Ticker

6/recent/ticker-posts

Kimar Mace a Ma’aunin Matakan Rayuwar Maguzawa

Cite this article as: Abdullahi I.S.S. & Dalha I. (2025). Kimar Mace A Ma’aunin Matakan Rayuwar Maguzawa. Zamfara International Journal of Humanities,3(3), 213-222.www.doi.org/10.36349/zamijoh.2025.v03i03.020

KIMAR MACE A MA’AUNIN MATAKAN RAYUWAR MAGUZAWA

Na

Ibrahim Sarkin Sudan Abdullahi
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Da

Ibrahim Dalha
Ɗalibi a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Tsakure: Tun gabanin Hausawa su karɓi kowane saukakken addini mata suke da kima a wurinsu. Manufar tabbatar da wannan hasashe shi ne ya ja hankali aka gudanar da ƙwarya-ƙwaryan nazari saboda a ƙyallaro shi a cikin aladun matakan rayuwar Maguzawa na aure da haihuwa da mutuwa. Takardar ta yi amfani da karance-karance a matsayin hanyar bincike. An ɗora nazarin a kan tunanin Hausawa da yake cewa: “Inda aka san darajar goro nan ake nema masa ganye.” Takardar ta yi garkuwa da wasu misalai na al’adun Maguzawa guda goma sha biyar (15) waɗanda suka ratsi matakan rayuwarsu na aure da haihuwa da mutuwa; saboda a tabbatar da kimar da mace take da ita a wurinsu. Wasu daga cikin sakamakon da aka iya hangowa a dalilin wannan bincike sun haɗa da: Sanin kimar mace tare da tabbatar da ita a aikace da Maguzawa sukan yi, ya taimaka ta fuskokin ɗorewar tarbiyarsu da kyautatuwar zumuncinsu da tausaya wa junanusu tare da haɗin kan da yake tsakaninsu. Bugu da ƙari, wannan nazari ya gano cewa, kimar da mace take da ita a aladun Maguzawa ita ce ta yi tasiri matuƙa har ya zuwa bayan da wasunsu suka karɓi addinin Musulunci. Ke nan, wannan ya tabbatar mana da abin da Hausawa suke cewa: “Daɗin goyo shi ke sa jijjiga.”

Keɓaɓɓun Kalmomi: Kima da Mace da kuma Matakan Rayuwa.

Gabatarwa

Maguzawa mutane ne da suka daɗe da sanin kimar ɗan’adam duk kuwa da kallon da ake yi musu na waɗanda suka bambanta da mafi yawan Hausawan da suka karɓi addinin Musulunci. Idan aka waiwayi rayuwarsu cike take da tanade-tanaden da suke tabbatar da kiyaye haƙƙin ɗan’adam da sauran batutuwan da suka shafi zamantakewa. Sanin kimar ɗan’adam a zamantakewar Maguzawa, shi ne ya sa al’ada ta tilasta yara su riƙa mutunta manya tare da taimaka musu ta fuskokin riƙa musu kayan da ke hannunsu ko kuma kama musu wani aiki domin su samu sauƙi. Haka abin yake ga manya, su ma alada ta tanadar musu da haƙuri da tausayawa ga lamuran da suka shafi yara. Irin wannan tarbiya ita ce ta yi amo a zamantakewar da take tsakanin miji da mata. Hasali ma mata suna cikin wani ɓangare da al’adar Maguzawa ta tanadar musu da wata kima ta musamman. Ga al’ada, sanin kimar ɗan’adam da kiyaye haƙƙoƙinsa shi yakan haifar da tausayi a tsakanin alumma. Hakan ya sanya Nuhu (2020:395) ya yi amannar cewa, zaman tare yana buƙatar masu zaman da su tausaya wa juna a duk wani abu da zai shafi abokin zama. Duk da kallon da wayewar kan zamani take yi wa wasu daga cikin aladun Maguzawa na gargajiya, akwai abin koyi daga cikinsu, musamman waɗanda suka shafi kiyaye kimar mace. Ɓatan dabon da wasu aladun Maguzawa na kiyaye kimar mace suka yi saboda guguwar sauye-sauyen zamani, shi ya haifar da kallon da wasu suke yi musu na mutanen da suka ƙanƙame ɗabi’unsu na gargajiya. Hasali ma wasu da suke da masaniyar Maguzawa suna gudanar da noma da wasu aikace-aikacen gida tare da matansu, sai suke tunanin suna barin su a cikin ƙuncin rayuwa. Sun kasa gane cewa, tukunyar da ake tuƙa farin tuwo a cikinta, bayanta baƙi ne.

Maƙasudin wannan takarda shi ne, fayyace wasu abubuwan da suka shafi kimar mace a aladun Maguzawa na matakan rayuwa. An yi wannan tunani ne saboda a toshe wata kafa ta ilimi da aka hango. Baya ga haka kuma, nazarin zai ƙara tabbatar da yadda Maguzawa suke da ƙoƙarin kiyaye kimar mace tun kafin guguwar rajin kare haƙoƙin mata da take kaɗawa a wannan lokaci ta bayyana. Nazarin ya yi la’akari da cewa, ayyukan da Ibrahim, (1982 da 1985) da Abdullahi (2008) da Nuhu (2020) suka gudanar ba su keɓe wani fasalin da suka yi bayanin kimar mace a Maguzance ba. Wannan dalili ya sa aka ga dacewar cike wannan giɓi na ilimi, saboda a tabbatar wa da masu rajin kare haƙƙoƙin mata cewa, Maguzawa sun daɗe da wannan wayewar tun kafin su haɗu da kowace al’umma.

Hanyoyin Bincike

Nazari kan lamarin da ya shafi rayuwar Maguzawa yana buƙatar tuntuɓar wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar a kansu. Wannan dalili ya sa aka yi wa takardar guzurin da ya kai ga leƙa wasu daga cikin ayyukan da suke da dangantaka da aladun Maguzawa domin su zama jagora ga bayanan da aka fito da su. Takardar ta samu nasarar yin ido biyu da wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar a matakan digiri na uku da na biyu da kuma na ɗaya. Har wayau, an ci nasarar leƙa wasu maƙalu da aka gabatar a mujallun ilimi waɗanda suka tattauna batutuwan da suke da alaƙa da binciken da aka gudanar. Ayyukan da aka samu damar kaiwa gare su, an same su ne ta hanyar leƙa ɗakunan karatu daban-daban.

Hanyar Ɗora Aiki

A wannan bincike, hanyar ɗora aiki tana nufin tafarkin da magabata suka samar domin zama jagora ga ayyukan ilimi, saboda nazarce-nazarcen da aka gudanar su samar da kyakkyawar alƙibla ga alumma. A ƙoƙarin ganin wannan nazari ya samu wannan tagomashi, an ɗora shi a kan tunanin Bahaushe da yake cewa: “Inda aka san darajar goro nan ake nema masa ganye.” An yi amfani da wannan tunani ne saboda dacewarsa da yanayin yadda Maguzawa suka san daraja da kimar mace, inda suke ba ta wani matsayi na musamman a al’adunsu na matakan rayuwa (aure da haihuwa da mutuwa). Kimar da mace take da shi a wurin Maguzawa, shi ne ya sanya al’adarsu ta yi wani tsari na musamman wanda ba ta yi wa namiji ba. Kenan, a wannan bincike, mace ita ce tamkar ɗan itaciyar “goro” wanda ga al’ada akan lulluɓa masa ganye da manufar darajanta shi, saboda ba a son ya bushe. Sakamakon bushewarsa kamar walaƙantawa ce a gare shi.

Bayanin Fitulun Kalmomin Taken Bincike

Ƙoƙarin wannan takarda na yin susa a gurbin da yake ƙaiƙayi, shi ne ya sa aka ware wannan muhalli domin fito da maanonin kalmomin da suka gina taken da aka sanya mata. Kalmomin da aka bayyana maanoninsu saboda su zama jagora wajen fahimtar wannan takarda su ne: Kima da mace da matakan rayuwa.

Kima

Kima dai kalma ce da Hausawa suke amfani da ita wadda take da ma’anar “daraja” ko kuma matsayi. A wannan takarda, kalmar kima tana nufin darajar da mace take da ita a tsarin matakan rayuwar Maguzawa. Hakan bai rasa nasaba da tuntuɓar wasu Ƙamusoshi na Abraham (1977:626) da CNHN (2006:311) inda aka gano cewa, maanonin da suka bayar duka sun yi tarayya da juna.

Mace

Mace kalma ce da take nuna jinsin da yake kishiyantar namiji. Bugu da ƙari, Newman (2020:168) da CNHN (2006:311) duka sun aminta da cewa, mace kishiyar jinsin namiji ce. Don haka CNHN (2006:311) ya bayyana cewa, kalmar mace tana nufin jinsin halitta na mutum ko dabba mai ɗaukar ciki ta haihu, kishiyar namiji. Har wa yau, aikin Ingawa (1984:1) yana da ra’ayin cewa, “Macen mutum halitta ce wadda Maɗaukakin Sarki Allah ya yi wadda take ta bambanta da halittar namiji. Dukkan mata na duniya suna da wasu abubuwa na daga halittun jiki iri ɗaya, sai dai kawai wata macen ta fi wata girma, ko kuma ƙanƙantar abin da aka halitta, ko kuma ta fi ta farar fata ko baƙi.

Matakan Rayuwa

Ana iya bayyana matakan rayuwa da ma’anar wasu tsare-tsare na al’ada wanda mutum yake shiryawa daga farkon rayuwarsa zuwa ƙarshenta. Bunza, (2013:426) ya bayyana cewa, a falsafar alada, kowane mutum yana hawa matakai uku a rayuwarsa. Idan muka zura wa waɗannan matakai ido, suna da tsari kamar haka:

i.                    Idan aka haifi mutum ya kai munzalin aure, ya kammala mataki na farko.

ii.                  Mataki na biyu kuma shi ne, idan ya haihu, ya sami ɗa ko ɗiya.

iii.               Baya ga wannan, matakin da zai shiga na mutuwa shi ne na ƙarshe a rayuwar ɗan’adam. Wannan dalili ya sa manazarta suka haƙiƙance cewa, ɗan’adam yana da tsarin matakai uku a rayuwarsa. Shi ne suke taƙaita su da matakan rayuwa na aure da haihuwa da mutuwa.

Muhallin Mace a Matakan Rayuwar Maguzawa

La’akari da bayanan da aka gudanar a muhallin da ya gabata, an tsara fayyace kimar da mace take da ita a rayuwar Maguzawa ta hanyar matakai guda uku. Mataki na farko shi ne na aure sai aka shiga na haihuwa, sannan aka ƙarƙare da na mutuwa.

Kari a Wurin Gaɗa

Gaɗa dai wasa ne da ‘yan mata suke gudanarwa domin nishaɗantar da junansu a lokacin da suke cikin nishaɗi. A ganin CNHN (2006:149) wasa ne na ‘yan mata na waƙa da tafi da yan tsalle-tsalle. Ƙoƙarin Maguzwa na tabbatar da mace tana da kima a wurinsu, idan yan mata suna gaɗa, shi ne ya sanya samari sukan taru su yi wa budurwar da suke ƙauna karin kuɗi da manufar ta fito ta yi rawa a gaban makaɗi. Bugu da ƙari, kimar da mace take da shi a wurinsu ita ta sanya hatta makaɗin da yake cashe kiɗa ga ‘yan matan yakan amfana da kyautar kuɗi ko wani abu mai daraja a lokacin da suke wasan gaɗa. Idan babu mace a wurin gaɗa, wasan ma ba zai gudana ba ballantana ya yi armashin da za a sami kari na kuɗi ko wani abu mai daraja.

Toshi a Wurin Neman Aure

Toshi dai wata nau’in kyauta ce da namiji ko wani nasa yakan bayar ga macen da yake da muradin aura da manufar nuna so da ƙauna da kuma jawo hankalinta ko na wani nata domin ƙara wa dangantakarsu tagomashi. Kimar mace a wurin Maguzawa ya sanya suke ba wannan al’ada muhimmanci, inda akan fara ta tun daga ranar farko da aka haɗu tsakanin masoyan juna har zuwa lokacin ɗaura aure. Toshi bai tsaya ga ba da kuɗi kawai ba, aikace-aikacen da saurayi yakan yi ko wani nasa ana ɗaukarsa a matsayin toshin yarinyar da aka nuna ana so da aure. Duk wani aiki na kyautatawa ga iyayen yarinyar da yake ƙauna kamar noma da sauran aikace-aikacen gida na yau da kullum ana kallonsu a matsayin toshi. Kimar da mace take da shi a wurin Maguzawa, shi ne ya sa aladar toshi ta samu karɓuwa matuƙa. Tun daga lokacin da iyayen yaro suka nuna suna shaawar haɗa shi da wata yarinya suke fara bayar da toshi. Har ila yau, magabatan yaro sukan samu lokaci na musamman su tanadi wani abu da za su kai gidan surukan ɗansu. Duk lokacin da ake wani buki a gidansu yarinyar da suka yi wa ɗansu kame da ita, sukan yi ƙoƙarin bayar da gudunmawa har sai inda ƙarfinsu ya ƙare. Ga al’ada, kowace ranar kasuwar da ya san budurwar da yake so tana ci sai ya nemi abin da ya kai ya sayar don ya yi mata toshi. Yayin da budurwa ta aminta da saurayi ya tafi gidansu, a duk lokacin da ya je zance ba zai je hannu sake ba. Dole ne ya nemi abin da zai bayar. Idan kuma wasu bukukuwa sun tashi na danginta nan ma sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Kimar mace ta ɓangaren ba da toshi a wurin Maguzawa ba ta kaɗaita ga bayar da wani abu ba. Gungun abokan masoyan mace (samarinta) daban-daban sukan haɗu su yi ta karakaina wajen kai gayyar aiki a gonakin iyayenta. Hakan yana tabbatar wa da iyayen mace cewa, ‘yarsu tana da tagomashin samari masoya. Kimar mace ta sanya iyayenta sukan ci albarkacinta, inda samari sukan yi musu toshi na ayyukan gona da sauransu.

Tsarance

Wata al’ada ce ta Maguzawa inda saurayi da budurwar da zai aura za su kwana a kan shimfiɗa ɗaya ba tare da wani tunani na lalata ya kasance a tsakaninsu ba. Kowane ƙauye ko kowace ƙasa ta Maguzawa da irin fahimtar da kuma tsarin da aladarsu ta tanadar wa tsarance. A tsarin zamantakewar Maguzawa, duk saurayin da ya kasa yaƙi da zuciyarsa a lokacin tsarance har ya taɓa ko da hannun budurwar ne, mutuncinsa ya zube a wurinta da iyayenta da abokansa da ma ƙawayenta. Sakamakon haka za su riƙa kallonsa a matsayin marar amana, kuma bai san kimar macen da zai aura ba. Hasali ma hakan kan iya sanyawa al’umma su tsangwame shi ta yadda zai kasa sake jiki saboda kunya. Idan lamarin ya yi tsanani ma har barin garin sai ya yi, domin baya ga tsangwama daga iyaye da abokai, budurwar da ya yi wa haka ma ba za ta sake yarda da shi ba.

Al’adar Aron Amarya

Ga al’adar Maguzawa, zaman da amarya take yi a gidan lalle, maƙunshiya za ta yanka wa yan matan amarya ɗan akuya, a ba su su ci, ita kuma ta ɗauki karfata ɗaya (ƙafar akuya ta gaba). Idan akwai wata maƙunshiyar ita ma haka za ta yi kafin a mayar da aron amarya. Wani lokaci akan samu mai aron amarya fiye da ɗaya, musammman idan amaryar tana da dangi da yawa. Hakan kuma wani abin alfahari ne a wurinta da kuma danginta. Wannan al’ada tana gwada kimar da mace take da ita a wurin Maguzawa. Wasu daga cikin hikimar da aka iya ganowa ta kimar mace a wannan al’ada sun haɗa da: Kimar mace ta sanya danginta na ɓangaren uba da na uwa suke rububin ɗaukar aron ta. Daɗin daɗawa, samun masu aron amarya da yawa yana gwada yawan dangin da amarya take da shi, sannan kuma yana tabbatar da kimar da mace take ta shi a wurin Maguzawa. Kyautatawar da mai aron amarya take mata tare da ƙawayenta wata madogara ce da take ƙara tabbatar cewa, mace tana da ƙima. Idan an lura, namiji (angon) da zai yi aure babu wani bayani da yake nuna ana yi masa irin wannan hidima a aladun Maguzawa.

Wankan Amarya

Abin da ke gaba bayan ɗaura aure ga al’adar bukin Maguzawa shi ne wankan amarya.Wannan al’ada cike take da hikimar nuna kimar mace a idon Maguzawa. A tunanin Maguzawa, dole ne a tsabtace mace kafin a kai ta gidan mijnta, saboda ta shigo wani sabon yanayi na sabuwar rayuwa. Ana gudanar da wankan amarya da manufar wanke ƙazantar da ta ɗauka ta budurci da zaman gidan iyaye, saboda a shirya yadda za ta yi zaman gidan miji. Wankan amarya yana tabbatar da cewa, mace ta samu sauyin ‘yanci, inda yanzu za ta zauna a ƙarƙashin miji maimakon iyaye. Don haka ita ma ana kallon ta ne a matsayin uwa, maimakon yarinya. Kenan, wankan da akan yi wa amarya yana alamta sauya sabuwar rayuwa ne a gare ta. A cikin aladar wankan amarya na Maguzawa, sukan cuɗanya ruwan da ganyen yaɗiya. Hakan yana da nasaba da tunanin da suke da shi na cewa, cuɗanya ruwan da ganyen yaɗiya saboda ya yi yauƙi ta yi ta yaɗuwa a gidan da ta je zaman aure. Kimar mace ya sa mata ne suke gudanar da wannan al’ada, saboda haka suke taruwa, in ban da yara da kuma wasu tsirarun samari da ba a rasa ba. Kuma samarin ba koyaushe suke zuwa ba. Yanayin yadda ake wankan amarya tare da ɗaura mata farin saƙin zani, kan sa danginta yin kukan rabuwa da ita, tare da nuna takaicin barin gidansu. Duka waɗannan suna nuna kimar da mace take da shi a idanun Maguzawa. Wani abin armashi, babu inda al’adarsu ta tanadi wankan ango kamar yadda ake na amarya.

Kai Bante

CNHN(2006:36) ya bayyana kai bante da, “Kai budurci.” A al’adar auren Maguzawa yana daga cikin abin farin-ciki da murna ga mace da iyayenta har ta yi aure ba tare da wani namiji ya taɓa saduwa da ita ba, shi ne sukan ce wance ta kai ɗiyaucinta. Kamar yadda a ɓangare ɗaya kuma yake zama abin baƙin ciki ga iyaye da dangi ga wadda ta taɓa yin lalata. Sanin kimar da ke tattare ga mace ya sanya Maguzawa suke ƙoƙarin tabbatar da nesantar aikata lalata duk kuwa da shaƙuwar da za su yi da juna. Tsoron abin kunyar da za a iya shiga a dalilin lalata shi ne ya sa mata suke tsoron aikatawa, saboda yakan rage kimarta da ta iyayenta a idon alumma. Kasancewar ɗan’adam tara yake bai cika goma ba, Maguzawa suna da wasu hanyoyi da suke amfani da su domin tabbatar da kimar macen da ba ta taɓa lalata ba. Misali, Maguzawan Kaibaki da na Ƙwanƙi duka suna amfani da wasu tsafe-tsafensu da suke haɗawa da ɗan’akuya wajen tabbatar da kimar mace na cewa ta kai bantenta. Su kuwa Maguzawan Kaita ango ne da kansa yake bayyana cewa amaryar da ya aura ta kai bantenta ko ba ta kai ba. Abdullahi (2008:194) ya rawaito cewa, akwai manazartan da suke da ra’ayin ana iya raba tsafin da Maguzawa suke yi na tabbatar da mace ta kai ɗiyaucinta dangane da abin da suke bauta wa. Masu bautar Kurmawa suna da nasu tanade-tanaden; kamar yadda masu amfani da tsafin Uwargona suke da nasu. Abin dai da ake so a fahimta a nan, shi ne, hikimar da ke cikin tanade-tanaden tabbatar da mace ba ta sadu da wani namiji ba in ba wanda aka aura mata ba, shi ne domin a nuna kimar da ke gare ta. Wadda ta taɓa saduwa da namiji kafin aure kuwa, al’adar Maguzawa ta tanadi wasu abubuwa da za su tabbatar mata da zubewar kimarta a idanun al’umma. Wasu daga cikinsu sun haɗa da: Kunyatar da iyayenta da saurayin da zai aure ta da kuma ita kanta akan cewa ta ci amana. Akan rage wa mace dukiyar auren da aka tanadar mata, saboda zubewar kimarta a dalilin lalatar da ta aikata. Bugu da ƙari, akan hana kowane saurayi ya aure ta, sai dai ta auri tsoho, wani ma zai iya kaiwa shekarun kakanta. Haka kuma, takan sami rashin tabbas a rayuwarta, musamman idan aka doge sai an gudanar da wasu aladunsu na bukin aure. Alada ta tanadi huda ƙwarya a sanya a ɗakinta ko a kai ta gidan miji tare da kuikuyo yana nuna alama ce ta rashin kima a Maguzance. Wannan ya nuna Maguzawa suna lura da kimar da ke ga mace, don haka suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tabbatar da ita. A ƙoƙarin tabbatar da wannan ƙimar, mace da iyayenta sukan tashi tsaye wajen ganin sun sami wannan nasarar.

Ɗaukar Amarya

Kiyaye kimar mace da Maguzawa sukan yi, shi ne ya sa a al’adarsu amarya take samun tagomashi a lokacin da za a kai ta gidan mijinta yayin da ake shagalin bukin aure. Wasu daga cikin al’adun da ake gudanarwa waɗanda suke nuna kimar da mace take da ita a wurin Maguzawa sun haɗa da: Dangin miji maza da mata, babba da yaro sukan zo ɗaukar amarya; kamar yadda abokan ango sukan zo. Abokin ango shi yakan ja goɗiyar da za a ɗora amaryar a kai domin a kai ta gidan mijinta. Ana raka amarya gidan mijinta ne da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, wani lokaci ma akan haɗa da busa algaita. Idan ba a sami goɗiyar da za a ɗora amarya a kanta ba, to wasu Maguzawan sukan goya ta a baya. Za a sami mata daga cikin dangin ango su riƙa goya amaryar. Idan wannan ta gaji sai ta ba wata har a kai ta ɗakin mijinta. Wasu kuwa abokin ango ne zai ɗauke ta ya saɓa a wuya zuwa gidan mijinta. Wasu kuma idan kusa ne da ƙafarta za ta tafi. Daga cikin masu raka amaraya, akan sami masu hawa dawaki da jakuna. Kimar amarya a wurin Maguzawa ya sa ake ɗora ta a kan goɗiya ko a goye ta a baya kamar wata sarauniya.

Zaman Aure

Shi ne haƙiƙanin rayuwar da take gudana ta fuskar zamantakewa a tsakanin miji da mata. Duka wanda ya yi aure ana sa ran a ga kyakkyawar zamantakewa mai ɗorewa a tsakaninsa da wadda ya aura. Ga al’adar Maguzawa, ba a samun bambanci ta fuskar yanayin zaman aure. Tun daga ranar da aka kai amarya, da zarar jama’a sun watse ta fara zaman aure ke nan. Maguzawa ba su gina wa ango da amarya gida su kaɗai daga shi sai ita, ko da kuwa yana da arzikin da zai iya gina gidan kansa. Dole ne akwai mutane a cikin gidan suna zaune tare da su musamman iyayen miji. Sukan yi aikin gona tare da mijinta, sannan kuma ita ma tana da wata gona da takan yi nata aikin na ƙashin kanta. Duka abin da ta noma na gonarta nata ne, kuma tana iya amfani da shi a gidan a ci in ta ga dama. Tana iya sayarwa ta yi sabgar dangi, ko ta maƙwabta. Baya ga haka kuma, tana iya sayar da abin da ta noma ta sayi ’yan awaki ta yi kiwo ko kuma ta sami jarin yin wata ’yar sana’a a lokacin rani. Wannan dama da ake ba mata tana taimaka musu wajen mallakar abin hannunsu inda suke tsayawa da ƙafafunsu ba tare da sun dogara da mazansu ba. Baya ga haka kuma, hakan ya fito da kimar da mace take da ita, ta yadda Maguzawa ba su tauye matansu ta fuskar taimaka musu wajen ginuwar tattalin arzikinsu.

Guɗa

Wata nau’in ɗaga murya ce da mata sukan yi a lokacin da suke cikin wata murna bisa wata ni’ima da ta same su. Hasali ma Hausawa sukan yi mata kirari da, “In ka ji guɗa da labari.” Don haka suka aminta da cewa, “guɗa ba a rangaɗa wa asara.” CHNN (2006:172) ya bayyana ta da, “ɗaga sauti da ƙaraji wanda galibi mata kan yi, ta hanyar amfani da baki, da hanci don nuna murna wajen biki ko wucewar sarki ko jin wani labari mai daɗi, ko ganin wani abu da ake jiran zuwansa.” Wannan ma’ana ta ci karo da kalmar da Newman, (2020:92) ya fassara, inda ya yi ƙoƙarin bayyana maanarta da wata kalmar Turanci da take nuna ɗaga murya mai ƙara da niyyar murna ko baƙin ciki. Ga aladar Maguzawa, murna ce take sanya a yi guɗa, baƙin ciki idan ya faru kuka akan yi. Kimar mace a wurin Maguzawa ya sanya sukan yi guɗa guda huɗu idan jaririyar da aka haifa jinsinsu ce, amma idan namiji ne akan yi guɗa guda uku. Falsafar da ke cikin bambancin adadin guɗar da ake wa mace da namiji sun haɗa da: Kara ga mai haihuwa, saboda an samu jinsinta. Son kai ga mata, saboda su nuna jinsinsu aka samu. Ƙoƙarin da mata suke na tabbatuwar zamantakewa ta fuskar ɗawainiyar riƙon gida da kula da duk wasu ayyuka da sukan wanzar da ingantacciyar rayuwa a gidan da suke. Haka kuma, suna alamta cewa, alaurar mace ta fi ta namiji yawa.

Ba Mace Damar Zaɓen Suna

Kasancewar al’adun Maguzawa suna bambanta daga wuri zuwa wuri a kan sha’anin tsare-tsaren da suke gudana waɗanda suka shafi raɗa sunan abin da aka haifa. Al’adar Maguzawan Kainafara tana ƙunshe da tabbatar da kimar mace yayin da aka zo raɗa wa abin haihuwar da aka samu suna. Bayan abin haihuwar da aka haifa ya ɓace tun daga ranar haihuwa zuwa kwanaki goma sha huɗu. Ranar da kwanakin suka cika, bayan sun tabbatar da abin da aka haifa ya dawo daga wurin tsafinsu, sai wasu tsofaffi maza waɗanda adadinsu ya kai guda goma su zauna a gindin wata bishiya da ke ƙofar gidan da aka yi haihuwar. Tsofaffin za su sami karare su yi zane a kowane ɓari na su, sai su kira ungozoma su ce ta kai wa maijego ta zaɓi guda ɗaya daga cikinsu. Idan Ungozoma ta dawo musu da wanda ta zaɓa, sai su yi la’akari da nau’in zanen da yake jikin karan su bayyana sunan abin da aka haifa, tare da ba ta umarnin ta koma ta bayyana wa mai haihuwar. Kodayake, ba za a bayyana sunan ba sai ranar aurensa ko aurenta (abin da aka haifa ɗin). Don haka za a yi ta kiran jaririn/jaririyar da laƙabin da kakanni suka sanya masa. Su kuwa Maguzawan Kudancin Katsina ba sa raɗa wa jaririn/jaririyar da aka haifa suna sai bayan kwanaki arba’in da haihuwa. Idan aka zo zanen sunan, mata dangin uba da na mahaifiyar jaririn/jaririyar ne suke haɗuwa a gidan da aka yi haihuwar. Suna kiran wannan al’adar da Kantsaki. Lokaci da yanayin da aka haifi jariri/jaririyar, su ne suke tsayawa a matsayin mizanin sunan da ya dace a sanya masa. Keɓe mahaifiyar jariri ko jaririyar da aka haifa ko kuma wasu dangin mahaifansa mata wajen tabbatar da sunan da ya dace gare su ya fito da kimar da mace take da shi a wurin Maguzawa.

Ba Mace Damar Sauya Miji In Ba Ta Gamsu Ba

Yana daga cikin kimar da Maguzawa sukan ba mace na ba ta dama ta sauya mijin da za ta aura idan ba ta gamsu da shi ba. Maguzawa sukan ƙulla aure ta hanyar yi wa miji kame tun yarinya tana ƙarama. Wani lokacin idan yaran sun girma, akan samu bambancin raayi a tsakaninsu, inda wani daga cikinsu yakan samu sauyin tunani dangane da alƙawarin kamen da iyayensa suka yi masa. Wani lokaci kuma, waɗanda suka ƙulla alƙawarin ne wani daga cikinsu yake mutuwa, dalilin haka idan wani ya shigo sai ya ɗauke wa yarinyar hankali ta rabu da wanda aka yi mata kame tun da farko. Idan haka ta faru, akan sami wani daga cikin manya ya ba mace damar ta zaɓi wanda take so ta aura a cikinsu, saboda ƙoƙarin daidaita su da aka yi abin ya ci tura. Ga aladarsu, iyayen macen ne suke biyan abin da aka kashe mata na kuɗi ko kuma wasu kaya na zahiri da ya taɓa ba ta; sai dai ba a biyan aikace-aikacen da ya yi wa iyayenta.

Har wayau, yana daga cikin dalilan ba mace dama ta sauya miji a wurin Maguzawa, idan ta gaji da miji ko kuma ta ji ba ta son sa aka kuma tabbata akwai wanda take ƙauna. Idan haka ta faru, akan gane haka idan ta fito, ana tsammanin yaji ta yi, amma ba ta je gidan iyaye ba, tana gidan wani. Wannan wanda ta koma gidansa shi ne sabon miji, sai ya nemi tsohon mijinta ya biya shi abin da ya kashe na dukiyar aure. Sakamakon yana da wahala ya iya biyansa dukkanin abin da ya kashe, yana iya karɓar wani abu a wurin wanda matar ta koma gidansa. Misali, kamar jaki ko doki ko kuma saniya. Sukan yi haka ne saboda tsohon mijin ya rage hasara. Duk da haka, idan tana da ciki, ya zama na sabon mijnta da ta koma gidansa. Idan kuma suka sami saɓani da sabon mijin bayan wani lokaci ko kuma shekaru, tana da damar ta koma gidan tsohon mijinta ba tare da an biya shi dukiyar aurensa ba. Idan kuma tana so ta koma babu wani saɓani a tsakaninsu, takan gudu ne a ɓoye ba tare da sanin sabon mijin ba. Don haka a ɓoye za ta kwashe kayanta tare da ‘ya’yanta su koma gidan mijinta na baya. Hakan ya sa take kwashe kayan ta bayan gida tare da taimakon ‘ya’yanta ba tare da sanin kowa ba. Wannan al’adar ta tabbatar da tilasta mace ta zauna da mijin da ba ta so ba ya daga cikin ɗabi’un Maguzawa. Bugu da ƙari, hakan ya nuna Maguzawa sun bar mata cikin walwala ba tare da sun tauye su ba saboda kimar da suke da ita.

Biko Idan Mace ta Yi Yaji

Biko dai wata hanya ce ta al’ada da Maguzawa suke amfani da ita wajen sasanta ma’auratan da suka sami saɓani a tsakaninsu, ta hanyar ba macen da ta tafi yaji haƙuri domin ta dawo gidan mijinta. CNHN (2006:46) ya fassara kalmar biko da, neman dawo da matar da ta yi yaji. Shi kuwa Rambo, (2007:119) yana da raayin kalmar biko ta samo tushenta ne daga bi da ake wa matar da ta yi yaji domin ta dawo ɗakinta. A ɓangare ɗaya kuma, biko yana nufin hanyar sasantawa a tsakanin namiji da mace bayan sun ɗan samu wani saɓani da ya haifar da ta bar ɗakinta (Rambo, 2021:697). A zamantakewar rayuwa, duk kyawun da zama ya yi tare da juna a tsakanin ma’aurata, wani lokaci akan iya samun cin karo da buƙatun juna. Hakan kuma shi yake haifar da samuwar saɓani a tsakanin ma’auratan. Duk lokacin da aka samu matsala tsakanin mata da miji, idan lamarin ya yi tsamari, macen takan tafi gidansu ko kuma wurin wani daga cikin dangin iyayenta a matsayin yaji. Takan yi haka ne da manufar kai kukanta dangane da wani abu da aka yi mata wanda bai dace ba. Idan haka ta auku, akwai wasu tanade-tanade da al’ada ta tsara waɗanda akan yi su domin daidaita tsakaninsu. Wasu daga cikin hanyoyin da Maguzawa sukan bi idan haka ta faru sun haɗa da: Iyayen miji ko shi kansa ko kuma abokansa sukan bi matar gidan iyayenta su bayar da haƙuri saboda a rarrashe ta domin ta dawo. Har wa yau, sukan sanar da iyaye domin sanin halin da ake ciki, saboda a fara laluben hanyoyin sulhunta su tare da ba ta haƙuri. Maganganun da suka shafi rarrashi (lallashi) da bayar da haƙuri su ne suka fi shahara a lokacin da aka je wurin biko a al’adar Maguzawa. Waɗanda suka je bikon sukan kira miji su ja hankalinsa ta hanyar ja masa kunne, saboda kauce wa maimaituwar abin da ya faru. Sakamakon cewa, a al’adar Maguzawa, kasawa ce magabatan miji a riƙa yawan ganinsu suna zuwa bikon matar ɗansu. A ɓangare ɗaya kuma, al’adar Maguzawa ta aminta da miji ya kai ƙorafin matarsa idan tana abin da bai dace ba. Hasali ma, magabata sukan yi godiya tare da alƙawarin jan kunnenta ga muhimmancin da ke tattare ga bin dokokin mijinta. Baya ga haka, suna ganin rashin hikima ga mace ta rayu ba a gidan mijinta ba, sai dai idan wani yanayi na mutuwa ya gitta. Wannan dalili ya sa wasu iyayen idan suka ga jan kunnen bai ba da mafita ba, sukan haɗa da magani domin a gudu tare da tsira tare.

Shawartar Bazawara Game da Wanda Take So ta Aura

Bazawara ita ce matar da ta yi aure suka rabu da mijin da ta aura, walau ta hanyar saki ko kuma mutuwa. Idan mace ta fara zawarci, takan sami manema da dama waɗanda suke nuna sha’awarsu ga aurenta. A lokacin da bazawara take ƙoƙarin tsayar da wanda take so, a tsarin aladar Maguzawa ba a tursasa ta dangane da wanda ya kamata ta aura. Sukan dai ba ta shawara, saboda yaƙinin da suke da shi na cewa, tana da masaniyar yanayin zama da miji. Bazawara tana da damar sauya raayi a kan namijin da ta yi wa alƙawarin aure idan ta ji ba ta son sa, sai dai daga baya a zo a sasanta a mayar masa da a bin da ya kashe.

Kulawa da Macen da Take Takaba

Bayan tabbatar da mutuwar mamaci, babu abin da ke gaba idan an binne shi sai shiga takaba da matansa za su yi. Maguzawa suna fara takaba ne bayan kwanaki bakwai da rasuwar mijinsu, wato ranar da ake ƙare zaman makoki. Lamarin kwanakin da mace take ɗauka na zaman takaba ya danganta daga yanayin al’adar wuri. Misali, Ibrahim (1982: 177) ya nuna akwai Maguzawan da suke shafe watanni bakwai da kwana goma a matsayin kwanakin zaman takaba. Su kuwa Maguzawan Kainafara da Ƙwanƙi da da kuma Lezumawan Babban Kada duka suna shafe watannin biyar suna zaman takaba. Saɓanin Maguzawan Gidan Bakwai, tasu al’adar ta zaman takaba tana kai adadin watanni shida. Darussan da ke cikin zaman takabar Maguzawa su ne, macen da take zaman takaba tana samun kulawa matuƙa, saboda haka takan kasance a cikin gida tsawon waɗannan watanni ba tare da zuwa ko’ina ba. Akan ɗauki matakan lura da ita saboda kiyaye kimarta da ta mijinta da ya mutu. Sakamakon ba sa ƙaunar ta aikata wani abin kunya da zai zubar da kimarta da ta mijinta da ya mutu da kuma ta zuriyarsu. Hakan ya sa hatta aikace-aikace ma ɗauke mata ake yi.

A ɓangare ɗaya kuma, Maguzawa sun lura da maganar Hausawa da take cewa: “Da abokin daka akan sha gari.” Wannan dalili ya sa a al’adar Maguzawan Kaibaki da ke Fago maza suke wa matansu da suka rasu takaba. Yanayin takabar maza ya bambanta da yadda mata suke gudanarwa. Idan namiji ya tsinci kansa a yanayin mutuwar matarsa, yakan shiga takaba ne bayan kwanaki bakwai da mutuwar matar. Takabar namiji ba ta wuce ta juya rigarsa ya sanya ta baibai na tsawon kwanaki uku ba. A cikin kwanakin da yake takabar, ba a so ya gudanar da wasu aikace-aikace da suka danganci zuwa gona da makamantansu. Duka wannan al’ada, tana tabbatar da kimar da mace take da shi a wurin Maguzawa.

Auren Matar Mamaci

Ga al’adar rayuwa, bayan an yi aure an haihu babu wani mataki da ke gaba kuma sai na mutuwa. Duk da yake lamarin mutuwa ba daɗi ne da shi ba, amma kasancewarta abin da babu makawa sai ya riski mai rai, shi ne ya sanya ta zama mataki na ƙarshe a rayuwarsa. Yana daga cikin aladun Maguzawa, duk macen da mijinta ya mutu tana da damar yin wani auren musamman idan tana da sauran shekarun da wani zai iya aurenta. Idan kuma ta tsufa da yawa, takan dangana ga yanayin da ta tsinci kanta ta ƙarasa rayuwarta ba tare da sake wani sabon aure ba. A tsarin zamantakewar Maguzawa, alhakin aurar da wadda mijinta ya mutu ya rataya a kan dangin mijinta ne ba iyayenta ba. Dangin mijinta da yayanta (idan akwai manya a cikinsu) sukan yi tsayin daka wajen nemo mata wanda ya dace da ita. Abin da yake nuna kimar mace a wannan al’ada tasu shi ne, dangin mijinta da ya rasu za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da cewa, mijin da suka aura mata zai kiyaye darajarta kamar yadda ɗan’uwansu ya yi mata. Don haka ba za su yarda su aurar da ita a hannun wanda zai tozartar da ita ba. Sakamakon suna tunanin cewa, tozartar da ita tamkar cin amanar ɗan’uwansu ko mahaifinsu ne da ya mutu. Tabbatar da hakan ya sanya tun daga nema zuwa ɗaurin aure da ɗaukar ta zuwa ɗakin sabon angonta, a ƙofar gidan mijinta da ya mutu ake gudanar da waɗannan al’adu.

Bugu da ƙari, a duk lokacin da macen da mijinta ya mutu ta fita daga takaba, akan gudanar da buki, inda yanuwa da abokan arzuki sukan zo su taya ta murna. Sukan gayyaci makaɗi ya zo ya kwana yana buga gangarsa, mahalarta taron kuma suna tiƙar rawa. Mutanen da suka shaidi bukin suna haɗa rawar da suke gudanarwa tare da kewaya wutar da suka hura zuwa wayewar gari. Su kuma matan mamacin kowace takan ɗaura farin saƙi ta yi ƙunshi da lalle a ƙafarta. Idan gari ya waye kafin taron bukin ya watse, kowace daga cikinsu takan saki ɗan akuya da kuma zakaran da suka zo da shi a cikin mazan da suke rawa. Su kuma za su yi ta wawar su, kowa ya yagi abin da ya yaga, waɗanda suke da ƙarfi ma sukan iya ɗauke su gaba ɗaya. An nuna cewa, wasu matan sukan ɗauko zakaran da suka zo da shi su danƙa shi ga wanda suke so ya aure su. Idan haka ta faru, nan take sukan tafi gidansa shi ke nan ta zama matarsa. Wannan ya tabbatar da kimar mace a wurin Maguzawa. Ba don kimar da mace take da shi ba, ba za su zo su kwana suna rawa, sannan a ƙare da wasoson zakara guda ba. Domin zakara guda bai fi ƙarfin arzikinsu ya yi ba.

Sakamakon Bincike

 Wasu daga cikin sakamakon da wannan bincike ya iya tsinkayowa sun haɗa da:

              i.            Sanin kimar mace tare da tabbatar da ita a aikace da Maguzawa sukan yi, ya taimaka ta fuskar ɗorewar tarbiyarsu da kyautatuwar zumunci da tausaya wa junansu tare da haɗin kai a tsakaninsu.

            ii.            Bugu da ƙari, wannan nazari ya gano cewa, kimar da mace take da ita a al’adun Maguzawa ita ce ta yi tasiri a ɗabi’un wasu daga cikin Hausawan da suka karɓi addinin Musulunci.


         iii.            Maguzawa mutane ne da suka ɗauki mata a matsayin iyaye, saboda haka al’adarsu ta ba su wata daraja ta musamman.

         iv.            Al’adun Maguzawa ba su tauye wa mata yanayin walwala ba. Sun ba su dama daidai da kimar da al’ada ta ba su.

            v.            Watsi da wasu al’adun Maguzawa waɗanda suka ƙunshi kiyaye haƙƙoƙin ɗan’adam a wannan lokaci, shi ya haifar da kallon da ake wa wasu Hausawa na rashin sanin kimar mata a zamantakewarsu.

Kammalawa

Matsayin da mata suke da shi na kasancewarsu iyaye ga kowa, ba ƙaramar kima ya tabbatar musu ba a cikin alumma. Wannan dalili ya sa matakan rayuwa na alada ba su wofintar da su sun zama koma baya ba. Takardar ta mayar da hankali wajen fito da kimar da mata suke da ita a ma’aunin al’adun Maguzawa na matakan rayuwa. Binciken ya samu nasarar leƙo wasu aladu da suke tabbatar da darajar da mata suke da ita a wasu daga cikin aladun Maguzawa na aure da haihuwa da kuma mutuwa. Duk da cewa, wasu Hausawan da suka karɓi addinin Musulunci suna bambanta kansu da Maguzawa, amma hakan bai hana su amfana da nagartattun ɗabi’unsu na darajanta ɗan’adam ba. Domin ko ba komai, tarsashin waɗanan ɗabi’u sun yi tasiri a rayuwar Hausawa ta yadda lamarinsu ya zama tamkar abin da masu magana suke cewa: “An tashi daga kan faƙo, an koma kan daɓe.”

Manazarta

1.      Abdullahi, I.S.S. (2008). “Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Kudin Digiri na Uku (Ph.D). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

2.      Abdullahi, I.S.S. (2012). “Zawarci da Auren Bazawara a Maguzance.” Cikin Amfani, A. H. da Wasu (Editoci). Champion of Hausa Cikin Hausa: A Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad, Pp. 473-479. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

3.      Abdullahi, I.S.S. (2021). “Takabar Maguazawa.” Cikin Yakasai, S. A. da Wasu (Editoci). A Great Scholar & Linguist: A Festschrift in Honour of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy, Pp. 740-748. Kaduna: Amal Printing.

4.      Abraham, R. C. (1977). Dictionary of the Hausa Language. London: Hodder & Stoughton Educational Ltd.

5.      Bunza, A. M. (2013). “Littafin Ruwan Bagaja a Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe.” Cikin Bunza, A. M. da Noofal, M. A. (Editoci), Ruwan Bagaja in Perspectives, Pp. 425-447. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

6.      Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

7.      Garba, Z. (2016). Nazari a kan Sababbin Sana’o’in Mata Hausawa a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

8.      Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri na Biyu (M.A). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

9.      Ibrahim, M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci. Cyclostyled Education. Zaria: Hausa Publication Centre.

10.  Ingawa, Z. S. (1984). Magungunan Hausa Don Mata:Nazari kan Matan Hausawa da Ire-iren Buƙatunsu na Magunguna. Kundin Digiri na Ɗaya (B.A). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

11.  Newman, P. & Newman, R. (2020). Hausa Dictionary: English-Hausa/Hausa-English. Kano:Bayero University Press.

12.  Nuhu, A. (2020). “Zamani Abokin Tafiya: Wasu Al’adun Maguzawan Ƙasar Katsina a Ƙarni na 21. Kudin Digiri na Uku (Ph.D) Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

13.  Nuhu, A. (2020). “Kyawawan Al’adu da Ɗabiu a Matsayin Hanyar Samar da Ingantacciyar Alumma: Waiwaye Daga Wasu Waƙoƙin Hausa na Zamani. Cikin Bunza, M.U. da Wasu (Editoci) Nigeria in Search of Stability: The Relevence of History, Language, and Religious, Pp. 388-396. Kaduna: Pyla-Mark Services Limited.

14.  Rambo, R. A. (2007). “Nazari a kan Wasu Keɓaɓɓun Al’adun Auren Hausawa da na Dakarkari.” Kudin Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

15.  Rambo, R. A. (2021). “Falsafar Yaji da Biko: Nazari a kan Zamantakewar Auren Hausawa da na Dakarkari.” Cikin Yakasai, S. A. da Wasu (Editoci). A Great Scholar & Linguist: A Festschrift in Honour of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy, Pp. 694-703. Kaduna: Amal Printing.

16.  Safana, Y. B. (2001). “Maguzawan Lezumawan Babban Kada Gundumar Safana (Jihar Katsina). Kundin Digiri na Ɗaya (B.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jamiar Usmanu Danfodiyo.

17.  Sallau, I. A. (1981). “Taƙaitaccen Nazari Kan Maguzawa da Aladunsu. Zariya: Kundin Digiri na Ɗaya (B.A). Sashen Koyar da Harsuna da Aladun Afirka, Jamiar Ahmadu Bello.

18.  Sani, S. M. (1988). “Kainafara Arnan Birchi.” Kundin Digiri na Ɗaya (B.A). Zariya: Sashen Koyar da Harsuna da Aladun Afirka, Jamiar Ahmadu Bello.

Kimar Mace a Ma’aunin Matakan Rayuwar Maguzawa

Post a Comment

0 Comments