Daga
Malam Zaharaddeen Ibrahim Kallah
Bayan wani gajeren rubutu da na yi a kan gasar gajerun labarai ta Bashir Othman Tofa da aka gudanar a Kano, na samu tambayoyi a kan yanayin da littattafan Hausa suke ciki, musamman na rashin ingantattun zarurrukan labarai da kyan bugu littattafai da rashin kyakkyawan tsarin kasuwancin su a Najeriya ta yadda za a yaɗa su a duniya?
Akwai waɗanda suke ganin su kansu marubutan ba su samu
gudunmawar da ta dace ba, inda sabbin marubuta ma ba sa samun kulawa da gata na
horon da ya kamata, kamar yadda takwarorinsu na Turanci suke samu.
Tabbas harshen Hausa yana da
miliyoyin al'umma, wanda idan aka yi amfani da ilimi da tsare-tsare masu kyau,
sannan aka zuba jari a cikin harkar za a samar da dubban makaranta. Duk kuwa da
barazana da ake samu daga kafofin sadarwa na zamani da na'ura mai ƙwaƙwalwa.
A halin da ake ciki a yanzu babu
wani ƙasaitatcen
kamfani a duniya da yake buga littattafan Hausa don kasuwanci. Ko rawar da
littattafan Hausa na wancan zamani suka taka ta samo asali ne daga gudunmawar
Turawan mulkin mallaka, da kamfanonin ɗab'i
na wancan lokaci.
Na yarda marubutan wannan zamani
tun daga 1980 zuwa yanzu sun bada babbar gudunmawa, musamman ta tabbatar da yin
rubuce-rubuce cikin harshen Hausa da yaɗa
shi a duniya. Amma rashin manyan kamfanonin ɗab'i
da wallafe-wallafe ya taka rawa wajen halin da rubuce-rubucen Hausar ke ciki.
Kamfanoni irin su Macmillan da
Heinemann da Longman ba sa kallon marubutan Hausa. Da yawansu suna ganin ba za
su samu ribar da ta kamata ba. Waɗannan
kamfanoni suna da ƙarfin jari da tsarin kasuwancin zamani, ta yadda za su tura
littattafansu ko'ina a faɗin
duniya.
Idan da irin waɗannan kamfanoni za su
rungumi marubutan Hausa, sannan a samar da abin da wasu ke kuka a kai na rashin
masu bada horo (mentorship), za a samu abin da ake so. Domin shi kamfani idan
yana son aikin marubuci zai tabbatar sai ya kai mizani da ake so a duniya.
Za su iya cimma haka ta hanyar
shirya taron sanin makamar aiki da haɗa
marubuci da edita da zai dinga bibiyar aikinsa. Kamar yadda Rupert East ya yi
wa Abubakar Imam a lokacin rubutun 'Magana Jari Ce' da wasu littattafai da ya
rubuta.
Amma me ake tsammani idan
marubuci shi ne zai kasance mai rubutawa, mai tace kayansa, sannan ya buga shi?
Bayan ya bugawa shi ne zai yaɗa
shi tare yin kasuwancin kayansa.
Sannan shi ne zai shirya
tarurruka tsakaninsa da makaranta don taimakawa wajen isar da abin da littafin
ya ƙunsa.
Sannan uwa-uba yin sharhin littafin da gabatar da tattaunawa a rubuce ko a
zahiri.
Duk waɗannan ba ƙananan ayyuka ba ne dake buƙatar
kuɗi da ƙwarewa
a kowanne ɓangaren da
na zayyano. To amma marubutan Hausa sun dogara ne wajen buga littattafansu da
kansu saboda rashin waɗannan
kamfanoni.
Ko ƙananan kamfanonin buga litattafai da muke
da su a Arewa, yawancinsu basu da banbanci da masu aikin buge-bugen takardu.
Domin ba za su iya buga littafin marubuci a tsarin da aka san shi a duniya ba.
Dole sai marubuci ya sauke musu kuɗin
aikin littafin, sannan da zarar sun buga za su miƙo masa kayansa.
Shi kansa ingancin bugu da ƙa'idodi
rubutu akwai rauni sosai a ciki. Wannan ya sa ko makarantun mu na gida ba sa
karɓar irin waɗannan littattafai, bare
kuma na ƙasashen
ƙetare.
Idan ana son samun cigaba mai ɗorewa sai an yi aiki tuƙuru.
Dole sai masu ruwa da tsaki a cikin harkar rubutun sun haɗa kan su. Duk wani da yake
da hanya ta samar da jari ko kamfanonin da za su saka jari sai ya shigo.
Ta haka ne za a iya karkato da
tunanin manyan kamfanonin ɗab'i
zuwa littattafan Hausa, ko kuma a samar da wasu da za su saka jari don ciyar da
hankar gaba.
Akwai kasuwa sosai a cikin
rubuce-rubucen Hausa. Amma harkar tana buƙatar a inganta, abin da Bature yake kira
'packaging'. A wannan zamani da ake da kafofin sadarwar zamani, akwai hanyoyi
sosai na yaɗawa da
tallata littattafai.
©
Zaharaddeen Ibrahim Kallah

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.