Ticker

6/recent/ticker-posts

Dabarun Jawo Hankali a Wakar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Dankwairo Maradun

Article Citation: Isa, B.M. (2025). Dabarun Jawo Hankali a Waƙar Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun. Zauren Waƙa, 4(2), 34-40. www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.004.

DABARUN JAWO HANKALI A WAƘAR ‘YANDOTAN TSAHE ALHAJI ALIYU TA ALHAJI MUSA ƊANKWAIRO MARADUN

Na

Babangida Magaji Isa PhD
Ruwantsa Ƙofar Fada
Ɗambatta Local Government, Kano State
isa.babangida@yahoo.com
08065951124

Tsakure

Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar sarauta da jami’anta kiɗa da waƙa. Sai kuma makaɗan game-gari, waɗanda suke yi wa sauran jama’a kiɗa da waƙa. Wannan kasona makaɗan game-gari ya haɗa da makaɗan attajirai da masu sana’a da ‘yan siyasa da makaɗan bandariya da na bege da sauransu. Dukkanin waɗannan makaɗa suna amfani da dabarun jawo hankali domin isar da saƙonsu cikin sauƙi da burgewa ga jama’a. Sukan yi hakan ne kuwa domin kwarzanta wanda suke yi wa kiɗa da waƙa, a ɗaya ɓangaren kuma su kushe abokan adawar waɗanda suke wa waƙar. Irin waɗannan dabarun jawo hankali sun haɗa da: kwatantawa wadda ta ƙunshi kamantawa da siffantawa da kuma jinsintarwa. Haka kuma makaɗan sukan yi amfani da dabbantarwa da alamtarwa da sauran dabarun jawo hankali.Wannan takarda ta taƙaita ne ga nazarin siffantawa a cikin waƙar ‘Yandotan Tsahe ta Alhaji Musa Ɗankwairo. Manufar wannan takarda ita ce, bin diddigi tare da bayyana wuraren da Ɗankwairo ya yi amfani da siffantawa a cikin wannan waƙa da kuma hikimomin da suke tattare da yin hakan. Hanyoyin nema da tattara bayanan bincike su ne sauraron waƙoƙin Ɗanƙwairo a faya-fayan C.D da sauran su.

1.0 Gabatarwa

Dabarun jawo hankali hanyoyi ne da mawaƙan baka na Hausa suke amfani da su ta hanyar sarrafa kalmomi da maganganu domin cusa sha’awa da jin daɗi ga mai sauraron waƙoƙinsu. Siffantawa tana ɗaya daga cikin waɗannan dabarun jawo hankali inda makaɗi ke ɗaukar wani abu ya ce shi ne wani abin daban. A duba Sarɓi (2007:153) da Abubakar (2011:58). Ataƙaice, siffantawa a waƙoƙin baka na Hausa dabara ce ta jawo hankalin masu saurare inda makaɗi ke ɗaukar siffar wani ya ba wani domin fifita wani ko ƙasƙantar da wani cikin waƙarsa. Irin hakan takan kasance ta hanhoyi da dama. Misali amfani da wata dabba mai daraja ko ƙarfi ko kuma kyawun halitta ya siffanta wanda yake waƙewa da kuma ɗaukar siffar wani abu kasasshe ya ba wani domin naƙasar da wani mutumin da yake son kushewa. Saboda haka mawaƙa kan yi amfani da siffantawa da manufofi biyu, wato yabo ko fallasa. Ba Alhaji Musa Ɗankwairo ne kaɗai ke amfani da waɗannan dabaru ba. Kusan ace dukkan makaɗa da mawaƙan baka na Hausa suna amfani da ire-iren waɗannan dabaru. Misali, Alhaji Ɗan’anace a waƙar Ɗandunawa yana cewa:

Maza ga giwa masha dafi

Zaki mai ƙashi guda

Gwanki mai kiwon ɓata

 (Abubakar, 2011:60)

A wannan ɗa za mu ga cewa Ɗan’anace ya siffanta Ɗandunawa da manyan namun daji guda uku domin kwarzanta shi.Wato ya siffanta shi da giwa da zaki da kuma gwanki. Waɗannan dabbabi,ko shakka babu, sun yi fice wajen kwarjini da tsoratarwa ba ga mutane kaɗai ba, har ma ga sauran namun daji. Abin lura a nan shi ne, Ɗan’anace siffanta wanda yake waƙewa ya yi ta hanyar ɗaga dajajarsa da kuma kwarzanta shi,

Haka nan Salihu Jankiɗi a waƙar Sardauna yana cewa:

Ga gaskiya ku bar bin gaibu

In ga farin wata mai haske

Kun san ya fi na tauraruwa

(Abubakar, 2011:62)

Nan kuma Jankiɗi siffanta Sardauna ya yi da farin wata sannan ya kushe abokan adawar Sardauna ta hanyar siffanta su da tauraruwa. Ko shakka babu, hasken farin wata ya fi na tauraruwa, don haka Jankiɗi ya ɗaga darajar Sardauna ta wannan hanya da kuma dakushe sauran abokan adawa ta hanyar ba su siffar taurari.

2.0 Bitar Ayyukan da Suka Gabata

Masana da manazarta sun yi ayyuka daban daban a waƙoƙin baka na Hausa da suka danganci nazarin dabarun jawo hankali da kuma nazarin harshen waƙa. Irin waɗannan ayyuka sun haɗa da: Garba (1998), Birniwa (2004), Kurawa (2005), Sarɓi (2007), Gusau, (2008), Gusau (2009), Abubakar (2011), Satatima (2014), Gobir da Sani (2021), Bakura da Sani (2023), Gummi da Sani (2025) da sauransu.

Sarɓi (2007) Ya kawo bayani a kan dabarun jawo hankali a babi na tara, inda ya yi magana a kan kwatantawa wadda ta ƙunshi kamantawa da nau’o’inta, wato kamantawar fifiko da ta daidaito da kamantawar kasha, wato kasawa ko kasarwa. Haka kuma ya kawo siffantawa inda ya rarrabata zuwa gajeriyar siffantawa da doguwar siffantawa. Sai kuma ya kawo bayanai a kan jinsintawa da dabbantawa da kuma abuntawa da abuntawar- abuntawa. Daga ƙarshe ya ƙarƙare da alamtawa da hoto cikin bayani da kambamar zulaƙe da kuma jerin sarƙe. To sai dai Sarɓi (2007) ya yi aiki ne a kan rubutacciyar waƙar Hausa, wato waƙen Hausa.

Shi kuwa Gusau, (2008) littafi ne da ya ƙunshi bayanai a kan waƙoƙin baka a ƙasar Hausa yanaye-yanayensu da sigoginsu. Littafin ya kawo bayani a kan mazauna ƙasar Hausa da kiɗa na Hausa da kayan yinsa. Sai kuma ya kawo makaɗan baka na Hausa, asali da tasowar su da kuma rabe-raben makaɗan baka na Hausa. Daga nan kuma sai ya kawo Halayya da nau’o’in makaɗan baka na Hausa. Daga ƙarshe ya ƙarƙare da awo turke da nau’o’insa a waƙoƙin baka na Hausa.

A wani aikin kuma daban Gusau, (2009), wato Diwanin waƙoƙin baka na Hausa-zaɓaɓɓun matani na waƙoƙin baka na Hausa. Littafin ya ƙunshi matanan waƙoƙin fada inda aka kawo wasu waƙoƙin fada guda tamanin da tara (89) daga mawaƙa daban daban da kuma waƙoƙi mabambanta. Daga nan kuma sai aka kawo waƙoƙin game-gari guda hamsin da huɗu (54) daga mawaƙan jama’a daban daban. Wannan littafi ya taimaka matuƙa gaya dangane da wannan takarda. Hasali ma daga littafin ne aka ɗauko waƙar da aka yi bincike a kanta. Saboda haka aikin bai samu matsalar rubuta waƙar bat un da yake an same ta a rubuce a littafin. Ke nan aikin ya mayar da hankali ne kawai ga manufar da ta haifar da shi, wato bin diddigin siffantawa a wannan waƙa.

Abubakar, (2011) Ya yi aiki mai taken Siffantawa a waƙoƙin baka na Hausa. Littafin ya kawo ma’anar siffantawa da nau’o’inta a waƙoƙin baka na Hausa waɗanda suka haɗa da: siffantawar fifiko da ta daidaito da ta kashi da kuma ta kambame. Sauran su ne siffantawar tsoratarwa da ta alaƙantawa. Wannan takarda tana da dangantaka ta ƙut da ƙut da aikin Abubakar kasancewar dukkan ayyukan sun yi magana ne a kan siffantawa. Amma sun bambanta ta wata fuskar, domin aikin Abubakar kan rabe-raben siffantawa ne da kuma kallon da ake yi wa siffantawa, ga kuma uwa-uba irin mawaƙan da ake nazari. Shi Abubakar ya yi nazarin mawaƙa daban-daban wato ta fuskar misalai. Yayin da wannan aiki ya keɓanta da waƙar Ɗanƙwairo kuma ko a Ɗankwairon dai ma, waƙa ɗaya tak aka keɓe domin yin nazari.

Satatima, (2014) ya kawo bayanai da suka shafi harshen waƙa a cikin waƙoƙin Hausawakuma ya ɗora misalai daban-daban daga cikin waƙoƙin baka da kuma rubutattu. Takardar ta kawo fitattun hanyoyi na zubin harshe har guda goma (10) waɗanda suka haɗa da: kutse ga nahawun harshe da alamtawa da kambame da sarrafa haruffa ko sautuka da jerin sarƙe da kamantawa. Saura hanyoyin sun haɗa da kinaya da kuma amsa-kama.Wannan takarda tana da ‘yar alaƙa da aikin Satatima kasancewar sun yi magana a kan dabarun jawo hankali. Amma sun bambanta saboda aikin Satatima ya kalle shi ta fuskar harshen waƙa wato bayani goma. Yayin da wannan takarda ta keɓanta ga nazarin siffantawa a waƙar Alhaji Musa Ɗankwairo.

3.0 Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu ta Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

An samo wannan waƙa a (Gusau, S M 2009). Kuma kamar yadda bayani ya gabata, dabarun jawo hankali a wannan waƙa hanyoyi ne da Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun ya bi wajen isar da saƙonsa ta hanyar sarrafa kalmomi da sauran maganganu domin kwarzantawanda yake waƙewa da kuma kusheda wanda yake fallasa. Tun a karon farko na wannan waƙa ta Alhaji Aliyu, mawaƙin ya fara da siffanta wanda yake waƙewa da shingen ƙaya domin ya nuna cewa ‘Yandoton Tsahe ba kanwar lasa ne ba. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Mai lihidin faɗagimshimin shamaki

‘Yan amshi: Baba shingin ƙaya mai wuyar ratse

Kamar yadda muka gani, a wannan ɗiyan waƙa, Alhaji Musa Ɗankwairo ya kwarzanta Alhaji Aliyu ta hanyar siffanta shi da shingen ƙaya (mai wuyar ratse).Ga alama abin da Ɗankwairo ke ƙoƙarin nunawa anan shi ne, yana nuna jarunta da kwarjinin wanda yake waƙewa ga jama’a. Ga wata ɗiyar waƙar kuma:

Jagora: Aluux2

‘Yan amshi: Namijin zuma mai wuyar cima,

 Kowa hi ka harbi shi sha kainai

A wannan ɗiyar waƙar ma, an siffanta Aliyu da namijin zuma domin a nuna jajircewarsa da bunƙasa da kuma kwarjini da dabarun yaƙi. Ga waɗanda suka san zuma, an santa da harbi. Amma kuma namijin zuma ya fi faɗa da kuma zafin harbi. Don haka da Ɗankwairo ya tahi siffanta Aliyu bai tsaya ga zuma kaɗai ba, sai ya siffanta shi da namijin zuma. Haka nan kuma a ɗiyan da ke biye da wannan, an siffanta Alhaji Aliyu da abubuwa biyu, zarto da bindiga. Ga abin da mawaƙin yake cewa:

Yaro: Zartu kake mai ciwon yanka

‘Yan amshi: Ali bindiga mai zahin tashi

 Maza da shirinka koyaushe ta samu

Kamar yadda aka gani a ɗiyar da ta gabata, layi na ɗaya da na biyu sun ƙunshi siffantawa kai tsaye da aka yi wa Aliyu. Da farko an siffanta shi da zarto, wani abin yanka katako ne mai haƙora wanda kafintoci ke kiran sa majaujawa. Yankan zarto ba kamar yankan wuƙa yake ba. Domin shi zarto idan ya yi yanka sai kowane haƙoransa ya sami inda ya nutse ga jikin wanda ya yanka. Amma ita wuƙa yankanta bai ɗaya ne. Ita kuma bindiga wadda ake wa laƙabi da ciki da mugunta, gamo da kasawa ce. Wato gaba ɗaya take tashin abin da aka nufa daga aiki. An siffanta Aliyu da waɗannan abubuwa guda biyu domin a ƙara nuna irin jaruntarsa da kuma tsoratarwarsa ga abokan adawarsa. A wani ɗiyan waƙar ma an yi makamanciyar irin wannan siffantawa da ke nuna jaruntar wanda ake waƙewa, ga abin da Ɗanƙwairo ke cewa:

Jagora: Goshin gulbina malam

‘Yan amshi: Uban Gandu kowaj ja da kai

 Ya wuce da shi yanzu

A wannan ɗiyar ma, an siffanta Aliyu da goshin gulbi, kamar sauran ɗiyoyin da suka gabata, domin a nuna jarunta da kwarjinin Aliyu. Gulbi ruwa ne da yake gudana da ƙarfin gaske. Duk mutumin da ya y i ganganci ya tarye shi idan ba a yi dace ba zai tafi da shi wataƙila ma ya halaka, Allah Ya tsare! Ɗanƙwairo ya siffanta Aliyu ta wannan siga domin ya nuna cewa duk wanda ya yi jayayya da shi zai kwana ciki. Ma’ana zai sha wahala marar misaltuwa. Ba nan kaɗai ta taƙaita ba, a ɗiya nagaba ma Alhaji Ɗanƙwairo Maradun ya siffanta Alhaji Aliyu da shahararrun namun daji guda biyu duk dai da nufin nuna cewa Aliyu tsayayyen namiji ne wanda ba a kai masa wargi. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Ali jan damisa kawo jat talaka

‘Yan amshi: Uban mai Damma zaki tsayayye

Damisa tana ɗaya daga cikin namun daji da suke da haɗari.Har ma ana yi mata kirari da “damisa ƙi sabo” da kuma “damisa kin ƙi gani biyu”. Ma’ana, ba a yin sabo da damisa kamar yadda ake yin sabo da wasu namun daji irin su giwa da kura da makamantansu. Haka abin yake ga zaki inda ake masa laƙabi da “manyan dawa”.Duk irin ƙasaitar da ke tattare ga waɗannan namun daji, an alaƙanta Aliyu da su.Ma’ana shi Aliyu damisa ne kai tsaye haka kuma zaki ne kai tsaye.Idan ka ganshi ka ga damisa kuma ka ga zaki. Wani ƙarin jaddadawar ma shi ne, damisar ma ja, domin ita jar damisa ta fi faɗa, da kwarjini ba ga mutane ba ma, har ga sauran dabbobi. Haka nan kuma, zaki ne tsayayye, wato tuni a shirye yake yana zuba idanu ya ga wanda zai wuce ya far masa. Duk waɗannan siffofi, suna nuni ne kai tsaye cewa Alhaji Aliyu fa ba kanwar lasa ne ba. Abin nufi, yana zaune da shiri a kowane lokaci aka nemi a far masa domin shi Aliyu ba shi da sabo idan aka nemi a taka shi. Kamar yadda Ɗanƙwairo ya siffanta shi a wannan ɗiyan waƙa na gaba:

Yaro: Gizago ba ka da sabo wandara

 Gamda’aren ‘yanware tsayayye

Gizago dai wani kayan aiki ne da mafi yawanci masassaƙa ne ke amfani da shi. Yana da kaifin gaske, kuma ba wuya mutum ya sare hannunsa idan yana aiki da shi. Ke nan komai sabon mutum da shi, lallai zai iya yi masa rauni. Kamar cinnaka yake, bai san na gida ba. To, an siffanta Aliyu da gizago ne domin a nuna cewa komai sabon mutum da shi Aliyun, idan aka nemi a hau shi ta reshe lallai za a yaba wa aya zaƙinta. Zama tare da Aliyu ba hujja ce ta idan abokan adawa sun taƙale shi zai saurara ba. Sannan kuma an yi masa ƙari da cewa shi wandara ne. A duk inda ka ji an ambaci mutum da wannan suna “wandara” ana ƙoƙarin nuna cewa shi mai ƙarfin gaske ne. Don haka baya ga kasancewar Aliyu gizago, to kuma wandara ne domin kuwa shi Aliyu ba a faɗa masa, kamar yadda aka siffanta shi a wani ɗa na gaba yana cewa:

Yaro: Toron giwa kake mai Garewa Alu x2

‘Yan amshi: Ba a hwaɗa ka, tilas a kauce ma x2

Duk da ganin cewa akan yi sabo da giwa, ba kamar damisa ba, amma ko ga sauran namun daji kuma ba su cika faɗa wa giwa ba. Ko shakka babu, akan kauce wa giwa domin ta wuce bago. Ɗanƙwairo ya siffanta Alhaji Aliyu da toron giwa domin ya nuna irin matsayinsa ta fuskar zafi/girma daƙarfi da kwarjini da kuma ƙasaita.Ko cikin giwaye, toron giwa ne mafi ƙasaita da cika a matsayin abin tsoro. Saboda haka Ɗanƙwairo ya yi amfani da wannan dabara ta kwalliyar harshe (siffantwa) domin yin yabo ga ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu.

Kammalawa

A wannan takarda an yi ƙoƙarin nuna ɗaya daga cikin dabarun jawo hankali da Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun yake amfani da ita wajen isar da saƙonsa ga jama’a domin jawo hankalinsu. Wannan hanya kuwa ita ce siffantawa. An ga yadda Ɗanƙwairo ya siffanta wanda yake waƙewa, wato Alhaji Aliyu ta hanyoyi daban daban domin kwarzantawa da nuna isarwa da kuma ƙasaita. A wannan waƙa da aka nazarta, dukkan siffantawar da aka yi amfani da ita an danganta ta ne ga wanda ake waƙewa. Wato dai an fifita wanda ake waƙewa akan sauran abokan adawarsa. A wannan takarda an gano cewa babu wata ɗiyar waƙa da mawaƙin ya kawo wadda take nuna kasarwa ga abokan adawar Alhaji Aliyu. Saboda haka, ana iya cewa wannan waƙa ce ta yabo tsantsa. Ita siffantawa daman takan zo ɗayan biyu ne, ko dai a kasar da wanda ake son kushewa ko kuma a ɗaga darajar wanda ake so a yabawa. To, a wannan waƙa darajar wanda ake waƙewa aka ɗaga. Sannan an lura da cewa daga cikin dabarun jawo hankali da masana da manazarta suka bayyana kamar yadda suka zo a bita, Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi amfani ne da siffantawa kai tsaye. Ga alama mawaƙin yana son nuna cewa Sarki ba shi da wani abokin burmi na kwatance ko da kuwa ta fuskar yabo dai ne. Ga alama shi ne ya sa ya yi ta luguden siffantawa kai tsaye domin cimma wannan buri.

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U.  (2023). Tsattsafin fanɗare wa addinin Musulunci: Wata yasasshiyar gona a gandun waƙoƙin baka na Hausa. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, (6)10, 482-489. https://doi.org/10.36349/easjehl.2023.v06i10.002.

Birniwa, A.H. (2004) Siffantawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa. Journal of Hausa Studies Vol 1 No 1 Department of Nigerian Languages Sokoyo, Usman Ɗanfodiyo Uniɓersity

Garba, M. (1998) Azancin Magana a Waƙoƙin Makaɗan Baka. Kundin Bincike na Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Kano, Jami’ar Bayero

Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD.

Gummi, M.F. & Sani, A-U. (2024). Exploring dietary habits through Hausa royal songs: A study of traditional foods in Makaɗa Sa’idu Faru’s compositions. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 415-424. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.057

Gusau, S.M (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited Kano. Nigeria

Gusau, S.M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka. Zaɓaɓɓun Matani na Waƙoƙin Baka na Hausa. Century Research and Publishing Limited, Kano, Nigeria

Kurawa, H.M (2005) Adon Harshe Cikin Waƙoƙin Sardauna na Ɗanƙwairo. Kundin Bincike na Digirin Farko, Sashen Harsunan Nijeriya Kano Jami’ar Bayero.

Sarɓi, S.A. (2007) Nazarin Waƙen Hausa. Samarib Publishers, Kano, Nigeria

Satatima, I.G (2014) Harshen Waƙa: Ma’anarsa da Rabe-rabensa. In a Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo.

 

Rataye

Makaɗi: Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun

 Ubangida: ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu 11 (1960-1991)

Gindin Waƙa: Shirya kayan faɗa Maigida Tsahe

 : Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.

 

Jagora: Mai lhidin faɗa gimshimin shamaki,

Y/Amsh: Baba shingin ƙaya mai wuyar rates

 

Jagora: Ina gudun marmara x2

‘Y/Amshi: Ba mutum ne ba. x2

Jagora: Ni sabo nika aiki da shi,

‘Y/Amshi: Ni na san amanar da ta hwaru.

 

Jagora: Aluu, x2

‘Y/Amshi: Namijin zuma mai wuyar cima.

 :Kowa hi ka harbi shi sha kainai. x2

 

Yaro: Zartu kake mai ciwon yanka,

‘Y/Amshi: Ali bindiga mai zahin tashi,

 :Maza da shirinka ko yaushe ta samu.

 

Jagora: Ɗan Shehu na Shehu baban Ayaga,

 :Mai Tsahe mai halin ya kamata,

 ‘Y/Amshi: Kowa da riga da doki na zama,

 :Kwab bi ka yana wadata uban Kado,

 :Ba ya taɓewa.

 

Yaro: Ku dai ba mu gida na hairan,

 :Kowaz zo ya sha ya yi wanka,

‘Y/Amshi: Kowag g aka Ali ɗan Ali ya ƙaru.

 : In yac ce yana sonka shi ke nan,

 : Bai yada ɗaukan mutum ba ya yasai,

 :’Yandoto kai ad da halin mazan dauri,

 : Ba a saran mutum gun na jekada,

 : In yat tashi bai ba a hana mai,

 : Ba sarkin da a kai ba Maradun,

 : Bai ciyam man da haƙƙin jama’a ba.

 

 Yaro: Na yi lura dai Daudu na gane,

 : Abokin bahili bahili ne,

 : Abokin mai alheri,

 ‘Y/Amshi: Ba ya zama da ɗai bai yi hairi ba,

 Ga wani godogon bahwade,

 Raba shi da ahu ya ce jidali ne,

 Allas sa jidali ya kama shi,

Ya dace da hushi na saarki,

 Yak wan talatin babu sisi,

 Kuma babu tsimma na sisi ga kyasa tai.

Jagora : Shi adda dibara.

 

Jagora: Na Magaji ‘Yandoto,

‘Y/Amshi: Jikan Mamman,

 Na Alasan na Turaki mai gayya.

Jagora: Taka lafiya,x2

‘Y/Amshi: Ali ɗan Ali,x2

Jagora: Mai kayan faɗa,x2

‘Y/Amshi: Tarnaƙin gaba,x2

Jagora: Tofo na faɗin,x2

‘Y/Amshi: Babba ɗan babba,x2

Jagora: Goshin gulbi na Malam,

‘Y/Amshi: Uban Gandu kowaj ja da kai

 : Ya wuce da shi yanzu.

‘Y/Amshi: Yanzu!Yanzu!!

 

Jagora: Ali jan damisa kawo jat talaka,

‘Y/Amshi: Uban mai Damma zaki tsayayye.

 

Jagora: Shiri kowa bamban da bamban,

Sarkinmu ‘Yandoto yai kyau sarauta,

‘Y/Amshi: Ga wani bai yi kyawun sarauta ba,

Tundumi bai yi kyaweu da naɗi ba,

Ya yi mamu fuska tai kamar tsoro,

Hattara dai dai da idon jama’arka,

Kakka tsone su,

Wanga ɗan tsiko.

 

Yaro: Don samu muka waƙa ko can,

In ko yaz zan babu samu,

‘Y/Amshi: Sai mu bari mu huta mu dakanta,

Tun da kau ba salati ba ne,

Balle mu dage mu zan yin shi don gobe.

 

Yaro: Gizago ba ka da tsoro wandara,

Gamda’aren ‘Yanware tsayayye,

‘Y/Amshi: Gagara ƙaryana Amadu hattara,

Guru ba ka da daɗin taki,

Kowat takai sai yai raki,

Yanzu ka iske ɗinki a farcenai

 

Jagora: A kwashi tuwon sarki a taso,

‘Y/Amshi: Ana taƙama to daɗa an ciko taiɓa.

 

Jagora: Ana gani, sai nak kau da kaina,

‘Y/Amshi: Ba ni gaishe shi, don me? Bahili na,

In ka kwana salatil Fati,

Ba ni gaishe shi Mamman ya kabre ni.

 

Yaro: In ganin hanya ab bai da unhwani x2

‘Y/Amshi: In ka zo garai ba ka more mai, x2

Na rena burodi mai kumburin banza,

Na saye na gani bai yi abki ba,

Burodi mun gane cikinka iska ne.

 

Jagora: Mai Bodo da Gurbi da ‘Yardiddiba,x2

‘Y/Amshi: Ga tinjimin Ƙogo mai Unguwar Dodo,x2

 

Jagora: Mai Kwa-da-Ƙwabri da sabon-Hegin-Baza,

‘Y/Amshi: Mai Kabla da ‘Yanza da Mandaɓa.

 

Jagora: Duk makaɗan da at Tsahe na shahe,

 : Hab baƙi har ‘yan gida su duka,

‘Y/Amshi: Babu mai shirya waƙa kamat tawa.

 Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,

‘Y/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara man,

 : Inna ƙulla waƙa a ƙara man,

: Mu huɗu duk azanci gareb mu,

Shin a’a mutum guda za ya yarde mu.

 

Yaro: Toron giwa kake mai Garewa Alux2

‘Y/Amshi: Ba a hwaɗa ka, tilas a kauce ma x2

 

Yaro: Inda ka za ka zamanin yaƙi,

 : Da maza ba su ɗaukar rigimarka.

‘Y/Amshi: Ko mazaizai na farko na asali,

: Tun azal Ali ab ba su jimra ma.

 

Yaro: Kyawun ɗan sarki talatin,

 : Ɗan sarki duk yay yi sittin.

‘Y/Amshi: Bai gaji gidansu ba ta ɓace mai,

 : Sai biɗar jalli, ai gudun jakkai,

 : A samu na shan dawo, ka a lalace.

 

Yaro: Ahmadu Bello Abubakar mun yaba,x2

‘Y/Amshi: Da mnistocin gidan shawara,

: Sun ce, Tsahe an zaɓi sarkin da ya I ma iko,

:Aikin da sarki duk yas sa shi ya yi,

:Ga mota biyu gun na jekada,

:Ga ta sarki Alu ga ta yaranai, x2

:Jagora: Ko cikin birni ko cikin daji,x2

‘Y/Amshi: Ko da ganin Alu ka ga ikonai,x2

Yaro: Mu jirkita faifan ba da labarai,

:Ƙannenai da bayi da barwa,

:Y aba su ƙawa duka ta ishe su,

‘Y/Amshi: Mu ko masarta ya gyara kowa,

 Bai maishe mu hurin da kiɗa ba.

 

 Yaro: Batun kiɗi ko ba ku nan yi mukai,

:Kun karantar da mu, mun yi kidan baƙi,

:Mui wasulla, mun yi tayi,

:Yanzu ilmi mukai tun da mun sauka,

:In hwa waƙa ce duk mun,

:San yadda za mu ƙulla ta,

:In an ce mutum mai tujara ne,

:Sai ya haihwa ɗa mai tujaran nan.

:In an ce mutum gas hi samna ne,

:Sai ya haihwa samna haƙiƙan ne,

:In Allah Yaw wa mutum ƙwazo,

:Ya bar haihuwa ɗanai ya lalace,

:Tun da gado ne.

‘Y/Amshi: Mun gani tun ga ɗiyan masara,

:Abu goye kowa da gemunai.

 

Yaro: Ni na ci na kwan da mamaki,

:Na ga ɗan sarki mai baƙar rowa,

:Ko ka ce Allah Ya yi mai rabo.

‘Y/Amshi: Sai ya gintse maka ba ya tankawa

:Wanga aikin kaba ne hita zamba,

:Wanga aikin kaba bai sarauta ba,

:Kai wasu hwadawa akwai kyauta,

:Kai ji su wane an kwashe yallaɓai.

 

Yaro: Sun nuna hairai mun gode,

‘Y/Amshi: Alhaji Tambaya, Alhaji Mande,

:Sun zo Makka sun yi hawan Arfa,

:Sun yi kuɗi sun ko ci ribarsu,

:Koway yi mana kyauta don mu hwaɗi,

:Kullum yana ba mu kuɗɗin sayen gora,

:Sannan yana ba mu kuɗɗin sayen dussa,

:Sarkin Fawa na Tsahe ya kyauta.

 

Jagora: Na Magaji ‘Yandoto jikan Mamman,

‘Y/Amshi: Shi an na Alasan na Turaki mai fayya.

Jagora: Daudu Wakili nag ode,

:Ya taimaki ƙwairo mai turu,

‘Y/Amshi: Don ya ƙi barin larura ta kama ka.

Jagora: Alƙali nag ode mai,

:Ya taimaki ƙwairo mai turu,

‘Y/Amshi: Don ya ƙi barin larura ta kama ka.

Jagora: Hal Liman nag ode mai,

‘Y/Amshi: Ya taimaki ƙwairo mai turu,

:Don ya ƙi barin larura ta kama ka.

Jagora: Ham Musa nag ode mai,

:Ya taimaki ƙwairo mai turu,

‘Y/Amshi: Don ya ƙi barin larura ta kama ka.

Jagora: ‘Yanware nag ode mai,

:Ya taimaki ƙwairo mai turu,

‘Y/Amshi: Don ya ƙi barin larura ta kama ka.

Jagora: Sarkin Fada na Mamuda,

‘Y/Amshi: Kwanon tuwo shi y tsare man,

:Yarana shidda ni an na bakwai,

:In mun ka jera garai ba mu canye shi,

:Haka kan aka so Maifada,

:Alheri garai ga tsaron gaskiya,

:Ba ya son tsegumi ko kaɗan na,

:Bagobiri Kallamu gaskiyar Ali.

Dabarun Jawo Hankali a Wakar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Dankwairo Maradun

Post a Comment

0 Comments