Ticker

6/recent/ticker-posts

Karancin Daliban Hausa a Manya Makarantun Kasar Nan: Laifin Malaman Hausa Ne

ƘARANCIN ƊALIBAN HAUSA A MANYA MAKARANTUN ƘASAR NAN: LAIFIN MALAMAN HAUSA NE

Daga

Abdulrahman Aliyu Ph.D

A cikin 'yan kwanakin nan maganganu ke ta yawo na cewa ana samun koma baya wajen karantar harshen Hausa a manyan makarantun ƙasar nan, musamman samun ƙarancin ɗalibai. Wanda lamari kacokam na danganta shi ga laifin malaman saboda abubuwa kamar haka;

1. Rashin tafiya da zamani

Kaso 70 na malaman da ke koyar da Hausa a manyan makarantun ƙasar nan ba sa tafiya da zamani, abin da suka ɗauka nazarin harshen Hausa ya tsaya ne kacokam kan harshe da adabi da al'ada. Ba su zurfafa bincike kan abubuwan da suka shafi kimiyya da fasaha na zamani da Hausawa ke ta'ammali da su, ba a cika ganin rubuce-rubucensu a sauran fannoni ba, kadan ne kake ganin rubuce-rubucensu a Ingilishi kai hatta harshen Larabci da Faransaci da suke da kusanci sosai da Hausa ba za ka ga malaman Hausa na bayar da gudumuwa a mujallin ɓangarorin ba. Malaman Hausa ba su cika ɗaukar sabon abu ba, da zaran ka zo da sabon abu domin nazari a madadin a jira a gani sai ka ga an fara suka ana kore shi daga nazarin Hausa, hujjar kawai su ba su san abin ba, kuma ba za su bari a sanar da su ba.

2. Rashin iya Amfani da Kayan Aikin na Zamani;

Kaso 90 cikin ɗari na malaman Hausa a manyan makarantun ƙasar nan ba su san yadda ake amfani da kayan aikin zamani ba na koyo da koyarwa, misali ɗakin gwaje-gwaje na harsuna (Language Laboratory) a duk jami'o'i da manyan makarantun ƙasar nan ba za a yadda a buɗe sashen koyar da harsuna ba, sai an samar da wannan ɗaki na gwaje-gwaje amma baka da ɗalibi ɗaya na Hausa daga shekarar 2001-2025 da zai ce ma an taɓa kai shi wannan ɗakin domin yin nazari ko kuma yin gwaji ko samar da wasu abubuwa na zamani ta dalilin amfani da dakin, saboda ba wani malami da ya san yadda ake sarrafa na'urorin kuma ba wanda ya taɓa bukatar ya koya domin amfanin daliban harshen. 

A wani binciken sirri da muka yi kaf jami'o'i da kwalejoji da ake koyar da harshen Hausa ba inda ake amfani da wannan ɗaki domin bayar da ilimi kuma akwai shi a dukkan jami'o'in, sannan shi Language Laboratory wata kafa ce da za ta iya samar wa sashen kuɗin shiga da kuma matattara ta bincike daga ciki da wajen jami'a ko kwaleji amma malaman sashen Hausa ba su ma san akwai wanann damar ba sam balle su yi amfani da ita. Ta amfani da wannan ɗakin na gwaje-gwajen harsuna har likitoci malam Hausa za su iya taimaka wajen tantance yanayin inda matsala take a maƙoshi da kuma abubuwan da suka taɓu a maƙoshin, kazalika za su iya bayar da shi haya ayi amfani a tace sautuka na wa'azi da maganganu da waƙoƙi ga wasu na waje. Sannan a zamanance za a iya amfani da shi wajen fassara harsuna da dama. Wani abin takaici sai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Ekiti ne ake wasu ayyukan Hausa da shi wannan ɗakin na gwaje-gwajen harsuna mu nan da muke koyar da Hausar mun banzatar da shi ba mu san amfaninsa ba kuma mun ƙi tafiya neman iliminsa mun tsaya kukan babu ɗaliban Hausa ko Jamb na mana zagon ƙasa.

3. Rashin Tsayayyar Ƙungiya ta Ƙasa da Ƙasa. (Scholars Association) 

Babu wata ƙungiya ta malaman Hausa da ke lumfashi wadda za ta iya bada shedar ƙwarewa a fannin kamar sauran harsuna ko fannonin ilimi, in ma akwai ta wasu ne kawai suka zagaye ta suka ƙi barin matasa 'yan zamani su shiga cikinta domin kawo gyara da shirya taruka na ilimi da bada lambobin girmamawa na matsayi, sai aka bar ƙungiyoyin cikin gari da masu sha'awa na shirya taruka yadda suka fahimci Hausar. Amma su waɗanda Hausar ta yi wa riga da wando sun fake a cikin jami'o'i da kwalejoji sun tsuke kansu ba su fita ko'ina kuma sun ƙi zamanantar da koyarwa yadda za ta bayar da sha'awa ga na baya suyi tururuwar zuwa cikinta kamar yadda magabatansu su ka yi. Da za a samar da wannan ƙungiyar kuma tayi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyin ƙasashen waje da hukumomin gwamnati to ina mai tabbatar maka karantar Hausa sai ta koma sai mai rabo saboda tarin damarmakin da waɗanda suka karanci Hausa suke da shi a duniya kamar yadda mu ke gani a yanzu.

4. Rashin Faɗaɗa Bincike a Matakin PG

Sau da yawa nazarin harshen Hausa a matakin karatun digiri na biyu zuwa na uku an tsuke shi kuma an ƙuntace shi ta yadda ɗaliban ba su cika samar da wani bincike na azo a gani da zai tafi daidai da zamani ba, babban abin da zai baka takaici a wanann zamanin ace wai har yanzu a digiri na biyu ko na uku ana nazarin salo da zubi da tsari da jigo wanann abin takaici ne ƙwarai da ya kamata a ce an wuce shi tuni, a kalli kimiyya da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da za su taimaki ɗaliban su samar da wani sauyi mai inganci, misali a gargajiyancen ma Shata da sauran mawaƙa sun yi waƙoƙi da suka yi magana kan Fasahar samar da ATM da jirgin sama da yanayin ƙasa da albarkatun da ke ciki, to amma da ka ce za ka yi bincike kan kimiyya da fasahar to a nan fa za a fara dirama ana gaya ma kai ba sashen Technology kake ba. Ko kuma ba Geography kake ba balle ka yi bayanin kan yanayin ƙasa.

Kai ko gine-ginen Hausawa da inda suka riƙa yin su kimiyya ce ta nazarin yanayin ƙasa da abinda za ta iya yi. Sana'o'in zamani na yanzu irin su POP da zane da ake a ɗakunan alfarma duk kimiyya ce ta Bahaushe da ya kamata a ce a makarantun mu ake samar da waɗanda za su yi wannan sana'o'i saboda a gine-ginen Bahaushe aka sansu. 

Sarrafa magungunan Hausawa su tafi daidai da zamani ta amfani da ɗakunan gwaje-gwaje duk Hausawa ne aka sani, akwai ministan da na san ya ya ce zai ɗauki nauyin gwajin irin waɗannan magungunan a ɗakunan gwaje-gwaje domin a gane sinadaran dake ɗauke cikinsu ba wanda ya kula shi. Da zamu faɗaɗa bincike a matakin karatun PG ko shakka babu tuni harshen Hausa zai fita tsara a fagen nazari.

4. Rashin Bayar da Ƙwarin Guiwa ga Ɗalibai.

Kaso 65 cikin ɗari na malaman Hausa ba su bayar da ƙwarin guiwa ga dalibai, kuma ba su fita neman ɗaliban sam, sun tsaya ne kawai sai ɗaliban sun kawo kansu. Kuma da yawa malaman ba su yadda ma da kansu ba balle har wasu ɗaliban su yi sha'awarsu su ji suna so su zama kamar su. Ni zan bada misali a karin kaina da farko Hausa bata daga cikin abinda nake son karanta a rayuwata, amma yadda naga Farfesa Malumfashi Ibrahim Aliyu Mohammed na baza Capacity a dandalin Yahoo groups wajen shekarar 2003-4 shi ya ja hankali na na so zama irinsa, kuma na cimma burina a karin kaina. A makarantar da na ke aikin wucin gadi yanzu haka ɗaliban Hausa sune suka fi kowa yawa kuma da yawansu saboda ni ne misali zangon karatu na 2023-24 sai da na samar da dalibai 38 a zangon 24/25 kuma na samar da 35 kuma da yawa nine ke fita neman su da kuma buɗa masu damarmakin da ke cikin karantar Hausa kuma su gani a ƙasa su tabbatar. A ɓangaren digiri na biyu zuwa na uku na sa ɗalibai sama da goma sun koma karatun Hausa wasu har gidajen su nake binsu ina jawo hankalinsu kamar na zo musuluntar da su. 

Amma kana malamin Hausa kuma kana kallon ƙalubalen matsalar ɗalibai ka fake da cewa laifin Jamb ne kai me ka yi kan hakan? Kwamfuta ma baka iya ba, email ma sai ka ce a duba ma ba ka san yadda za ka yi amfani da Microsoft word da PowerPoint da Excel ba, ba ka san yadda za ka sarrafa AI ba a wannan zamanin shin waye zai yi mafarkin ya zama irin ka har ma yaji yana sha'awar abinda ka karanta? Yadda ake ba wanda ke koyar da direba jirgin sama da mai koyar aikin fiɗa da mai koyar da injiniyoyi kaima haka gwamnati ke biyanka, shin me zai sa ba za ka tashi ka nuna wa duniya abinda ka karanta ya fi na kowa ba? Ha tarin damarmaki nan na jiranka, me zai sa ba za ka koyi yadda za ka samar da manhajojin Hausa na zamani ba da za su baka wasu ƙarin kuɗaɗen shiga? Sai kuma an rasa ɗalibai saboda tsabar sakakinku gwamnati ta gaji da biyanku ta rufe sashen ku ce an zalunceku , ba ruwan gwamnati ku ne. 

Malaman Hausa in zamu gyara mu gyara kawai amma matsalar ɗalibai daga garemu ne, mu tafi da zamani mu bi zamani kawai mu sabunta koyar da harshen Hausa daidai da zamani. 

Wasu tarin matsalolin ma ba su faɗuwa a nan sai ka samu kanka sashen kawai.

Abdulrahman Aliyu, Ph.D
17/08/2025

Karancin Daliban Hausa a Manya Makarantun Kasar Nan: Laifin Malaman Hausa Ne

Post a Comment

0 Comments