Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Ka Iyawa, Duk Dagewarka, Ba A Yaba Ma, (Dankali Sha Kushe)

Daga

Mubarak Idris Jikamshi

Wannan takarda gudunmuwa ce ga al'umma masu toƙabo da harshen Hausa, domin ganin an magance matsalolin da suke addabar harshen musamman abin da ya shafi koma bayansa a wajen nazartarsa a jami'o'i. Takardar ta ahamo domin fito da wasu daga cikin matsalolin da kuma bayyana gudummuwar da harshen Hausa yake bayarwa tare da bijiro da hanyar da za a bi don inganta shi.

Har wa yau, takardar daɗin gushi ne na wasu bayanai daga cikin bayanan da malumammu suka riga suka aiwatar. Sai dai masu iya magana na cewa fahimta fuska, kowa da irin tasa. Ni a tawa mahangar, ina kallon waɗannan matsalolin ta fuskoki uku da zan yi bayaninsu daki-daki in sha Allah. Shi ya sa ma takardar na yi mata laƙabi da ''Ba Ka Iyawa, Duk Dagewarka, Ba A Yaba Ma, (Dankali Sha Kushe), ba don komai ba, sai don ganin gwadaben da tirka-tirkar da harshen ya ratso. Kama daga kushen gwamnati da rashin ƙarfafa gwiwar malamai da kuma uwa uba jan ƙafar da al'ummar Hausawa ke yi wa masu karantar harshen duk kuwa da irin tagomashin da suke bayarwa ga al'umma da gwamnati da ma addinai baki ɗaya.

A ra'yina, idan ba harshe ba rayuwa, domin babu al'ummar da za ta yi rayuwa mai inganci ba tare da yin amfani da wani harshe kacokan wanda za ta ta'allaƙa al'amuranta a kansa ba, kama daga abubuwan da suka shafi rubuce-rubuce da fasahohi har ma da kimiyya, dukkan waɗannan abubuwan idan ba harshe babu wanda zai wanzu. Amma duk da haka mun yi shagulatin ɓangaro da al'amarin nazarin harshen Hausa, wanda ba yadda za ka cire shi daga cikin sauran jerin harsunan duniya masu kwarjini da balaga har ma da kokawar rigimar ɗaukar halin tsuntsun nan da ake yi wa laƙabi da HANKAKA...

Kada in cika ku da surutu bari in tafi kai tsaye domin fara sharhin inda matsalolin suke tare da bayar da shawarwari ta yadda za a magance su.

Matsala ta farko na yi mata take da:

1. Sai Bango Ya Tsage....: Gaskiyar ɗiyan Bawo, da yake cewa, 'Sai bango Ya tsage, ƙadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al'umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al'umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaɗuwa kamar wake ɗan arba'in. An taɓa yin wani shugaban ƙasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin ɓata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk ƙasar da ya ratsa a Arewacin ƙasar domin yaƙin neman zaɓe, da harshen Hausa yake magana.

Abin da nake nufi a taƙaice, gwamnati ta yi watsi da harkar koyo da koyarwar harshen Hausa, domin a ganinta ba shi da amfani, wannan ne ya sa har harshen Yarabanci wanda ko kwalar harshen Hausa bai kai ba a wajen tara manyan manazarta kama daga Farfesoshi da kuma yawan gidajen yaɗa labarai da jaridu da makarantun duniya waɗanda suke amfani da harshen Hausar ba.

Kaɗan daga cikin gudunmuwar da gwamnati ta bayar wurin ci bayan nazarin harshen Hausa sun haɗa da: a. Mayar da karatun Hausa a matakin sakandare ZAƁI. b. Tsaurara matakin neman gurbin karatun jami'a domin karantarsa da JAMB suka yi. c. Rashin bayar da tallafin karatu domin nazartar harshen kamar yadda sauran harsuna da kuma gwamnatoci ke yi a wasu darussan. Da sauransu da yawa.

Na sa wa batu na biyu taken:

2. Ka Ƙi Naka, Duniya Ta So Shi: Haƙiƙa da yawan al'ummar Hausawa ba sa alfahari da harshen Hausa musamman ta fannin zuwa su nazarci harshen kamar yadda Turawa da Larabawa ke nazartar nasu harsunan, duk kuwa da irin tasirin da hakan yake da shi a rayuwa bakiɗaya. Amma a haka sai ka iske ƙasashen waje sun dage wajen gabatar da rubuce-rubuce da yaɗa harshen ta kafafe mabambanta har ma da karantar da shi a manyan jami'o'in duniya. Amma mu a nan kallon uku aho ake yi wa da yawan waɗanda suke nazartar Hausa. Abin takaicin masu wannan dattin ƙwaƙwalwar kuma su ne za ka tarar a kaso 90 na rubututtukansu a shafukansu na sada zumunta da Hausa suke yi, idan suna koyon littafan addini duk sai an fassara masu da Hausa ko da kuwa da wane irin harshe aka rubuta littafin addinin nan, ko ka san ɓatan ɓakatantan!

Abin dariya abin tausayi, wai kunama ta harbi ɗan tsako. Yanzu bai zamo abin kunya ba, a ce ƙasa kamar Nijar wadda masu magana da harshen Hausar ƙasar ba su kama ƙafar rabin na Arewacin Nijeriya ba, amma a ce ƙasar sun ayyana harshen a matsayin harshen ƙasa. Me ya sa gwamnatocin Arewa ba za su ayyana shi a matsayin harshen Arewacin ƙasar ba, idan ana toƙabon ƙasar bakiɗaya tana da manyan harsuna guda 3?

Har wa yau, wasu daga cikin malamai suna bayar da gudummuwa wajen ƙin nazartar wannan harshe, musamman ta fuskar yadda suke mu'amalantar ɗalibansu musamman ta fuskar ƙwauron maki da bayar da wahala yayin bincike na ba gaira babu dalili, wanda a hasashena ba komai yake kawo haka ba, sai don kawai a razana ka, wanda hakan ne ya razana da yawa suka ƙauracewa nazartar harshen.

Batu na uku na yi masa ishara da:

3. Idan An Bi Ta Ɓarawo.. Lallai malamai da ɗaliban harshen ya kamata su ci gaba da ayyukan da na san an faro da daɗewa na fassarar muhimman kalmomi na fannonin ilimi da dama, wanda hakan shi zai ba wa masu nazartar harshen dama wajen kutsawa kowane fanni da yin kaka-gida wajen fito wa da ɗalibai abubuwan a sarari domin sauƙaƙa fahimtar darussan. Kamar yadda sauran harsunan duniya irin su: Larabci da Turanci da Indiyanci da Sinanci (Chinese) da sauransu, suka yi.

Gudummuwar Harshen Hausa.

Ido ba mudu ba, amma ya san kima. Ga kaɗan daga cikin wasu gudunmuwar da harshen yake bayarwa a taƙaice:

1. Babu wani littafi na addini da ake karantarwa a ƙasar nan wanda ba a fassara ba ko ake yunƙurin fassara shi zuwa harshen Hausa.

2. An fassara da yawan littattafan kimiyya da na Lugga da na lissafi haɗa har da na tarihi da sauransu domin ci gaban al'umma.

3. Babu wata kafar sadarwa da harshen Hausa bai yi zarra a cikinta ba, kama daga Instagram da Tiktok da WhatsApp da X (Twitter) har ma da uwa uba Facebook.

Haka nan, Harshen Hausa shi ne ya mamaye kafafen yaɗa labarai na Amuruka da Sin da Faransa da sauransu. Bar batun jaridu da kullum ake fito da su cikin harshen domin nusar da al'umma halin da duniya ke ciki.

4. Bugu da ƙari, Manazarta sun samar da kundayen bincike na falsafa da al'ada haɗi da adabi da ma harshe. An kuma rubuta manya da ƙananan littattafai waɗanda ba wanda ya isa ya faɗi adadinsu da irin fannonin da littattafan suka taɓo. Ana kuma samar da muƙaloli a fagage mabambanta ba don komai ba sai don ƙoƙarin ciyar da harshen da ƙasa da kuma al'umma gaba.

SHAWARWARI:

Akwai matakai da yawa da ya kamata a ɗauka domin dawo da martabar koyon wannan harshe mai albarka. Ga kaɗan daga ciki:

1. Tafiya da zamani.

2. Sauƙaƙa hanyoyin koyo da koyarwa.

3. Mayar da nazarin harshen wajibi a ƙananan makarantu na firamare da sakandire.

4. Sanya koyon shi ya zama wajibi ga duk ɗalibin ƙasar waje da ya zo yin karatu a ƙasar nan, kamar yadda da yawan ƙasashe suke yi.

5. Kutsawa fannonin kimiyya da fasaha da fannin likitanci da magunguna domin ci gaba da gudanar da nazarce-nazarce.

6. Sanya shi a cikin darussan dole Gens/GSE manhajar koyarwar jami'o'i da kwalejojin ilimi da na kimiyya.

7. Mayar da harshen Hausa ya zamo harshen hukuma a yankin Arewa idan ma ba ƙasar (Nijeriya) duka bakiɗaya ba.

8. Ƙarfafa gwiwar iyaye da ta abokai har ma da uwa uba malamai ga masu nazarin harshen Hausa.

9. A aje ƙwarya a burminta. Ka da a ɗauki aikin da aka san manazarcin harshen Hausa ne kaɗai zai iya a danƙa shi ga wani, musamman abin da ya shafi ayyukan fassara da na talife-talife.

Aiwatar da waɗannan da ma wasu abubuwa za su taimaka gaya wajen ganin an dawo da kima da kuma martabar nazarin harshen Hausa.

Kammalawa:

A taƙaice wannan takarda ta tattaro wasu bayanai ne da suka shafi matsalolin da harshen Hausa yake fuskanta waɗanda suka haddasa mashi koma baya, da kuma gudummuwar da harshen Hausar yake bayarwa a zamanace da addini da ma rayuwa bakiɗaya, daga ƙarshe kuma takardar ta bijiro da wasu hanyoyi da za a bi domin ganin an dawo da martabar nazartar harshen a ƙasa bakiɗaya.

Mubarak Idris Jikamshi
Ranar Hausa TA Duniya
26/08/2025

Ba Ka Iyawa, Duk Dagewarka, Ba A Yaba Ma, (Dankali Sha Kushe)

Post a Comment

0 Comments