Ticker

6/recent/ticker-posts

Ranar Hausa Ta Duniya - 2025

Ranar Hausa Ta Duniya (26 ga watan Agusta na kowace shekara) rana ce da ake keɓe wa don tunawa da harshen Hausa da al’adun Hausawa, tare da ƙarfafa cigaba da wanzuwarsu. A wannan rana, ana shirya taruka, hira, wasanni, da gabatar da adabi domin nuna armashin harshen da tumbatsar adabi da al'adunsa.

Manufarta ita ce ƙara haɗin kan Hausawa a duniya, da kuma tunatarwa cewa Hausa harshe ne mai tarihi, ɗaukaka, da tasiri a fagen siyasa, kasuwanci, da ilimi. A taƙaice, rana ce ta alfahari da gadonmu.

Ku turo mana hotuna ko rubuce-rubuce game da shirye-shiryenku ko yadda kuka gudanar da bikin Ranar Hausa Ta Duniya a yankinku. Mu kuma za mu tallata muku su a kyauta, da ikon Allah.

001 - Daga Daura
Soron Inyanga

RANAR HAUSA: 26 Agusta 2025 - A bana za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar Katsina. kuma ana sa ran baƙi daga ƙasashe aƙalla 24 za su halarta.

Hoton da aka kawo a sama, shi ake kira Soron Inyanga.

Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) ya bayyana cewa, Makaɗa Musa Danƙwairo Maradun ya ambaci wannan Soron a cikin faifansa na Marigayi Mai martaba Sarkin Daura na 59, Alh. Dakta Muhammadu Bashar mai amshi "Mamman jikan Abdu, gagara k'arya mai ban tsoro".

"Hay yaz zo yas sabka,
Bakin Soron Inyanga".

002 - Daga Ghana

Ranar Hausa Ta Duniya - 2025

003 - Daga Kano

Ranar Hausa Ta Duniya - 2025

Daga Sakkwato

Ranar Hausa Ta Duniya

Daga Jami'ar ABU

ABU


Post a Comment

0 Comments