Citation: Sani, A-U. (2025). Raujin hikima: Gurbin waƙoƙin gargajiya a rayuwar Hausawa. Njinga & Sepé: Revista Internacional de Culturas, Línguas Africanas e Brasileiras. São Francisco do Conde (BA), UNILAB, Brazil, 5 (Especial I), 11-23. https://revistas.unilab.edu.br/index.php/njingaesape/article/view/2340
RAUJIN
HIKIMA: GURBIN WAƘOƘIN
GARGAJIYA A RAYUWAR HAUSAWA
(Echoes
of Wisdom: The Relevance of Waƙoƙin Gargajiya (Traditional Songs) in the Hausa
Culture)
By
Abu-Ubaida
Sani
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 |
WhatsApp: +2348133529736
Abstract
Waƙoƙin Gargajiya (traditional songs) hold
a significant and distinct place in Hausa culture, functioning as an informal
educational system that imparts valuable lessons in both knowledge and social
conduct. This paper examines the role of these songs in shaping the lives of
the Hausa people, particularly in the past. It explores examples from various
forms of traditional songs, including songs from folktales, community games,
lullabies, and work songs sung by women during household chores. The study
finds that Waƙoƙin
Gargajiya have long played an essential role in teaching ethics, arithmetic,
language skills, and in preserving cultural traditions and history. The paper
concludes with recommendations for modernizing these songs through audio
recordings, animated videos, and mobile applications, to ensure that they
continue to provide valuable benefits for future generations.
Keywords: Hausa, Hausa People, Hausa Traditional
Songs, Hausa Oral Literature, Hausa Culture
Tsakure
Waƙoƙin gargajiya suna da gurbi na musamman
a rayuwar Hausawa. Sun kasance tamkar makaranta mai zaman kanta wadda daga gare
ta ake koyon darussa masu yawa na ilimummuka da zamantakewar rayuwa. Wannan
takarda ta mayar da hankali wajen nazartar tasirin waƙoƙin gargajiya wajen daidaita alƙiblar rayuwar Hausawa, musamman a da. An zaƙulo misalan waƙoƙin da aka yi amfani da su daga tatsuniyoyi da wasannin
dandali da wasannin tashe da kuma waƙoƙin reno da waɗanda mata suke rerawa yayin gudanar da aikace-aikace a
cikin gidajensu. Binciken ya gano cewa, waƙoƙin gargajiya sun daɗe suna taka rawa wajen koyar da tarbiyya da lissafi tare
da taimakawa wajen naƙaltar harshe da sanin al’adu da tarihi
da makamantansu. Daga ƙarshe binciken ya bayar da shawarwari
da suka haɗa da
nuna dacewar zamanantar da waɗannan
waƙoƙin
gargajiya zuwa tsarin odiyo da bidiyoyin katun da manhajoji domin ci gaba da
morar gagarumin alfanun da yake tattare da su.
Fitilun
Kalmomi: Hausa,
Hausawa, Waƙoƙin Gargajiya, Adabin Baka, Al’adun
Hausawa
1.0
Gabatarwa
Waƙa
tsararren zance ne wanda ake shiryawa ta hanyar zaɓan kalmomi na musamman da jera su bisa
wani tsari mai armashi da zai ba da wani ƙayataccen
rauji.[1] Waƙoƙi
sun kasance masu matuƙar jan hankali da tasiri a rayuwar
Hausawa. Masana da manazarta sun gudanar da ayyuka daban-daban dangane da waƙoƙi,
inda suka nuna alaƙarsu da sha’anonin rayuwar Hausawa.[2]
Waƙoƙin
gargajiya suna da tsohon tarihi a matsayin makarantar koyar da ilimummuka da
kuma maƙerar sarrafa harshe da luguden
kalmomin fasaha. Sauye-sauyen zamani sun yi matuƙar
tasiri a kansu ta yadda har sun fara dusashewa, musamman yanzu da waƙoƙin
zamani suka maye gurabunsu. A bisa haka, akwai buƙatar
bitar waƙoƙin Hausawa na gargajiya domin ƙwanƙwance
gudummawarsu ga cigaba da bunƙasar ilimi da zamantakewar Hausawa.
1.1
Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Kadadar
wannan binciken ba ta fita daga da’irar adabin Hausawa ba. Ko a cikin adabin,
an taƙaita ta zuwa waƙoƙin
gargajiya. An tsamo misalan da suka dace da takardar daga cikin ɗimbin waƙoƙin
gargajiya da ake da su a Hausa. Sun haɗa
da waƙoƙin da ake samu a cikin tatsuniyoyi da
waƙoƙin reno da na wasannin dandanli da na
tashe da sauransu. Bitar ayyukan da suka gabata masu alaƙa
da adabi, musamman adabin gargajiya, ya taimaka wajen yi wa aikin jagoranci.
Bayanai da aka samu daga karance-karancen rubuce-rubucen da aka yi masu alaƙa
da aikin sun daidaita wa binciken alƙibla.
An ɗora binciken a kan tunanin Hausa ta
“da tsohuwar zuma ake magani.” A bisa wannan fahimta, binciken yana ganin cewa,
sauyawar zamani bai kamata ya kawo ƙarshen ɗimbin alfanu da hikimomin da suke
tattare a cikin waƙoƙin gargajiyar Bahaushe ba. A maimakon
in an ci moriyar ganga a ya da kwaurenta, abin da ya fi dacewa shi ne, a
zamanantar da su domin ci gaba da tatsar hikimomin da suke cikinsu.
2.0 Gurbin Waƙoƙin Gargajiya a Rayuwar Hausawa
Waƙoƙin
Hausa na gargajiya su ne waƙoƙin da Hausawa suka fara mu’amala da su
a rayuwa. Sun mamaye dukkannin fannonin al’ada da adabin Bahaushe. Wannan ya haɗa tun daga wasanni da tashe da
bukukuwa da ayyukan gida, har ma da fannonin zamantakewa da suka shafi aure da
haihuwa da reno da sauransu. Kasancewar waƙa zancen hikima wanda yake tasiri a
kan ruhi tare da sanyaya rayuwa ko saka mata karsashi ko ziguwa (wanda ya
danganta da nau’in waƙar da muhallin da ake rera ta),
Hausawa sukan samar da waƙoƙi a kusan kowace gaɓar rayuwa da suke gudanar da wata
muhimmiyar al’ada. Kamar yadda Gobir & Sani (2021 p. 9) suka nuna, waƙoƙin
gargajiya na Hausa sun haɗa
da waƙoƙin tatsuniyoyi da wasannin dandali da
na tashe da waƙoƙin aikace-aikace da makamantansu.
Waƙar
gargajiyar tana ɗaukar
fasaloli daban-daban bisa manufar ƙirƙirar ta
da muhallin da ake amfani da ita da kuma aikin da ake buƙata
ta aiwatar. Wannan ya sa waƙoƙin gargajiya suka ɗauki manya da ƙananan
jigogi daban-daban, tun daga kan koyar da lissafi da jarumta da nitsuwa da faɗakarwa da huce takaici har zuwa ƙarfafa
guiwa da makamantansu. A ƙasa an kawo jerin alfanun waƙoƙin
gargajiya ga rayuwar Hausawa.
2.1 Faɗakarwa
Faɗakarwa yana nufin jan hankali ko
hannunka-mai-sanda zuwa ga aikata wani abu mai kyau
ko hani kan aikata wani mummunan aiki. Faɗakarwa yana iya kasancewa tunatar da mutum game da wani
abin da ya shagala. A irin wannan yanayi, akan ankarar da shi a fargar da shi
daga shagalar da ya yi. Waƙoƙin gargajiya sun kasance babbar
hanyar faɗakarwa da jan
hankali. A duba misalin da aka kawo a ƙasa:
Waƙar Tashen Ke Kika Je Ki Gidansu
Direba
Wannan
wasan tashe ne wanda yara mata suke gudanarwa. Akan samu yarinya guda ta cusa
tsummokara a cikin
rigarta, daidai cikinta yadda zai yi tulu tamkar mace mai ciki. Za kuma ta
shafe fuskarta da shuni ko
gawayi ko baƙin
bayan tukunya ko dai wani abu mai kama da wannan. Daga nan za ta shiga gaba
yayin da sauran masu tashe suke biye a baya.
Yayin
da aka iso wurin gabatar da tashe, yaran za su riƙa
zungurar wannan mai ciki tare da tuhumar ta da cewa, ita ta kai kanta gidansu Direba
har ta samo cikin shege. Ita kuwa za ta riƙa bayyana dalilin da ya sa ta je
(Gidansu Direba). Duk wannan yakan kasance ne cikin waƙa,
kamar haka:
Yara: Ke kika je ki gidansu Direba!
Mai Ciki: Da ban je ba ina zan samu?
Kullum biredi,
Kullum Shayi
Kullum tsire yanka goma,
Yanzu likita ya auna ni,
Ya ce cikin direbobi ne,
Wayyo Direba ka cuce ni!
Wayyo
Direba ka ci amana!
Idan
aka lura da wannan waƙa, tana ɗauke da gargaɗi game da kwaɗayi. Wannan mai cikin shege ta bayyana
da kanta cewa kwaɗayi ne
ya kai ta, inda take lissafo abubuwan da suka ja ta gidansu Direba. Sun haɗa da biredi da shayi da tsire.
Daga ƙarshe sai ake nuna irin halin ƙaƙa-ni-ka-yi
da ta shiga a dalilin wannan kwaɗayi,
wato samun cikin shege. Haƙiƙa wannan togaciya ce da kuma hannunka-mai-sanda ga ɗaukacin mata da ‘yanmata da kuma iyayensu. A ɓangare ɗaya kuwa, gargaɗi ne ga iyaye da sauran mariƙa
da su riƙa kula da jin daɗi da walwalar waɗanda Allah ya damƙa
musu a hannunsu.
2.2 Nishaɗantarwa
Nishaɗi yana nufin wani yanayi na jin daɗi ko farin ciki da annashuwa da ɗan’adam ko wata halitta takan iya
shiga. Mai nishaɗi yana
kasancewa cikin walwala da rashin damuwa. Nishaɗi yana da amfani matuƙa ga
rayuwar ɗan’adam,
domin yakan taimaka wurin kauce wa kamuwa da wasu cututtuka musamman waɗanda suka shafi zuciya da ƙwaƙwalwa.
Kusan
dukkanin waƙoƙin gargajiya suna ɗauke da nishaɗantarwa ta fuskokin da suka haɗa da:
a. Nishaɗantar da mai rera waƙar
b. Nishaɗantar da mai sauraron waƙar
A
duba misalin da aka kawo a ƙasa:
Waƙar Wasan Tashe Ta Macukule
Wannan
wasan tashe ne na maza manya. Akan samu ɗaya daga cikin masu wasan ya yi shigar Gwari, sannan ya
shafe fuskarsa da farar ƙasa ko wani abu mai kama da
wannan. Zai kuma riƙe ƙwarangwal
na kan wata dabba, kamar akuya ko tinkiya da makamantansu. Yayin da aka iso
wurin gabatar da tashen,
wannan mai shigar Gwarawa zai riƙa ba da waƙa,
saura kuwa suna amsawa. Ga yadda abin yake:
Bayarwa: Salamu’alaikum, ga baƙonku na
Gwari,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Shekara ta dawo,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Ni ma na dawo.
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Zan muku tashen Gwari,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: A can ƙasarmu
Gwari,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Kan kare da daɗi,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Romon kan jaki daɗi,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Tun ba wurin idon ba,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Tana ko taliya ce,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Kan ƙuda
kuɓewa,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Majina kitse ne,
Amshi: Macukule.
Bayarwa: Tumbuɗi da daɗi,
Amshi: Macukule.
….
…..
Haƙiƙa
wannan wasa yana
samar da nishaɗi musamman
ga masu kallo. Idan mutum ya dubi yadda mai waƙar ya
taƙarƙare
yana maganar Gwari, dole abin ya ba shi sha’awa da dariya. Bugu da ƙari,
zantukan cikin waƙar suna ɗauke da ban dariya da nishaɗantarwa, musamman yadda ake bayyana waɗannan abubuwan da Hausawa ba sa cin su
a matsayin abinci mai daɗi.
Lissafi a
nan yana nufin ƙidaya, wato ƙididdige
adadin wani abu kamar kuɗi
ko ‘ya’yan itatuwa, ko duwatsu da dai makamantansu. Abu ne mai kyau ya kasance
mutum ya iya lissafi, domin kuwa lissafi yana ɗaya daga cikin gishirin rayuwa. Waƙoƙin
gargajiyar da suke koyar da lissafi sun haɗa da:
Waƙar Wasan Ɗura-Ɗura
Ɗura-ɗura wasa ne na
yara mata. Masu wasan za
su nemo ƙananan duwatsu ko ɗanyun ‘ya’yan kanya ko makamancin
wannan, kowa guda bibbiyu. Daga nan wadda za ta fara wasa za ta riƙe
dutse ɗaya a hannun
dama ɗaya kuwa a
hagu – idan wasan ‘yar
hannu biyu ce. Sai ta riƙa cilla su sama cikin ƙwarewa
tare da canza musu hannu. Wato sai ta riƙe na hannun dama da hannun hagu, na
hannun hagu kuwa ta cafe shi da hannun dama. Da zarar ta faɗi, sai abokiyar wasanta ta karɓa. Ana kuma gudanar da ‘yar
hannu ɗaya, ko ‘yar
duwatsu uku a maimakon biyu.
Mai
gudanar da wannan wasa za ta riƙa lissafi/ƙirge
cikin waƙa. Waƙar ta
danganta da ɗurawa
take yi ko fanshewa. Ga misalin waƙar ɗurawa:
Ɗura-ɗura ɗaya,
Ɗura
ya ban biyu,
Ɗura
ya ban uku,
Ɗura
ya ban huɗu,
Ɗura
ya ban biyar,
Ɗura
ya ban shida,
Ɗura
ya ban bakwai,
Ɗura
ya ban takwas,
Ɗura
ya ban tara,
Ɗura
ya ban goma.
Goma ya ban ɗaya,
Goma ya ban biyu,
……. ……. ……..
Ishina.
Ishi ya ban ɗaya,
Ishi ya ban biyu,
…….
……. ……..
Haka
za a ci gaba da yi har a je: Talana wato talatin (30) ke
nan; Arbana wato arba’in (40) ke nan, …. Riɗana wato ɗari
(100) ke nan...
Haka
abin zai ci gaba har zuwa wurin da mai wasa ta faɗi. Haƙiƙa
wannan hanya ce ta koyon lissafi, musamman ƙidaya.
2.4 Ƙarfafa Danƙon Zumunci
Zumunci ko
zumunta yana nufin kyakkyawar alaƙa ko dangantaka ta jini ko ta abota da
akan samu tsakanin mutane. Za a iya hasashen cewa kalmar ta samo asali ne
daga zumu da ke ɗaukar
ma’anar ɗan uwa ko
sa’a ko aboki. Waƙoƙin gargajiya suna taka rawar gani
matuƙa wurin ƙarfafa ɗanƙon
zumunci tsakanin yara da kuma iyayen yaran kansu. Taruwa wuri ɗaya da ake yi domin rera waƙoƙin
tare da yabon ƙawaye da aiki tare duk suna taimakawa
wajen ƙarfafa danƙon
zumunci. A duba misalin da aka kawo a ƙasa:
Waƙar Wasan Gariye
Yara
mata ne suke gudanar da wannan wasa. Masu wasa za su yi da’ira mai faɗi ta hanyar barin ‘yar tazara a
tsakanin juna. Daga nan ɗaya
za ta shigo tsakiya. Za ta riƙa bayar da waƙa
saura kuwa suna amshi tare da tafi. Waƙar ita ce kamar haka:
Bayarwa: Duk garin nan,
Amshi: Gariye.
Bayarwa: Ba ni yaya,
Amshi: Gariye.
Bayarwa: Ba ni ƙanwa,
Amshi: Gariye.
Bayarwa: Sai ƙawata
wadda muke mutunci,
Mutuncin ma mutunci.
Amshi: Gariye.
Bayarwa: Sai ƙawata
Laraba[3] zo mu cashe,
Amshi: Gariye.
Bayarwa/Amshi: Gariye na malilisi,
Gariye,
Girgiza wando, fatari, siket,
Addinin ‘yanmata.
Ke kika yarda? Aka sa miki?
Girgiza wando,
fatari, siket,
Addinin
‘yanmata.
A
wannan gaɓa, yara za su
taka rawa su cashe. Daga nan kuma wadda ta ba da waƙa
za ta koma cikin sauran yara. Wata daban kuma za ta fito domin ba da waƙa.
Haƙiƙa wannan waƙa
tana ƙara danƙon
zumunci tsakanin yara, kamar yadda ambaton sunan wata a matsayin ƙawa
yakan faranta mata rai tare da nuna mata cewa an damu da ita matuƙa.
Addu’a
dai a taƙaice tana nufin roƙon
wani abu daga Allah shi kaɗai
ta amfani da waɗansu
lafuzza na musamman (Ainu, 2007 p. 52). Akwai waƙoƙin
gargajiya da dama da suke ɗauke
da addu’ar alheri. A ƙasa an kawo misali:
Waƙar Kaɗi Ta Allah Ba Ni Kaɗa
Kaɗi ɗaya ne daga cikin daɗaɗɗun
sana’o’in Hausa na gargajiya. Ya shafi sarrafa auduga domin samar da zare.
Akwai waƙoƙi daban-daban da masu kaɗi suke rerawa yayin gudanar da
sana’arsu. Ga misali daga ciki:
Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,
Amshi: Ayeye ye ranaye.
Bayarwa: In yi zare na kaina,
Amshi: Dela ba Dela ba Kande.
Bayarwa: In yanke zugage,
Amshi: Ayeye ye ranaye.
Bayarwa: Dela nan tara nan talatin,
Amshi: Dela ba Dela ba Kande.
Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,
Amshi: Ayeye ye ranaye.
Bayarwa: In wa masoyi riga,
Amshi: Dela ba Dela ba Kande.
Bayarwa: In wa masoyi wando,
Amshi: Ayeye ye ranaye.
Kamar
yadda aka gani a sama, wannan waƙa tana ɗauke da addu’ar alheri. Mai rera waƙar
tana addu’ar Allah Ya
ba ta kaɗa saboda ta yi
zare na kanta. Har ma tana bayyana ƙudurin alheri dangane da abin da za ta
aiwatar da kaɗar idan ta
samu, wato saƙa wa masoyinta sutura.
Kalmar al’ada tana
nufin tsarin rayuwa ta gaba ɗaya
wanda ta haɗa da sanannun
sababbun al’amuran da suke gudana yau da kullum bisa wasu tsararrun ƙa’idoji
da matakai da kuma waɗanda
aka saba da wanzuwarsu kara zube ba tare da wata ƙa’ida
ta musamman ba. Waƙoƙin gargajiya masu yawa suna taimakawa
wajen adana kalmomi[4] da al’adu. A duba wannan misalin:
Waƙar Tashen Jatau Mai Magani
Maza
ne suke gudanar da wannan wasan tashe. Ɗaya
daga cikinsu da ake kira Jatau zai yi shigar boka, har da layun wasa. A wurin
wasa Jatau zai riƙa rera waƙa
saura suna amsawa, kamar haka:
Jatau: Jatau mai magani,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kogo-kogo na shiga,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kogon kura na shiga,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kogon damusa na shiga,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kogon ɓauna na shiga,
Amshi: Jatau.
Jatau: Balle na maciji ɗan tsiya,
Amshi: Jatau.
Jatau: To iya wanne za ki sha,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ko na ciki ko na haihuwa,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ko na korar kishiya,
Amshi: Jatau.
Jatau: Idan na ba ki na haihuwa,
Amshi: Jatau.
Jatau: Yau ki haifo sha biyar,
Amshi: Jatau.
Jatau: Gobe ki haifo sha biyar,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kin ga talatin sun cika,
Amshi: Jatau.
Jatau: Idan na ba ki na kishiya,
Amshi: Jatau.
Jatau: Larai ta zo ta fita,
Amshi: Jatau.
Jatau: Maimuna ta zo ta fita,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kafin sati ko guda,
Amshi: Jatau.
Jatau: Kin kore mata ɗari,
Amshi: Jatau.
….
Akwai ɓangaren waƙar
inda Jatau yake bayanin kayayyakin haɗin
magungunan da suke cikin tarkacensa na bokanci, yana cewa:
Jatau: Ka ga wannan gwanda ce,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ko da ba ta magani,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ko don zaƙi
za ka sha,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ka ga wannan zogala,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ko ba ya magani,
Amshi: Jatau.
Jatau: In an yi kwaɗo ai za ka ci,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ka ga wannan yakuwa,
Amshi: Jatau.
Jatau: Ai ko ba ta magani,
Amshi: Jatau.
Jatau: Za a yi taushe za ka sha,
Amshi: Jatau.
Lallai
wannan waƙar tana adana kalmomin Hausa da suka
shafi dabbobi da magunguna. Bugu da ƙari, tana adana al’adu masu yawa ciki
har da bayyanannu (magunguna[5] da tsirrai da tufafi da sauransu) da
kuma ɓoyayyu (yarda
da bokanci da sauransu).
Barin
kashi a ciki ba ya maganin yunwa! Yayin da wata damuwa ta dabaibaye zuciyar
mutum, ba zai samu sukuni ba har sai ya furzar da ita. Ana amfani da waƙoƙin
gargajiya wajen bayyana muradin zuci a bagiren da bayyanawar take da wahala ba
domin albarkacin waƙoƙin ba. Ga misali a ƙasa:
Waƙar Wasan Mama Ta Ƙi Shillona
Yara
mata ne suke gudanar da wannan wasa. Sukan yi da’ira, sai kuma
yarinya ɗaya ta
fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa
sauran kuma suna amsawa tare da tafi da rangwaɗa. Suna cewa:
Bayarwa: Ayyaraye iye dije,
Amshi: Yaraye iye dije.
Bayarwa: Jajjage ruwan lemo,
Amshi: Arziki na Allah ne.
Bayarwa: Mama ta ƙi
shillona,
Amshi: Baba ya ƙi
shillona.
Bayarwa: Tun da kun ƙi
shillona,
Amshi: Ni na tafi yawona.
Bayarwa: Ran bikin Halimana,[6]
Amshi: Don Allah ku aika min.
Bayarwa: Ran bikin Umaimana,
Amshi: Don Allah ku aika min.
Bayarwa: Za mu je mu watsa kuɗi,
Amshi: Sai ya fi dubu hamsin.
Bayarwa: Za mu je mu taka rawa,
Amshi: Sai ya fi na ‘yan bori.
Wannan
waƙa a kaikaice fitar da abin da yake
damun ‘ya’ya mata ne a zuciya dangane da watsi da su da ake yi a rayuwa. A
cikin waƙar suna barazanar tafiya yawon duniya,
tun da arziki na Allah ne. A ƙarshe har suka nuna cewa idan
bikin ‘yan uwansu ya zo, to za su zo da kuɗi mai yawa sannan su taka rawar da har ta fi ta ‘yan
bori. Haƙiƙa wurin da za a samu kuɗaɗen nan sannan a koyi wannan rawa, ba wurin alkairi ba ne.
2.8 Bin Doka Da Ƙa’ida
Bin
doka da ƙa’ida yana daga cikin abubuwan da suka
bambanta rayuwar mutane da dabbobi. Waƙoƙin gargajiya masu yawa suna tafiya
tare da dokoki. Ga misali a ƙasa:
Waƙar Wasan Gidan Kurciya
Wannan
waƙa ce da ake gudanarwa yayin wasan
dandali. Masu wasan suna
tsayawa bisa tsarin da’ira, sannan su ba da ‘yar tazara a tsakankaninsu,
tare da riƙe hannuwan juna. Daga nan kuma ɗaya daga cikin masu wasa zai riƙa
sunkuyawa yana wucewa ta tsakankanin ‘yan wasa (ƙarƙashin
hannunsu da suke riƙe da na juna). Yayin da yake shige da
fice, za su riƙa rera waƙa
kamar haka:
Waƙa: Gidan
kurciya,
Amshi: Shaya.
Waƙa: Wanda
ya ɓata,
Amshi: Shaya.
Waƙa: Zai
sha duka,
Amshi: Shaya.
Waƙa: Har
da muntsini,
Amshi: Shaya.
Ƙarara a cikin wannan waƙar
ana jaddada cewa, duk wanda ya ɓata
“zai sha duka, har da muntsini.” Wannan yana nuna dole ne mai wasar ya kiyaye
tsarin dokokin da aka gindaya domin wanyewa lafiya. Yayin da mai wasa ya yi
kure, yana shan duka kamar dai yadda aka yi alƙawari a
cikin waƙar. A taƙaice
dai, wannan waƙa tana koyar da bin doka da ƙa’ida
tare da nuna sakamako marar kyau ga wanda ya taka doka.
2.9 Koyar Da Halaye Nagari
Hali
shi ne mutum! Na gari na kowa! Kowane uban ƙwarai
yana son ganin zuri’arsa ta tashi cikin tarbiya mai kyau abar yabawa, haka ma
uwa ga ‘ya’yanta. Wannan ya haɗa
da kunya da gaskiya da riƙon amana da sanin ya-kamata da girmama
na gaba da dai sauran halayen ƙwarai makamanta waɗannan. Wannan ne kuma ya sa Hausawa
suke da waƙoƙin gargajiya masu koyar da halaye
nagari. A duba wannan misalin:
Waƙar Wasan Tsakiyata Ta Tsinke
Yara
mata ne suke gudanar da wannan waƙar yayin wasannin dandali. Sukan yi
da’ira sannan su kakkama hannayen juna sannan su tsuguna yayin rera waƙa
kamar haka:
Tsakiya
tsatsakiya,
Tsakiyata ta tsinke,
A ɗakin masoyina,
In sunkuya in ɗauka,
Abin na da kunya,
Ba da kunya ba,
Ala tsine ‘yar kunama,
A
cikin duhun ciyawa.
Wannan
waƙa tana nuna kunya ga ‘ya mace. Ga shi
dai tsakiyar wannan yarinya ta tsinke, tana so ta sunkuya domin ɗauka, amma dole ta haƙura
saboda kunya. Kunya kuwa abar so ce ga ‘ya mace, domin duk yarinyar da ba ta da kunya,
tarbiyarta ragaggiya ce.
2.10
Lura Da Mai Da Hankali Da Nutuswa
Rayuwar ɗan’adam ba ta tafiya kan tsari
sai idan ya kasance mai lura tare da mayar da hankali kan abubuwan da yake
gudanarwa cikin rayuwarsa ta yau da kullum. Rashin Natsuwa ko mayar da hankali yakan
jefa mutum cikin halin yawan mantuwa (marar dalili) da yawan kuskure da dai
makamantansu. Akwai waƙoƙin gargajiya da suke koyar da
natsuwa da mayar da hankali. Misali:
Waƙar Wasan Jini Da Jini
Wannan waƙa ce da yara suke gudanarwa. Ɗaya daga cikinsu
zai riƙa ambatar sunayen abubuwan da suke da jini. Yara kuma za su riƙa amsawa
da “danja!” Ana cikin haka zai shammace su ya ambaci abin da ba shi da jini a
jikinsa. A nan yara za su amsa da “babu!” Duk wanda ya yi kuskuren amsawa da
“danja!” to ya faɗi, don
haka hukuncin wasa zai hau kansa. Ga yadda abin yake:
Liman: Jini da jini,
Mamu: Danja!
Liman: Rago da jini,
Mamu: Danja!
Liman: Akuya da jini,
Mamu: Danja!
Liman: Riga da jini.
Mamu: Babu!
Haƙiƙa
wannan waƙa tana buƙatar
natsuwa da mayar da hankali. Duk yaron da ya shagala da wani tunani na daban,
zai samu kuskure wurin ba da amsar da ba ta dace ba.
Motsa
jiki yana da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan’adam. Akwai waƙoƙin
gargajiya waɗanda suke ba
wa yara ƙarfin guiwar motsa jiki, musamman
yayin wasannin dandanli. Ga misali daga cikinsu:
Waƙar Wasan Karya Gaɗiɗi
Wannan
wasa ne na yara mata. Masu wasan suna tsayawa manne da juna a
layi ɗaya. Ɗaya
daga cikinsu kuma za ta fito gaba. Za su riƙa waƙa
da tafi yayin da wannan yarinya da take gaba za ta riƙa
faɗowa jikinsu. Su kuwa
za su riƙa tallabar ta suna cillo ta gaba.
Haka za a ci gaba da yi har sai an kai ƙarshen
waƙar. Ga yadda take:
Mai Direwa: Karya gaɗiɗi,
Karya gaɗiɗi.
Masu Cilli: Garya gaɗis!
Kainuwa.
Mai Direwa: Kainuwa dashen Allah,
Masu Cilli: Kainuwa.
Mai Direwa: Ba dashen mutane ba,
Masu Cilli: In dashen mutane ma.
Mai Direwa: Ko ruwa ba na sha ba.
Masu Cilli: Kainuwa.
Mai Direwa: Ko kunu ba na sha ba.
Masu Cilli: Ya ishe ki ‘yar Malam Adamu,
Ya
ishe ki ‘yar Malam Adamu.
Haƙiƙa
akan motsa jini yayin gudanar da wannan wasa. Gishirin wasan kuwa, shi ne waƙar
da ake rerawa a ciki,
domin kuwa waƙar ta kasance linzamin wasan.
Takaici yana
nufin baƙin ciki ko sosuwar zuciya ko haushi da mutum kan ji dangane da wani mutum ko wani al’amari da
bai gamshe shi ba. Waƙoƙin gargajiya na Hausa sun kasance
wata kafa da Hausawa suke bi domin huce takaicinsa. Ga misali:
Waƙar Niƙa Ta Kishiya
Wannan
waƙa ce da take ɗauke da habaici. Kishiya tana iya rera wannan waƙa
yayin da take niƙa da zummar caka wa kishiyarta baƙaƙen
maganganu a kaikaice. Ko ba komai, zuciyarta takan yi fari yayin da ta yi hakan. Ana rera wannan waƙa
kamar haka:
Ayye yaraye iye nanaye,
Ayye yaraye iye nanaye.
Ga wata kishiya ruwan sanyi ce,
Wata ko na zafi ya fiye mata.
Kishi da ‘yar Malan nake gudu,
Ta yi maka magani ta saka a hanya.
Hanyar gidanku ta barkace maka,
Allah ba ni kishiya mai yaji.
Kamin
ta dawo na ci duniya.
2.13 Samun Abokin Hira/Abokin Taya Aiki
Mata dai
an san su da zaman kaɗaici
a gida, musamman idan aka ce ba su da ‘ya’ya ko jikoki ko wasu abokan zama. A
irin wannan yanayi, sukan kasance cikin kaɗaici yayin da mazajensu suka fita wurin fafutukarsu ta
yau da kullum. Waƙoƙin gargajiya suna taimaka wa ire-iren
waɗannan mata a matsayin
abokan hira yayin da suke aikace-aikacensu a cikin gida. Ga misali a ƙasa:
Waƙar Niƙa Ta Naƙuda Ta Tashi
Wayyo naƙuda ta
tashi,
Ciwon naƙuda ya
tashi.
Kuma ciwon naƙuda
ya motsa,
Yau kam babu zama zaure.
Wayyo Inna ki cece ni,
Ciwon naƙuda ya
tashi.
Da kis sha daɗinki,
Ke tuna da Inna ta cece ki?
Ko ke tuna da baba ya cece ki?
Wayyo naƙuda
‘yar ziza!
Ciwon naƙuda
bori ne,
Ko ko naƙuda
hauka ce!
Wayyo naƙuda ta
tashi,
Wayyo
naƙuda ta motsa.
Idan
aka lura da wannan waƙa, za a tarar cewa an gina ta ne kan
raha. Za a fahimci hakan yayin da aka yi duba zuwa wasu daga cikin kalaman da
aka yi amfani da su a cikin waƙar, misali naƙuda ‘yar ziza; ko
wataƙila mota ce? Haka ma mai ƙorafin
ciwon naƙudar, sai ga ta tana mayar wa kanta
martani tamkar dai wadda
take wa ƙorafin ne take mayar da martanin, wato
tuhumar ta da cewa,
ta tuna lokacin da ta ɗauki
cikin?
2.14
Bara
Mabarata
da suka haɗa da musakai ko miskinai da kuma
almajirai sukan yi amfani da waƙoƙi daban-daban a wurin bara. Hakan
yana ƙara armashi ga barar tasu tare da jawo
hankalin wanda suke roƙa. Waƙoƙin
suna ɗauke da
kalmomi masu taɓa zuciya
da kuma ban tausayi, wanda hakan kan sa a ba su sadaka. Daga cikin waƙoƙin
da almajirai suke barar abinci da su akwai:
Waƙar Bara Ta Iya Allaro
Wannan
waƙa dai almajirai na amfani da ita wurin bara, musamman lokacin da zuke zagayawa
gida-gida domin neman abinci. Ga yadda waƙar take:
Iya Allaro,
Allaro iya,
Iya Allah ba ku mu samu,
Iya Allah sa mu ga Annabi,
Iya ko loma ɗaya ma,
Iya ko gaya ne ba miya,
Iya
ko loma ɗaya ba miya.
Haƙiƙa
wannan waƙa tana ɗauke da kalamai masu ban-tausayi da
suke taɓa zuciya,
musamman wurin da mai barar yake nuna ko da loma ɗaya, wadda kuma ba miya, to yana buƙata.
Bugu da ƙari, waƙar
tana ɗauke da addu’ar alheri zuwa ga wanda ake roƙa.
3.0
Sakamakon Bincike
Wannan
bincike ya fahimci cewa, waƙoƙin gargajiya sun kasance wata
kammalalliyar makaranta musamman ga yaran Hausawa a da. Suna ɗauke da fannonin ilimi daban-daban.
Daga cikinsu har da ilimin ƙidaya da bin ƙa’ida
da zurfafa tunani. Haka kuma, yana taimakawa wajen inganta zamantakewa da samar
da gogewa a kan dabarun zaman duniya.
Haka
kuma, binciken ya gano cewa, waƙoƙin gargajiya suna tattare da ɗimbin alfanu inda tasirinsu ya karaɗe illahirin rayuwar Hausawa. A da, sun
kasance masu muhimmin gurbi na musamman ta yadda ake damawa da su a kusannan
duk wani al’amarin rayuwa.
Wani
hanzari ba gudu ba shi ne, yanzu waɗannan
waƙoƙi sun dusashe matuƙa.
Zamani da abubuwan da ya zo da su dangin intanet da na’urori sun kawar da
ire-iren waɗannan
gadaddun hanyoyin gudanar da rayuwa. Waƙoƙin zamani da ake sauraro a na’urori
sun dusashe karsashin na gargajiya. Haka kuma, makarantun boko da na isilamiya
da kallace-kallacen talabijin sun maye gurbin tatsuniyoyi da wasannin dandali
waɗanda a cikinsu ne aka
fi samun waƙoƙin. Haka kuma, dusashewar wasannin
tashe sun haifar da ɓacewar
waƙoƙin tashe.
4.0
Kammalawa
Sarki
goma zamani goma! Haƙiƙa dukkannin alƙaluma
sun nuna cewa, babu yadda za a yi waƙoƙin gargajiya su yi gogayya da sababbin
sauye-sauyen da zamani ya kawo. A bisa haka, hanyar da za ta fi ɓullewa ita ce sanya wa waɗannan waƙoƙi
rigar zamani. Za a iya hakan ta hanyar sabunta su cikin odiyo da bidiyoyi da
bidiyoyin katun. Ana kuma iya samar da manhajoji ƙayatattu
da suke ɗauke da waƙoƙin
kamar yadda suke fitowa a cikin tatsuniyoyi da wasannin dandali da na tashe. Ta
waɗannan hanyoyi za a iya
ci gaba da cin gajiyar waƙoƙin gargajiya da suke ƙoƙarin ɓacewa baki ɗaya.
Manazarta
Ainu, A. H. (2007). Rubutattun
waƙoƙin
addu’a na Hausa: Nazarin jigoginsu da salonsu [Kundin digiri na uku da ba a wallafa ba]. Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto.
Bashir, R. (2024). Bitar rabe-raben waƙoƙin
Hausa: Laluɓen matsayin
waƙoƙin ƙarni na
ashirin da ɗaya a
fagen nazari. Tasambo
Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 381–389. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.044
Danhassan, F. A. (2024). Tubalin yabon
mata a wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Tasambo Journal of Language, Literature,
and Culture, 3(2),
219–224. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.028
Gobir, Y. A., & Sani, A.-U. (2018,
April). Traces of supernatural in Hausa oral songs: A special reference to Dr.
Mamman Shata. International
Journal of Recent Advances in Multidisciplinary Research, 5(4), 3755–3760. ISSN:
2350-0743. Available at: https://www.ijramr.com/issue/traces-supernatural-hausa-oral-songs-special-reference-dr-mammanshata
Gobir, Y. A., & Sani, A.-U.
(2021). Waƙoƙin Hausa na gargajiya. Kaduna: Amal Printing &
Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin ra’i da tarke a adabi da
al’adu na Hausa. Kano:
Century Research and Publishing Limited.
Idris, Y., & Sani, A.-U. (2018).
Future situation of Northern Nigeria from poetic mirror: The outstanding
prophesiers from Hausa poets. The
International Journal of Social Sciences and Humanities Invention, 5(10), 4998–5002. https://doi.org/10.18535/ijsshi/v5i10.01
Sani, A.-U., & Bakura, A. R.
(2023). The origin and spiritual distribution of Zamfara drummers and
singers. South
Asian Research Journal of Arts, Language and Literature, 5(4), 108–123. https://doi.org/10.36346/sarjall.2023.v05i04.003
Sarkin Fada, I. (2024). Nazarin
kalmomin ta’addanci a cikin wasu waƙoƙin baka. Tasambo Journal of Language, Literature,
and Culture, 3(1),
358–363. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.041
[1] Domin samun ƙarin
bayani game da ma’anar waƙa a tunanin Hausawa ana iya duba
Bashir (2024 p. 382) da Sarkin Fada (2024 p. 360),
[2] Rubuce-rubuce da aka yi game da
waƙoƙi sun haɗa da Gusau (2015) da Idris & Sani
(2018) da Gobir & Sani (2018, 2021) da Bakura & Sani (2023) da
Danhassan (2024)
[3] A wannan gaɓa, mai waƙa
takan ambaci sunan ɗaya
daga cikin ƙawayenta. Wadda aka ambaci sunanta
kuwa za ta ji daɗi tare
da yin murna da farin cikin kasancewar an damu da ita.
[4] Ɗaya
daga cikin ɗabi’un
harshe shi ne samun sauye-sauye daga lokaci zuwa lokaci. Akan samu kalmomin
harshe sun karfafa, ko an maye gurbinsu da wasu.
[5] Domin samun ƙarin
bayani game da magungunan Hausawa ana iya duba Bunza (1995) da Abdullahi (2008)
da Gobir (2012).
[6] A
nan za ta faɗi sunan
wata ƙawarta ko ƙanwa ko kuma yarta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.