Ticker

6/recent/ticker-posts

Ranar Hausa Ta Duniya

ABDULBAKI TUKUR BABBAN GAWO
(Manazarcin Harshen Hausa)
07068721372
a.m.babbangawo@gmail.com

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Fiyayyen Halitta, Shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W. Amincin Allah ya ƙara tabbata ga duk wani Bahaushe da ke doron duniya, gafara da yafiyar Ubangiji su ƙara tabbata ga Hausawan da suka bada gaskiya Allah.

Lallai da uba ake ado ba da rigar aro ba. Hausawan wannan zamani mun zama hankaka (maida ɗan wani naka). A wannan rana da ake bikin ranar Hausa ta Duniya, mi za ka iya gwadawa a matsayinka na Bahaushe wanda za ka iya alfahari da shi cewa lallai kana alfahari da harshenka kuma ka bayar da wata gudunmawa domin haɓɓakar wannan harshe namu mai albarka.

 Matsayin Harshen Hausa a Duniya:

Bisa ga binciken UNESCO da wasu masana harshe, Hausa tana cikin jerin harsuna 10 mafi yawan masu magana a Afirka. A duniya baki ɗaya, tana cikin harshen farko 30–40 mafi yawan masu magana (domin akwai harsuna da dama kamar Sinanci, Turanci, Hindi, Sifaniyanci, Larabci da sauransu da suka fi yawan masu magana).

 Adadin Masu Magana da Harshen Hausa

A halin yanzu, ana kiyasta cewa akwai mutum sama da miliyan 80–100 da suke magana da Hausa a matsayin harshen uwa (mother tongue).

Idan aka ƙara da masu amfani da Hausa a matsayin harshe na biyu, adadin zai iya haura mutum miliyan 150 ko fiye a doron duniya.

Yawancin masu magana da Hausa suna zaune a:

1. Nijeriya (arewa maso yamma da arewa maso gabas).

2. Nijar (kudu maso yamma da tsakiyar ƙasa).

3. Kuma akwai ƙananan ƙungiyoyin masu magana a ƙasashen Chadi, Kamaru, Ghana, Sudan, da ƙasashen ƙetare (sakamakon hijira).

Bisa la'akari da wannan ƙididdiga za mu fahimci harshen Hausa ya yi nisa a duniya, a halin yanzu manyan jami'o'i a duniya suna yin Digiri na farko da na biyu da ma na uku a kan harshen Hausa. Misali:

Manyan Jami’o’in Ƙetare

Waɗannan sun haɗa Hausa a cikin shirin su na African Languages / African Studies:

1. Moscow State University (Russia) – Institute of Asian & African Studies.

2. University of Hamburg (Germany) – African Languages and Cultures (Hausa a ciki).

3. Sebha University (Libya) – Hausa a shirin African Languages.

4. University of Warsaw (Poland) – Hausa a sashen African Studies.

5. SOAS, University of London (UK) – Hausa a cikin African Languages.

6. University of Oxford (UK) – Hausa a ƙarƙashin African Studies.

7. Harvard University (USA) – Hausa a cikin African Languages program.

8. University of Ghana (Ghana) – Hausa a matsayin harshen koyarwa.

9. University of South Africa (UNISA) – Hausa a fannin African Languages.

10. ILCAA, Tokyo University of Foreign Studies (Japan) – Hausa a cikin African Linguistic

 Sharhi

Abun na ci man tuwo a ƙwarya, idan na kalli yadda Hausawa muka yi watsi da ɗabi'unmu da kuma al'adunmu da aka san mu da su na kunya da kara da mutunta na gaba da mu, mun ɗauko ɗabi'un baƙi mun alkinta su, sannan mun fifita su sama da namu waɗanda muka gada. A duk wata ƙabila dake duniya Hausawa ne kawai da aka zo musu da Addinin Musulunci ba a sha wuya ba, domin da daman ɗabi'unmu ba su saɓa wa Addinin ba, sai waɗanda ba a rasa ba.

Abun kunya, abun ban takaici, wai Bahaushe ne zai riƙa kallon masu karatun harshen Hausa yana musu gori, wai miye a cikin Hausar da sai na karance ta, bayan yarena ce. Wallahi ranar duniya idan na shiga kafofin sada zumunta na zamani, kamar in hauda hannu bisa kai in fasa makoki. Kaso casa'in da biyar cikin ɗari wallahi ba su iya rubutun Hausa ba. Kawai yamutsa shi suke yi ba ruwansu da sun yi daidai ko ba su yi ba. Amma su ne gaba-gaba wajen yi wa mutane gyara idan sun yi kuskure a Yaren Ingilishi.

Ina mamakin yadda wasu ke cewa wai in ka karanci Hausa to aikin mi za ka yi? Ina so su karanta wannan su ji:

Ayyuka a Gwamnati

1. Malami/Ɗan koyarwa – a makarantar firamare, sakandare, ko jami’a (Musamman idan ya ƙware a Hausa Education).

2. Mai aikin jarida – a gidajen rediyo da talabijin na gwamnati (NTA, FRCN, ARTV, Radio Nigeria, da sauransu).

3. Ma’aikacin gidan gwamnati – musamman a ma’aikatun da ke hulɗa da jama’a ta Hausa (Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Ma’aikatar Ilimi, Ma’aikatar Al’adu da yawon buɗe ido).

4. Mai fassara ko Interpreter – musamman a kotu, ma’aikatar wajen (Foreign Affairs), ko hukumar ‘yan sanda da DSS idan ana buƙatar harshen Hausa.

5. Civil Service – shiga aikin gwamnati a fannoni daban-daban ta hanyar amfani da Hausa wajen sadarwa da al’umma.

6. Hukumar Gwamnati – aiki da hukumomi irin su NOA (National Orientation Agency), INEC, NIMC, da sauransu inda ake amfani da Hausa wajen wayar da kai.

Ayyuka a Kamfanoni masu zaman kansu

1. Media & Publishing – aikin jarida, rubutu, shirya mujallu, wallafa littattafan Hausa, da shirya fina-finai/series.

2. Public Relations / Corporate Communication – kasancewa mai hulɗa da jama’a ta hanyar Hausa a manyan kamfanoni (MTN, Airtel, Dangote, BUA da sauransu).

3. Translator/Interpreter – kamfanoni da ƙungiyoyin ƙetare (NGOs) suna buƙatar Hausa wajen sadarwa da al’umma (UNICEF, WHO, Red Cross, Mercy Corps, da sauransu).

4. Advertising & Marketing – kamfanonin talla suna amfani da Hausa wajen isa ga masu saye a Arewa.

5. Content Creation – rubuta ko fassara abubuwan Hausa a yanar gizo (websites, apps, manhajojin wayar hannu).

6. Tourism & Culture Industry – jagora (tour guide), mai fassara al’adu, da gudanar da shirye-shiryen yawon buɗe ido.

 Ƙarin Hanyoyin Ci gaba

Ƙirƙirar kansa (Entrepreneurship): wallafa littattafan Hausa, kafa jarida ko rediyo, yin fassarar fina-finai zuwa Hausa.

Ƙwarewa a Hausa + wani fanni (misali Hausa + Law, Hausa + Mass Communication, Hausa + ICT) – hakan yana ƙara damar samun aiki sosai.

Kira zuwa ga Gwamnati

Amadadin ƙungiyar Ɗaliban Hausa da ƙungiyar masu kishin harshen Hausa da al'adunsu, gami da ƙungiyar Hausawa zalla, muna kira ga:

1. Yan majalisar Dattawan Nijeriya da Yan majalisun Wakilai na ƙasa, da su kawo ƙudiri na maida harshen Hausa a matsayin har gwamnati (Official Language) a jihohin a Arewacin Nijeriya, domin ƙara haɓɓaka harshen a duniya.

2. Gwamnatocin jihohi su mayar da darasin Hausa a cikin darussan da aka wajabta ga kowane ɗalibi, kamar dai Lissafi da Turanci. Hakan zai taimaka matasanmu su iya rubutun mai inganci a cikin harshen Hausa.

Daga ƙarshe ina yi wa kowa fatan alheri. Allah Ya dauwamar da zaman lafiya a Jihohinmu da garuruwanmu. Ya Allah Ka ƙara ɗaukaka harshen Hausa da Hausawa a duk inda suke a faɗin Duniya. Muna taya ku murnar Ranar Hausa ta Duniya.

Ranar Hausa Ta Duniya

Post a Comment

2 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.