Ticker

6/recent/ticker-posts

Matakan Malamai Da Jagororin Mutane Na Fuskantar Matsalolinsu

Takardar da aka gabatar a taron kammala karatu da malamai ƙarƙashin Ƙungiyar Izala, a Abuja ranar Jumu’a 21/02/2025 a babban ɗakin taron ta ƙarƙashin jagoranci Sheikh Bala Lau, Shugaban (JIBWIS) ta Ƙasa

MATAKAN MALAMAI DA JAGORORIN MUTANE NA FUSKANTAR MATSALOLINSU
(DUBA CIKIN BITA-DA-ƘULLIN TATTALIN ARZIKI DA ZAMANTAKEWAR AL’UMMA)

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza
Professor of Hausa Studies
Department of Nierian Languages
Usman Danfodiyo University, Sokoto
mabunza@yahoo.com/0803-431-6508

Gabatarwa

Addininmu sanannen addini ne a duniyar mutane na yau, da jiya da shekaranjiya da shekaranjiya ban da jiya. Manzon addininmu masanin duniyar da aka aiko shi a cikin ne, da wadda ta gabace shi, da wadda za ta biyo bayan ƙaurarsa. Don haka, a falsafar al’adun hatsunan mutane duniya ta kasu uku: A koyaushe rana ta fito sunan ranar “yau”. Idan ta faɗi sunan ranar “jiya”. Idan ba ta fito ba, sunan ranar “gobe”. Abin lura a nan shi ne, addininmu na Musulunci na jiya ne, da yau, da gobe. Ƙin miƙa wuya gare shi cikin ɗaya daga cikin ranakun nan uku ita ce ake cewa “bijirewa” wanda Musulunci ke cewa “ridda”. Yarda da shi a kowace rana shi ake cewa “miƙa wuya” wanda nassoshin ayoyin Alƙur’ani ke kiran masu shi: “”Yaa allaziina aamanuu…” Ke nan cikin muminai ake samun “malamai” kuma cikin muminai ake samun “shugabanni” wani ba su ba shi ne mabiyansu masu koyi da su. Don haka malamai da shugabanni kowace al’umma su ne makaman gyara al’umma da fuskantar duk wani abu da ke yi wa al’umma takin saƙa ga cigaban rayuwarsu. Ga yadda bincikena ya fuskanci taken takardata.

Shimfiɗa

Manufar wannan bincike fayyace wane ne malami ko waɗanne ne malamai. Wane ne shugaba? Mene ne dangantakar malamai da shugabannin al’umma wajen biyan buƙatar al’ummar da tsare ta ga abubuwan da ke kawo mata cikas? Matsalolin da ke yi wa tattalin arzikinmu da zamantakewarmu ɓannan ƙasarmu ta kasa cigaban da ya kamata ƙasa ta samu. Ke nan, in babu malami da shugabanni al’umma tsarin demokradiyya da mulkin soja ba su kasuwa a bangon ƙasa a kafa tsakakakkiyar ƙasa. Masana suna ganin babu ƙasar da za a ji sunanta in ba ta da malamai da shugabanni masu limancin mazaunanta dubi yadda adabin Hausawa na kimanin shekaru ɗari biyar ya tabbatar a bakin yara a fagen wasannin ɗare:

Jagora: Ko waj je Kano ya ga Maikano

 : Ya ga uwar cikin Maikano

 : Ni na je Kano na ga Maikano

 : Na ga uwar uwar cikin Miakano

: Hat tab ba ni bayi tara

: Ukku suna Kano

: Ukku na Daura

: Wasu ukku na Zariya

: Yar ƙaramursu an nan

: Tana luguden kutumar uban

: Wanda yay yi da ni

: Da maza da mata duka

: Ban da Sarakuna

: Ban da Malammai

: Bisa hankalina nike

: Ban da uwar cikina

: Da tah haife ni….

 Amshi: Yaro alo iye yara nanaye

: Anye! Iye nanaye.

Yadda addinin Musulunci ya girmama malamai da shugabanni hadda adabin Hausa ya girmama su. Tattalin arziki da zamantakewa malamai da shugabanni su ne jagora. Tabbas ayar Alƙur’ani ta ce: “Ku yi wa Allah biyayya ku yi wa AnnabinSa da shugabanninku”.

Wane Ne Malami?

Ga al’adar karatu maimaita wa mutum abin da ya sani shi ne karatu. A aƙidar Musulunci malami shi ne:

Mutumin da aka shaida da tsoron Allah bisa ga karatun da karantarwa da ya koya ga masana karatu da karantarwa. Aƙidar Musulunci ba ta nuna ƙwarewa ga rubutu wata babbar daraja ta zama malami ba domin Manzonmu da aka aiko gare mu fasahar harda da karatu yake da ba ta rubutu ba.

A aƙidar Musulunci malami ya kasance mai ilmin, sanin littafin Allah komai ya iya in Alƙur’ani bai zauna a kirjinsa da leɓensa ba, ba malami ba ne. A fannin ilmi na boko akwai waɗanda ake cewa malamai. A ƙa’idar karatun boko malami shi ne:

Wanda ya iya karatu da rubutu cikin harshen ‘yan Mulkin Mallaka. In ya iya karatu da rubutu cikin harshensa na gado ba malami ba ne sai ya san na Turawan Mallaka. Sanin addini saukakke ko na gargajiya a boko ba mallantaka ba ne.

Waɗannan malamai biyu zamanin da suke su ne ke riƙe da ragamar shugabantar mutanensu da karuwar duk wani gurɓata zai zo ga arzikin mutane da kyautata musu zamantakewarsu. A ɓangaren Musulunci da boko dole a tarar da malami mai fasahar hardace karatu da karanto shi. A fagen da suka saɓa wa juna shi ne zancen “rubutu”.

Wane Ne Shugaba?

A nahawu Hausa kalmar shugaba gaɓa uku take da su /shu/ga/ba/. Kalmar /shu/ tana nuni ga saka mabiya “shuru” ba za a ce komai sai abin da suka faɗa a saurara. Kalmar “gaba” tana nuni ga kasancewar gaba ga mutane ko su mutane su sa shi gaba. Ai daga nan aka samo: gabaci, magabaci, shugabanci, da sauransu a taƙaice mutum na kasancewa shguaban kansa na gidansa, unguwarsa, garinsa ko ƙasarsu. A duban masana zamantakewa cewa suka yi shugaba shi ne:

Wanda mutanensa suka aminta da ɗabi’unsa da halayensa da ƙoƙarinsa wajen karɓo haƙƙoƙinsu da ƙwato su da kare rayuwarsu. Kalmar “shugaba” ta riga kalmar “sarki” bayyana na al’adun mutane da ke bayyana a adabinsu. A al’adance shguaba dole ya kai ga shekarun cikakken hankali ya kuma kasance kuɓutacce ga manyan cutuka da halitta da ta saɓa wa magoyan bayansa.

Waiwaye

A wannan mataki muna son mu kalli matsayin malami da shguaba cikin mutanen da suke taru da su. Abin da ya kyautu a sani a nan shi ne:

i. Tun gabanin saukakkun addinai a duniyar mutane ƙwararrun masana a wani ɓangare na rayuwa su ke kan kujera irin ta malamai a yau.

ii. Shugabanni a al’adance zaɓen mutane ne ko gadon abin da suka zaɓa ya shiga gaba da ayyukansu.

iii. A yau, malamai addini da ilmin sana’a suke jagora, su kuwa shugabanni siyasar zamantakewa suke jagora.

iv. A kan haka za mu ce da malamai da shugabanni suke riƙe da mutane a yau, kuma su ke da ikon sa baki a kan buƙatun mutanensu ga gwannatin siyasa ko ta soja ko ta gauraye-gauraye.

v. Waɗannan hujjoji sun nuna kowace irin matsala ta taso wa mutane a kowane irin lokaci malamai da shugabannin mutane su ke da bakin maganar a yi ko a daina ko a yi hattara ko a sake lale.

Mece ce Babbar Matsalar Mutane?

Ba abin mamaki ba ne kowa ya kawo matsalolin da ya sani daban-daban kuma a samu wani wuri an yi canjaras wani wuri in saɓa wa juna. Tabbas duk wani malami da zai jawo mutane zuwa ga kusantar karatunsa ko makarantarsa ya fahimci matsalolin waɗanda yake yi wa karatu. Haka kuma, babu wani mai mulki da zai ci nasarar shugabantar mutanensa face ya fahimci wasu matsalolinsu da yadda za a bi a shawo kansu. Gaskiya matslaolin mutane ba su ƙyarguwa sai dai a lisafa abin da aka gani ko aka ji. Duk da haka masana falsafar rayuwa sun ce Arziki da Tattalinsa ita ce babbar magana. Da malamai da shugabanci al’ummomi su sani matsalar da ke cikin tattalin arziki ita ce matsalar “samu” da “rashi”. Samu daga ginuwar arziki yake, rashi kuwa daga rushewar arziki yake, a nemo hanyoyin dahowarsa. Idan muka dubi abubuwan da ke aukuwa cikin ƙasarmu a yau na hargitsi, satan mutane, ta’addanci, kashe-kashen mutane da ta shafi addini, da ƙabila, da yankin wurin zama, idan aka duba tushensu “rashi” wanda ake ce wa “tsiya”. A addinance an fito da hanyoyin yi wa tsiya tawaye waɗanda ta shafa su samu waraka daga gare ta. Ga yadda addinin Musulunci ya fito da hanyoyi na kare kawunan magoya bayansa. A addininance muna da:

i. Zakka

ii. Bashi

iii. Kyauta

iv. Gado

v. Sadaka

vi. Aro

vii. Taimako

viii. Rance

ix. Fansa

x. Wasiyya

A wannan ƙarni da muke cikin musamman idan aka dubi halin da Musulmin Nijeirya suke ciki babu wani abu da ya fi waɗannan abubuwa goma fito da tattalin arzikinmu. Za mu ga babbar hanyar da za ta taimaki mabuƙatanmu ba su wace waɗannan goma ba. Za a ga daga cikinsu biyu kowai ne dole (farilla) wato zakka da Gado. Su ma za mu ga Zakka:

i. Sai wanda dukiyarsa ta kai matsayin babbar dunikiya a zamanin da ake da ita.

ii. Waɗanda taka kai gare su ‘yan kaɗan ne cikin mu.

iii. Wasu masu karɓar ta ba su cancance ta ba, kuma ba a barin ba su, ba sa barin karɓa.

iv. Masu bayar da ita ba su ankaro cikin kurakuran masu raba musu ita ba ga mabuƙata.

v. Har yanzu Musulmin Nijeriya ba su da tabbataccen kwamiti na amintattu addilan masu rabon zakka ba.

A ƙa’idar tattalin arziki na Musulunci akwai gado. Rabon gado wani baba ne babba daga cikin babukan fiƙihun Musulunci wanda ya kalli tattalin arziki sosai. Gado doka ce ta rabon arzikin Musulmi wanda ya mutu ga ‘yan’uwansa na jini. Masu rabon ko ba su da gado a ciki a ba su wani abu na biya ga ayyukansu. Kai! Shari’a ta yarda hatta da kallon rabon (mabuƙata) a ‘yanmu wani abu. Yar matsalar a nan ita:

i. Matance nawa ke da dukiyar da za a raga wa magada?

ii. Dukiyar gado nawa za a arziki da ita? Wata ranar da aka raba ta wasu masu gado ke cinye ta.

iii. Dukiyar gado ‘yan’uwan magada ake ba ita.

iv. Waɗanda ba ‘yan’uwansa ba, ba su da rabo. Ke nan ‘yan uwansa kawai ke cin ta. Waɗanda ba ‘yan’uwansa ba fa? Mun ko san sun fi yawa a bangon duniya da garinsu da gidansu.

v. Daga cikin dukiyar gado wasiyya kawai ke shiga hannun waɗanda ba magada ba in an yi ta, in an yi wa magata ita akwai zantukan masana da yawa.

Bita

Idan muka cire Zakka da Gado za mu ga abubuwan da suka rage don ƙarfafa tattalin arziki ne ga waɗanda arzikinsu bai bunƙasa ba kamar bashi ga mai kasuwanci. Kyauta ga wanda ya yi hasara da ƙarfafa arzikin mai nema. Taimako domin ƙara ɗaukaka zumunta ta jini da addini. Rance domin a ƙara wa dukiyar mai nema ƙarfi. Fansa domin kuɓutar da wanda ke tsare da Wasiyya da mamaci ya yi ga wasu magada da wasu ayyuka ko wasu mutane. Babban abin kula a nan shi ne, idan malamai sun yi la’akari da matsalolin tattalin arziki suka sa shi gaba cikin koyarwarsu da karatunsu wasu matsalolin da ke damuwarmu musamman matsalolin:

1. Ta’addanci

2. Sata

3. Zanga-zanga

4. Cin hanci

5. Rashawa

6. Maguɗi

7. Zamba cikin aminci

8. Yaudara

9. Siddabaru

10. Sihiri

11. Tsafe-tsafe

12. Dabo

13. Caca

14. Kore

15. Luwaɗi

16. Zina

17. Shaye-shaye

18. Fashi

19. Ƙarya

20. Kashin kai

21. Juyin mulki

Idan muka yi nazarin waɗannan matsaloli da kyau za mu ga sun ƙunshi abubuwa uku manya. Na farko “rashi” wanda ya haifar da talauci da miyagun ɗabi’u. Na biyu buƙatar arziki a kasance cikin masu abu ba masu jiran abu ba. Na uku wadata, a kasance hanyar samun iko ko tara marasa a gidan mai samu.

Matakan Malamai na Gyara Matsaloli

A musulunce da an ce wa mutum “Malam” ya shiga cikin wani babban bagire na faɗa a saurara, a yarda, a yi koyi da kai. Babban matakan da malamai ya kamata su ɗauka su ne: Malami ya kasance mai karatu mai koyon karatu ga waɗanda suka fi shi karatu ya kasance maganganunsa sun dace da nassoshi tabbatattu. Ya tuba da fadanci in yana yi, ya nisanci fadanci in bai shiga ba:

1) Ya nisanci raba kan muminai wajen saka su a ɗariƙarsa ko ƙungiyarsa ko aƙidarsa ko halayyarsa.

2) Ya jawo muminai kusa gare shi ga abubuwan da aka ba shi sadaka, ko kyauta, ko zakka, ko agaji domin su sami ɗan abin sana’a ka da su tsunduma cikin fasicci da talaucin da ke haddasa saɓon Allah.

3) Ya kasance mai daɗin baki wurin isar da saƙon addini domin muminai su saurara su kama sanaoin yardaddu da za su fitar da su ga saɓon Allah. Ka da ya yi amfani salon maganarsa wajen fassara nassoshi domin son ransa ba.

4) Ya kawar da gaba ga komai idan gaskiya ta bayyana ga abin ko da ta saɓa wa ɗariƙasa da ƙungiyoyarsa ko aƙidarsa ko halayensa.

5) Ba haramun ba ne ya fi son wata ƙungiyar siyasa bisa ga wata. Duk da haka dole ya nisanci yin siyasa wajen tsinewa wata ƙungiya ko tozarta su, ko haramtar da wata a kan wata. Matsayin malami na jagora ya yi hattara da takaro gaba da ƙiyayya cikin masu saurarensa.

Shugabanni

Da malamai da shugabannin mutane duk ayyukansu suna kusa ga juna musamman na farfaɗo muna da tattalin arziki da zamantakewa, sai dai su shugabanni sun shiga cikin wani tsari da ya saɓa wa da malamai kamar haka:

1. Shugabanni iyakai gare su na iko/mulki ba irin na malamai da za a ce ko’ina kake nasu kake in ka saurari karatunsu ba.

2. Shugabanni wani lokaci gadonsa suke yi ko da ba su cika wasu halayya ba malami kuwa zaɓen ilmi ne sai an yi karatu ake iya yin sa.

3. Shugabanni akwai na ƙabila akwai na ƙasa akwia na sanaoi, malamai babu irin su a ciki. Ashe tattalin arzikinmu ya fi yin kusa ga shguabanninmu fiye da malamanmu.

Matakan Cika Gurbi

Matsalolin da ke damuwar ƙasarmu gaba ɗaya suna son a samu haɗin kan mutane uku: Na farko shguabanni, na biyu malamai na uku waɗanda ba su ba. Da malamai sun kula da irin matsayinsu ga mutane da gudunmuwarsu za a yi amfani, a tayar da komaɗan tattalin arzikinmu a faɗaɗa zamantakewarmu ƙasa ta ƙaru da arziki da tattalin arzuka mutanen da ke cikinta a ji su, a gan su, a girmama su. Manyan matakan cika gurbi ne su ne: A bi hanyoyin sama wa waɗanda suka yi karatu na kowace gurbi ayyukan sana’o’in da ke cetonsu.

1. A ɗebe ta’addancin siyasa da ƙabilanci da ɓangaranci a kafafe yaɗa labarai a ƙarƙashin kowane irin hali.

2. A tsame hannun matasa cikin ta’addancin siyasa maza da mata. A tabbata suna da abin yi kamar yadda ake yi a China da Germany da Japan da sauran ƙasashe na gari.

3. A ɗebe matasa masana masu wayo da ladabi cikin waƙe-waƙen siyasa. Haziƙƙai ne a sa su cikin manyan ayyukan hukuma ko a samo musu kamfanonin kore talauci a ƙasa.

Sakamakon Bincike

Babbar godiyarmu ga Allah da Ya lurar da wasu ƙungiyoyinmu na addini da zamantakewa cewa, mun fara ganin muna cikin matsalolin cigaba. Babban abin da na hango shi ne, in kowa ya fahinci matsalolin da ake icki, kuma kowa ya fahinci babu ɓangaren da ba su da hannu a ciki to hanyar cin nasara ta buɗe gare mu domin mun fahinci kurakuranmu mu gano yadda za a gyara su. Zancen wani adiibi gaskiya ne da yake cewa:

Jagora: Koz zaka bangon duniyar ga

: Yay yi bakwai ɗaya ya yi laifi

: Sai in bai da idanu babu baki

: Sai dai rahamar Allah

: In Shi nai muna

: Alhaji Gambo mai kalangu

: Ba dai wani aiki mai yawa ba.

Naɗewa

Tattalin arzikin  mutane duniya ya rataya ga shugabannin mutanen duniya. A duniyar zamaninmu shugabanni iri uku muke da su. Shugabannin gargajiya da addini da siyasa da ma’aikatan tsaro (sojoji) in ƙaddara ta turo su. Don haka abin da ya rage gare mu shi ne bin dokokin mahaliccinmu kai tsaye babu gudu babu ja da baya.

Matakan Malamai Da Jagororin Mutane Na Fuskantar Matsalolinsu

Post a Comment

0 Comments