Cite this article as: Bashir A. (2024). Koyar da Hausa a Matsayin Ginshiƙin Cigaban Al’umma: Taskar wasu Kundayen Digiri a Jami’ar Tarraya Gusau. Proceedings of International Conference on Rethinking Security through the lens of Humanities for Sustainable National Development Interdisciplinary Perspectives. Pp. 362-371.
KOYAR
DA HAUSA A MATSAYIN GINSHIƘIN CIGABAN AL’UMMA: TASKAR WASU KUNDAYEN DIGIRI A
JAMI’AR TARRAYA GUSAU
Na
Abdullahi
Bashir
Sashen
Koyar da Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau
Tsakure: An lura da cewa, yawancin al’umma musamman na
wannan zamani suna yi wa ɗalibai masu nazarin Hausa kallon waɗanda suka gaza ko
waɗanda ba su da wata makama a ƙarshen karatunsu. Irin wannan matsala ce takan
dakushe tunanin ɗaliban tare da zare masu lakka wajen ganin sun cimma burinsu
na kawo cigaban al’umma da ma ƙasa baki ɗaya. Wannan maƙala ta fito da irin
gudunmuwar da manyan makarantu da cibiyoyin ilimi suke bayarwa a fagen ilimi,
musamman ɓangaren bunƙasa harshen Hausa da al’adun Hausawa. Har ila yau, binciken
ya yi amfani da hanyar tattara bayanai ta duba wasu littattafai da kundayen
bincike da maƙalu da mujallu. Binciken ya gano yadda wasu ayyukan bincike da
aka gabatar a sashen Koyar da Harsuna da Al’adu na Jami’ar Tarayya Gusau suka
taimaka wajen bunƙasa rayuwar Hausawa a ɓangaren harshe da al’ada da adabi,
musamman a garin Gusau da kewaye. Domin kuwa, a lokacin gudanar da irin waɗannan
bincike-bincike, ɗalibai sukan ziyarci wasu masu sana’o’i da sauran ƙwararru
don samun bayanai a kan wani batu da ake son samar da wasu hanyoyi da za su
taimaka wajen warware wasu matsaloli, ko kuma da nufin cike wani giɓi da aka
bari a fagen nazari don bunƙasa rayuwar al’umma. Maƙalar ta bayar da shawarwari
ga hukumomin gwamnati da masu zaman kansu dangane da taimaka wa masu bincike a
fannoni daban-daban wajen kawo cigaban harshen Hausa da al’adunsu musamman ta
fuskar la’akari da cigaban zamani.
Fitulun Kalmomi: Bincike, Batu, Kundi, Digiri, Ɗalibi, Jami’a.
1.0 Gabatarwa
Wannan aiki ya yi
duba ne a kan yadda harshen Hausa ya
yi tasiri a kan zamantakewar Hausawa ta fuskar
koyar da shi a manyan makarantu, musamman Jami’o’i. Haka kuma, an ɗauki
Jami’ar Tarayya da ke Gusau ne a jihar Zamfara wajen ganin irin yadda koyar da
harshen na Hausa ya yi tasiri ga rayuwar al’umma, tare da kakkaɓo irin ayyukan da aka
taskace a sashen koyar da Harsuna da Ala’adu na wannan babbar Jami’a da aka
kafa a 2013 kuma suka fara gudanar da ayyukan karatu gadan-gadan a shekarar
2014, inda aka fara yaye Ɗalibai a shekarar 2018. An gudanar da wannan bincike ne domin a kawar da shakku tare da daƙile hanyar nan ta yin
zurmuguɗu ga wasu raggwayen Ɗalibai, sannan a zaburar da masu kishi da kuma
ƙaimi ko karsashin aiwatar da bincike ko nazari a kan Harshen Hausa da Al’ummar
Hausawa. Saboda haka, an yi
bayanin dalilin bincike, sannan an
kawo muhimmancin wannan bincike, sai farfajiyar bincike da gudunmawar bincike a cikin wannan babi na farko.
1.1
Dalilin Bincike
Dalilin da ya sa aka
gudanar da wannan bincike shi ne don a kawo yadda nazarin harshe da adabi da al’adun Hausawa
suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa da kuma canza ɗabi’un Hausawa da ma sauran masu nazari ta
fuskar cigaban ƙasa da kuma samun ilimi don gudanar
da kyakkyawar mu’amulla a tsakanin al’umma. Haka kuma, wannan bincike zai
taimaka wajen samun abin karatu musamman a wannan fanni na nazarin harshe da adabi da al’adu ta
hanyar yin nazari a kan yadda lamurra suke
tafiya tare da zamani, musamman a nan ƙasar Hausa tare da kwatanta yadda rayuwa
take cin karo da zamani, a inda akan samu harshen Hausa ya yi tasiri na kai
tsaye ko kaikaice ga wasu harsuna, wanda hakan yakan taimaka wa Hausa ta yi
naso ga wasu baƙin al’adu, har ma a dama da ita a cikin tsara, a wani lokaci ma
takan yi wa sa’annin nata fintinkau wajen bunƙasa da kuma cigaban zamani.
1.2
Manufar Bincike
Manufar
wannan bincike ita ce, fito da yadda ake yin aiki tuƙuru wajen samar da batu (topic) na kundayen digiri na farko a Sashen Koyar da Harsuna da Ala’adu, da ke Jami’ar Tarayya Gusau a jihar Zamfara. Don
a nuna yadda shi wannan aikin rubuta kundin bincike, yakan dogara ne daga sashe
zuwa sashe a matsayinsa na wani ɓangare
na cikamakon sharuɗɗan samun shaidar kammala
digiri na ɗaya (B.A. Hausa). A nuna yadda ake gano wata matsala ko wani giɓi a fagen
bincike, kafin daga bisani a bai wa ɗalibi dama domin gudanar da bincike.
Sannan a fito da matsaloli da akan fuskanta a yayin samar da take ko batu na
bincike, inda a wasu lokuta hakan yakan haddasa yin aikin da ba zai karɓu ba, musamman
wanda aka yi zurmuguɗɗu. Akan ci karo da kan labari daban, gangar jiki daban.
Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin fito da hanyoyin da ake bi wajen samar da batu daga
ɗalibai da kuma nuna irin tsarin da ake bi wajen duba ayyukan bincike, musamman
a fannonin da Malamai suka ƙware na harshe da adabi da al’ada tare da tabbatar
da su a kan tsari da kuma adana su a sashen da ake nazarin Hausa na wannan
Jami’a.
1.3
Farfajiyar Bincike
Wannan bincike zai taƙaita
ne a Jami’ar TarSayya da ke garin
Gusau da kewaye a jihar zamfara. Don haka, wannan
aiki ya keɓanta ne kawai a kan taskace kundayen bincike na ilimi, na matakin
digiri na farko (B.A) da aka yi a
kan abin da ya shafi harshe, adabi da ala’adun Hausawa, musamman a sashen koyar
da Harsuna da Al’adu na Jami’ar daga 2018 zuwa 2021.
1.4 Muhimmancin Bincike
Muhimmancin wannan bincike ya haɗa da taimaka wa masu nazari
fahimtar yadda ake gudanar da bincike,
musamman wajen zaɓen batu (topic) wanda ya shafi Harshe ko Adabi ko Al’ada
a ƙasar Hausa. Sannan an nuna yadda ya kamata bincike ya kasance a wannan lokaci, ta hanyar yi
wa zamani kallon ƙwaƙwaf don a samar da cigaba ga al’umma.
Haka kuma, zai ƙara wa masu nazari ƙaimi domin yin nazari ko bincike a kan rayuwar al’ummar Hausawa da ma sauran al’ummomi, musamman ta fuskar zamantakewa
da sauran hanyoyin mu’amala a rayuwar ɗan’adam ta yau da kullum. Sannan, aikin
ya fito da dabaru da ma sauran hanyoyin neman ilimi da aikin yi, musamman
tsakanin matasan Hausawa maza da mata da maƙwabtansu ko baƙi ta fuskar
mu’amala.
1.5 Hanyoyin Gudanar da Bincike
Hanyoyin gudanar da wannan bincike sun haɗa da
manya da ƙananan hanyoyi, inda aka duba rubutattun kundaye a ɗakunan karatu
(libraries), tare da duba bugaggun littattafai da bugaggun maƙalu (mujallu) da
ma waɗanda ba bugaggu ba. Akwai kuma kundayen binciken da ɗalibai suka gabatar
a fanoni mabambanta na sashen koyar da harsuna da al’adu na jami’ar Tarayya
Gusau. Sannan an duba mujallu da maƙalu da kuma hira da masana ko ƙwararru, da magabata ta fuskar harshe da adabi
da ma al’adun Hausawa, musamman a manyan makarantu na gaba da sakandare.
2.0 Ma’anar Bincike
Bincike abu ne da ya shafi rayuwa wajen
tafiyar da kowane irin abu da ya shafi rayuwar al’uma ta yau da kullum. Duk da
haka, masana sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar kalmar bincike.
Kelinger (1973:21) ya bayyana cewa, “Bincike
wata tsararriyar hanya ce da ake bi ko yin amfani da ita don a gano wata
matsala da niyyar yin gyare-gyare ko yin bayanai masu gamsarwa a kan abin da
ake bincike a kai don cimma wata manufa ko ƙudurin da aka sa a gaba”. A wani
ƙaulin kuwa, an bayyana bincike da cewa, shi ne matakin
kai wa ga ingantacciyar mafita ko samar da ingantacciyar hanya wajen warware
wata matsala ta hanyar bin wani tsari daidaitacce kuma ƙayyadajje da yakan
bayar da dama a fitar da tsari tare da yin sharhi a kan wasu muhimman bayanai
(Osuala, 2005). Babu wata al’umma a doron ƙasa da za ta rasa
kalmar ‘bincike’ da dabarun gudanar da shi a cikin taskokinta na adana
tunaninta (Bunza, 2017:1). Har ila yau, an bayyana binciken ilimi da cewa, wani
fage ne mai faɗin gaske wanda har kullum masana da manazarta suke ci gaba da
rubuce-rubuce game da lamura daban-daban da suka shafe shi (Sani da Kurawa,
2023:256). A yayin da Maikwari da Ƙaura (2024:202) suka bayyana bincike a
matsayin “wani tsararren tafarki ne da ake amfani da shi domin shawo kan wata
matsala da niyyar ilmantarwa a cikin al’umma”.
A nan, za a iya cewa, bincike yana nufin neman
sani na ilimi a kan wani abu da a da ba a san shi ba, ko lalubo wata hanya don
samun mafita a kan abin da ya gagari kundila wajen warware shi. Haka kuma, bincike yakan iya ɗaukar ma’anar bin diddigi
ko ƙalailaita a kan wani fage na ilimi da nufin kawo hanyoyi, muhimmanci da
kuma illoli dangane da wani batu na musamman da aka ware domin a gudanar da
binciken a kansa da nufin samar da sakamakon da zai kore shakku ta dogaro da
nagartattun hujjoji.
2.1 Ire-iren Bincike
Akwai ire-iren bincike da kuma hanyoyin da
akan bi wajen gudanar da shi a fagen nazari da ma sauran hanyoyi don cimma wani
ƙuduri da aka sanya a gaba wajen ganin an fito da wani sahihin sakamako wanda
al’umma za ta yi na’am da shi, daga nan har a yi ƙoƙarin ɗora shi a wani mizani
na musamman don amfanin al’umma baki ɗaya.
a – Bincike na Ilimi
b – Binciken Ƙwanƙwancewa a fagen Kimiyya
c – Binciken ƙwaƙwaf a farfajiyar Tsaro
d – Binciken fashin-baƙin Masana
e – Binciken Auna Harshe, Adabi da Al’ada
2.2 Bincike na Ilimi
Binciken ilimi yana
buƙatar sadaukar da kai da ɗawainiyar adalcin ilimi. Don haka ake buƙatar ɗalibin
ilimi ya fake amanar ilimi kuma ya tabbatar ya ƙyallaro ayyuka masu ma’ana na
ma’abota ilimi domin ya yi wa bincikensa babban turke (Bunza, 2017). Haka kuma,
yana da kyau mai yin bincike da ya yi la’akari da waɗannan muhimman abubuwa da
aka kawo a (Bunza, 2017:17) domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu a yayin gudanar
da aikin bincike mai inganci. An ce, “Waiwaye Adon Tafiya” kuma "Mai Nema
Yana tare da Samu.” A nan, ana bayni ne a kan yadda wasu manazarta sukan nuna
halin ko-in-kula wajen tabbatr da ingancin ayyukan da sukan dub aa lokacin
gudanar da bincikensu, musamman a fagen ilimi, inda mutane ke tsammanin
ingantattu kma sahihan bayani da za iya dogara da su don kafa hujja a lokacin
warware wata matsala da ta shafi rayuwar al’umma. Masana a fannoni da dama sun
yi abin a zo a ga ni, a kan dabaru da hanyoyin gudanar da bincike.
3.0 Taƙaitaccen Tarihin Garin Gusau
Garin Gusau, ya kasance ɗaya daga
cikin manyan garuruwan ƙasar Hausa da aka kafa tun bayan jihadin Shehu Usmanu
Ɗanfodiyo a 1811, a inda aka taso daga tsohon mazaunin garin da ke ‘Yandoto a
1806 a karƙashin Malam Sambo Ɗan Ashafa wanda ya kasance ɗaya daga cikin
almajiran Shehu (Gusau, S.M. (2015). Garin Gusau yana ɗaya daga
cikin manyan garuruwan tsohuwar jihar Sakkwato kafin daga bisani ya zama babban
birinin jihar Zamfara da aka ƙirƙiro a shekarar 1996. Kamar yadda kundin tarihi
na 1920 ya nuna, garin Gusau yana nan a kan titin Sakkwato zuwa Zariya, watau
kimanin kilomita 210 tsakaninsa da Sakkwato. Daga gabas garin ya yi iyaka da
jihar Katsina. A yayin fa ya yi iyaka da jihar Sakkwato daga yamma, sai kuma
daga Arewa inda ya yi iyaka da jihar Kaduna da kuma jihar Neja daga yamma duk
dai farfajiyar ƙasar Hausa. Bayan haka, gari ne da ke ɗauke da Hausawa da
Fulani waɗanda suka ƙware wajen harkokin noma da kiwo da kuma kasuwanci domin
dogaro da kai da kuma bunƙasar tattalin arzikin ƙasa, a inda Allah Ya albarkace
ta da manoma, makiyaya, maƙera, magina, makaɗa, masunta da sauransu. Haka kuma,
mutanen garin Gusau ba a bar su a baya ba wajen neman ilimin addini da ma na
zamani.
3.1 Tarihin Kafuwar Jami’ar Tarayya Gusau
An kafa wannan
Jami’a ne a ranar 18/02/2013, lokacin da Gwamnatin tsohon shugaban Ƙasar
Nijeriya , watau Dr. Goodluck Ebele Jonathan ta ƙirƙiro Jami’o’i goma sha biyu
(12) a faɗin kasar nan (www.fugusau.edu.ng/2023). Kuma
Jami’ar ta fara gudanar da aiki a shekarar karatu ta 2013/2014 bayan da ta samu
sahalewar hukumar kula da Jami’o’i ta ƙasa (NUC) bisa sharaɗin bin ingantaccen
tsarin karantarwa mafi ƙaranci na bayar da shaidar karatun digiri a jami’a
(BMAS) da sauran masu ruwa da tsaki, musamman ƙwararru da ke cikin al’umma.
Kuma an fara ne da kafa ɓangaren karatun share-fagen kimiyya (School of
Pre-Science Studies) da kuma sauran manyan tsangayoyi guda uku kamar haka:
1. Tsangayar Ilimi da
Fasahar Ɗan’adam (Faculty of Humanities & Education)
2. Tsangayar Kimiyya
(Faculty of Sciences)
3. Tsangayar Gudanarwa
da Zamantakewa (Faculty of Management & Social Sciences)
Haka kuma, an fara
gudanar da dukkan waɗannan karatuttuka ne a mazauninta na wucin gadi da ke
ZACAS Gusau, kafin daga bisani ta dawo mazauninta na dindin da ke Sabon-Gida,
kusa da Kwatarkwashi a kan babban hanyar Sokoto Zuwa Zariya idan ka fita garin
Gusau. Jami’ar tana da faɗin murabba’in kilomita uku 3 da kuma tsawon kadada
shi ma na kilomita uku 3. Har ila yau, Jami’ar tana da ma’aikata kimanin dubu ɗaya
da ɗari ɗaya da tamanin da bakwai 1187 a ƙididdigar shekarar 2023, kuma a
ƙarƙashin wannan adadi akwai Malamai 299, sai kuma manyan mai’aikata waɗanda ba
masu koyarwa ba 481, da kuma 407 ƙananan ma’aikata. Sannan kuma, akwai
ma’aikatan wucin-gadi aƙalla 107 a fannoni daban daban na jam’ar. Idan muka
juya ta fuskar ɗalibai kimanin dubu 14,712 a shekarar karatu ta 2023.
Bugu da ƙari, a
lokacin gudanar da wannan bincike, wannan Jami’a tana da sassa 17, a inda akan
gudanar da harkokin karatu domin bayar da shaidar matrakin Digiri na ɗaya
(B.A/Bsc.) aƙalla 27 a ƙarƙashin tsangayoyi huɗu (4), kamar haka:
1. Tsangayar Fasahar
Ɗan’adam (Faculty of Humanities)
2. Tsangayar ilimi
(Faculty of Education)
3. Tsangayar Kimiyya
(Faculty of Sciences)
4. Tsangayar Gudanarwa
da Zamantakewa (Faculty of Management & Social Sciences)
Bayan haka, jami’ar
ta ɓullo da shirin gudanar da karatun bayar da shaidar Digiri na biyu da na uku
(M.A./Msc. & PhD.) domin kuwa har an buɗe tsangayar kula da karatun Babban
digiri na Biyu da na Uku (Postgraduate Studies) a ƙarƙashin jagorancin Marigayi
Furofesa Muhammad Lawal Mayanchi. Kuma shirye-shirye sun yi nisa wajen fara ɗaukar
darasi daga sababbin ɗalibai da aka ɗauka a wannan fanni a shekarar karatu da
ta ciki ta 2023/2024.
Har ila yau, an kawo
shirin bayar da shaidar karatun Difloma a ɓangagrori daban daban waɗanda a
yanzu haka akan gudanar a ranakun ƙarshen mako domin bayar da dama ga ma’aikata
don samun ƙarin girma da matasa masu son samun share fage ko ma ƙwarewa a
fannoni daban daban na rayuwa, a ƙarƙashin kulawar sashen tuntuɓa na Jami’a
(Consultancy Services).
A yayin da ake ci
gaba da ƙoƙarin ganin an ƙirƙiro wasu ƙarin tsangayoyi da sassa nan ba da daɗewa
ba, waɗanda a yanzu haka aiki ya yi nisa wajen ganin an tabbatar da
gine-ginensu da ke cikin harabar Jami’ar na dindindin kuma suna kan hanyar
kammaluwa tare da fatan ganin sun fara aiki da yardar Allah, waɗannan sababbin
tsangayoyi su ne kamar haka:
5. Tsangayar Fasahar
Ƙere-ƙere (Engineering)
6. Tsangayar Kimiyyar
Haɗa-Magunguna (Pharmaceutical Sciences)
7. Tsangayar Kimiyyar
Lafiya (College of Health Sciences)
Haka kuma, a
karƙashin waɗancan tsangayoyi masu aiki, akwai sassa a ƙarƙashinsu wanda kuma a
cikinta ne wannan sashe mai albarka na Harsuna da Al’adu ya fito kamar haka:
1. Tsangayar Fasahar
Ɗan’adam (Faculty of Humanities):
a. Sashen koyar da
Harsuna da Al’adu (Department of Languages & Cultures)
b. Sashen koyar da
Harkokin Addinin Musulunci (Department
of Islamic Studies)
c. Sashen koyar da
Harshen Ingilishi da Adabin Turawa (Department
of English &
Literature)
d. Sashen koyar da
Harshen Larabci (Department of Arabic Studies)
e. Sashen koyar da
Tarihi da Hulɗar Ƙasashen Ƙetare (Department of History & International
Studies)
Haƙiƙa, akan kafa
makaranta ne da nufin ilimantar da al’umma musamman na wannan bagire da aka
kafa ta, wannan ne ya sa al’ummar jihar Zamfara da ma maƙwabtanta da kuma
sauran ‘yan ƙasa sukan garzaya domin samun ilimi a wannan jami’a. Idan muka yi
duba da na tsanaki da kuma bibiyar tarihi da ma rubuce-rubucen masana za mu ga
cewa, tabbas Gusau da ma jihar Zamfara suna cikin farfajiyar ƙasar Hausa, a don
haka ba abin mamaki ne ba don a taras da tsarin koyar da kwas da nufin bayar da
shaidar digiri a kan Hausa ba. Samar da wannan ne ya sa ɗalibai sukan kwararo
domin samun wannan tabarraki da zai zama jagora a gare su da ma sauran al’umma
baki ɗaya. Kasancewar ana bayar da shaidar Digiri na ɗaya (B.A. Hausa) a sashen
koyar da Harsuna da Al’adu na wannan jami’a da ke Gusau, ya sa akan koyar da
kwas na musamman da yakan yi bayani a kan abin da ya shafi yadda akan gudanar
da bincike na ilimi da kuma dukkan irin hanyoyin da ya kamata a bi don ganin
“An fitar da A’i ga Rogo”, watau dai an koyar da ɗalibai hanyoyin gudanar da
binicike (Research Methods), inda a nan ne ɗalibi zai zaɓi wani fanni da yake
da sha’awar ganin ya ƙware a kai a fannoni daban-daban na rayuwa ta fuskar
ilimi a kan abin da ya karanta a tsawon lokacin karatunsa na jami’a.
3.2 Kundayen Digiri
Na Hausa A Jami’ar Tarayya Gusau daga 2018 – 2021
A sakamakon fara gudanar da karatu don bayar
da shaidar Digiri na Ɗaya a sashen koyar da Harsuna da Al’adu na wannan Jami’a
shekarar 2014, watau a zangon karatu na 2014/2015. Tsarin dokar karatun digirin
shi ne, an tanaji shekaru huɗu (4) ga ɗaliban da suka shigo ta hanyar JAMB, a
yayin da masu shaidar Diploma ko NCE sukan yi shekaru (3) kafin mallakar
Digirin. Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin tattaro ayyukan da aka gabatar a cikin
zangunan karatu uku kamar yadda aka yi bayani a farfajiyar wannan bincike
dangane da (Harshe da Adabi da Al’ada) kamar haka:
3.2.1 Kundayen Da Aka Samu A Shekarar
(2018/2019)
1.
Usman, Jafar (2018). Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙokin Siyasa
Na Kabiru Yahaya Kilasik. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu,
Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1520104005
2.
Labbo, Shafa’atu Salihu (2018). Hoton Mata A Karin Magana
(The Image of Women In Hausa Proverbs). B.A. Hausa, Sashen Koyar Da
Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1520104001
3.
Dogara, Umar Yahaya (2018). Ganuwar Gusau Da Ƙofofinta.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1410104007
4.
Murtala, Aminu (2018). Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1410104006
5.
Lawali, Abdurrahman (2018). Tsafe-Tsafen Maguzawa: Nazari
A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da
Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1520104002
6.
Kabiru, Sadiya (2018). Buki Salatin Mata: Rawar Mata A
Bukukuwan Garin Tsafe . B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1520104004
7.
Haruna, Bashiru (2018). Karin Harshen Zamfarci (Musamman
A Garin Gusau). B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1410104003
8.
Umar, Bilya (2018). Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan
Zamfara Jiya Da Yau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1410104001
9.
Aliyu, Sama’ila (2018). Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Baka
.B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1410104002
3.2.2 Kundayen Da Aka Samu A Shekarar
(2019/2020)
1.
S. Pawa, Abdulrashid (2019). Sarautar Fawa A Garin Gusau.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1510104001
2.
Abubakar, Amina (2019). Adashen Mata A Garin Gusau. B.A.
Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1620104005
3.
Kwatarkwashi, Nura Sani (2019). Auren Gargajiya A Garin
Kwatarkwashi. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1620104001
4.
Isyaku, Bashar (2019). Shaye-shaye A Garin Gusau. B.A.
Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1510104003
5.
Sani, Adamu (2019). Ingausar Yarbawa Da Hausawa A garin
Gusau, Jihar Zamfara. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1510104010
6.
Ibrahim, Aliyu Salisu (2019). Jibiyanci A gurbin Hausa.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1620104002
7.
Mustapha, Sa’idu (2019). Kalmomin Sana’ar Fawa A Garin
Faskari. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Lambar Ɗalibta: 1620104004
8.
Bala, Abdulrahman (2019). Taubasantakar Bazamfare Da
Badakkare. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1510104009
9.
Hassan, Nasiru (2019). Nazari A kan Jawabin Kama Aiki Na
Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa . B.A. Hausa, Sashen
Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1510104004
10.
Ibrahim, Ɗayyaba Mustapha (2019). Kwalliyar Matan Garin
Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Lambar Ɗalibta: 1510104005
11.
Ɗanlami, Hizbullahi (2019). Birkila Messin A Garin Gusau.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1620104003
12.
Hassan, Abubukar (2019). Faskare A Garin Faskari. B.A.
Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1510104007
3.2.1 Kundayen Da Aka Samu A Shekarar
(2020/2021)
1.
Tukur, Abdurrahaman (2020). Rukunin Hausar Masu Sana’ar
Waya A Garin Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1720104006
2.
Balarabe, Makiyyu (2020). Bikin Saukar Karatun Alƙur’ani
A Garin Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1720104001
3.
Bala, Abdulrashid (2020). Gala Sabon Salon Zaurance A
Garin Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104018
4.
Sani, M. (2020). Tasirin Magurzar Auduga A Garin Mayanci.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1610104010
5.
Rabi, Sarkin Zamfara (2020). Salon Kambamawa A Cikin Wasu
Waƙoƙin Kassu Zurmi. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104015
6.
Lawal, A.Tijjani (2020). Kokawa A Ƙasar Katsina Ko Wasa.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1610104021
7.
Mahmud, Ridwan (2020). Sana’ar Kwari (Fasa Dutse) A Wasu
Yankunan Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104024
8.
Ibrahim, Jamilu (2020). Rukunin Hausar ‘Yan Fursuna A
Garin Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1720104008
9.
Nafisa, Garba Ɗan’azumi (2020) Kutsen Baƙin Al’adu A
Kamun Amarya Jiya Da Yau A Garin Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da
Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1720104003
10.
Lauwali, Bashiru (2020). Sana’ar Gyartai, Cigabanta Da
Komabayanta A Garin Shinkafi. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu,
Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1720104015
11.
Binta, Gambo (2020). Laluben Al’adun Hausawa A Cikin Wasu
Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104005
12.
Isma’il, Abdurrashid (2021). Fassara A Gidan Rediyon
Tarayya ‘Pride FM’. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104019
13.
Hussaini, A.B. (2021). Sana’ar Tuggu A Ƙasar Maru. B.A.
Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1610104023
14.
Garba, M. Abdulwasiu (2021). Nazarin Ararrun Kalmomi Daga
Harshen Hausa Zuwa Harshen Burmanci. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da
Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104025
15.
Sa’idu, Abdulmalik (2021). Ƙagaggun Labarai A Kafafen
Sadar Da Zumunta A Faifan Nazari. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da
Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1720104002
16.
Sani, Kabiru (2021). Rayuwar Makaɗa Sani Kare ‘Yandoton
Daji Da Waƙoƙinsa. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104033
17.
Morai, Hussaini Yari (2021). Ɗanbalade Morai Da
Waƙoƙinsa. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya
Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104016
18.
Saudatu, Ɗalhatu (2021). Nazarin Jeren Ɗakin Amarya Jiya
Da Yau A Garin Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104004
19.
Tanimu, Kabiru (2021). Ingausar Harshen Dakkaranci Da
Hausa A Ƙasar Zuru. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104017
20.
Khadija, Ɗanbuba (2021). Nazari A Kan Auren Jari A Garin
Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Lambar Ɗalibta: 1610104029
21.
Mustapha, Mahadi. (2021). Yanayin Tsaro A Garin Gusau.
B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau. Lambar
Ɗalibta: 1610104007
22.
Muhammad, Yusif (2021). Nazari A Kan Hausar ‘Yan Ƙurƙura
A Kantin Kwari, Kano. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104022
23.
Muhammad, Umar (2021). Gudunmuwar Sana’ar Walda A Garin
Gusau. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Lambar Ɗalibta: 1610104001
24.
Yusuf, Sadam (2021). Nazari A Kan Itaciyar Kuka A
Bahaushiyar Al’ada. B.A. Hausa, Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau. Lambar Ɗalibta: 1610104026
4.0 Sakamakon Bincike
Wannan bincike ya
haifar da ɗa mai ido domin kuwa, haƙiƙa ya fitar da jaki daga cikin duma, ganin
irin yadda zurmuguɗɗu ya yi yawa a fagen nazari dangane da ayyukan bincike.
Domin kuwa, an gano hanyoyin da ake bi wjen samar da batu ga ɗalibai, wato ta
hanyar la’akari da ɓangarorin nazarin harshe guda uka da ake da su kamar haka:
i. Harshe ii. Adabi iii. Al’ada tare da yin duba a kan wani giɓi da aka bari a
cikin kowane fanni domin neman a cike shi da wani bincike na ilimi.
Samar da batu na binciken ilimi ya abu ne da ya danganta ga sashe
zuwa sashe na jami’ a da sauran manyan kwalejojin ilimi. A wannan sashe da ke
wannan jami’a, akan yi tsari ne a kan waɗannan abubuwa kamar haka:
1.
Mutum
ɗaya ne (Ɗalibi) yakan gudanar da bincike
2.
Ɗalibi
ne yakan bayar da batu ba sashe ba
3.
Akan gudanar da taro na malaman sashe a
ƙarƙashin jagorancin shugaban sashe ko wakilinsa domin amincewa da batu na
bincike wanda ɗalibai suka gabatar don su duƙufa wajen tattaro sahihan bayanai
da nufin bayar da gudunmuwa a fagen ilimi.
4.
Duba ayyukan ɗaliban ya danganta ne da fannin
da kowane malami ya ƙware (area of (specialization) kamar haka:
i.
Malaman
da ke da ƙwarewa a ɓangaren harshe, sukan duba ɗaliban da suka zaɓi wani batu
daga wannan fanni. Misali, akwai fannin nazarin ilimin kimiyyar harshe, wanda
ya ƙunshi; ilimin tsarin sauti, ilimin ƙirar kalma, ilimin ginin jumla, ilimin
ma’ana da sauran ɓangarori, musamman na gamayyar ilimin kimiyyar harshe da wasu
fannoni da sauransu.
ii.
Su
kuwa Malaman da suke da ƙwarewa a fannin nazarin adabi, sukan duba ayyukan ɗalibai
ne masu sha’awar yin nazari a wannan ɓangare na ilimin adabi.
iii.
A
yayin da Malaman sashe, masu ƙwarewa a fannin ala’adun Hausawa na gargajiya
suke duba ayyukan da suka shafi fannin don kwalliya ta biya kuɗin sabulu wajen ilimantar
da al’umma.
5.
Daga
ƙarshe, akan umurci ɗalibai da su kawo kwafin kundayen ayukansu tare da ɗanyen
kwafi (soft copy), inda akan adana su domin Nazari da Bincike a nan
gaba. Duk da cewa, ba sai an gayyace su don kare ƙudurin ba (defense)
bayan sun kammala.
A nan, wannan maƙala
ta yi ƙoƙari wajen gano adadin kundayen da aka samar tun daga shekarar karatu
ta farko (2018/2019) da aka fara rubuta kundin bincike na digiri na ɗaya (B.A.
Hausa) a sashen harsuna da al’adu da ke jami’ar tarayya Gusau, zuwa inda
binciken ya tsaya kamar haka:
|
LAMBA |
SHEKARA |
ADADI |
FANNI |
ADADI |
FANNI |
ADADI |
FANNI |
ADADI |
|
1. |
2018/2019 |
9 |
Harshe |
3 |
Adabi |
2 |
Al’ada |
4 |
|
2. |
2019/2020 |
12 |
Harshe |
3 |
Adabi |
0 |
Al’ada |
9 |
|
3. |
2020/2021 |
24 |
Harshe |
6 |
Adabi |
6 |
Al’ada |
13 |
|
|
JIMILLA |
45 |
|
12 |
|
8 |
|
26 |
Haƙiƙa wannan
jaddawali da ke sama ya nuna mana yadda wannan bincke ya fito da adadin
kundayen da aka samar a kowane fanni, inda fannin Al’ada yake da kaso mafi
rinjaye na kundaye 26, a yayin da fannin Harshe yake rufa masa baya da guda 12,
sai fannin Adabi mai adadin kundaye 8 kacal. Saboda haka, ana fatan kundayen da
aka buga a ɓangaren Al’ada za su taimaka wajen bunƙasa al’adun Hausawa na
duniya da na Arewa maso yamma da ke Nijeriya da sauran al’umma, musamman
mazauna garin Gusau da kewaye. Har ila yau, waɗannan kundaye arba’in da biyar
(45) da aka lalubo a rumbun ajiyar kayan karatu ‘Library’ sun taimaka
matuƙa wajen kauce wa yin daɓen-kwale dangane da maimaita ayyukan nazari da ma
aiwatar da satar fasaha ko zurmuguɗɗu (plagiarism) a lokacin gudanar da
bincike daga ɗalibai da sauran masu nazari, musamman a harshen Hausa a yau.
Bugu da ƙari, an gano yadda koyar da harshen Hausa yakan taimaka sosai wajen
ilimantar da al’umma a wannan Jami’a ta Tarayya da ke Gusau, wanda hakan ya
ƙara nuna muhimmancin Hausa da ma yadda ta kasance ba abin jefarwa ce ba, domin
kuwa, Hausa tana da ƙima a idon duniya, ba kamar yadda wasu marasa kishinta
suke yi mata kallo ba. An lura cewa, a lokacin gudanar da aikin bincike, wasu
daga cikin ɗalibai sukan ci karo da tarihin Hausa da Hausawa daga bakin masana
da tsofaffi a kan yadda Hausawa suke da hanyoyin tafiyar da rayuwarsu tun kafin
haɗuwarsu da sauran al’ummomi na duniya. Kuma hakan ya sa an ga yadda zamani ya
yi tasiri a kan wasu daga cikin al’adun Hausawa na gargajiya. Matasan Hausawa
sun samu ilimin tafiyar da rayuwa cikin sauƙi, kamar wajen samar da aikin yi da
koyon sana’o’i da inganta su, tare da girmama na gaba, da iya hulɗa ko mu‘amala
da yin alfahari da harshenmu na gado, da fito da kyawawan al’adu da ɗabi’un
Hausawa tare da wayar da kan al’umma dangane da hanyoyin cigaban rayuwa da
sauransu.
4.1 Shawarwari
i. Akwai buƙatar
malamai da ɗalibai su mayar da hankali wajen yin la’akari da tasirin zamani a
cikin rayuwar Hausawa, ta yadda za a samar da kundayen bincike da suka shafi
zamani ta hanyar ingata harshe da adabi da al’adun Hausawa.
ii. Haka kuma, zai yi
kyau idan hukumar Jami’a ta bayar da dama ga ɗaliban sauran sassa waɗanda sukan
nuna sha’awarsu a kan harshen Hausa wajen rubuta kundin bincike a kan wani batu
da zai bunƙasa harshen na Hausa a duniya.
iii. A rinƙa koyar da ɗalibai
tare da ba su shawarwari tun daga aji ɗaya a kan yadda ake samar da batu da ma
nuna masu hanyoyi da dabarun rubuta kundin bincike mai inganci.
iv. A yi ƙoƙari wajen
samar da wani jaddawali na sunayen kundayen da aka gabatar a wannan sashe, mai ɗauke
da sunaye da batutuwa da fanni da kuma shekarun da aka gabatar da su. Hakan zai
taimaka sosai wajen samar da ƙayatattun batutuwa tare da kauce wa satar fasaha
(zurmuguɗɗu).
v. A umurci ɗalibai,
su rinƙa aikawa da kundayensu ga shafukan ilimi na intanet domin al’ummu su
amfana, da nufin haɓaka harshe da al’adun Hausawa, da kuma bin sahun sauran
harsuna wajen shiga a dama da su ta fuskar cigaban zamani, a cikin shirin
duniya a tafin hannu (globalization).
vi. Zai yi kyau, idan
aka bai wa ɗalibai damar kare aikin binciken da suka rubuta da hannayensu don a
kawar da shakku game da zargin satar fasaha ko kuma dogaro ga wasu wajen rubuta
shi.
5.0 Naɗewa
Daga ƙarshe, wannan
takarda za ta zaburar da masu nazari a Hausa da ma sauran harsuna wajen ganin
an kauce wa hanyar nan ta yin zurmuguɗɗu a yayin gudanar da bincike. Sannan an
kawo taƙaitaccen tarihin jami’ar Tarayya Gusau, da yadda aka samar da kundayen
bincike a kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Babu ko tantama, hakan zai
ƙara kaimi ga masu nazari a nan gaba, domin kuwa, an gudanar da wannan bincike
a kan doron ilimi da ya shafi Harshe da Adabi da Al’ada ta hanyar auna su a
farfajiyar rayuwar al’umma ta yau da kullum. “Don gobe akan wanke Tukunya”.
Manazarta
Bunza, (2021). Suna Linzami Ne: Jagora ga Mai Rubuta
Matashiyar Binciken Maƙalu da Kundaye. Sashen Koyar da Harsuna, Sokoto:
Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A.M. (2017). Dabarun
Bincike (A Nazarin Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa). Zaria: ABU Press
Limited
Bunza, A.M. (2022).
PLAGIARISM: Zurmuguɗɗu, Fashin Baƙinsa da Fassarorin Kadadarsa. Takardar da
aka Gabatar a Darasin HAU 901 ‘Research Method’na Ajin Ɗaliban PhD. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben
Adabin Hausa (Sabon Tsari). Zariya: Amana Publishers Limited.
Eissa, A.I. (2014). Kwatanta Bukukuwan da suka shafi Addini na Mutanen Kano da Murzuk,
Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.
Funtuwa, A.I. da Gusau, S.M. (2010). Al’ada da Ɗabi’un
Hausawa da Fulani. Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S.M. (2015). Fulanin Zamfara Katsina Laka Da Tasirinsu A Daular
Sakkwato, Kano: Century Research and Publishing
Limited.
Ibrahim, M.S. (1984) ‘Tasirin Addinin Musulunci a kan
Al’adun Hausawa’, Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero Kano.
Kerlinger, F.N.
(1973). Foundations of Behavioural
Research. London: Holt-Rine hard and Witson.
Maikwari, H.U. & Ƙaura,
H.L. (2024). Mai Biɗa Ya Bar Jin Gajiya: Tsokaci a kan Bincike na Haƙiƙa a
Fagen Ilimin Zamani, A Cikin Tasambo
Journal of Language, Literature and Culture (JLLC). ISSN: Print
2757-6730 ISSN: Online 2782 - 8182, Volume 3, No. 2. DOI: 10.36349/tjllc.2024.v03i02.025
Muhammad, A. (2021). Nazari a Kan Sana’ar Yankan Farce a
Garin Gusau. Kundin Digiri na Ɗaya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Tarayya Gusau.
Newman, P. (1996). African Linguistic Biograpies, Hausa
and the Chadic Language Family: A Biography, Vol. 6. Kolni: Rudinyer Kopper
Verlag.
Osuala,
E.C. (2005). Introduction to Research Methodology. 3rd edition,
Onitsha: Africana First Publishers Limited.
Sani, A-U. & Kurawa, H.M. (2023). Kama da Wane ba ta
Wane: Matakan RairayeBincike da ba Bincike ba. A Cikin Nasara Journal of Humanities, (JLLC). ISSN: Print
1118-6887, Volume 2, No. 1&2.
Tsafe, B.A. da
Sadi, S.A. (2010). Hanyar Binciken Ilimi a Hausa. Gusau: Farin Batu
Press.
Zaruk, R.M., Kafin Hausa, A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar
Hanyar Nazarin Hausa don Ƙananan Makarantun Sakanadare, Littafi na Uku. Zariya: University Press.
www.fugusau.edu.ng / Information Unit: Federal
University Gusau, Zamfara State.
eduproject.ng.com ‘A History of Gusau in the Colonial Period’
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.