Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Wanda Ya Rufa Asirin Wani, Allah Zai Rufa Nashi!

Daga
Abbas Musa Jega

A cikin ƙasar Jega, wani gari wanda ya kasance matattara ta ilimi da kasuwanci, aka yi wani malami mai koyar da mutane ilimin addini da kuma na rayuwa. A wata rana wannan malami kamar yadda ya saba ya shigo zauren da yake karatu ya samu waje ya yi zaman tamataila kamar yadda aka sani ga al'adar malamai, shi dai wannan malami, daccijo ne mai yawan hikima da basira da ilimi. Bugu da ƙari wannan malami ya kasance ɗan kasuwa,  kuma mai jagora wajen ba ɗalibai ilmi da tarbiyya da kuma sanin makamar rayuwa, a kowane lokaci malamin yakan zuba karatu ga ɗalibai tare da sharhi a lokacin da buƙatar haka ta taso. Wata rana ana tsakiyar ɗaukar karatu kamar yadda aka al'adanta, wani mutum baƙo a majalisin ya shigo, bayan sallama, sai ya samu waje ya zauna ba tare da ya takura wani ba, ya yi zuru yana sauraren karatun da ake yi wa sauran ɗalibai duk da cewa ba wata alama irin ta ɗalibi a tattare da wannan baƙo, hasalima ya fi kama da babban mutum wanda budurwar wawa ta juyawa baya. Sai dai wani abin mamaki a tare da wannan baƙo shi ne akwai wata kwalba a tare da shi wadda ke cike da wasu ruwa wadda ya yi wa riƙon alewar yara. Bayan malamin ya kammala karatu ga ɗaliban da ke nan kamar yadda ya saba, ya juya zuwa ga wannan baƙo cikin sakin fuska ya jefa tambaya ga wannan baƙon cewa shin kana da buƙata ne da kake so a biya maka, ko ka zo fawata ne? Cikin ƙarfin hali wannan baƙo ya ce, ba ko ɗaya daga cikin abin da ka ambata, ina son dai ka sani cewa ni ɗan kasuwa ne, na ji labari irin na ilimi da kyawawan halaye da hikima da ke gare ka, shi ne na zo, idan ka yarda ina son zan yi kasuwanci da kai, zan sayar maka da wasu ruwa na musamman da ke cikin wannan kwalba, ka sani ya kai wannan malami na yi rantsuwa ga wanda ya daidaita a kan al'arshi, irin daidaita wadda ta dace da shi cewa ba zan sayar da wannan kwalbar ba sai ga wanda ya san ƙimar wannan ruwan da ke ciki. Ka sani, a ɗan zaman da na yi da kuma labarin da na ji game da kai, ba wani kokonto kai ne mafi cancanta da ka sayi wannan ruwa, kuma sun fi dacewa da kai.
Cikin fara'a malamin ya ce miƙo min ita na gani? Karɓar wannan kwalba ke da wuya malamin ya jujjuya ta a kan hannunsa, sannan ya yi jim haka, irin na mamakin yadda duniya take da hali irin na ƙwallon mangwaro, daga bisani, ya yi murmushi sannan ya dubi wannan baƙo ya ce masa nawa ne kuɗin wannan ruwan? Ba tare da wata fargaba ba, baƙo ya ce kuɗin wannan ruwan shi ne dubu ɗari, cikin ƙarfafawa malam mai hikima ya ce wa baƙo lallai waɗannan ruwan idan aka yi la'akari da ƙima da darajar da suke da ita,  kamata ya yi ma sukai dubu ɗari da hamsin, sai dai wannan baƙon ya nace a kan dubu ɗari ma sun wadatar babu ragi ba ƙari. Ba tare da wani jan lokaci ba, daccijon malami ya ce wa ɗansa, shiga wajen mahaifiyarka ka miƙa mata wannan ruwan, kana ka karɓo min dubu ɗari, yaro ya shiga ya karɓo kuɗin kamar yadda aka umurce shi. Yaro ya miƙa wa baƙo kuɗi, ana miƙa kuɗin ga baƙo ya buga tufafinsa ya juya cikin farin ciki kamar mai azumi a lokacin buɗa-baki, ya bar mutane suna ta mamakin malaminsu mai hikima da basira da yadda ya iya sayen waɗannan ruwa da kuɗi maƙudai haka! 
Dare ya raba, kowa ya kama waje domin ya ɓoye tsufa da asirinsa, amma wannan yaron na malami ya gaza haƙuri ya iske mahaifiyarsa ya karɓi wannan kwalba ya buɗe domin ya ɗebe kokonton da ya hana shi barci fiye da rabin dare game da sha'anin ruwa na musamman, bayan ya buɗe kuma ya haƙiƙance lallai an yaudari mai hikima yau, sai ya tashi ya nufi ɗakin mahaifin nasa jiki a sanyaye da tarin tambayoyi fal a tare da shi, amma ladabi da tarbiyyar da ya samu sun fadaƙar da shi cewa, yanzu kam ko babansa bai kwanta ba, to lallai yana buƙatar kaɗaita kasancewar dare ya raba. Yaro ya je ya kwanta cikin kasala kamar wanda ya yi kwanaki bai runtsa ba, amma duk da haka Alla-allah yake garin Allah ya waye kamar dai ya tashi ya kira assalatu tsabar ɗoki! Bayan garin Allah ya waye, masu sallah sun yi, waɗansu kuma sun wanke fuska, yaro ya iske mahaifinsa a cikin ɗaki, cikin ladabi da biyayya ya gayar da baban nasa, sannan ya ce Baba lallai jiya an saɓa lamba, baƙo ya wuce da ɗan masu gida, cikin mamaki baban ke ce masa yau kuma da Ɗan'anace ka tuna ke nan?
Ba wani wani ɓoye-ɓoye yaro ya ce, Baba yau fa ranar wanka ce, a taƙaice dai wancan baƙon yaudara ce kawai ya zuba ta amfani da daɗin baki da kuma shiga mai kyau da yi, wannan ruwan da ka saya gare shi, ruwa ne dai kamar sauran ruwan da ke akwai a kowane gida ko gari! Ba tare da wata razana ba, cikin murmushi daccijon malami ya ce wa ɗansa, mayar da wuƙar ai lokacin yanka bai yi ba, ka sani ya kai ɗana, ka raba kana ta nazari, kana ka ƙure kusan basirar da ke gare ka, sannan ka gane ruwa ne wanda aka saba amfani da su yau da kullum, amma ni kuma a tun lokacin da wannan baƙon ya shigo, na yi amfani da tawa basira kuma na gane mutum ne babba wanda duniya ta dena yayi, kuma tun lokacin da na karɓi kwalbar, na gane ko ruwan mene ne, amma ka sani wannan mutumin yana ɗauke da ruwan fuska da ƙimarsa ne a cikin wannan kwalba, amma girma da matsayin da ya taka a dauri, su suka hana masa ya zubar da wannan ruwan a gaban jama'a saboda gudun ƙasƙanci da kunyata, ka sani ba yaudarata ya yi ba, kawai na fahimci halin da yake ciki ne, kuma kai kanka ya kamata ka fahimci wani abu tun farko, saboda na nemi na sayi waɗannan ruwan sama da kuɗin da ya ambata, amma sai ya dage a kan yadda ya ce a farko, sai na fahimci mai gaskiya ne, buƙatar da yake da ita a yau ta kuɗin da ya ambata ne, saboda haka godiya ya kamata ka yi, ta yadda Allah ya taimaki mahaifinka ana iske shi da buƙatu irin haka, kuma yana fahimtar buƙatu na gaskiya kuma yana ƙoƙarin tsare mutunci da ƙimar mutane, domin da wani ne sai ya tozarta shi a gaban jama'a kafin ya tafi! Ka sani da zan yi rantsuwa da Allah, wannan abin da na ba shi kaɗan ne idan aka kwatanta da abin da Allah zai maye min da shi a duniya da kuma gobe ƙiyama. Sannan ka sani duk wanda ya rufa asirin wani, Allah zai rufa nashi.

Abbas Musa Jega
17021447H
11082025M.
Duk Wanda Ya Rufa Asirin Wani, Allah Zai Rufa Nashi!

Post a Comment

0 Comments