Article Citation: Bunza, D.B. (2025). Nazari Da Sharhin Waƙar Begen Annabi (S.A.W.) Ta Kabiru Yahaya Classic. Zauren Waƙa, 4(2), 16-33. www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.003.
NAZARI DA SHARHIN WAƘAR BEGEN ANNABI
(S.A.W.) TA KABIRU YAHAYA CLASSIC
Daga
Dano Balarabe Bunza (PhD)
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Email: danobunza@gmail.com
Phone No: 07035141980
Tsakure
Sunan maƙalar ‘Nazari da Sharhin Waƙar Begen Annabi
(S.A.W.) ta Kabiru Yahaya Classic. A cikin maƙalar an yi sharhin
babba da ƙananan saƙonni da waƙar ke ɗauke da su da suka haɗa da yabon Annabi (S.A.W.) da ƙanana
irin yabo kan asali da kyauta da jaruntaka da sauransu. Haka kuma an fito da
salailai daban-daban da aka tsinta a cikin waƙar gwargwadon fahimta.
Daga cikin salailan da aka kawo akwai salon share fage da na buɗe waƙa da
salon addu’a da na kamancen fifiko tare da na kasawa da aron kalmomi da
tsakuren nassi da salon amshi domin waƙar mai amshi ce da
kuma salon rufewa. A taƙaice abubuwan da maƙalar ta ƙunsa ke
nan da bayanai da misalan da suka biyo na kowane abu da aka ambata a cikin maƙalar.
1.0 Gabatarwa
Waƙoƙin begen Annabi
Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi muhimmai ne, kuma duniyar
ilimi ta san da su musamman a ɓangaren addinin
Musulunci. Waƙoƙi ne da suka samo
asali daga addinin Islama. Ana kiran masu rubuta waƙoƙin tare da rera su
madihai (jam’i) da ko madihu (tilo). Ishiriniyar Alfazazi na ɗaya daga cikin manyan waƙoƙin bege da aka
sani tun daɗewa har kuma yau
ana ambaton ta daga cikin waƙoƙin yabon Manzon
Allah (S.A.W). Haka kuma, akwai hamziyya da alburda da sauransu daga masu
rubuta waƙoƙin bege
daban-daban. Muhimmancin waƙoƙin da matsayinsu a
cikin addini ya sanya ana nazarin su a makarantun ilimin addinin Islama (na
muhammadiyya), har da na boko. Dpmin tabbatar da haka an sami Abdullahi Bayero
Yahya ya yi rubutu a kan waƙoƙin bege a cikin
kundin digirinsa na uku. An samu wasu daga cikin malaman addini sun rubuta waƙoƙin begen Annabi
Muhammadu (S.A.W.) a ƙarnoni daban-daban.
Haka an sami yawaitar madihai a ƙarni na ishirin da
na ishirin da ɗaya fiye da sauran
ƙarnoni da suka
gabace su. An samu wasu malamai kamar Malam Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu
wanda ya rubuta waƙoƙin yabon Annabi
Muhammadu (S.A.W.) da sauransu da dama. A ƙarnin da muke ciki ma an sami shahararrun marubuta irin
Fadar Bege da Kabiru Classic, sun rubuta tare da rera waƙoƙin begen Annabi
(S.A.W.). A cikin wannan maƙalar za a nazarci
waƙar Kabiru Classic
ta farko da ya yi a kan begen Annabi Muhammadu (S.A.W.) domin a yi sharhin ta
bayan an yi nazarin ta. Waƙa ce mai tare da
amshi, kuma Kabiru Classic ne jagora inda Naja’atu ce ke yi masa karɓi. Za a dubi jigo (babba da ƙanana) da kuma
salailan da mawaƙin ya yi amfani da
su a cikin waƙarsa. Za a yi
amfani da misalai a kowane batu da aka kawo domin tabbatar da abin da aka faɗa dahir ne ba ƙaƙawa aka yi ba daga
abubuwan da mai waƙar ya faɗa.
2.0 Dabarun
Bincike
A cikin kowane
bincike da aka yi ko ake da gurin aiwatarwa akwai dabarun da aka yi amfani da su
ko kuma za a yi amfani da su domin gudanar da wannan bincike. Saboda haka
wannan binciken da za a gudanar na da nasa dabarun binciken da za a yi amfani
da su domin cimma nasarar aiwatar da shi. Daga cikin dabarun da aka yi amfani
da su domin gudanar da wannan bincike akwai samun kaset na bidiyon wannan waƙar domin kallo da
sauraron waƙar. Za a kuma
rubuta waƙar a takarda domin
hakan zai taimaka a yi nazarin kafin a kai ga yin sharhin abubuwan da ke ciki.
Bayan haka kuma, za a yi hira da masana waƙa gwargwadon hali domin neman bayanan da suka shafi waƙar da ake aiki
kanta. Ba waɗannan kaɗai ba, za a shiga ɗakunan karatu
domin duba ayyukan da aka yi masu alaƙa da wanda ake yi. Waɗannan su ne kaɗan daga cikin dabarun binciken da za a yi la’akari da su a
wajen yin nazari da sharhin wannan waƙar bege ta Kabiru Classic.
3.0 Dalilan
Bincike
Bayan dabarun
binciken da aka kawo a sama akwai dalili ko dalilan da suka haddasa aiwatar da
wannan bincikeda ake gudanarwa. Daga cikinsu akwai buƙatar fitowa da
bambancin waƙoƙin da Kabiru ya daɗe yana yi da kuma waƙoƙin bege da ya faɗi cewa ya koma gare su kuma ba zai koma ga waɗanda ya fara yi ba, tare da jin dalilin faɗar hakan. Haka kuma akwai buƙatar jin dalilin
da ya faɗa da bakinsa na daina
yi wa kowane mutum waƙa da abin da ya
sanya shi komawa ga waƙoƙin yabon Annabi
Muhammadu (S.A.W.). Haka kuma akwai buƙatar taskace abubuwan da mawaƙin ya faɗa a cikin waƙar domin adana shi
saboda wata rana a ɗauki a duba domin
a ga tarihin abubuwan da suka gudana gabani. Haka kuma ana son jama’a su san da
cewa taro aka yi na musamman domin a ƙaddamar da waƙar begen da Kabiru
ya rubuta tare da rerawa. Haka kuma, domin a san Kabiru ya cika sha’iri domin a
ka ya karanta waƙar ba tare da
duban komai a takarda ba.
4.0 Muhimmancin
Bincike
Wannan bincike na
da muhimmancin gaske ga manazarta waƙa da masu ra’ayin waƙa ta fuskar da aikin zai taimaki musu son gudanar da irinsa
na wasu mawaƙa na daban ba
Kabir Classic kaɗai ba. Binciken
zai zama ja-makahi ga duk mai son gudanar da irinsa. A taƙaice aikin zai
zama na gaba idon na baya musamman ga ɗalibai masu koyon
sanin makamar aiki irin wannan. Babu shakka aikin zai taka muhimmiyar rawa
wajen taimaka wa masu koyon yadda ake sharhin waƙa irin wannan duk
lokacin da buƙatar yin hakan ta taso.
Wani muhimmancin da wannan aiki ke ɗauke da shi shi
ne, kasancewarsa taskar tarihi dangane da komawar Kabiru Classic a ɓangaren waƙoƙin begen Annabi
Muhammadu (S.A.W.) da dalilin barin yi wa kowa waƙa. Waɗannan su ne kaɗan daga cikin
muhimmancin wannan maƙala da aka gudanar
da bincike a kan waƙar begen Annabi
Muhammadu (S.A.W.).
5.0 Taƙaitaccen Tarihin Kabiru Classic
An haifi Kabiru
Classic a garin Talata Mafara ta jihar Zamfara a unguwar Ɗangawo a shekarar
1978. Ya sami laƙabin Classic daga
wani ubangidansa mai suna Abdullahi Classic wanda ke da shagon bayar da hayan
kasasuwan bidiyo wanda ya sanya wa suna ‘Classic Video Center’ da Kabiru ke
kula da shi. Sannu a hankali sai sunan Classic ya bi Kabiru har ana yi masa laƙabi da shi, saboda
haka, sannu a hankali mutane suka rinƙa cewa shagon Kabiru Classic. Sunan mahaifinsa Malam Yahaya,
sunan mahaifiyarsa kuwa ana kiran ta Safiya. Kakanninsa na gefen mahaifinsa
mutanen Talata Mafara ne. Mahaifinsa ya rasu a shekarar 1994 a lokacin da yake
karatu a makarantar sakandare. Mahaifiyarsa mutummiyar Maradun ce.
Ya tashi a hannun
yayan mahaifinsa mai suna Alƙali Muhammadu
wanda alƙalanci ne aikinsa.
Kabiru ya yi ƙuruciyarsa a garin
Talata Mafara da wasu garuruwan da yayan mahaifinsa ya yi aikin alƙalanci kamar garin
Sabon Birni da Yabo a jihar Sakkwato da kuma Jangebe da Ƙaura Namoda da
Kwatarkwashi da kuma Mada a jihar Zamfara. Kabiru bai tashi raggo ba, yana da ƙoƙarin neman zufan
na kansa domin har sana’ar sayar da rake da shayi ya yi. Ya yi ƙoƙarin neman kuɗi lokacin da yana sayar da rake har ya tara kuɗi ya sayi akuya. Sayen akuyar ya sanya Kabiru ya rinƙa sana’ar sayar da
awaki da tumaki. Haka kuma ya koyi aikin gina ta hanyar bin malaminsa mai suna
Malam Rabi’u har Allah ya ƙaddari ya iya
aikin ginin sumunti. Haka kuma Kabiru ya taso da sha’awar wasanni da barkwanci
da kuma waƙa. Ya tashi yana
da hazaƙa ƙwarai da gaske da
iya sarrafa harshe. Ya ƙware da rera waƙoƙin baka na makaɗa daban-daban da suka haɗa da Maidaji Sabon Birni da Musa Ɗanba’u da kuma Ɗanƙwairo da sauransu.
Kabiru ya haddace mafi yawan waƙoƙin waɗannan mawaƙa saboda hazaƙar da Allah ya ba
shi. Ya faɗi cewa duk wurin
da Ɗanba’u zai yi hira
a Sakkwato yakan je domin ra’ayin waƙoƙinsa. Ya ce yana
gaisawa da Ɗanba’u ta waya
kafin ya rasu. A lokacin tashen watan azumi kuwa, shi ke jagorantar abokansa
wajen shirya waƙoƙin tashe.
Kabiru ya yi
karatun addini ƙarƙashin malamai da
dama, kuma ya fara karatun a garin Jangebe tun yana ɗan shekara biyar. Bayan ya taɓa karatu daga malumansa sai aka ɗauke shi aka kai shi wajen wani malami mai suna Malam na
Barikin Daji. Yana cikin karatun sai aka yi wa mahaifinsa canjin wurin aiki
daga Jangebe zuwa Sabon Birni. Daga can kuma sai Talata Mafara. A nan kuma sai
ya ci gaba da karatu a makarantar Malam Rabi’u, kuma a nan ne ya sauke Ƙur’ani. Bayan haka
sai ya ci gaba da karatun littattafai a wurin Malam Mukhtar. Ya karanci Ƙawa’idi da Ahlari
da Iziyya da Risala da sauransu.
Ya yi karatun
firamare a makarantar Abubakar Tunau Model Primary School a garin Talata Mafara
daga 1984 zuwa1990. Dagan nan ya tafi makarantar sakandaren Sheik Abubakar
Mahmud Gummi Memorial Colege Sokoto daga 1990 zuwa 1996. Bayan ya ƙare sakandare ya
tafi makarantar kimiyya da fasaha ta Talata Mafara, wato Abdu Gusau Polytechnic
kuma ya yi satifiket a fannin mulki.
Kabiru ya fara waƙa tun lokacin da
suke zaune a garin Jangebe, kuma waƙarsa ta farko wata rijiya ce ya fara yi wa. Dalilin yi wa
rijiyar waƙa shi ne muzurun
da yake kiwo ya faɗa cikin rijiya har
ya mutu. Haka kuma ya yi wata waƙa lokacin da yake
makaranta da aka shirya wata wasan kwaikwayo.
Ba wannan kaɗai ba, Kabiru Classic ya sami nasarar zama ɗan majalisar tarayya a shekarar 2019 a matsayin mai waƙiltar ƙaramar hukumar
Anka da Talata Mafara. Ana da labarin yana da mata uku da ‘ya’ya tara a lokacin
da aka yi digiri na biyu ta hanyartarken waƙoƙinsa na siyasa.
Dagan an kuma, tarihi ya tsaya saboda rashin samun nasarar yin hira da shi.Wannan
bai rasa alaƙa da matsayin da
yake a kai saboda yawan uzurran da ke gabansa.
6.0 Nazari Da Sharhin Waƙar Begen Annabi
(S.A.W.) Ta Kabiru Yahaya Classic
Kafin a shiga cikin maƙalar sosai ya dace a ɗan ƙyallaro ma’anar fitillun kalmomin da suka fito a cikin
taken maƙalar. Kalmomin da suka fito da ke matsayin fitillu a
cikin taken maƙalar sun haɗa da nazari da sharhi da kuma bege, ba da waƙa ba domin an sha gani a cikin rubuce-rubucen masana da
manazarta. Ba dogon bayani za a yi a kansu ba sai dai, za a sami ma’anoni kamar
biyu daga littattafan ƙamus biyu aƙalla. Za a yi la’akari da ƙamusun Bargery (1934) da kuma ƙamusun Jami’ar Bayero (2006) na Kano.
Bargery cewa ya yi, nazari na nufin reading silently (pg. 818). Ma’anarsa
ita ce karatu a natse ko karanta abu cikin natsuwa (Fassarar mai bincike).
Dangane da ma’anar sharhi kuma, cewa ya yi, yana nufin commentary (pg. 930). Ma’anar
kalmar ita ce ƙarin bayani (Fassarar mai bincike).
A cikin Ƙamusun Jami’ar Bayero na Kano kuwa cewa suka yi, nazari
na nufin duba abu da yin tsokaci a kansa (shafi na 358). Shi kuma sharhi na nufin
rubutaccen bayani don ƙara fahimtar abu (shafi na 409).
Ga sharhin waƙar begen Annabi
Muhammadu (S.A.W.) ta Kabiru Classic kamar haka:
6.1 Jigon Waƙar
Masana da manazarta waƙoƙin Hausa sun bayyana ma’anar jigo a cikin rubuce-rubucen
da suka yi wanda ba sai an kawo dukkan abin da suka faɗa ba a nan. A taƙaice, sun bayyana cewa jigo na nufin muhimmi ko babban saƙon da rubutacciyar waƙa ke ɗauke da shi. Dangane da haka bayan nazarin da aka yi na
waƙar Kabiru Classic ta bege an gano cewa babban saƙon da take ɗauke da shi, shi ne yabon Manzon Allah Annabi Muhammadu
(S.A.W.). Mawaƙin da kansa ya faɗa da bakinsa a wasu baitocinsa inda ya ce:
K: Na tuba da wasa kowa maras tabbas da zato
da kokwanto,
Ga gaske da gaskiya Annabin rahama ceto da mai ceto,
Shi tsuntsaye suke wa yabo mai daɗi in suna ƙoto,
Balle ni ɗan Adam ka ga ba ya
yiwuwa in kulle bakina.
Kabiru Classic ya jima yana yi wa jama’a waƙoƙin yabo daban-daban, amma daga baya tunaninsa ya ba shi
cewa duk waƙoƙin da yake yi wa mutane yana yabon su ba su kai waƙar da zai yi wa Annabin rahama ba, domin yi masa waƙa ana yabon sa/begen sa lada ake samu ba zunubi ba. Su
kuma waƙoƙin da ya sha yi wa jama’a wani lokaci har laifi yake
aikatawa inda mai yiwuwa ne ya yi ƙari a ciki. Sanin akwai laifukan da ya aikata a cikin waƙoƙin da ya yi wa wasu mutane ya sanya shi fara baitin da ke
sama da gabatar da tubarsa ga Allah a kan waƙoƙin da ya yi wa wasu mutane. Ya fahimci akwai matsala a
cikin waƙoƙin day a gabatar na wasu mutane domin babu tabbas wanda
ka yaba ya yi maka abin da kake tsammani sai dai koyaushe kana cikin tunanin ko
a ba ka ko a hana ka. A layi na biyu sai ya bayyana cewa a yi waƙa a yabi/ a yi begen Annabi (S.A.W.) shi ne aikin
gaskiya, domin Annabi ma mai gaskiya ne kuma abin gaskatawa, ba irin sauran
mutane ba da ke aikata son rai a cikin ayyukan da suke yi ba. A layi na gaba
kuma Kabiru ya bayyana cewa tsuntsaye ma na yabon Annabi a lokacin da suke cin
abinci (ƙoto), ina gare shi (mutum) da Allah ya ɗaukaka a kan kowace
halitta da ke a bayan ƙasa? A nan ya ƙara da cew a ba ya
yiwuwa ya kulle (rufe) bakinsa ba tare da ya yabi manzo ba. A cikin wannan
baiti za a fahimci Kabiru ya tuba da yi wa kowa waƙa domin babu tabbas ga samun biyan buƙatar da yake da a rayuwa, amma yabon Annabi aikin ibada
ne kuma ana samun lada idan an yi shi. Ba lada kaɗai ake samu ba, har da
la’ada domin da mutum zai ga irin kuɗin da aka yi wa Kabiru kari da su zai tabbatar da bayan
lada akwai la’ada. A nan za a fahimci cewa Kabiru Classic ya tuba tare da daina
yi wa kowa waƙa, sannan ya koma zuwa ga waƙoƙin yabon Annabin rahama domin ya tsira da mutuncinsa a
duniya da lahira. Domin tabbatar da komawarsa ga begen Annabi ga abin da ya faɗa a wani baiti:
K: Ni ban ga zama ba Alhaji Kabiru idan ban gaida Manzon
ba,
In ratsa garin masoyi ma’aiki domin godiya babba,
Don shi aka wa yabo babu ƙarya kuma ba a kauce hanya ba,
In ba Allah ba komai
ka ce wa Nabiyullahi ba ɓarna.
A cikin baitin Kabiru ya nuna shi kam bai ga zama ba idan
bai yi begen Annabi ba domin ya gano cewa yabon Annabi ya fi yabon kowane mutum
da ke ban ƙasa, kuma ba a ƙarya a cikin yabon
Annabi, sannan ba a saɓa wa Allah ba domin Allah da kansa ya yabi Annabi. Idan
aka tsaya a nan kaɗai za a fahimci cewa babbar manufar Kabiru a cikin wannan
waƙar ita ce yabon Annabi ta fuskar bege wanda ba haramun ba
ne, ga kuma ladan da ake samu a cikin yabon sa. Kabiru bai tsaya a nan kaɗai ba, sai da ya ƙara tabbatar wa duniya cewa ya daina yi wa kowa waƙa face Annabi ta fuskar bege. A taƙaice, Kabiru ya sauya ra’ayi daga yabon wasu mutane a
cikin waƙoƙinsa tare da komawa ga waƙoƙin yabon manzon Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W.). Ga abin
da Classic ya ƙara faɗa dangane da hakan:
K: …………………………………………………….,
Mafi jinƙai da tausai Muhaiminu ya Allahu Alfatta,
Daɗo hikima da ilmi na yin bege in ɗaɗa muryata,
Na bar waƙa ga kowa Muhammadu ɗai nika yi wa begena.
A wannan baiti Kabiru ya yi yabo da kirari ga Allah da
kuma roƙon Allah ya ƙaro masa hikima da ilimin yin begen Annabi Muhammadu
(S.A.W.) domin ya faɗa kowa ya ji. A layin ƙarshe kuwa nan ne ya ƙara fito da jigon waƙarsa inda ya ce ya
bar waƙa ga kowa Muhammadu ɗai yake yi wa begensa. Wannan na nufin ya canza sheƙa daga waƙoƙin yabon jama’a zuwa begen Annabi Muhammadu (S.A.W.).
6.2 Ƙananan Jigogin Waƙar
Bayan tantance bege/yabo a matsayin babban jigon waƙar Kabiru Classic, akwai wasu ƙananan saƙonni da ke matsayin ‘yan rakiyar babban jigo da za a duba
a cikin waƙar. An nazarci waƙar an gano tare da
tantance ƙananan jigoginta kamar haka:
6.2.1 Yabo ta Fuskar so da Ƙauna
So da ƙauna abubuwa ne da ke da alaƙa da juna. A wani wuri an bayyana ma’anar so da cewa yana
nufin buƙata ko ƙauna ko shauƙi ko niyya. Haka kuma an ƙara da cewa so na nufin buƙaci ko ƙaunaci ko ɗaura niyya (Ƙamusun Hausa: 397). Ita ma ƙauna an bayyana ma’anarta da cewa, tana nufin son wani
abu (Ƙamusun Hausa : 279). A tawa fahimta so da ƙauna abubuwa ne biyu da ke nufin abu ɗaya, sai dai ƙauna ta fi so tsanani ko nauyi, domin so na ƙarewa ya bar ƙauna bat a ko rage ba
balle ta ƙare. Kabiru Classic ya bijiro da ƙaramin jigon so da ƙauna a cikin waƙarsa ta begen Annabi Muhammadu (S.A.W.) a cikin wasu
baitocin waƙarsa kamar haka:
K: Farin duba abun Nana na A’isha ka shige raina,
Sabilin so da ƙaunar ka Annabi har
nis san ciwon kaina,
Muhammadu sahibul karamati kana da gije a ruhina,
Ganinai ne muradinmu
Jalla ka ƙara biyan muraduna.
A cikin baitin da ke sama Kabiru ya yabi Annabin rahama
ta fuskar son sa da ƙaunar sa inda ya ce wa Annabi farin duba mai nufin wanda
ganin sa alheri ne ga mai duban sa. Haka ya yi masa kirari da ce masa uban Nana
Faɗima kuma mijin Nana A’isha. Babu ɗiyar da ta kai Nana
Faɗima, ɗiyar manzon Allah daraja a duniya Ya ƙara da cewa saboda so da ƙaunar da yake yi wa manzo ya sa har ya san ciwon kansa. Haka
ya faɗa cewa Annabi ma’abucin karamomi ne kuma yana cikin ransa
saboda so da ƙaunar da yake yi masa. Ba wannan kaɗai ba, ya faɗa cewa kowa na son
ganin sa da kuma roƙon Allah ya biya masa wannan muradi na ganin Annabi
Muhammadu (S.A.W.) a ranar lahira. Idan aka yi la’akari da abubuwan da Kabiru
ya faɗa dangane da manzon tsira ba shakka akwai so da ƙauna a ciki. An sami wani wuri da ya ƙara faɗar cewa:
K: Sirrin ƙaunar ma’aiki a yau sai cigaba na ta samu na,
Da ma dai walidaina suna ta aza ni kan biyar sunna,
Son Annabi son iyalansa son makusantansa ja’iz na,
Waƙa in ba ta Manzo ba ce ni kan ban sanya bakina.
Kabiru ya faɗa cewa yana samun cigaba sosai ga al’amurransa saboda ƙaunar manzon Allah da yake yi. Haka ya ambaci cewa
iyayensa sun hore shi da ya riƙe sunnar manzon Allah da son sa da son iyalansa da kuma
son makusantan manzon Allah domin abubuwa ne masu kyau sosai. A ƙarshen baitin Kabiru ya faɗa cewa idan dai waƙa ce a halin da ake ciki yanzu, idan ba ta manzon Allah ba
ce ba ya sanya bakinsa. Wannan ya ƙara tabbatar da so da ƙaunar da Kabiru ke yi wa manzon Allah a fili kamar yadda ƙaramin jigon so da ƙauna ya tabbatar.
Bayan nan akwai wani baitin da Kabiru ya ƙara bayyanar da son
Annabi da ƙaunarsa kamar haka:
K: Kowa da gwaninsa to sai ku bar ni gun nawa,
Ni dai Manzo Muhammadu Rasulallahi nib bi ba ni dawowa,
Na zaɓi abin da Allah da kansa kullum ke mutantawa,
Ashe ko ka ga ba zan
tsaya ba a dole in sanya bakina.
Kabiru ya faɗa cewa kowa na da nasa gwani (masoyi), don haka a bar shi
wurin Annabi domin shi ne masoyinsa. Ya ƙara da cewa Annabi
Muhammadu ne masoyinsa (gwani) kuma shi ya bi ba ya komowa. Ya faɗi dalilin bin Annabi
inda ya ce ya zaɓi Annabi domin shi Allah ya zaɓa kuma kullum mutanta
shi yake yi. A saboda hakan ba zai yi shuru ba face ya nuna wa duniya masoyin
Annabi ne. Idan aka lura da abubuwan da Kabiru ya faɗa dangane da so da ƙaunar manzon Allaha babu shakka akwai so tare da ƙaunar da ya faɗa idan aka yi la’akari da abubuwan da ke cikin baitocin
da aka kawo a sama.
6.2.2 Yabo ta Fuskar Asali
Asali kalmar Larabci ce aka ara ana amfani da ita yadda
ma’anarta take, wato ‘asal’. Kalmar asali na nufin mafari ko tushe ko salsala (Ƙamusun Hausa: 20). An sami bayyanar ƙaramin jigo ta fuskar yabo kan asali a cikin waƙar Kabiru Classic ta bege. Ga baitin:
K: Amma a faɗi a ƙara halittar Allah ɗai maras tamka,
Bai laifi ba ya yin kuskure sarki kaka zuwa kaka,
Mai kyan hali da kyawon halitta haifaffen garin Makka,
Baƙureshe ɗan Hashimawa kuma mai daɗin faɗin suna.
A layin ƙarshe na baitin Kabiru ya ambaci asalin Manzo (S.A.W.)
inda ya ce babu halittar da Allah ya yi tamkar (kamar) Annabi Muhammadu
(S.A.W.), haka kuma ba ya aikata laifi balle kuskure. Wannan na da alaƙa da shaidar da Allah ya yi masa a nassin Alƙur’ani cewa ba ya magana da son ransa face abin da aka
aiko zuwa gare shi. Bayan haka kuma ya faɗa cewa Annabi Muhammadu mutum ne mai kyan hali da kyan
halitta kuma an haife shi a garin Makka. Wurin da zancen asali ya fito shi ne a
layin ƙarshe inda Kabiru ya ce Baƙureshe ne ɗan ƙabilar Hashimawa kuma mai sunan da ke da daɗin faɗa. A nan takardar na
da tunanin cewa sunan Annabi da ke da daɗin faɗa shi ne wanda ke cikin kalmar shahada, wato Muhammadur
Rasululla. Idan aka koma ga ma’anar asali za a tarar da cewa akwai canjaras
tsakanin jigon yabo kan asali da abin da Kabiru Classic ya faɗa a ƙarshen baitin.
6.2.3 Yabo ta Fuskar Jaruntaka
Akan yabi mutum
mai jaruntaka kuma a lokaci ɗaya a kushe raggo.
A fahimtata, Jaruntaka na nufin tsayawa kai da fata domin ganin an cimma duk buƙatar da aka
tunkara ta hanyar amfani da ƙarfi da ƙarfe. Ana iya
cewa, jaruntaka na nufin yin fice ta hanyar samun nasara ga dukkan ƙalubalen da aka haɗu da shi, idan kuma na kokawa ne a sami mutum shi ya yi kaye
ba shi aka kayar ba. Wannan ya faru ga Annabi lokacin da ya fita zuwa wurin yaƙi domin gwabzwa da
arna. Ga abin da Kabiru Classic ya faɗa dangane da
wannan:
K: In ko yaƙi akai shi yake gaba faufau ba ya ɓoyewa,
Wata rana da yaf fito ga shi bayyane ya yi shiri na
burgewa,
Wayyo Allah kirarin da yay yi ta yi na sa ni godewa,
Yac ce shi ne
Muhammadu la fahran a cikin dubun arna.
Marubuci waƙar ya yabi Annabi (S.A.W.) ta ɓangaren jaruntaka
inda ya faɗi cewa, ko yaƙi ake gwabzawa shi ke
gaba ba baya ba, balle a ce ya ɓoye. Kabiru ya buga misali da wata rana da Annabi ya fito
zuwa wurin yaƙI tare da siffanta shirin da ya yi gwanin sha’awa da burgewa.
Ba wannan kaɗai ba, har kirari manzo ya yi a lokacin inji Kabiru, kuma
har da faɗar sunansa a cikin dubban arna. Babu wanda arna ke son
kashewa a wurin yaƙi ko wurin da ba can ba kamar Annabin rahama (S.A.W.). Bayan
haka har ya fito a cikinsu ya ce shi ne Muhammadu ɗan Abdullhi, wace
irin jaruntaka ce babu da ba a nuna ba? Tabbas, duk inda jarumi ke kai Annabi
ya hurce nan. Har yanzu marubucin ya ƙara da cewa:
K: Mai yin yaƙi a kan raƙuma ka san ya kai a gaida shi,
Mai yin yaƙi da hannu jinin Galib asalin ƙabilarshi,
Mai yin ɗamara da ya zo maza na ɓoyewa da dubin shi,
Mayaƙa ne akwai wani gwarzo laisa mutum wala jinna.
Domin tabbatar da jaruntakar Annabi da zuwa wurin yaƙi a fafata da shi Kabiru ya faɗa cewa a kan raƙumarsa yake yaƙi kuma sara in sara
yake yi ba da bindiga yake amfani ba balle a ce yaƙin sunƙuru ne. Ba a yaƙin nesa da nesa face
kusa da kusa, domin a fage ɗaya ake. Duk nisan da ke akwai tsakani bai zarce nisan
mai kibiya tsakaninsa da wanda zai harba ba. Haka kuma mayaƙi ne wanda idan ya yo shirin yaƙi da maza sun gan shi sai batun gudu a ɓuya. Kabiru ya ƙara da cewa daga cikin mayaƙan akwai wani ba mutum ba ne kuma ba aljani ba. A nan ana
jan hankalin mai karatu ya gano cewa, akwai halittu iri daban-daban a cikin
rundunar yaƙin Annabi da suka haɗa da mutane da aljanu da mala’iku da sauransu waɗanda Allah ke umurta
su je domin taimaka wa Annabi. Babu shakka akwai jaruntaka a cikin wannan baiti
da aka kawo. Ba wannan kaɗai ba, Kabiru ya ƙara kawo misalin
jaruntaka a cikin wani baiti inda ya ce:
K: Allah ya ba shi gwarzo maras tsoro jama’a ku yo lura,
Kafin Manzo ya zo ya yi jihadi tsoro zai bi kuffara,
Ya tarwatsa duz zukatansu sosai kanda a zo a faffara,
Su razana sun ji
tsoro a take suke karaya su gurfana.
A layi na farko da ke cikin wannan baiti Kabiru ya faɗi cewa Annabi na da
wani gwarzo (sarkin yaƙi) wanda da yawa wasu na gane shi da faɗar haka. Duk da haka
wasu na sha’afa su kasa tuna shi. Takardar na da fahimtar cewa mutumin shi ne
Aliyu bn Abi Ɗalib, kuma surukin Annabi ne. Kafirai kan kiɗime a cikin tsoro duk
ranar ko lokacin da za a gwabza tsakaninsu da Musulmai. Kafin ma a fara yaƙin zukatan arna sun raurawa tsoro ya rufe su baki ɗaya. Nan take su
karaya, su gurfana saboda jin tsoro. Tsoron da arna ke kamuwa da shi lokacin
karawarsu da Annabi na nuna jaruntakarsa a fili da kuma ɗaukakar da Allah ya
ba shi. Baitocin da aka kawo sun nuna jaruntakar Annabi ta fuskar yaƙi da maƙiyansa.
6.2.4 Yabo ta Fuskar Halayen Kirki
Hausawa na cewa “Hali zanen dutse” Kowane mutum da irin
halin da ake halittar sa da shi. Akwai mutane masu halayen kirki da marasa
kirki. A duniya baki ɗaya babu mutum ɗaya da ya kai Annabi (S.A.W.) halaye masu kyau. Dangane
da halayen Annabi S.A.W. ga abin da marubucin ya kawo:
K: Kyawawan haluka ba su ƙirgo don ba a san iyaka ba,
Domin da yawa waɗanda sunka yi imani ba da yaƙi ba,
Kyawon halinsa yak kai su yin imani ba takubba ba,
Sun auna sun gwada
sun ga Annabi ya ci a bi shi daidai na.
Allah da kansa ya yabi Annabi a kan halayen kirki kuma
babu wanda ya san yawansu sai shi kaɗai. Akwai kafiran da suka karɓi kalmar shahada ba
saboda yaƙi ba face sanadiyyar halayensa kyawawa da Allah ya azurta
shi da su, domin su kasance abin lura da misali ga al’umma baki ɗaya. Kyawawan halayen
Annabi suka yi sanadiyyar yin imaninsu ba kaifin takobi ba ko tsoron mutuwa. Babu
shakka arna sun gwada halayensa sun gano masu kyau ne, kuma sun gwada shi ƙiri-ƙiri ta fuskar ƙoƙarin ƙure shi kan wasu abubuwa ba tare da sun ci nasara ba, sai
dai shi ya ci nasara a kansu. Ganin haka ya sa arna suka aminta tare da ba da
kai bori ya hau suka amince da Annabi manzon Allah ne. Mai kyawawan halaye irin
waɗannan ya dace a aminta da shi kuma a yi masa mubayi’a
tare da kwaikwayon halayensa kasancewarsu kyawawa. A wani wuri kuma marubucin
ya ƙara da cewa:
K: Shi ba ya fushi, yana murmushi Manzo ba kyalkyatawa
ba,
Bai dubin mai ɓata kodayaushe a sunkuye bai ɗago kai ba,
Sanyin lafazi idan Ɗaha na magana ba zai
kurarra ba,
Sai ma ka rubuta
zancensa domin ba sauri ma’aikina.
Wasu halayen Annabi kyawawa su ne rashin yin fushi da yin
murmushi ba tare da ƙyalƙyatar dariya ba. Haka kuma ba ya kushe mutum don ya ga ɓatacce ne domin yana
son kowa ya shiriya kasancewarsa Annabin rahama. Haka kuma maganarsa na sanyaya
zuciyar mutane, kuma ba ya yin kuskure idan yana magana ba kamar sauran mutane
ba domin Allah ya riga ya kare shi daga tuntuɓen harshe. Idan yana
magana kowa na ji kuma yana fahimta domin ba ya sauri sannan harshensa ba ya
gargada, maganarsa na fita sosai yadda kowa ke ji kuma a fahimta. Waɗannan halaye ne abin ƙauna ba na ƙyama ba ga kowa. Idan aka sami mai ƙyamar halayen Annabi ba domin ba ya son su ba ne, sai don
hasada kawai. Dalili kuwa shi ne, duk halin da Allah ya yaba na ƙwarai ne ba na banza ba. Allah ya yabi Annabi da halaye na
kirki a cikin littafinsa mai tsarki. Har yanzu marubucin ya zo da wasu halayen
Annabi kyawawa kamar haka:
K: A faɗa a cika a kan alƙawal ko da kuffaru
sun shaida,
Da kyauta babu ƙyarga ta bayan Manzo
mijin Sauda,
Shi ba ya gudun talauci Muhammadu shi kullum akwai ke da,
Hannun baiwarsa na ƙwad da dud duniya wallahi ba sauna.
Baitin da aka kawo a sama marubucin na faɗa wa al’umma cewa
cika alƙawari na daga cikin halayen Annabi (S.A.W.). Annabi ba ya
da mummunar ɗabi’a ko ɗaya. Kyauta na daga cikin abubuwa masu faranta wa mutum
rayuwa da daɗi idan aka yi masa ita, kuma tana faranta ran wanda aka
yi wa ita musamman idan aka yi ta mai yawa. Haka kuma Annabi ba ya gudun
talauci domin ya riga ya san duk abin da Allah ya ƙaddaro wa bawa sai ya same shi. A kan haka kullum yana
tare da wadatar zuci, kuma babu mutumin da ya kai shi godiyar Allah. Bayan
wannan duk abin da Annabi ya riƙa da hannunsa ya ba mutane komai yawansu zai ishe su
domin mu’ujiza ce daga Allah.
6.2.5 Jigon Tuba
Tuba na nufin daina yin saɓo da dawowa kan hanya
ta gari. Haka ma tuba na nufin neman gafara daga wani. Har yanzu an ba da
ma’anar tuba da cewa tana nufin dawowa kan hanya ta gari a daina aikata saɓo (Ƙamusun Hausa: 440). A tawa fahimta, tuba na nufin barin
ayyukan saɓon Allah domin jin tsoron Allah kuma tsakani da Allah ba
tare da niyyar wata yaudara ba, kuma mai tubar ya tabbatar da yana da niyyar ƙin komawa ga ayyukan laifin da yake aikatawa da yake yi.
An yi sa’a marubucin ya gano da kansa cewa wasa (yabon) wasu mutane da yake yi
akwai ƙari a ciki da sauran laifukan da bai faɗa ba. Ga wani wuri da
ya ambaci tuba da kansa kamar haka:
K: Na tuba da wasa kowa maras tabbas da zato da kokwanto,
Ga gaske da gaskiya Annabin rahama ceto da mai ceto,
Shi tsuntsaye suke wa yabo mai daɗi in suna ƙoto,
Balle ni ɗan Adam ba ya yiwuwa
in kulle bakina.
Kabiru ya fara baitinsa da faɗar “Na tuba” mai
nufin ya gano kuskurensa dangane da waƙpƙin da ya yi wa wasu mutane. A kan haka sai ya yi niyyar
barin wannan aiki kuma yana neman Allah ya karɓi tubarsa tare da
yafe masa laifukan da suka gabata. Duk mutumin da ba Annabi ba maras tabbas ne
kuma sai dai a yi zato babu haƙiƙa tare da samun rabuwar hankali kan kowane al’amari. A
layi na biyu marubucin na nufin Annabi a wurin da ya ce “Ga gaske da gaskiya”
kuma an faɗi cewa a ranar lahira shi Allah zai ba izinin ceton bayi
baki ɗaya. Bayan haka tsuntsaye ma na yabo gare shi lokacin da
suke yin ƙoto, ina gare shi shi da yake mutum mai hankali da basira
da Allah ya ɗaga darajarsa sama ga tsuntsu? Ya ce ga tsuntsu ya yi yabo
ga Annabi balle shi? Saboda haka ne ya ce ba ya yiwuwa ya rufe bakinsa bai yabi
Annabi ba har ya ce zai ci gaba da yin bege har sai zuwa lokaci mutuwarsa.
Muhallish shahid a nan shi ne fitowa da jigon tuba kamar yadda marubucin ya
ambata.
6.2.6 Yabo ta Fuskar Addu’a
Addu’a kalmar
Larabci ce mai nufin roƙo ga wanda ake
bauta ma Hausawa suka ara suna amfani da ita da ma’anarta ta Larabci. A wani
wuri cewa aka yi addu’a na nufin roƙon ubangiji (Ƙamusun Hausa, 2006:
3).
Dangane da ma’anar
addu’a wani mai bincike ya ce “Addu’a tun asali kalma ce ta Larabci wadda ke
nufin ‘Da’autu fulan’ wato na kira wane, ina neman shi da ya fuskanto ni. A
cikin addinin Musulunci kuwa, sai ma’anar ta faɗaɗa zuwa wani nau’i
na yin ibada ta hanyar fuskantar Ubangiji Allah (SWT) da kiran sa da ganawa da
shi da ƙasƙantar da kai da
nuna kasawar bawa zuwa ga Mahalicci (Allah) domin kwaɗayin samun taimakonsa na alherin duniya da na lahira. Haka
kuma da neman kariyarsa ta hanyar tunkuɗe masa duk wani
sharri da bala’i da yayewar baƙin ciki ko gusar
da jin tsoro da tabbatar da aminci zuwa ga mai yin addu’a” (Ainu, 2007).
Ma’anonin da aka bayar na addu’a sun yi canjaras da
manufar mai yi wa mawaƙin/marubucin amshi a inda aka sami ta kai kuka ga Allah
domin ya yafe mata laifukan da take aikatawa dare da rana. Ta yi wannan addu’a
tare da yin tsani da Annabin rahama (S.A.W.). Ta ƙara da cewa idan ta sami yardar Allah (ta sami an karɓa mata addu’arta) to
babu shakka ta dace kuma ba za ta kasance a cikin matsala ba, wato ta fita cikin
matsala ke nan. Ga abin da ta ce:
N: Naja’atu ce ta Annabi wannan waƙar kad da kab ban ni,
Allah domin Muhammadu duk laifukkana ka yafe ni,
Idan na samu yardarka Allah ba ni zama cikin rana,
Ba ni zama cikin
rana.
Ba a nan kaɗai aka tsinci addu’a ba, akwai wurin da jagoran ya yi
tasa addu’a ga Annabi (S.A.W.) domin neman Allah ya ƙara salati da aminci, kuma ya haɗa da sahabbai inda ya
ce:
K: Allah ka yi mai salati ka ninka salami gwargwadon
sonka,
Maras farko da ƙarshe, maras adadi
muddin daɗewarka,
Daɗo shi ga wanda kaw wa yabon girma tun ba halittarka,
Ta’ala yanzu har ma
sahabbai yardaddu maso juna.
Ya nemi Allah ya yi ƙara tsira ga manzonsa
kuma ya roƙi Allah ya ninka amincinsa ga Annabin rahama. Daɗin salati da salamin
da ya roƙa ya siffanta shi da cewa maras farko kuma maras ƙarshe kuma wanda ba ya da adadi har ila masha Allahu ke
nan. Ya ƙara roƙon Allah ya daɗo salatin da sallama ga duk wanda ya yi wa yabo tare da
roƙa wa sahabban Annabi waɗanda suke yardaddu ne
kuma masu ƙaunar juna. Wannan addu’ar da Kabiru ya yi ta fito da
gaskiyar soyayyar da yake yi wa Annabi da sahabbansa a fili. Haka kuma ya ƙara tabbatar da gaskiyar maganar da ya yi ta cewa ya
daina waƙa ga kowa sannan ya koma ga manzon Allah baki ɗaya. Wannan na nufin
ya kwashe kayansa wurin kowa ya mayar a wurin Allah da manzonsa. Addua’ar da
Classic ya yi ba ta tsaya ga Annabi da sahabbansa kaɗai ba, ya haɗa da shehunan malamai
a inda ya ce:
K: A karamar barzahu ya Ta’ala ƙaƙƙara ma shehunnai,
Kamar Tujjani har ɗan uwanai Aljelani tauyinai,
Da Shehu Usmanu gwarzo na Allah ka haska ruhinai,
Da gwarzo malamina na
allo wanda ya kama hannuna.
Addu’ar ta haɗa da Shehu Tijjani da Jelani da Shehu Usman Ɗanfodiyo wanda ya kira gwarzo tare da roƙon Allah ya haskaka ruhinsa. Kabiru bai manta da
malaminsa ba a cikin wannan addu’a domin bai manta da karantarwar da ya yi masa
ba. Alal haƙiƙa kabiru ya nuna kirki a nan ta inda ya tuna da waɗannan mutane tare da
yi musu addu’ar fatan alheri. Allah ya karɓi addu’a, amin.
A ƙarshe, Kabiru ya haɗa da yi wa kansa addu’a ta fuskar roƙon Allah ya biya masa dukkan buƙatocinsa. Ga wurin da addu’ar ta fito:
K: Farin duba abun Nana na A’isha ka shige raina,
Sabilin so da ƙaunarka Annabi har
nis san ciwon kaina,
Muhammadu sahibul karamati kana da gije cikin raina,
Ganinai ne muradinmu
Jalla ka ƙara biyan muraduna.
Ya yabi Annabi ta fuskar kiran sa farin duba mahaifin
Nana kuma mijin A’isha. Ya ce ya san ciwon kansa saboda ƙaunar da yake yi masa. Ya kira shi ma’abuci karamomi
sannan yana ƙaunar sa matuƙa a cikin ransa.
Kabiru ya ce ganin Annabi na daga cikin buƙatocinsu har yana
addu’a da cewa maɗaukakin sarki ya ƙara biya masa
muradunsa. Da wannan za a tabbatar da cewa, mutum na yi wa kansa addu’a kuma
yana iya yi wa wani ko wasu.
6.2.8 Yabo ta Fuskar
Tarihi
Tarihi na nufin labarin abubuwan da suka wuce (shuɗe. Haka kuma yana
nufin fannin ilimi na abubuwan da suka faru a zamanin da ya wuce (Ƙamusun Hausa: 429). Ma’anonin tarihi da aka bayar a sama
duk sun yi daidai da abin da Kabiru Classic ya faɗa a ɓangaren jigon tarihi
da ya kawo a cikin waƙarsa. Ga abin da ya ce kamar haka:
K: Kabir ne Classic ɗan Yahaya ba baƙo ga waƙa ba,
Ba alfahari ba sai gode Allah ni ba malami ne ba,
Na dai zauna gaban malamai har yau ban bar karatun ba,
Na sauke, nai karatun
sani domin in bauta Rabbina.
Faɗar da ya yi cewa ɗan Yahaya ne, zamani ne mai nisa yake magana a kai idan
aka yi la’akari da lokacin da aka haife shi. Haka kuma ya ce ba baƙo ba ne a fagen waƙa . Ke nan, ya daɗe yana yi. Ya kuma ƙasƙantar da kansa ba tare da yin girman kai ba inda ya ce ya
zauna gaban malamai shi ba malami ba ne, amma kuma har yau bai bar karatu ba.
Ya ce ya sauke Ƙur’ani, ya yi karatun sani domin ya sami ilimin bauta wa
Allah.Da ji an bi sawun malamai, kuma akwai alamun malanta domin sha’iri
musamman na fagen addini ai malami ne. Idan aka dubi abubuwan da marubucin ya
faɗa babu shakka za a tantance akwai tarihi a cikin baitin
da aka kawo.
Akwai tarihi a cikin baitin da ke biye kamar
haka:
K: Amma a faɗi a ƙara halittar Allah mai maras tamka,
Bai laifi ba ya yin kuskure sarki kaka zuwa kaka,
Mai kyan hali da kyawon halitta haifaffen garin Makka,
Baƙureshe ɗan Hashimawa kuma mai daɗin faɗin suna.
Idan aka dubi layi na uku da ke cikin baitin da na huɗu da ke cikin
turarren rubutu akwai tarihi a ciki. Faɗar da aka yi cewa haifaffen garin Makka tarihi ne domin
duk inda aka yi zancen tarihin manzon Allah tilas a ce a garin Makka aka haife.
Idan ma ba a ce hakan ba aka faɗi cewa an haife shi a wani gari da ba Makka ba, to an gurɓata tarihi. Faɗar da aka yi cewa Baƙureshe ne kuma ɗan Hashimawa tarihi ne da babu ƙarya a ciki. Haka ma cewar da marubucin ya yi Annabi
Muhammadu mai daɗin faɗin suna ne gaskiya ne. Takardar na da fahimtar cewa ya fi
kowa daɗin faɗin suna domin akwai sunansa a cikin kalmar shahada. Haka
kuma idan aka ce Allah a mafi yawan ayoyin Ƙur’ani ana cikawa da sunansa. Wani dalilin faɗar cewa yana da daɗin faɗin suna shi ne,a
cikin salatin da ake yi na Ibrahimiyya akwai sunansa. Haka kuma duk inda aka ce
Muhammadur Rasulullah duk wanda ya cika da sallallahu alaihi wasallam, za a ba shi
lada. Wanda ka ambaci sunansa aka ba ka lada babu shakka sunansa na da daɗin faɗa. Idan kuma aka juya
ga laƙabin da mutanen garin Makka suka yi masa na ‘Al’amin’ mai
nufin amintacce, wane ne ba ya son a kira shi hakan? Takardar na goyon bayan
Kabiru Classic kan cewa sunan Annabi Muhammadu na da daɗin faɗa sosai ba kaɗan ba.
6.2.9 Yabo ta Fuskar Kyauta
Kyauta na nufin bai wa mutum wani abu don ra’ayi ba tare
da ya yi wani aiki ba (Ƙamusun Hausa: 271). Dangane da jigon kyauta a cikin waƙar begen Annabi (S.A.W.) da Kabiru ya yi ga abin da ya ce
da ya tabbatar da Annabi mutum ne mai yawan ba da kyauta:
K: A faɗa a cika a kan alƙawal ko da kuffaru
sun shaida,
Da kyauta babu ƙyarga ta bayan Manzo
mijin Sauda,
Shi ba ya gudun talauci Muhammadu shi kullum akwai ke da,
Hannun baiwarsa na ƙwad da dud duniya wallahi ba sauna.
Yin kyauta na ɗaya daga cikin halayen manzon Allah. Idan aka dubi layi
na biyu kyauta ta fito a nan mai nufin Annabi ba ya da rowa. An ce komai ya
samu rabawa yake yi ga mutanen da ke kewaye da shi. Haka an ce ba ya tsoron
talauci, kullum yana da sanin Allah ke bayarwa kuma shi ke hanawa. Fahimtata a
nan ita ce, duk wanda Allah ke so ai ba ya da talauci tare da shi sannan yana
da samun duniya da na lahira. Don haka zancen talauci bai taso ba gare shi. Maganar
da aka faɗa a layin ƙarshe ta ƙara warkar da zuciyar mai tababa inda aka ce hannun
baiwarsa na ƙwad da dud duniya wallahi ba sauna. Haƙiƙa Allah ya albarkaci Annabi da hannu mai daraja wadda duk
yadda abu yake kaɗan misali abinci komai yawan jama’a idan ya taɓa abincin da hannun
ya yi addu’a, komai yawan jama’ar da ke wurin za su ci har su raga idan abinci
ne. Idan kuma abin sha ne za su sha sai sun bar saura. Haka kuma an ce Annaabi
kaɗai aka samu mutumin da Allah ya yi wa wannan baiwa. An faɗi cewa wata rana sun
komo daga wurin yaƙi jama’a sun tagayyara saboda yunwa. Da suka isa wani
gari aka ba su kyautar abinci ammam ba ya isar jama’a. An ce Annabi ya yi
umurni da a kawo abinccin gare shi. An ce da ya sa hannunsa mai daraja ya yi
addu’a ya ƙare sai ya ce kowa ya ci a kan hankali ba tare da rigima
ba. An ce sai da kowa ya ƙoshi aka bar sauran abincin. Don haka faɗar hannun Annabi mai
daraja ce, gaskiya ne ba ƙarya ba. Allah ya ƙara wa Annabi daraja,
amin.
6.3 Salailan da ke
Cikin Waƙar Begen Annabi
(S.A.W.) Ta Kabiru Classic
Akan sami salo ko ɗaya ne a cikin waƙar da sha’iri ya rera
ko ya rubuta domin ko salo mai lami aka yi amfani da shi a cikin waƙar, ya karɓi sunan salo. Kafin a fara kawo salailan da aka tsinta a
cikin waƙar yana da kyau a kawo ma’anar salo ko ɗaya ne ko biyu daga
wani ko wasu masana. Ga ma’anonin salo da aka kalato daga wasu masana da suka
haɗa da Abdulƙadir Ɗangambo da Abdullahi Bayero Yahya kamar haka:
Abdullahi Bayero
Yahya cewa ya yi:
“Salo
yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda ake bi
domin isar da saƙo, ita wannan
dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta
yadda saƙon waƙar zai isa ga mai
sauraro ko mai karatun waƙar”.
Shi kuma Ɗangambo ga abin da ya faɗa dangane da ma’anar
salo:
“Salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin yin amfani da
wata kalma, lafazi, yanayi, hanya ko tunani a maimakon wani. Zaɓin da duk mutum ya yi
wajen isar da saƙon da yake so ya isar zai yi tasiri ga wanda ake isar da
saƙon gare shi. Ana iya cewa, armashin zance/saƙo ya danganta da irin batutuwan (kalmomi da yadda aka yi
zaɓin sarrafa su) na wanda ke isar da saƙon. Idan an tsaya an yi tunani sosai an zaɓo kalmomi da suka
dace, an saƙa su a muhallin da za su burge, to saƙo zai yi kyau”. An sami salailai a cikin waƙar da suka haɗa da:
6.3.1 Salon Share Fage
Salo ne da aka samu waƙoƙi ruwa biyu na ɗauke da shi domin waƙoƙi ne da ke ɗauke da sifofin rubutattun waƙoƙi da kuma na baka. Akan sami share fage kafin mawaƙi ya fara waƙarsa ta hanyar rera amshi da maganganun da suka yi kama
da amshi. Mawaƙi da mai yi masa amshi ko masu yi masa amshi kan rera
wasu baitoci kafin a shiga ainihin waƙar. Idan waƙa mai amshi ce za a ji jagora da ‘yan amshi na maimaita
amshin waƙarsu ta hanyar faɗi-in-faɗi ko kuma a sami kowannensu ya rera baiti sukutum nasa na
kansa. Akan sami labarin abin da waƙarsa ta ƙunsa a cikin share fagen da ya yi kamar yadda shi ma
Kabiru Classic ya share fagen waƙarsa ta bege a inda yake cewa:
KN: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
K: Classic na yi murna da begen Annabi ya zame tsani,
Na tsira wanda zai kai mu har Manzon Allah ya cece mu,
Muhammadu ɗan Amina,
Ɗan Amina.
K: Komai girman kujera ba za ta hana ni na rinƙa bege ba,
Idan da akwai ta wallahi ban ƙaunar tab a za ni karɓa ba,
Muhammadu nif fi ƙauna,
Naja’atu yau taƙaice.
N: Naja’atu ce ta Annabi wannan waƙar kad da kab ban ni,
Allah domin Muhammadu duk laifukkana ka yafe ni,
Idan na samu yardarka Allah ba ni zama cikin rana,
Ba ni zama cikin rana.
K: Habibi sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
N: Habibi sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
K: Habibi sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
N: Habibi sayyadil
wara Annabi baban Zara manzona
Idan aka lura sosai, da farko jagora da mai yi masa amshi
sun rera amshin waƙar tare. Bayan nan kuma jagora ya yi baiti biyu ba tare da
mai amshi ta ce uffan ba. Daga nan kuma sai aka sami ita ma ta yi nata baiti
inda babu wurin da aka sami baitinta idan ba nan ba. Biye da baitinta kuma, sai
aka sami jagoran ya fara furta amshin waƙar, ita kuma mai yi
masa amshi ta faɗa bayan ya faɗa. Daga salon sharer fage sai salon buɗewa.
6.3.2 Salon Buɗewa
Mawaƙa na buɗe waƙoƙinsu ta fuskoki da dama dangane da salon da suka yi
amfani da shi. Mawaƙin ya buɗa waƙarsa da baitin da ke tafe kamar haka:
K: A kullum zan yi komai da sunan Allah za ni farawa,
Gwani na Rasulu sanya ka farko riba ta da dacewa,
Ya Arrahamanu kai ne Rahimun ka cancanci godewa,
Ko ban furta ba albaɗini ka san sirri na ƙalbina.
A cikin baitin ya faɗa cewa a kullum zai fara komai da sunan Allah yake farawa.
Ya ƙara faɗa cewa sanya Allah ko ambatonsa a lokacin fara kowane
irin abu shi ne tafarkin samun dacewa ga kowa. A cikin baitin har yanzu mawaƙin ya kira Allah da wasu sunyensa (Arrahamanu da
Arrahimu) tare da faɗar cewa babu wanda ya cancanci godiya (a gode masa) kamar
Allah. Ya ƙara bayyana imaninsa da Allah kan cewa shi ne masanin
abin da ke ɓoye a zuciyar kowa, don haka ya san duk abin da ke cikin
zuciyar bawa ko bai faɗa da baki ba. A taƙaice, mawaƙin ya yi amfani da salon buɗe waƙarsa da ambaton Allah tare da faɗar wasu sunayensa da
kuma haƙiƙance saninsa a kan komai.
6.3.3 Salon Kamancen Fifiko da na Kasawa
Mawaƙin ya yi amfani da salailai biyu a lokaci ɗaya, wannan kuma ya
faru saboda salailan na tare wuri ɗaya, duk lokacin da aka yi amfani da ɗaya ɗayan na nan biye ko
da kuwa babu niyyar bayyana shi sai ya bayyana a cikin waƙa. Salon kamance ɓangare ne na babban salon siffantawa. Salo ne wanda ke
bayyana siffar wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu daban tare da amfani
da kalmomin da za mu ba suna kalmomin mizani ( Yahya, Salo Asirin Waƙa (Sabon Tsari: 90). Akwai kalmomin mizani da ake amfani da
su wajen nuna fifiko da kasawa tsakanin abubuwa guda biyu da suka haɗa da wuce da zarce da
fi da take da gota da furce da tsere da kuma ɗara a ɓangaren kamancen
fifiko, inji Yahya, 2016: 90. Haka ma a ɓangaren kamancen kasawa akwai kalmomin mizani da suka haɗa da ‘kasa’ da ‘gaza’
da ‘wane’ da kuma kalmomi masu soke samuwa kamar ‘bai…. ba’. Akwai kuma kalmomi
masu tambayar kushewa kamar ‘ina ya yi…?’ da ‘ina zai kai…’? (Yahya, 2016: 90).
A fahimtata, duk inda aka samu kamancen fifiko na kasawa
na nan tare da shi musamman idan aka bi bayanin Yahya. Mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen fifiko a wurare da yawa
cikin waƙarsa sai dai za a kawo misali kaɗan domin tabbatar da
hakan. Ga wani wuri da aka sami ya yi amfani da kamancen fifiko kamar haka:
K: Komai girman kujera ba za ta hana ni na rinƙa bege ba,
Idan da akwai ta wallahi ban ƙaunar ta ba za ni karɓa ba,
Muhammadu nif fi ƙauna,
Naja’atu yau taƙaice.
K: Ina kare shi kurhunka Raziƙu Almannanu mai kyauta,
Mafi jinƙai da tausai
Muhaiminu ya Allahu Alfatta,
Daɗo hikima da ilmi na yin bege in ɗaɗa muryata,
Na bar waƙa ga kowa Muhammadu ɗai nika yi wa begena.
K: Ku taho ku ji ga muhimmin bayani kan waƙar yabon Manzo,
Waƙa in ba ta Manzo ba ce wannan sunanta kwakwazo,
Don ƙarya za ka yi ba
cikakke shiryayye irin manzo,
Kowa kaw wa yabo to akwai naƙasi in banda Manzona.
Mawaƙin ya yi amfani da kamancen fifiko a cikin dukkan
baitocin uku da aka kawo a wuraren da aka ture rubutu face layin ƙarshe a cikin baitin ƙarshe wanda shi kuma ke nuna kamancen kasawa kai tsaye.
Ya faɗi komai girman kujera ba ta hana shi yin bege. Idan ma
akwai kujerar cewa ya yi ba ya ƙaunar ta kuma ba zai karɓa ba ko an ba shi
saboda ƙaunar da yake yi wa Annabi Muhammadu (S.A.W.) ta fi
kujerar nesa ba kusa ba. A baitin da ke biye da wannan kuma ya kawo salon
kamancen fifiko a inda ya ceAllah ne ya fi kowa jinƙai da tausan bayi. A nan, mawaƙin ya yi amfani da nassi ne a wajen nuna tausayin Allah
da jinƙansa a kan bayi fiye da kowa. Mawaƙin ya yi nuni zuwa ga ayar nan mai cewa ‘Wallahu ra’ufun
bil ibad’ da kuma ‘Arrahmanur Rahim’. Haka kuma ya ce Allah shi ke yi wa mutum
buɗi fiye da kowa a inda ya kira shi Alfatta, duk a cikin
layin wannan baiti. Har yanzu mawaƙin ya ƙara kawo kamancen fifiko a cikin baitin da aka kawo da ke
biye da wanda aka ƙare sharhi a kai. Mawaƙin ya ce idan dai waƙa ba ta manzon Allah
ba ce, sunan ta a wajensa shi ne kwakwazo. Tun nan ana iya fahimtar kamancen
fifiko a fili. Idan ba a fahimta ba, ya bayyana a layin da ke biye inda ya ce duk
abin da mutum zai faɗa a cikin waƙar wani mutum ƙarya kaɗai zai faɗa domin babu cikakke
kuma shiryayye kamar manzon Allah (S.A.W.). Maganar mawaƙin haka take domin nassi ne a inda Allah ya ce ‘innaka
ala swiraɗin mustaqim’
Dangane da kamancen kasawa kuwa, idan aka dubi layin ƙarshe a baitin da ke sama mawaƙin ya kawo shi wurin da ya ce “Kowa kaw wa yabo to akwai
naƙasi in ban da manzona”. A nan yana nufin babu mutum ɗaya da ya kai Annabi
(S.A.W.) daraja. Saboda haka kuma, duk yabon da za ka yi wa wani mutum bai kai
yabon Annabi falala da kamala ba. Wannan na nufin babu mutumin da mutum zai yi
wa yabo ya sami lada in ba Annabi ba. A kan haka ne takardar ke ganin kamancen
fifiko da na kasawa tamkar Ɗanjuma ne da Ɗanjumai.. Duk inda
aka sami ɗaya, ɗaya na nan tare da shi.
6.3.4 Salon Aron Kalmomi
Ba komai ake nufi da aron kalmomi ba a nan face amfani da
kalmomin wani harshe a cikin waƙar da ba da wannan harshe aka yi ta ba. Misali, idan mawaƙi na waƙa da Fulatanci aka sami ya yi amfani da kalmomin Turanci
ko Larabci, za a ce ya yi amfani da kalmomin aro a cikin waƙarsa. A lokacin nazarin waƙar an tsinci wasu kalmomin aro daga bakin Kabiru Classic
kamar haka:
6.3.4.1 Aro Daga Larabci
Akwai wurare da dama da mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Larabci da ke matsayin
kalmomin aro domin an yi waƙar da harshen Hausa ba na Larabci ba. An sami kalmomi har
da sashen jimla na Larabci a cikin waƙar kamar yadda za a
gani a cikin misalan da za a kawo. Ga misalin aro daga Larabci a cikin wani
baiti kamar haka:
K: Mai yin yaƙi a kan raƙuma ka san ya kai a gaida shi,
Mai yin yaƙi da hannu jinin Galib asalin ƙabilarshi,
Mai rena maza da ya ga maza na ɓoyewa da dubin shi,
Mayaƙa ne akwai wani gwarzo laisa mutum wala jinna.
A cikin layin ƙarshe an sami kalmar
laisa da wala jinna da ke nufin shi ba mutum ba kuma ba aljani ba. Ba a nan kaɗai aka yi amfani da
kalmomin Larabci ba, akwai su da yawa a cikin waƙar, sai dai an kawo wannan a matsayin misali domin
tabbatar da abin da aka faɗa na cewa akwai kalmomin aro daga Larabci tabbas ne ba
shaci-faɗi ba.
6.3.4.2 Aro Daga Turanci
Mawaƙin ya yi amfani da kalmar Turanci ɗaya wadda babu ta
biyunta a cikin waƙar, wato Classic. Ga wuraren da kalmar ta fito duk da
yake ba a nan kaɗai mawaƙin ya yi amfani da ita ba:
K: Classic na
yi murna da begen Annabi ya zame tsani,
Na tsira wanda zai kai muhar Manzon Allah ya cece mu,
Muhammadu ɗan Amina,
Ɗan Amina.
K: Kabir ne ɗan Yahaya Classic
ba baƙo ga waƙa ba,
Ba alfahari ba sai gode Allah ni ba malami ne ba,
Na dai zauna gaban malamai har yau ban bar karatun ba,
Na sauke, nai karatun
sani domin in bauta Rabbina.
A binciken da aka yi wannan kalma ce kaɗai aka samu ta Turanci
da Kabiru Classic ya yi amfani da ita a cikin waƙar. Ita ma ba komai ya sanya shi amfani da ita ba sai
domin ambaton sunansa da aka laƙaba masa lokacin da yana kula da shagon kasasuwan bidiyo.
6.3.5 Salon Tsakuren Nassi
Tsakuren nassi na nufin kawo gundarin nassi ko nuni zuwa
gare shi ko gutsuro shi ko kuma yin ishara zuwa gare shi a cikin waƙa (ma’anar mai bincike). Akan sami irin haka a cikin waƙoƙi masu yawa inda mawaƙi kan kawo aya sukutum ko sashenta ko hadisi ko sashensa
ko kuma a yi wa mai karatu nuni zuwa ga wannan nassi. An sami haka a cikin waƙar da Kabiru Classic ya yi ta begen Annabi Muhammadu
(S.A.W.) a wurare da dama kamar yadda za a gani. Ga misalin wurin/wuraren da
aka tsinci tsakuren nassi kamar haka:
K: Matsawar dai ga shi Allah ba zai yi azaba
gun halitta ba,
Aya ce babba wagga ba wanda zai tawilin ba haƙiƙa ba,
Dum mai zunubi da ya zo ga Annabi to tubansa an karɓa,
Allah ne yaf faɗi a ayar Ƙur’ani babu son raina.
An sami tsakuren nassi a cikin wannan baiti kuma shi ake
kira nuni zuwa ga nassin Ƙur’ani. Ayar da marubucin ke nuni zuwa gare ta ita ce
inda Allah ya ce ‘Wama mu’azzibahum wa anta fihim” mai nufin “Ba zan yi azaba
gare su ba matuƙar yana (Annabi S.A.W.) cikinsu. Ƙarin bayani ya biyo daga bakin mawaƙin da kansa inda ya ce ayar Alƙur’ani ce. Haka ya ƙara da wani nuni ga
nassi inda ya ce duk mai zunubin da ya zo wurin Annabi har ya tuba, an karɓi tubarsa kuma an
yafe masa kura-kuran da ya aikata ya koma fari fyas tamkar jinjiri sabon
haihuwa. A kan haka ya ƙara cewa ayar Ƙur’ani ce inda Allah
ya ce “Waman taba wa amanaa wa amila amalan swalihan, fa innallaha gafurur
rahim”, ma’ana duk wanda ya tuba kuma ya yi imani sannan ya aikata ayyukan ƙwarai lalle Allah mai gafara ne kuma mai jinƙayi. Ga wani ƙarin misali:
K: Kyawawan haluka
ba su ƙirge don ba a san
iyaka ba,
Domin da yawa waɗanda sunka yi imani ba da yaƙi ba,
Kyawon halinsa yak kai su yin imani ba takubba ba,
Sun auna sun gwada
sun ga Annabi ya ci a bi shi daidai na.
A layin farko na baitin da ke sama akwai nuni zuwa ga
nassi a daidai inda Allah ke cewa “Innaka la ala khulqin azim”. Ma’ana haƙiƙa kana a kan kyawawan ɗabi’u”. Idan aka yi
la’akari da wannan za a fahimci akwai tsakuren nassi a cikin baitin da aka kawo
wanda ya yi daidai da ayar da aka yi bayani a sama.
6.3.6 Salon Tambaya
A kan sami marubuta na yin tambayoyi a cikin
rubuce-rubucen da suke yi na yau da kullum, ba domin a ba su amsa ba sai domin
su fito da anniyarsu ga abin da suke son yi a fili. Wani lokaci sukan yi
tambaya domin faɗakarwa ga mutane ta hanyar sheda musu muhimmancin abu. A
taƙaice, an samu tambaya ɗaya da marubucin ya
yi a cikin waƙarsa inda ya ce:
K: Ga wanda yake a kalmar shahada to wa za ni waƙewa?
Ga wanda Ilahu ke wa salati kullum babu katsewa,
Yawan begenka haske ga Allah mutum ke ƙara samowa,
Dum mai hikima da bai
bege wallahi yana cikin rana.
A nan marubucin na nuna Annabi S.A.W. ya fi duk wanda zai
yi wa waƙa daraja, don haka ba zai yi wa kowa waƙa ba face shi kaɗai saboda darajarsa da matsayinsa a wurin Allah. Allah ya
yi masa salati, kuma duk mai yi masa bege haske yake ƙara samu a wurin Allah. Haka kuma Kabiru ya ce duk wanda
Allah ya ba hikimar waƙa ya kasance ba ya yi wa Annabi S.A.W. bege to ya yi hasarar
hasken da mai bege ke samu a wurin Allah. Duk wanda ya rasa wannan haske kuwa,
ya yi hasara babba ba ƙarama ba. A taƙaice, Kabiru na ganin
ba wanda ya dace ya yi wa waƙar yabo da ya kai Annabin rahama.
6.3.7 Salon Amshi
Amshi na ɗaya daga cikin salailan da ake lura da su a lokacin da
ake nazarin waƙa idan mai amshi ce. Waƙar bege da Kabiru ya yi ta Manzon Allah mai amshi ce,
kuma ga amshin kamar haka.
K: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
N: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
K: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
N: Habibi Sayyadil
wara Annabi baban Zara manzona
Wannan shi ne tsarin amshin da marubucin ya rera tare da
mai yi masa amshi tun a cikin share fagen da suka yi na waƙar. A nan babu abin da mai amshi ke faɗa sai “Habibi
sayyadil wara Annabi baban Zara manzona” mai nufin masoyina shugaban halitta
baban Zara manzona. Wannan ne amshin waƙar begen Annabin
rahama da Kabiru Classic ya rera tare da ‘yar amshinsa Naja’atu.
6.3.8 Salon Rufewa
Akwai hanyoyi masu dama da marubuta waƙa ke bi domin rufe waƙoƙinsu idan suka zo ƙarshe. A nan ba za a
faɗi na wasu ba sai dai na wannan da aka yi nazari, wato waƙar begen Annabi (S.A.W.). Marubucin ya rufe waƙarsa ta hanyar maimaita amshin da suka fara da shi a
wurin share fage inda marubucin ya faɗa ita ma mai yin amshi ta faɗa. An sami kowannensu
ya faɗi amshin sau biyu kafin su rufe waƙarsu. Ga yadda suka rufe waƙar:
K: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
N: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
K: Habibi Sayyadil wara Annabi baban Zara manzona
N: Habibi Sayyadil
wara Annabi baban Zara manzona
7. Sakamakon Bincike
A cikin wannan maƙalar an gano cewa
linzami ya fi bakin kaza, saboda Kabiru Classic ya fito fili ya faɗi anniyarsa ta barin yi wa kowa waƙa tare da mayar da
kayansa wajen manzon Allah (S.A.W.), kuma ba da nufin kwance niyya ba. A kan
haka ya dace a sami ranar da za a yi bikin tubar Kabiru daga yin kwakwazo zuwa
begen manzon Allah S.A.W. Yin haka na da fa’ida domin tabbatar wa duniya cewa maganar
da ya faɗa a cikin waƙar bil haƙƙi ilal Lahi ce. Haka
ma binciken ya gano cewa Kabiru mawaƙin siyasa ne kuma ɗan siyasa, domin
halin da ake cikin a yau yana riƙe da muƙamin ɗan majalisan tarayya, wato ɗan majalisar waƙilai na tarayya
(House of Reps) yana waƙiltar ƙananan hukumomin
Anka da Talata Mafara da ke cikin jihar Zamfara. Ba wannan kaɗai ba, maƙalar ta gano cewa
Kabiru malami ne saboda ya faɗa da bakinsa cewa
ya yi karatun Alƙur’ani, ya sauke
har ya karanci wasu littattafan furu’a domin samun ƙarin sanin yadda
zai yi ibada ga mahaliccinsa. Haka kuma binciken ya gano cewa duk waƙoƙin da ake yi bas u
kai darajar waƙoƙin begen Annabi
Muhammadu S.A.W. ba, domin su suka yi daidai da shari’a kuma ba a rubuta wa mai
yin su laifi sai dai lada. Bayan haka binciken ya ƙara gano cewa, yin
waƙoƙin yabon Annabi
S.A.W (waƙoƙin begen sa) ibada
ne, su kuma waɗanda ake yi wa
sauran jama’a ba su yi kusa ga ibada ba ko kaɗan domin Kabiru ya kira su da suna kwakwazo, mai nufin
surutun banza. A ƙarshe, binciken na
ganin cewa Kabiru Classic na ɗaya daga cikin
mawaƙan da Allah ya yi
wa gamo-da-katar ta fuskar barin abin da shari’a ba ta aminta da shi ba zuwa ga
wanda ta yarda da shi. A nan ana nufin tuba daga yi wa kowa waƙa face manzon
Allah S.A.W.. Saboda haka binciken ya gano cewa Kairu ya yi hijira ne daga
barin abin dab a ya da asali zuwa ga wanda ke da asali.
8. Kammalawa
A cikin maƙalar an yi nazari
ta hanyar fito da babban jigo/saƙon waƙar da ƙananan saƙonnin da ke
cikinta da kuma salailan da take ɗauke da su da ba
sai an nanata su ba domin suna a ciki. Haka kuma an tattauna manufar binciken
maƙalar da
muhimmancin binciken da hanyoyin da aka bi wajen gudana da binciken. Bayan haka
kuma, an kawo sakamakon binciken da aka gudanar da kuma wannan kammalawa a ƙarshe.
Manazarta
Ainu, H. A. (2007). Rubutattun Waƙoƙin Addini Na Hausa: Nazarin Jigoginsu Da Salonsu. Kundin
Digiri Na Uku Da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo, Sakkwato-Nigeria.
Bargery, G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary And English-Hausa Vocabulary. Ahmadu Bello University Press Limited, Zaria-Nigeria.
Bunguɗu, A. I. (2017).
Tarken Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Yahaya Kilasik, Binciken da Aka
Gabatar Don Cikasa Wata Ƙa’ida Ta Samun Digiri Na Biyu (M. A.) A Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
CNHN, (2006). Qamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.
Yahya A, B, (1986). ‘The Verse Category Of
Madahu, With Special Refrence To Theme, Style And The Background Of Islamic
Source And Belief’, Ph D thesis, University Of Sokoto.
Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waqa. Kaduna: Fisbas Media
Services.
Yahya A.B. (2016). Salo Asirin Waqa (Sabon Tsari). Sokoto: Guarantee Printers.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.