN SOYAYYAR
ZAMANI A WAƘOƘIN ƘARNI NA ASHIRIN DA ƊAYA
Na
Ahmed
Sulaiman Baffa
Department
of African Languages & Linguistic
Yobe
State University, Damaturu
GSM:
07068946160
Da
Ogah
Muhammed Ibrahim
Department
of General Studies & Pre-ND
Isa
Mustapha Agwai I Polytechnic, Lafia
Tsakure
Shigowar
baƙin al’adun Indiyawa
da Turawa ga al’ummar Hausawa ya haifar da sauye-sauye masu ɗinbin yawa ga waƙoƙin ƙarni na 21. Wannan
dalili ya sa manazarta ke ƙoƙarin fito da sababbin sigogin da aka
gano. Saboda haka babban manufar wannan takarda shi ne, nazarin wasu waƙoƙin ƙarni na21 don fito da
sabo salo na taƙaddama. A yayin
gudanar da wannan nazari an yi amfani da hanyar Yahya (2001). Takardar ta bayyana
cewa taƙaddamar soyayya na
daga cikin manyan sauyi da aka samu, kuma taƙaddamar ta kasu gida
uku; farar taƙaddama da baƙar taƙaddama da taƙaddama mai dungu.
Kuma takardar ta gano cewa kowanne daga ciki ta kasu gida biyu dangane da
jinsi, wato ta taƙaddamar maza da ta
mata.
1.0
Gabatarwa
Sakamakon cuɗanya
da alaƙar Hausawa da wasu
al’ummomi waɗanda ba su ba, ta hanyar kallon
fina-finai da silima da majigi da karancc-karancen littattafan soyayya waɗanda
suka zama ruwan dare gama duniya. Irin waɗannan su ka zama
sanadin samuwar wasu sabbin salailai da saƙonni a waƙoƙin ƙarni na 21 na Hausa. Tasirin ɗabi’u da al’adun wasu
al’ummomi ya sa soyayya ta zama manufa ma fi girma a waƙoƙin ƙarni na 21, wanda hakan
ya haifar da samuwar sababbin salaialai da sauyawar sigogi a waƙoƙin ƙarni na 21. Daga
cikin irin waɗannan salailai akwai salo taƙaddamar soyayya. Taƙaddamar soyayya wani sabon salo ne da
ake samu a waƙoƙin ƙarni na 21, musamman waƙoƙim fina-finai inda
ake samun maza biyu su yi taƙaddama
kan soyayyar mace ɗaya, a wasu lokuta kuma ’yan mata biyu
ke yin taƙaddama kan soyayyar
namiji ɗaya. Irin wannan salo ana aiwatar da
shi ta fuskoki da dama, inda ake samun farar taƙaddama da baƙar
taƙaddama da kuma taƙaddama mai dungu. A wannan takarda za a
bayyana kowanne daga ciki da ɗaya bayan ɗaya.
Ta la’akari da sauye-sauyen da ake samu
a wannan ƙarni na 21 dangane da
abin da ya shafi waƙoƙi ana iya cewa, an samu ƙare-ƙare da dama ta fuskoki masu yawa musamman manufofin waƙoƙi a wannan ƙarni
kamar yadda za a bayyana a wannan takarda.
2.0 Sharhin Muhimman
Kalmomi:
Muhimman kalmomin da za a kawo ma’anoninsu
sun haɗa da harshe da taƙaddama da kuma soyayya. Ga ma’anonin
kalmomin kamar haka:
2.1 Harshe
Ƙamusun Hausa (CNHN 2006:) ya bayyana ma’anar harshe da cewa,
hanyar magana tsakanin al’umma iri ɗaya.
2.2
Taƙaddama
Kalmar taƙaddama asalinta kalma ce ta Larabci Bahaushe ya are ta daga
Larabci, tana da ma’anar gabatuwa wajen gudanar da wani abu. A wajen Bahaushe
kuma kalmar tana ɗaukar ma’anar jayayya ko musu ko rigima
ko gardama, Ƙamusun Hausa (CNHN
2006) ya bayyana ma’anar gardama da cewa, jayayya ce ta magana tsakanin mutum
biyu ko fiye.
2.3
Soyayya
Ƙamusun Hausa (CNHN 2006) ya bayyana ma’nar soyayya da nuna ƙauna daga ɓangarori
biyu na masu ƙaunar juna, musamman
mace da namiji.
3.0
Taƙaddamar Soyayya A Waƙoƙin Ƙarni Na 21
Ƙamusun Turanci da
Larabci (A/E), ya bayyana kalmar ‘taƙaddama’ da cewa, (progress). Ma’anar kalmar a Larabci na
nufin cigaba. Bisa fahimta a Hausa kalmar tana da ma’anar gardama. CNHN
(2006:158), ya bayyana ma’anar gardama da cewa, ita ce jayayyar magana tsakanin
mutum biyu ko fiye. Bisa fahimta an lura da cewa, akwai wata dabara da aka
kalle ta da matsayin taƙaddama, la’akari da
ma’anar da masana suka kawo.
Kasancewar
Allah Ta’ala ya sanya maganaɗisu na son juna
tsakanin maza da mata wanda ya haifar da soyayyar juna da shaƙuwa da ƙallafuwar rai tsakanin juna. Wannan ya sa masu shirya
fina-finai na bayyana taƙaddamar da ke faruwa
tsakanin masoyan. Saboda ƙoƙarin isar da wannan saƙo, da ganin an cimma buri kan abin da
ake buƙata, mawaƙa da dama na rera waƙoƙi waɗanda ke ɗauke da salon taƙaddama, don ganin saƙon ya isa kamar yadda ake so.
Duk
lokacin da aka ambaci taƙaddamar soyayya, abin
da zai fara zuwa cikin tunani shi ne maza ne kaɗai ke yin wannan taƙaddamar, alhali taƙaddama tana kasancewa tsakanin ‘ya’ya
mata a kan wani saurayi. Kamar yadda za a bayyana cikin wannan aiki da hakan
yana nuna irin matsayin da Hausawa suka kai a fagen soyayya a yau.
Bisa ga yadda bayanai suka gabata game da karkasuwa da
nau’o’in taƙaddama, idan a ka
lura da kyau za a fahimci cewa, taƙaddamar ta kasu gida uku, kamar haka
3.1
Farar Taƙaddama
An ambaci wannan nau’i ne da wannan
suna saboda yanayi ne na ja-in-ja tsakanin mutane biyu (mata ko maza) a kan
wanda suke so, alhali shi wanda ake son yana son kowanne daga cikin masu taƙaddamar. Mawaƙa da dama kan bayyana irin wannan salo,
inda wanda ake son zai rasa yanda zai yi, sai dai ya nemi masu taƙaddamar su yi sulhu ko kuma ya nemi
shawara daga gare su, don samun mafita. Za a iya ganin wannan salo a waƙar Umar M. Sharif mai suna “Taƙaddama”kamar haka:
Yarinya: Ku saurare
ni ku ji,
Zan yi kason so, don
ku ji,
Domin niy yo ku ji,
Kun cancata da so,
Kun cancanta da so
bai ɗaya.
Ku sulhunta ‘yan’uwa,
Ku sasanta ku yi yo
rantsuwa,
Wanda ya ɗakko
rawa,
Ba zan gaza ba ina,
Ba zan gaza ba ina
magiya.
(Umar M. Sharif: Waƙar Mujadala)
Irin wannan salo ya ci gaba da bayyana
a cikin waƙar Nura M. Inuwa,cikin
taƙaddamar da ta faru tsakanin Husuna da
Huzzuna a kan masoyinsu. Masoyin ya so kowanne daga cikinsu, sai dai kira yake
gare su, don su daidaita kuma su nema masa mafita. Don haka yake cewa:
Husunah da Huzuna,
yau guna kun zamo masoya,
Banbancinku ko a suna
bai da yawa, ko za a juya,
Har in babba yana da
laifi, yaro ma yana da ƙiuya
Kun samin farin ciki,
ku za ku fitar da yadda zan yi.
Babu abin da zan faɗi,
wanda ya wuce in ta son ku,
Sannan nai kira ga
kaina, domin kar ku dami kanku,
Daidaito nake nufin
yi, babu sifa irin ta tunku,
Domin kau da rigima,
so shi zai zamo manjanyi.
(Nura M. Inuwa: Waƙar Hussuna da Huzzuna)
3.2
Baƙar Taƙaddama:
An ambaci wannan nau'i ne da wannan
suna kasancewar jayayya ce da mutum biyu ke yi a kan masoyi guda, alhali shi
wanda ake taƙaddamar a kansa ba ya
ƙaunar masu taƙaddamar. Don akwai wanda yake so, ko
kuma ta hanyar munafuntar masu yin taƙaddamar. Umar M. Sharif a waƙarsa mai suna “Hafiz Kai Na So A Zuciya” ya bayyana wa masu
taƙaddama a kansa cewa ba ya ƙaunar su, kuma da wadda yake so kamar
haka:
Ƙanwa: Hafiz kai na so a zuciya, tsaya
ka saurare ni.
Yaya: Hafiz ka daɗe
a zuciya, kar ka kore ni.
Hafiz: A’a soyayya da
ra’ayi ni Hafiz da wacce nake so.
Hafiz: Allah ɗaya
gari banban, sam-sam ba ku dace da ni ba,
Dan ban kama da ku
ba, kalaman naku ba za su shigan ba,
Ba zan saki jiki ba na
saurare ku, ku ba tsari na ba,
Yaya da ƙanwa ya kuke hakan? Bai dace da ku ba.
(Umar M. Sharif: Waƙar Hafiz Kai Nake So)
Irin wannan salo ya sake bayyana a waƙar Ali Jita da Manga Muhammad mai suna
“Wacce Nake So Ita Ce Abokina Yake So” inda abokan biyu suka yi taƙaddama da juna kan mace ɗaya
ba tare da sani ba. Ashe yaudarar su take, ba son su take ba. Ga yadda suke
cewa :
Dakata na ce tsaya,
ya sunanta ba ka shaidan ba,
Kai sunanta kan ya ka
ɓoye min ba ka furtan ba,
Na tambaye ka, a’a ni
na tambaye ka.
Haba abokina, bai
kamata muna yin jayayya ba,
Mu bi abin a sannu,
a’a kai ya kamata ka bi shi a sannu.
Sunan tawa Sadiya
Allah sa, dai kai ba ita ce ba,
Sunan tawa Sadiya,
ina ganin ba daidai ne ba.
Wanda nake so ita ce
aminina yake so.
Wanda nake so, ita ce
aaminina yake so.
Mun gano ta, ita ce
Halimatus Sadiyya.
Mun gano ta, ita ce
Halimatus Sadiyya.
(Ali Jita da Manga: Waƙar Wanda Nake So)
3.3
Taƙaddama Mai Dungu
Wannan yanayi ne na taƙaddama wanda aka samu wanda ake taƙaddama a kansa ya karkata ga wani ɓangare
daga cikin masoyan. Irin wannan taƙaddama takan zamo mai zafi ainun fiye da sauran da aka
ambata a baya. A irin wannan taƙaddama
akan samu musanyan zafafan kalmomi a tsakanin juna. Za a iya ganin misalin haka
a waƙar “Uwargida da
Amarya”, kamar haka:
Uwar gida: Kai gafara
ka matsa mini, wawa baƙin namiji,
Wai ni ka yi wa
kishiya, ka ɗauke ni ban da aji,
Karya ka ɗauko
ko mutum ce mai kamar namiji,
Zafi kamar yaji,
maganarta kamar gunji,
‘Yar fim kamar juji,
mai satar miji ta aje,
Ƙarya take ƙarya kake, dube ka sha-ka-tafi.
Amarya: Ni dai mijina
zan kula, hakkinka za na tsare,
In dai ta zagen ban
kula ta, kar ka zo ka tare,
Aure take aure nake, ƙarya take na ware,
Ni dai ba zan bijire
ba, tilas na ɗauki tire,
A gare ta mui nazari,
ka taho ka ɗan share,
In ta guje ma zan riƙe ka, yaka zo mu tafi.
(Sadik Sani Sadik: Waƙar Uwargida Da Amarya)
Irin wannan taƙaddama ta ci baga da bayyana cikin waƙar da Sani Danja da Ali Nuhu suka yi taƙaddama kan masoyiya guda, cikin waƙa mai suma “Ga Ni Ga Ka”. Ga yadda abun
ya kasance:
Sani Danja: Sashina
na yi karewa, ga ni ga ka,
Kar ka shigo gona
tawa, ga ni ga ka,
Na riga ka tun da daɗewa,
ga ni ga ka,
Saura ƙiris mu yo tarewa, ga ni ga ka,
Ali Nuhu: Na zamo
tauraro, ga ni ga ka,
Ni aka sauraro, ga ni
ga ka,
Ni na zamo toro, zaki
a daji bai tsoro
Baƙar magana ka zazaro, ga ni ga ka,
Kai ne fa ka faro,
zamban aminci nai tsoro ga ni ga ka.
Masoyiya: So bai ƙarewa, so bai canzawa,
Wanda nake ƙauna da’iman,
Fa ba zai canza ba, ga ni ga ka.
(Ali Nuhu da Sani Danja: Waƙar Ga-ni-Ga-ka)
Bayan wannan kuma, bisa ga yadda bayanai da suka gabata suka
yi game da karkasuwa da nau’o’in taƙaddama, idan aka lura da kyau za a fahimci cewa, kowacce
daga cikin nau’in da aka bayyana a sama zai iya kasuwa gida biyu, wato ta
fuskar jinsin masu aiwatar da wannan taƙaddama, lura da cewa maza na yin taƙaddama a kan soyayyar mace, haka mata
ma na yin taƙaddama a kan soyayyar
namiji. Saboda haka taƙaddamar ta sake
kasuwa gida shida, kamar haka:
a. Farar
Taƙaddama Ta Maza
b. Farar
Taƙaddama Ta Mata
c. Baƙar Taƙaddama Ta Maza
d. Baƙar Taƙaddam Ta Mata
e. Taƙaddama Mai Dungu Ta Maza
f.
Taƙaddama Mai Dungu Ta Mata
4.1 Farar Taƙaddma ta Maza
Wannan taƙaddama
ce tsakanin maza biyu, kuma wanda ake taƙaddamar a kanta tana son masoyan gaba ɗaya.
Mawaƙin fim mai suna Umar
M. Sharif ya bayyana irin wannan salo a waƙarsa mai suna “Albishirinka Ɗan uwa” inda yake cewa:
Ƙani:
Bari in risina maka,
Don Allah kai ɗaukaka,
Ka bar ni in mallaki kin,
Ka bar ni in mallaki kintsattsiya.
Yaya: Girman yau na
bar maka,
Don son ta ya yi babbaka,
Ya ƙone ni don haka,
A cin girma fa abin zai wuya.
Yarinya: Ku sulhunta ‘yan uwa
Ku sasanta ku yiwo rantsuwa,
Wanda ya ɗakko
rawa,
Ba zan gaza ba ina,
Ba zan gaza ba ina magiya.
(Umar M. Sharif: Waƙar Mujadala)
Ta la’akari da waɗannan baitoti za a ga
yadda ƙani ke roƙon wansa ya ci girma ya bari ya mallaki
yarinya kintsattsiya. Shi kuma yayan ya nuna ya bar mar girman, ba zai iya haƙuri ba, saboda son masoyiyar ya ƙona masa zuciya har ta babbake. Ita
kuma ba ta ware wanda take so ba daga cikinsu sai dai tana ba su shawara su yi
sulhu da junansu su sasanta.
4.2 Farar Taƙaddama ta Mata
Wannan taƙaddama
ce tsakanin ‘yammata biyu da ke son saurayi ɗaya, kuma shi ma yana
son su gaba ɗaya. Irin wannan salo ya bayyana a
cikin waƙar Nura M. Inuwa
kamar haka:
Banbancinku ko a suna bai da yawa, ko
za a juya,
Har in babba yana da laifi, yaro ma
yana da ƙiuya
Kun sa min farin ciki, ku za ku fitar
da yadda zan yi.
Babu abin da zan faɗi,
wanda ya wuce in ta son ku,
Sannan nai kira ga kaina, domin kar ku
dami kanku,
Daidaito nake nufin yi, babu sifa irin
ta tunku,
Domin kau da rigima, na so shi za ya
zamo manjanyi.
(Nura M. Inuwa: Waƙar Hussuna da Huzzuna)
A cikin waɗannan baitoti Hafiz
ya bayyana yadda Hussuna da Huzzuna suka kamu da son sa, tare da nuna ƙaunarsa gare su. Kuma ya nuna banbancin
sunayensu bai da yawa. Saboda haka ba abin da ya wuce yai ta son su. Don haka
kar su damu a daidaita don kau da rigima tsakanin juna.
4.3 Baƙar Taƙaddama ta Maza
Wannan taƙaddama
ce da maza biyu ke yi a kan mace ɗaya, a yayin da ita
kuma ba ta son ko ɗaya daga cikinsu. Irin wannan salo ya
bayyana a waƙar Ali Jita da Manga
Muhammad mai suna “Wacce Nake So” inda abokan biyu suka yi taƙaddama da juna kan mace da ta yaudare
su, ba tare da sani ba. Ga yadda suke cewa:
Ali Jiti: Dakata na ce tsaya, ya
sunantan ba ka shaidan ba,
Manga: Kai sunanta kan yakan ɓoye
min ba ka furtan ba,
Na tambaye ka, a’a ni na tambaye ka,
Haba abokina, bai kamata muna yin
jayayya ba,
Mu bi abin a sannu, a’a kai ya kamata
ka bi shi a sannu.
Sunan tawa, Sadiyya Allah sa, kai ba ita
ce ba.
Sunan tawa Sadiyya, ina ganin ba daidai ne ba
Wanda nake so ita ce aminina yake so.
Wanda nake so, ita ce aminina yake so.
Mun gano ta, ita ce Halimatus Sadiyya.
Mun gano ta, ita ce Halimatus Sadiyya.
(Ali Jita da Manga: Waƙar Wanda Nake So)
Idan aka nazarci waɗannan baitioci, za a
ga yadda waɗannan abokai ke neman sanin sunan
yarinyar da ɗan’uwansa ke nema, daga ƙarshe suka ce bai kamata su yi jayayya
ba ɗaya ya ce sunan ta Sadiyya, ɗaya
kuma Halima. Sai suka fahimci yarinyar ɗaya ce yaudarar su
take ba son su take ba.
4.4 Baƙar Taƙaddama ta Mata
Wannan kuma taƙaddama ce ta ‘yammata bisa namijin da ba ya ƙaunar su dukkansu.Wannan nau’i ne na
jayayya da hamayya da ke faruwa tsakanin mata wajen ƙoƙarin kaɗaituwa ko mallakar
saurayin da suke ƙauna wanda yake son
wata daban ba su ba. Irin wannan ya faru a waƙar Umar M. Sharif mai suna “Hafiz Kai Nake So A Zuciya” inda
ya bayyana hakan ta hanyar wasu ‘yan mata biyu ya da ƙanwa suka kamu da soyayyar Hafiz kamar
haka:
Ƙanwa: Ni mai rai ce kamar kowa Hafiz, kar ka guje ni,
Dukkan Musulmi ‘yan uwan juna ne, gida
waje.
Zo ga makullin zuciyata ka riƙe. ka aje,
Ina da tabbacin duk inda za ka je, ni
ma za na je.
Yaya: Yaya kike hakan, ko so kike mu ɓata
da juna,
Kina ta ƙoƙarin shiga gonata, ki
daina,
Zamanki lafiya ki bar ni, ni da
masoyina,
Hafiz ka furta so, mu fara ka dace da
ni.
Hafiz: Allah ɗaya
gari bamban, sam-sam ba ku dace da ni ba,
Don ban kama da ku ba, kalaman naku ba
za su shigan ba,
Ba zan saki jiki ba na saurare ku, ku
ba tsarina ba,
Yaya da ƙanwa ya kuke hakan, bai dace da ku ba.
(Umar M. Sharif: Waƙar Hafiz Kai Nake So)
Idan aka mayar da hankali kan waɗannan
baitoci, za a ga yadda ya da ƙanwa
suka kamu da son Hafiz. Don haka ƙanwar ke ce wa Hafiz, ya riƙe makullin zuciyarta ya aje kuma, duk inda zai je ita ma za
ta je. Yar kuma ta nuna kar ta shiga gonarta, za su ɓata.
Zamanta lafiya shi ne ta bar ta da masoyinta. Shi kuma Hafiz ya nun aba su dace
da shi ba, bai kama da su ba, ba zai saki jiki ba, kalamansu ba za su shige shi
ba.
4.5 Taƙaddamar Maza Mai
Dungu
Wannan taƙaddama
ce da maza biyu ke yi kan mace ɗaya, alhali ta riga
ta karkata ga ɗaya daga cikinsu, kamar yadda za a gani
cikin waƙar da Sani Danja da
Ali Nuhu suka yi taƙaddama kan masoyiya ɗaya,
cikin waƙarsu mai suma “Ga Ni
Ga Ka”. Ga yadda abin ya kasance:
Sani Danja: Shashina na yi karewa, ga
ni ga ka,
Kar ka shigo gona tawa, ga ni ga ka,
Na riga ka tun da daɗewa,
ga ni ga ka,
Saura ƙiris mu yo tarewa, ga ni ga ka,
Ali Nuhu: Na zamo tauraro, ga ni g aka,
Ni aka sauraro, ga ni ga ka.
Sani Danja: Ni na zamo toro, zaki a
daji bai tsoro
Baƙar magana ka zazaro, ga ni ga ka,
Kai ne fa ka faro, zambar aminci nai
tsoro ga ni ga ka.
Masoyiya: So bai ƙarewa, so bai
canzawa,
Wanda nake ƙauna da’iman
Fa
ba zai canza ba, ga ni ga ka.
(Ali Nuhu da Sani
Danja: Waƙar Ga-ni-Ga-ka)
Idan aka yi la’akari da furucin Sani Danja za a ga yana
cewa, kar a shiga gonarsa, kuma shi ya fara soyayya da wannan masoyiya har ma
sun kusa aure. Shi kuma Ali Nuhu ya nuna shi tauraro ne, kuma dole shi za a
saurara. Ita kuma masoyiyar tasu tana nuna musu cewa, ba za ta canza wanda take
ƙauna ba har abada, wato dai, tana tare
da saurayinta na farko Sani Danja.
4.6 Taƙaddamar Mata Mai
Dungu
Taƙaddama ce da ‘yammata
biyu ke yi a kan namiji ɗaya, wanda ya karkata ga ɗaya
daga cikinsu. A irin wannan taƙaddama
akan samu musayar zafafan kalamai tsakanin juna. Za a iya ganin misalin haka a
waƙar “Uwargida Da Amarya”, kamar haka:
Uwar gida: Kai gafara ka matsa mini,
wawa baƙin namiji,
Wai ni ka yi wa kishiya, ka ɗauke
ni ban da aji,
Karya ka ɗauko, ko mutum ce mai
kamar namiji,
Zafi kamar yaji, maganarta kamar gunji,
‘Yar fim kamar juji, mai satar miji ta
aje,
Ƙarya take ƙarya
kake, dube ka sha-ka-tafi.
Amarya: Ni dai mijina zan kula,
hakkinka za na tsare,
Indai ta zagen ban kula ta, kar ka zo
ka tare,
Aure take aure nake, ƙarya take na ware,
Ni dai ba zan bijire ba, tilas na ɗauki
tire,
A gare ta mui nazari, ka taho ka ɗan
share,
In ta guje ma zan riƙe ka, ya ka zo mu tafi.
(Sadik Sani Sadik: Waƙar Uwargida Da Amarya)
A
kalaman uwargida ya bayyana ƙarara
cewa mijinsu ya juya mata baya, don haka ta kira shi da baƙin namiji, kuma ba ta da aji a wajensa.
A ɓangare ɗaya kuma amarya ta
bayyana cewa mijin ya share ya rabu da ita, in ta fita ma za ta riƙe shi. Wannan ya nuna karkatar mijin
zuwa ga amarya ke nan uwargida ce mai dungu tunda miji ya ba ta baya.
5.0
Kammalawa
Tsananin buƙatar amfani da kalamai a fagen taƙaddama don cin nasara, sai harshe ya
zama tamkar makami a fagen yaƙi.
Idan aka dubi yadda mawaƙan wannan ƙarni ke yin amfani da wannan salo wajen
bayyana irin yadda taƙaddamar ke yin
tsamari/ƙamari tsakanin
masoyan, tamkar yaƙi ne da makamin ƙare dangi. Saboda tasirin wannan da
kuma zamowar ta ruwan dare a ƙasar
Hausa a yau, ya sa mawaƙan wannan ƙarni na ashirin da ɗaya,
musamman mawaƙan finafinan Hausa,
sun yi ruwa sun yi tsaki a waƙoƙi kan taƙaddamar da mata ke yi a kan namiji, da wanda maza ke yi a
kan mace guda, da kuma kasancewar ta fara ko baƙa ko mai dungu, don haka aka samu farar taƙaddama ta maza da ta mata, da baƙar taƙaddama ta maza da ta mata, da taƙaddama mai dungu ta maza da ta mata. Haƙiƙa, wannan wani sabon zubi ne a salon waƙar ‘yan fim. Idan aka dubi mawaƙan dauri, za a tarar ba su yin amfani da
irin wannan salo a waƙoƙinsu.
Manazarta
Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation
Limited.
Atuwo, A. A. da Bunza, D. B. (2014).
“Transformation of Hausa Poems in the 21 Century” Taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa. Sashen Nazarin Harsunan Najerya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Auta, A. L. (2008). “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa a Ƙarni na Ashirin”.Ph.D Thesis, Kano: Sashen
Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.
Buba, A. (2015). “Nazari a Kan Waƙoƙin Sarkin Waƙa
Nazir Muhammad Ahmad 2000-2013”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da
Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗangambo, A. (2007). Daurayar
Gadon Feɗe Waƙa. Kano: Amana publishers.
Dunfawa, A. A. (2014). “Makaɗan
Zamani: Wani Ƙarin Kaso na Rukunin
Makaɗa”.Takarda da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa, ƙarni na 21, a Jami’ar Bayero, Kano.
Furnnis, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture. London,
EUP.
Gusau, S. M. (1988).
“Waƙoƙin Makaɗan Fada: Yanaye –Yanayensu da Sigoginsu”. Kundim Digiri na Uku, Kano: Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark
Publisher Limited.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark
Publisher Limited.
Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin na Hausa. Kano: Century Research and Publishers Limited.
Gusau S. M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya. Kano: Bayero University, Inaugural
Lecture.
Isah, Z. (2013). “Farfaganda A Waƙoƙin Fiyano Na Hausa Daga 2003-2013”. Kundin Digri na Biyu,
Zariya: Department of African Languages and Cultures Ahmadu Bello University, Zariya.
Nuhu, A. (2016). “Zumuncin Mawaƙa: Sakaɗen Gaishe-Gaishen
Juna A Wasu Waƙoƙin Fina Finan Hausa” Cikin Zauren Waƙa. Journal of Hausa Poetry Studies.
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokkwato.
Sa’id, B. (1982). Dausayin Soyayya:
Zaria,Gaskiya Corporation, LTD.
Sa’id, B. (2002). “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni
na Ashirin a Jahohin Sokoto da Kabi da Zamfara: Nazari a Kan Bunƙasarsu Da Hikimomin da ke
cikinsu”.Kundin Digiri na Uku, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero.
Usman B.B. (2018). Ruwa Biyu: Sabon
Zubin Waƙoƙin Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya A cikin Yobe Journal of Language, Literature and
Culture.Yobe; Department of African Languages and Linguistics.
Yahya, A. B. (1987). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas
Media Serɓices.
Yahya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas
Media Serɓices.
Yahaya, I. Y. (2002). Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin
Hausa. Zaria: Kamfa Kamfanin Buga Littattafai Na Arewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.