ZUCIYA, RUHI DA DAMTSEN ƘASAR HAUSA
Daga
Halima Ahmad
Matazu
Labarinmu, labari ne na waɗanda suka yi gwagwarmaya, kuma labarin sarakuna, malamai, da mayaƙa. Labari ne da ke dauke da shauki da radadin rayukan da suka shuɗe, da hasashen zamanninmu.
Kakanninmu ne, su ukun, tsaye kan wani tudu, a gabansu, idanuwansu na kintatar farfajiyar faɗin ƙasar Hausa.
Nana Asma’u, sanye da rigar alfarma da aka saka da zaren
ilimi. A gefenta, sarauniya Amina ta Zazzau, hasken idanuwanta tamkar kaifin
takobinta. Daurama, ce a dayan gefenta, murmushinta ya bayyana jeren
hakoranta farare tas,tamkar sassanyar, ruwan rijiyar Kusugu.
“Daga rijiyar mulkina.”
Ta faɗa
cikin tausasa murya. “Ruwan tushe ya gudana, iri wanda Hausa ta yadu, ta yi
yabanya a doron kasa!”
Asma’u ta gyada kai, muryarta tamkar busar sarewa.
“Yabanya da ta yadu cikin dausayin hikima, tamkar reshe mai
laushi wanda ke lanƙwasa ba tare da karyewa ba, ko saiwar tushe maras rauni wanda
ke riƙe
ƙasa.”
Amina, ta ja dogon numfashi, ta kuma girgiza mashin da ke
hannunta. “Ƙasar
da aka ƙera
a cikin wutar juriya,”
ta faɗa, muryarta tana
kugi, tamkar zugar makera. “Mu, ’ya’yanta, mun ɗanɗana zafin yaƙi, da ƙwaƙƙwaran
ƙuduri!”
Su duka suka dan yi jim, ba ka jin wani sauti, face nishin
da taurarin dake sararin samaniya ke yi.
Kowacen su, shaida ce ta wani fanni na ruhun kasar
Hausa. Tsaye suke sun dulmiya cikin tunanin abinda kowacen su ta gada.
“Nana Asma’u.” Daurama ta ce, muryarta ta a sanyaye.
“Kalamanki, kamar irin da iska ke watsawa, suna yin tushe a
nesa da kusa. Kina saƙa ilimi cikin waƙoƙi, gadon da aka saɓa a cikin gafaka.”
Nana Asma’u ta yi murmushi, ta ce, “Hikima, kamar iccen kuka
ce, tana girma da lokaci. Amma sakainar da ba komai ba za ta iya riƙe
ilimi ba. Ke, Daurama, kai ce tushe, rufin rumbu wanda ya ke dakon al’umma.”
Amina, ta yi wa tsinin mashin ta da ke ta sheki, kuri da
ido, ta kada baki cikin muryarta mai kama da tururin iskar hamada.
“Amma al’umma ba ta buƙatar labarai da addu’o’i kawai. Tana buƙatar garkuwa, da ƙwaƙƙwaran zuciya don kare
iyakokinta. Takobina ta yi magana a Zazzau, ita ta tabbatar da makomarmu a
fagen fama.”
Daurama ta dora hannunta a kafaɗar Amina, ta ce “Mashi ba tare da taswira ba
yakan yi yawo, Amina. Ƙarfinki garkuwa ne, amma ilimi yana jagorantar hannun da ke riƙe shi.”
Amina ta kuma Kallon Daurama, wani haske na fita daga
idanunta.
Nana Asma’u ta yi murmushi,
“Kalmomi kibau ne,
Amina, waɗanda suka fi
jifan mashi nisa. Suna iya gina gadoji a inda takubba suka bar tabo kawai.”
Nana Asma’u ta ƙara, “Ko da dai tunaninmu ya rarrabu, muna da alaƙa ɗaya, ƙarfin
da ya ƙi
iyaka. Mu uwaye ne, mayaƙa, kuma malamai, dukkan mu jigo daya ne a cikin tarihin kasar
Hausa.”
Dukkan su suka sake yin shiru, yayin da alfijir ya
fara keto sararin samaniya. Ko da yake tsawon ƙarnuka sun raba su, amma
sun yi tarayya da wata alaƙa da ba a iya gani, ƙarfi da juriya na matan kasar Hausa, da
tarihi ba zai manta su ba.
Daurama, wacce daga mulkinta kasar Hausa ta kafu, ta tuna
macijin da ya toshe jijiyar rayuwar al’ummarta.
Amina, sarauniyar jarumai, ta tuna yaƙe-yaƙen da
suka bar tabbuna da alhini.
Nana Asma’u, ta tuna sautin muryoyin ‘Yantarunta, da yaƙin da
aka yi da jahilci.
Amina ta sake kada baki ta ce, cikin murya tattausa. “Amma
nauyin rawani ya kai nauyi, haka zalika tafarkin sarauta tankame yake da kewa.”
Daurama ta kuma dafa hannun Amina. “Nauyin rawani yana da
nauyi,” ta ce a hankali, “amma sadaukarwar da muka yi, ita ta shimfiɗa hanyar makoma mai haske.”
Asma’u ta dafa dayar kafaɗar
Amina.
“Ko da tafarkin sarauniya ya kasance tankame da kewa, tafe
ta ke cikin doguwar inuwa,” ta ce. “Kuma a cikin wannan inuwar, wasu na iya
samun mafaka.”
Suka kuma yi wa bangon gabas zuru, a yayin da hasken rana ya
fara keto sararin samaniya. Ƙasar Hausa, ce baje a gabansu, kasa mai
dimbin tarihi da dakon nasararinsu. Biranen da suka ginu kamar duwatsu masu
daraja na hamada.
Daurama, idunawanta a kan tarin taurari masu nisa, ta sake
magana, muryarta cike da hikimar shekaru.
“Amma al’ada, kamar iskar hamada na iya canzawa. Masarautu
sun habaka, kasuwanci ya bunƙasa, ilimi ya bunkasa.”
Amina, ta ƙara da cewa, “An giggina ganuwowi, ba kawai na dutse ba, na ƙarfin
hali, da haɗin kai.”
Asma’u sautin muryarta a hankali kamar iskar da ke
kadawa da sanyin safiya. “Amma duk da haka, a cikin wannan kyakkyawan yanayi,
mun raya ilimi, muka saka tarbiya da zaren zinariya, muka ɗaga sautin muryoyin mu a
cikin waƙoki
waɗanda suka yi
hamayya da ƙarar
iskar jahilci.”
Iska mai daɗi
ya kada. Sarauniyoyin uku suka yi murmushi na fahimtar juna. Su ne zuciya, ruhi
da damtsen kasar Hausa.
Durama ta ɗaga
hannu. “Mu, sarauniyoyin ƙasar Hausa,”
ta furta, muryarta tana kugi da sabon ƙuduri, “ba a daure mu da sarƙoƙin abin da ya shuɗeba, mun rungumi sauyi, tare da kiyaye
gadonmu.
Amina da Asma’u suka gyada kai. Su ukun suka juya baya,
siffofinsu suka saje da hasken rana, tamkar gajimare a kan tsandauri.
Halima Ahmad Matazu
#RanarHausa2025
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.