Cite this article as: Kabir J. (2024). Haɗakar Adabi da Tsaro: Tsokaci a Kan Hanyoyin Samar da Tsaro da Inganta Shi a Cikin Waƙoƙin Alkanci da Rarara. Proceedings of International Conference on Rethinking Security through the lens of Humanities for Sustainable National Development Interdisciplinary Perspectives. Pp. 350-361.
HAƊAKAR ADABI DA TSARO: TSOKACI A KAN
HANYOYIN SAMAR DA TSARO DA INGANTA SHI A CIKIN WAƘOƘIN ALKANCI DA RARARA
Na
Jamilu Kabir
Sashen Hausa, Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma,
Katsina Nijeriya
Tsakure: Tsaro yana nufin yanayi
ko halin kwanciyar hankali da lumana a cikin kowane lamari da ya shafi
zamantakewar rayuwar kowace al’umma ta yau da kullum da ke samar da natsuwa da
gamsuwa ba tare da barazana ko firgici ba. Sannan tsaro yana samuwa ne ta hanyar
tsara kyakkyawan tsari ga hukumomi da gwamnatoci da bin kyakkyawan tsari
dangane da abin da ya shafi bin doka da oda ga al’umma, sannan tsaro yana
samuwa kuma ya inganta idan aka samar da abinci da tattalin arziƙi da kuma kula
da rayuwar al’umma da dukiyoyinsu. Wannan takarda mai taken “Haɗakar Adabi da
Tsaro: Tsokaci a Kan Hanyoyin Samar da Tsaro da Inganta Shi a Cikin Waƙoƙin
Alkanci da Rarara”, manufarta a nan ita ce, bayyana matakai da hanyoyi da
shawarwari da dabaru da za a bi wajen samar da tsaro a Arewacin Nijeriya da
inganta shi daga baitocin fitattun waƙoƙin tsaro na waɗannan mawaƙa. An yi
amfani da wasu littattafai da kafafen sadarwa na zamani wurin tattara bayanan
da suka gina wannan bincike. Wannan aiki an ɗora shi a kan Ra’in Rubutacciyar Waƙar
Hausa (Theory of Appreciation on Hausa Written Poetry). Sannan a ƙarshe,
binciken ya gano cewa, ta hanyar yin amfani da adabi musamman waƙa ana iya samo
bakin zaren lamarin tsaro dangane da samuwar shi da kuma inganta shi.
Gabatarwa
Waƙa tana cikin daɗaɗɗun hanyoyin isar da
saƙo ga al’umma cikin gaggawa tun daga da har yanzu. Sannan mawaƙa na cikin
mutane masu azanci, hikima da baiwar isar da saƙo ga al’umma ta hanyar rera
waƙa take yanke ko rubutawa.
Duk da juyin zamani da aka samu, musamman a
ƙarni na 21 amma tasirin waƙa da mawaƙa bai dushe ba, har gobe, suna da rawar
takawa a cikin al’umma har a kai ga gaci. Idan har za a yi sauraro na basira, a
kuma yi amfani da shawarwarin da Bello Shehu Alkanci ya bayar a waƙarsa ta “Tsaro
a Arewacin Nijeriya da da Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) a
waƙarsa ta “Fulbe” tabbas haƙa za ta cimma ruwa dangane da samar da
tsaro da inganta shi.
Ma’anar Adabi a Hausa
Alfakhuriy (1971) Ya bayyana a ma’anar
“adabi” tun asalinta tana nufin talaawinul qaul wato jujjuya magana
ko sarrafa harshe. Ya ce da haka ne kalmar ta sami yaɗuwar
ma’ana zuwa “ƙawata zance” da kuma tarin labaran aka rubuta da salailai masu
armashi (Alfakhury, 1971:8)
Manna (1981) Ya bayyana kalmar “adabi” kalmar
suna ce da ke da saiwa kamar haka –adb mai ma’anar “ladabi”
ko abubuwan da suka ƙunshi ilimin zantukan hikimar ɗan’Adam idan kuma aka
faɗaɗa ma’anarta zuwa kamar haka -adiib. Tana nufin masani ko mai ilimin
zantukan hikimar ɗan Adam
CNHN (2006) Ta bayyana ma’anar “adabi”da
cewa,”fannin ilimi wanda ya ƙunshi labarai da waƙoƙin baka da rubutattatun
Wasan Kwaikwayo da al’adu da abubuwan fasaha da na hikima”
Ɗangambo (2007:1-2) ya bayyana kalmar adabi
da “Ladabi” ko “Horo” ko “fasaha ko “Liyafa” ko kuma “Ilimin sanin rayuwar
duniya; A Hausa kuwa, tana nufin “halin ɗa’a”, watau Ilimi da sanin fannonin
rayuwa da zantukan azancin masu hikima da sauransu.
Masana da dama sun bayyana fahimtarsu dangane
da ma’anar adabi , daga cikin su akwai ;
Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007) Sun kalli adabi
a matsanyin “wata hanya ce ta musamman wadda bil adam (mutum) yake bi domin
sadar da abubuwan da suka shafi rayuwarsa da ‘yan uwansa, abubuwan da yakan
sadar ɗin kuwa mafi yawansu abubuwa ne da sukan daɗaɗa masa rai, wato na
annashuwa ko suke munana zuciya `don nuna baƙin cikinsa da abin, wato a taƙaice
dai adabi yana nufin rayuwar ɗan’adam dukkanta”.
Ɗangambo (2007) Ya bayyana adabin Hausa shi
ne; “ilimin nau’o’in azanci da fasaha da sarrafa harshen da ya ƙunshi
ƙirƙirarrun fasahohin magana cikin tsarin waƙoƙi da labarai da tatsuniyoyi da
tarihi da hikimun iya sarrafa harshe irin su karin mgana da kacici- kacici da
barkwanci da ƙarangiya da dai sauransu”
Malumfashi(2019) Ya bayyana adabi da cewa,
“adabi wani abu ne da ake daukowa daga rayuwar al’umma sai a gina shi ko dai a
waƙa ko a zube ko kuma a wasan kwaikwayo ko makamancin haka”.
Ma’anar Waƙa a Hausa
Kamar yadda aka saba, an fara da ƙoƙarin gane
abin da kalmar waƙa take nufi ga mutumin da ya tashi a ƙasar Hausa,idan ka haɗu
da mutumin a kasuwa ko bakin titi ko a wani wuri na gargajiya ka tambaye shi
abin da ake nufi da waƙa da Hausa abin da zai iya faɗa maka bai wuce “yawan son
yi “ko” maimaita abu ɗaya ba shi ya sanya za ka ji mutum yana cewa, kullum ina
waƙar zan zo mu gaisa amma abin ya faskara. Ma’ana yana ta saƙar zuci na son
zuwa inda wancan aboki yake amma bai je ba, ke nan waƙar abu na nufin ka yi ta
kururuta batu ko jan batun a zuci na tsawon lokaci, amma ba tare da aikatawa.
A nan, idan aka natsu kuma aka yi nazarin
waƙa a zahiri, za a ga wani zance ne ko magana da ake ta ja har ta yi tsawon
gaske.
Waƙa a Ƙasar Hausa
Zaren tarihi na samuwar waƙa a ƙasar Hausa ya
zayyana cewa, akwai nau’o’in waƙoƙi kamar haka:
Waƙar gargajiya
Waƙa
ta zamani
Yahya (1984) Ya ce “waƙa maganar hikima ce da
ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu
kalmomi zaɓaɓɓu,tsararru kuma zaunannu”
Waƙar baka ita ce ta farko wadda ta fara
samuwa kuma mai daɗaɗɗen tarihi a rayuwar Bahaushe.
Ita ce wadda tun daga tunanin ƙirƙiro ta har zuwa shigarta kunnuwan masu
saurara ba a yi amfani da alƙami da takardar ba.Wato masaƙar wannan waƙa cikin
kai take.idan aka saƙa ta sai a fitar da ita zuwa ga jama’a ta amfani da kayan
kiɗa.(Yahya 1996).
Waƙar gargajiya wato waƙar baka daɗaɗɗiya ce
wadda aka fara ta tun lokaci daɗaɗɗe mai nisan gaske.Waƙa ta rayu tana daɗa
bunƙasa tana haɓaka har zuwa yau.(Gusau 2003).
Ɗangambo (2008) ya bayyana waƙa da cewa,
“Wani saƙo ne da aka gina shi a kan tsarriyar ƙa’ida ta baiti da ɗango da
rerawa da kari (bahari) da amsa-amo (ƙafiya) da sauran ƙa’idojin da suka shafi
daidaita kalmomi, zaɓensu da yin amfani da su cikin sigogin da ba lallai ne
haka suke a maganar baka ba”.
Ra’in Rubutacciyar Waƙar Hausa (Theory of
Appreciation on Hausa Written Poetry)
Ra’in Rubutacciyar Waƙa ko Mazhabar
Rubutacciyar Waƙa kamar yadda (Gusau 2015) ya kira shi. Ra’i ne da yake magana
a kan wasu hanyoyi ko matakai da ake bi wurin yin tsokaci ko sharhi ko nazarin
rubutacciyar waƙa. Wannan ra’i ya fara tsirowa a shekarar 1972, a sakamakon
fara samar da kalmomin nazarin waƙa rubutacciya da wasu manazarta suka yi. Amma
a shekarar 1975 Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo ya tattara ra’ayoyin masana da tasa
fahimtar sannan ya fitar da maƙala ta farko kan hanyar feɗe rubutacciyar waƙa wadda
ya kira “Gadon Feɗe Waƙa”. A shekarar 1981 kuma ya gabatar da “Ɗaurayar
Gadon Feɗe Waƙa” a taron Argungu wanda Hukumar Fasaha da Al’adun Gargajiya
ta jihar Sakkwato ta shirya (Gusau 2015)
Ɗangambo (1975,198, 2007) ya bibiyi wannan
ra’i cikin ayyukansa daban-daban da suka haɗa da:
- Gadon Feɗe Waƙa (Ɗangambo,
1975)
- Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa
(Ɗangambo, 1981)
- Rikiɗar Azanci: Siddabarun
Salo da Harshe Cikin “Tabarƙoƙo” Tahamisin Aliyu Ɗansidi (Ɗangambo,
1981)
- Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa
Sabon Tsari (Ɗangambo, 2007)
Mabiya wannan Ra’i da Ɗangambo ya assasa sun
haɗa da :
-Abdullahi Bayero Yahaya-Sakkwato
-Isa Mukhtar-Kano
-Aminu Lawal Auta-Kano
-Halima Abdulƙadir Ɗangambo-Kano
-Mustapha Shu’aibu-Kano da sauransu(Gusau,
2015)
Manufar Ra’i
Babbar manufar wannan ra’i ita ce fitar da
wasu fitattun hanyoyi domin nazari da fayyace rubutacciyar waƙar Hausa domin
fito da jigo/saƙo cikin sauƙi, ta hanyar kallon tarihin mawaƙi, dalilin rubuta
waƙa da fayyace jigo da sharhin baitoci da saursansu.
Dacewar Ra’i da Aikin
Tabbas wannan aiki ya dace da wannan ra’i,
domin kuwa a wannan aiki bayan an yi shimfiɗar aikin da bayanan da suka shafi
ma’anar adabi da waƙa da tsaro da rashin tsaro an kawo tarihin mawaƙan sannan
an fito da ma’anar wasu baitoci da aka nazarta tare da fayyace su domin biyan
buƙatar wannan aiki,wanda an yi amfani da hanyoyi da wasu daga cikin nazarin
rubutacciyar waƙa ta Hausa.
Ma’anar Tsaro
Yunusa (2023) ya ruwaito cewa, Horaby
(2010:1335) ya bayyana tsaro a matsayin “Wani mataki ne da ya ƙunshi kariya (ko
tsaro ga ƙasa ko wani gini ko wani mutum daga hari ko wani haɗari da Sauransu
(Yunusa, 2023).
Sannan ya sake ruwaito cewa, Musa (2017:5) ya
kalli kalmar tsaro (Security), inda yake cewa; “yanayi ne na kasancewar kuɓuta
da wani hari ko haɗari ko wata barazana”.
CNHN (2006:453) ya bayyana ma’anar tsaro,
amma ba kai tsaye ba a cikin ƙamusun, an umurci mai dubuwa ya koma ya dubi
kalmar “Tsara” inda a shafi na 452 na ƙamusun aka bayar da ma’anar tsara
(tsara, fi’ili) ko a ce (aikatau) da ‘Kare’ tare da bayar da misali: Allah ya
tsare shi. Ita kuma kalmar “kare” (Karee, fi’ili) ko a ce aikatau) inda aka
bayar da ma’anarta a shafi na (234) na ƙamusun a matsayin:
i. Yin katanga don asirta wani abu
ii. Tsare wani abu
iii. Tokare ko datse
Ita kuma kalmar ‘kariya’ (Kaariyaa, sutura,
mace) na nufin yin amfani da wani abu don kange wani abu (2006:235).
Daga wannan bayani ana iya fahimtar cewa,
tsaro na nufin ɗaukar matakin kariya daga faruwar wani abu, musamman maras kyau
ko maras daɗi.
Tsaro yana nufin kariya daga wata tsangwama
da barazana ga walwalar al’umma tare da bai wa al’umma damar gudanar da hulɗa
da zamantakewa cikin lumana (Garba 2022).
Har ila yau, tsaro yana nufin duk matakan
kariya da ƙasa take ɗauka domin kare ‘yan ƙasarta daga barazanar cikin gida da
ta waje tare da tabbatar da kyakkyawan yanayi da ‘yan ƙasa za su gudanar da
ingantacciyar hulɗa da nagartacciyar zamantakewa. Daga cikin hanyoyin tabbatar
da tsaro ko ingantaccen yanayin tsaro ga ‘yan ƙasa akwai: kiyaye rayukan ‘yan
ƙasa da dukiyoyinsu da ingantaccen tattalin arziƙi da kiyaye mutuncinsu da
addininsu da ƙabilarsu da sauransu (Garba, 2022).
Mene ne Rashin Tsaro
Rashin tsaro kishiyar tsaro ce, wato rashin
tsaro na nufin halin rashin aminci da ke sabbaba rashin zaman lafiya da lumana
da kwanciyar hankali a zamantakewar al’umma ko a ƙabilu ko garuruwa ko yankuna
ko ƙasa gaba ɗaya.
Rashin tsaro babban tasgaro ne da yake mayar
da ƙasa baya ta fuskar tattalin arziƙi da abinci da cigaban ƙasa mai ɗorewa ta
kowace irin fuska.
Rashin tsaro yakan samu mazauni na dindindin
a ƙasa sakamakon siyasantar ko ƙabilantar ko addinantar da harkar tsaro
musamman daga gwamnatoci da hukumomi da ƙungiyoyi da al’ummomin ɓangare ko
yankin ko ƙasa.
Kamar yadda masana suka tofa albarkacin
bakinsu dangane da tsaro, haka shi ma Bello Shehu Alkanci ya bayyana ma’anar
tsaro a waƙe a fahimtarsa, ga misali daga wani baiti. Ga abin da yake cewa:
Tsaro samar da kariya kan jama’a dukkansu,
Tsare musu rayuwarsu ne ko ko dukiyarsu,
Tsame su da lafiyarsu kan komai yan nufo su,
Tun daga kansu har gari da ƙasar haihuwarsu,
Taƙaice tsaro nufinsa ne niƙe son bayyanawa.
(Tsaro A Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci).
A wani baiti na cikin wannan waƙa, mawaƙin ya
bayyana fahimtarsa dangane da haƙiƙanin abin da ake kira tsaro, wato hanya ce
ta samar da kariya kan jama’a dukkansu ta hanyar tsare masu rayuwarsu da
lafiyarsu da dukiyarsu daga barazanar cutarwa a ko’ina suke. Wato kar a cutar
da su a gidajensu ko garuruwansu ko ƙasashensu, don su kasance cikin zaman
lafiya da kwanciyar hankali da nutsuwa da lumana.
Wane ne Bello Shehu Alkanci?
An haifi Bello Shehu Alkanci a garin Gusau ta
tsohuwar jihar Sakkwato, a shekarar 1978. Ya fara karatun Allo a unguwar
Alkanci da ke Sakkwato, daga nan ya shiga makarantar Firamare ta (Sultan Ward
Primary), ya wuce zuwa makarantar Sakandire ta (Sheik Abubakar Mahmoud Gummi
Memorial College Sokoto), daga nan kuwa ya shiga Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a
garin Sakkwato wadda ya kammala a shekarar (2008), inda ya karanci harshen
Hausa.
Tun yana ƙarami, Bello Shehu Alkanci ya tashi
da sha’awar karatu da rubutun waƙokin Hausa, wadda ya yi gadon haka daga
mahaifinsa, wato marigayi Malam Shehu Alkanci wanda Shahararren sha’iri ne,
kuma ya lashe gasannin rubutun waƙa sau da dama. Bello ya fara rubutawa tare da
rera waƙoƙin Hausa tun yana yaro ƙarami a shekarar 1992. Haka kuma, Bello tun
yana makarantar Sakandire ya fara shiga gasar rubuta waƙa, kuma yana zama
zakara musamman a gasar mushahidai na shi’a a wurare daban-daban.
A yanzu haka, Bello Shehu Alkanci yana zaune
a garin Talatar Mafara kuma yana da aure da ‘ya’ya bakwai.
Zamansa a garin Talatar Mafara ya faru ne
sanadiyyar rasuwar mahaifinsa marigayi Shehu Alkanci a shekarar 1984. Daga baya
sai ƙanin mahaifinsa ya ɗauko shi a matsayin ɗan riƙo, sai Talatar Mafara ta
zama garinsa na zamantakewa da aiwatar da rayuwarsa ta yau da kullum.
Wane ne Rarara?
Dauda Adamu Abdullahi Kahutu wanda aka fi
sani da (Rarara), an haife shi ne a ƙauyen Kahutu da ke cikin ƙaramar Hukumar
Ɗanja ta jihar Katsina a ranar 13 ga watan Satumba a shekarar 1986.
Mawaƙin ya shahara ne a fannin waƙoƙin siyasa
da kuma Sarakuna duk da yana taɓa wasu ɓangarorin daban, musamman na talla da
yabo da soyayya. Ko a ‘yan kwanakin nan, sai da ya yi waƙa a kan masu tunar
ƙwaranda na zamani wato ‘yan ‘mining/crypto’, bayan karatun alƙur’ani
mai zurfi da mawaƙin ya samu, kuma ya ɗauki a ƙalla shekaru 20 yana yin waƙa,
duk da asalinsa Bakatsine ne, amma a Kano ya tashi, kuma a nan yake rayuwarsa
har yanzu shi da iyalansa.
Wannan mawaƙi yana da sunaye na Inkiya ko
laƙabi da yake kiran kansa ko mutane suke kiran sa da su, daga ciki akwai:
Ø Jami’a
Ø Gonar waƙa
Ø Shugaban ƙasar mawaƙa
Ø Na Kahutu
Ø Rarara (Rayuwa Ra’ayin Kowa
daban)
Ø Ƙolo da sauran su.
Hanyoyin Samar Da Tsaro a Waƙar “Tsaro a
Arewacin Nijeriya” ta Bello Shehu Alkanci. da Dauda Adamu Abdullahi Kahutu
(Rarara).
A wannan bagire, za a fayyace bayanan da ke
cikin wasu baitoci na waƙoƙin waɗannan mawaƙa dangane da hanyoyin da za a bi a
samu tsaro. A wasu baitoci na waƙar, mawaƙin ya bayyana wasu daga cikin
hanyoyin da idan aka bi su za a samu tsaro. Daga ciki akwai:
a.Samar da Ilimi
Hanya ta farko da za a bi a samar da tsaro
shi ne, a samar da ilimi mai amfani kuma nagartacce ga al’umma. Ga misali daga
wannan baiti kamar haka:
Ku san ilimi shi ka sa a yi komai da haske,
Ko in babu ilimi gun jama’a to da sake,
Komai sai su aikata don neman su warke,
Kam in babu arbi ba boko wanga take,
Komai mai hakan ga zai yi ba tuntunawa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
A fahimtar mawaƙin, yana ganin cewa, rashin
ilimi na Arabi da na Boko yana cikin abin da ya samar da yanayi na rashin tsaro
musamman a arewacin Nijeriya. Wanda idan za a samar da ilimi na Islama da na
Boko a bisa kyakkyawan tsari da kyakkyawar karantarwa, to za a iya magance
wannan matsala.
b. Haɗaka
Hanya ta biyu da za a samar da tsaro shi ne,
ta hanyar haɗaka ta al’umma wato kowa ya sanya hannu a yi da shi. Saboda kowa
yana da gudummuwar da zai iya bayarwa, ba wai kawai a bar hukumomi ko gwamnati
da lamarin ba. Kasancewar masu azancin magana suna cewa, “idan dambu ya yi yawa
bai jin mai. Sannan hannu ɗaya baya ɗaukar jinka. Misali:
Kiran da nake da shi musamman kowa da kowa,
Kan harkar tsaro mu san nauyi ne na kowa,
Kowannenmu na da hanyar da yake iyawa,
Kar mu tsaya jiran hukuma haka bai isarwa,
Kowa zai yi nasa to sai a ga warwarewa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
A wani baitin kuma ga abin da yake cewa:
A faro tsaro cikin gida shi ne wajibinmu,
A rinƙa kula zamantakewarmu da ‘yan uwanmu,
A san haƙƙin maƙwabtaka kowace unguwarmu,
A rinƙa kula da sa ido duk baƙon cikinmu,
Abin da ya saɓa tarbiyya sai a yi tsawatarwa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Mawaƙin ya cigaba da cewa:
Hukumomi su sa ido domin tabbatarwa,
Haƙoƙin da ke wuyayensu su bar sakewa,
Hakimmai Sarakuna na da rawab bajewa,
Haka za malamai su zan wa’azantar da kowa,
Harkokin gari da ƙauye ba ƙuntatawa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
A wannan gaɓa mawaƙin yana ishara ne da cewa,
sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe, sannan kowa ya yi ƙoƙarin bayar da tasa gudummuwa
wajen samar da tsaro, sannan za a kai ga gaci. Idan kowane mai ruwa da tsaki ya
taka rawarsa, wato tun daga cikin gida a matakin iyaye da yayye a lura da hali
da tarbiyyar kowa, a kan abin da yake na ba daidai ba a tsawatar, a sauke
haƙƙin zumunci da na ‘yan uwa da maƙwabta, kar a ba shaiɗan kafa.
Sannan hukumomi su lura, kuma su sanya ido
sosai wajen motsin kowa, ta yadda za a hana wa bara-gurbi rawar gaban hantsi.
Sannan Sarakunan gargajiya a ba su haɗin-kai wurin tabbatar da sanin halaye da
mutanen da ke zaune a garuruwansu, tun daga Sarki da Hakimai da Magajin gari da
Mai Unguwa, kowa a ba shi dama, kuma a taimaka masa wurin tafiyar da sha’anin
mulki.
Sannan a ƙarfafi malamai su rinƙa yin wa’azi
a kan usulubi mai kyau babu son zuciya ko wariya ko ɓangaranci ko son shahara a
kan muhimmancin zaman lafiya da alfanunsa da kuma illar da ke tattare da tayar
da fitina a addinance. Idan aka yi haka, to za a samu tsaro, kuma za a inganta
shi.
c. Addu’a
Addu’a ita ce hanyar neman kariya da tsari
daga kowace irin musiba ko fitina daga wurin Allah Maɗaukakin Sarki. Ta hanyar
yin addu’a babu nasarar da ba a iya samu, kuma babu wata fitina da addu’a ba ta
iya ganin bayanta. Ga abin da yake cewa:
Mu tashi da gaske mui ta roƙon Allah Azimu,
Mu tuba gare shi tunda duk mun san
laifukanmu,
Mu bar zargin waɗansu laifi mun take namu,
Mu guji zaman kawai sana’o’i kar a bar mu,
Mu bar cuta da gulma ɓarna suke haddasawa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Addu’a tare da tuba da neman gafara dangane
da ayyukan saɓo ko laifukan da aka aikata, kuma ake kan aikatawa na cikin
hanyar samun tsaro a arewacin Nijeriya, saboda ƙa’ida ce ta addini duk faruwar
wani abu marar daɗi tushen hakan daga saɓo ne ko mai alaƙa da saɓo. Sannan sai
a rungumi sana’a ko kasuwanci ko ƙwadago domin dogaro da kai, saboda zaman
banza yana cikin abin da yake haifar da ɓarna da rashin tsaro a ƙasa.
d. Son Juna da Kyautata Alaƙa
Daga cikin hanyoyin da za a samar da tsaro
akwai son juna. Misali idan al’umma tana son junanta, to za ta zauna lafiya,
saboda kullum masoyi ƙaunarsa ake ƙara yi ba tsanarsa ba.
Ƙabilanci mu ya da shi kar mu bari ya zauna,
Ku mu nemo abin da zai ƙara kusanta juna,
Kamar wasa na al’adu da muke da juna,
Komai za ya sa mu ɗinke mu yi ihiwana,
Kamar aure da kasuwanci da zamantakewa.
(Tsaro
a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu Alkanci)
Idan aka bar nuna ƙabilanci wanda shi ne yake
sanya tsana da gaba da raina mutane, to za a so juna tun da daman duk al’umma
kayan Allah ne, babu wani fifiko tsakanin juna sai wanda ya fi wani bin umurnin
Allah da tsoransa.
Al’umma ta ci gaba da mutunta juna da soyayya
da wasanni na al’ada da ke samar da nishaɗi da danƙon zumunci, uwa uba ma, haɗa
jini ko zuriyya ɗaya ta fuskar aure, ba tare da wani ya ƙyamaci wani ba ko
wannan ƙabilar ta ƙyamaci wannan da tunanin wai ita ce babba ko sun fi daraja
ko asali, alhali ba haka abin yake ba ga duk mai hankali. Idan aka yi haka za a
samu tsaro ingantacce.
Shi kuwa Rarara ga abin da yake cewa:
Tun da duk ƙwarya ta fi so a kai ta
mazauninta,
Aboki na zaman jini a ƙyale uwa hanta,
Tun da Hausa Fulani ake kiran mu ku fuskanta,
Ka saita makaminka kar ka harbe mazauninka.
(Fulbe: Rarara)
Mawaƙin yana ganin cewa, a akyautata alaƙa ko
zamantakewa, saboda dai kamar yadda hanta da jini suka tare ba a raba su, haka
dangantaka da alaƙar al’ummar Hausawa da Fulani take, wato babu mai raba
Bahaushe da Bafulatani sai Allah. Ya kamata a dawo da son juna a tsakani da
kyautata alaƙa kar son zuciya ya sanya mutum ya yi wa ɗan uwansa illa saboda
wani abu na daban ko mummunan tunani ko makirci ko zugar wasu, kullum ana kashe
juna ana murna da hakan.
e. Gaskiya Da Adalci
Daga cikin hanyoyin da za a bi a samar da
tsaro shi ne a yi gaskiya da adalci musamman ga gwamnati. Misali ga abin da
mawaƙin yake cewa a wasu baitoci:
Gwamnati duk abin da za tai ta yi ɗin da
gaske,
Ga al’ummarta kar ta bar su suna koke-koke,
Gwamnoni President mu ji sun doka take,
Gamssshe da ba siyasa su haɗe su narke,
Ga tsaro ba mu son ana zancen adawa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya:
Bello Shehu Alkanci)
Kamar yadda kowa ya sani ne cewa, babu wani
ɗan ta’adda ko wasu ‘yan ta’adda da suka gagari gwamnati, amma duk lokacin da
aka zo sha’anin tsaro sai gwamnati ta ringa jan-ƙafa a kan mataki tana yi wa
abin riƙon sakainar kashi. Har ‘yan ƙasa su gane cewa, wasan kwaikwayo ake yi
da rayukan mutane kawai, ana salwantar da rayuwar bayin Allah, wasu na azurta
kansu daga jinin bayin Allah. Sannan wasu sun samu hanyar neman takarar cin
zaɓe saboda alƙawurran da suke yi idan an zaɓe su, za su magance matsalar, amma
da sun hau madafun iko sai a ji tsit.
Ƙaramin misali kafin a kashe Shekau, an yi
ƙarya da ƙarairayi ana cewa an kashe shi, shi kuma yana bayyana cewa yana nan
da rai.
Sannan Dogo Giɗe da Ɓalleri, an sha yin
wannan wasan kwaikwayon amma daga baya ta kasance ba a kashe su ɗin ba. Saboda
gwamnati ba da gaske take yi ba, har dai ‘yan ta’adda za su yi bidiyo a Tiktok su
saki, su karɓi kuɗin fansa ta hanyar asusun ajiya na banki, su kira waya,
sannan su yi amfani da jirgi marar matuƙi (drone) amma wai duk gwamnati ba ta
san inda suke ba.
Sannan
ya ƙara da cewa:
Jami’an tsaro a sanya idanu a kansu,
Jiya ba yau ba nasu haƙƙoƙi duk a ba su,
Jarummai a zaƙulo su ana ƙarfafa su,
Jaruntar a zan yaba ta ana karrama su,
Jama’a za su gamsu har ma su yi jinjinawa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Daga cikin aiki da gaske da gwamnati za ta yi
domin samar da tsaro shi ne ta kyautatawa jami’anta musamman waɗanda ake turawa
faɗa da ‘yan ta’adda, ta hanyar ba su duk haƙƙinsu a babin kyautatawa. Idan ba
a yi haka ba kuwa za a samu waɗanda za su karɓi kuɗi su taimaka wa ‘yan
ta’adda, kuma haka na faruwa. Wanda ya yi abin kirki a karrama shi domin ransa
da farin cikinsa da na iyalansa ne ya sadaukar wa ƙasa da shi.
A wani baitin kuma ya ce:
A rinƙa hukunta masu laifi kuma ko su waye,
Adalci a lura na sa komai ya yaye,
A guji zubar jini da sauti maraye,
A tallafi duk maraunata da na birni da ƙauye,
A ƙara shirin da masu halinmu ka agazawa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci).
Wato bayan gaskiya abin da zai tabbatar da
tsaro shi ne adalci, wato yin komai a bisa yadda ya dace, kowane ya yi laifi
talaka ne, sarki ne ko mai kuɗi a hukunta shi. Duk lokacin da aka kama mutum da
laifin ta’addanci ba a hukunta shi ba sakamakon alaƙa da hukuma ko manya a sama
ko jam’iyya, wannan zalunci ne kuma hakan na ƙara ta’azzara rashin tsaro. Haka
ƙin hukunta ɓarayin gwamnati da ke sace kuɗaɗen da idan aka yi amfani da su a
wasu ɓangarori zaman lafiya zai samu, wanda idan ana so a yi adalci, sai an
hana faruwar hakan sannan za a samu tsaro ingantacce.
Shi
ma Rarara yana da fahimtarsa daga cikin hanyoyin da za a bi a samar da tsaro da
inganta shi, shi ne a yi gaskiya da adalci. Ga abin da yake cewa a waƙarsa ta
Fulbe:
A kowane yare akwai na ka da na ka zubda,
Ba ma na cikin ƙasar ba har na wajen Boda,
Ɗakin kwananka kar a zo ka ga ka huda,
Idan laifin wane ne a je a biɗo shaida,
Ko a tantance kar ka je ka ƙona
makwancinka.
(Fulbe: Rarara)
A wannan baiti, yana ishara da a dinga yin
adalcin magana a bar yin kuɗin goro idan wani daga wata ƙabila ya yi laifi,
kamar yadda mutane ke cewa ai ƙabila kaza ne kawai yana ganin wannan rashin yin
adalci ne kuma yana ƙara ta’azzara matsalar tsaro. Gaskiya da adalci shi ne a
ajiye komai yadda ya dace kar a ce, “Ai Hausawa ne suka fara tsokanar Fulani ko
Hausawa ne na gari ke yin zina (Wa’iyyazu Billah!) da matan Fulani wai idan sun
kawo tallar nono a gari, saboda haka masu yin laifin wai Hausawa ne ba Fulani
ba ne tsantsa, wai ‘ya’yan Hausawa ne daga gari”. Wannan magana babu adalci da
son zaman lafiya a tattare da yin ta, duk da cewa, wurare da yawa mutane na yin
irin wannan maganganu. Ko kuma a ce, “Duk Bafillace ɓarawo ne, dole sai ya yi
sata, ko idan aka yi garkuwa da mata aka yi musu fyaɗe a ce ai dama kwartaye
ne, kwartanci a ruga ba wani abu ba ne”, Waɗannan zantuka duk yin su rashin
adalci ne. Adalci shi ne, a cikin kowace al’umma da ƙabila akwai masu munanan
halaye, kuma sukan yi ta’addanci na babu sani babu sabo. Daga cikin hanyar da
za a samu tsaro a kuma inganta shi, shi ne yin gaskiya da adalci a magana a kan
kowane mutum dangane da halayensa da ɗabi’unsa da mutuncinsa da sauransu.
Haka adalci ne a hukunta duk wanda ya yi
laifi, babu sani babu sabo. Haka kuma, yana cikin hanyoyin da za a samar da
tsaro a inganta shi. Ga abin da Rarara yake cewa a wani baiti:
Wanda yay ba daidai ba sai a kai shi cikin
loko,
Bahaushe Bafulatani akwai su cikin iko,
Kai da ma sauran yarukan a daina biri boko,
A tsaurara duk bincike a can a ga daidanka.
(Fulbe: Rarara)
Idan
aka ɗauki matakin adalci ga duk wani mai laifi kowane ne ba tare da kallon
yanki alaƙa ko kusanci da dangantaka ta ƙabila ko wani abu aka yi hukunci na
adalci, to tabbas za a samar da zaman lafiya ingantacce kuma mai ɗorewa a ƙasa
gaba ɗaya.
f. Sulhu
Daga
cikin hanyoyin da za a samar da tsaro a yi sulhu. Ga abin da mawaƙin ya ce:
A bar ƙofa ta sulhu gun neman kwaranga,
Amma ‘yan ta’adda in har sun shaya daga,
A durfafa su ko’ina suke birni da rugga,
A bar roƙon su shi ka sa su yi hwaɗi a tcaga,
A bar musu lallami yana sa musu jin ɗagawa.
A fahimtar mawaƙin yana ganin wanda ya shirya
tuba da barin aikin ta’addanci a bisa raɗin kansa, a karɓi tubansa, matuƙar ya
yi tuba ta gaskiya, a yi sulhu da shi domin ya koma nagartaccen mutum. Saboda
wanda ya yi tuba ta kirki ubangiji zai karɓi tubansa, matuƙar tubar ta cika
sharuɗɗan tuba. Amma sulhu da ake yi da sunan sasanci a lokacin da ɗan ta’adda
yake ganiyar ta’addancinsa kuma shi ne zai sanya sharaɗi, kuma gwamnati ta
karɓa wannan ba sulhu ba ne, domin duk lokacin da ya buƙaci kuɗi ko wani abu zai
koma ga ta’addacinsa tun da makamansa na a hannunsa.
Ko a yi sulhu tsakanin wanda yake ta’addanci
da wasu mutane ba da wanda aka zalunta ba aka yi wa ta’addanci. Bayan an kashe
wa mutum ahali an kwashe masa dukiya, ba a mayar masa da komai ba, yana ganin
dukiyarsa (Musamman Dabbobi) a hannun wani, ko yana ganin wanda ya kashe masa
ahali ya ci mutunci da keta alfarmar iyalinsa, sai a ce masa kar ya yi masa
magana an yi sulhu wai, tabbas wannan ba sasanci ba ne, ya fi dacewa da
shashanci. Amma idan aka yi sulhu na gaske tabbas tsaro zai samu, kuma zai
inganta.
Shi ma Rarara yana da fahimtar a bi a hankali
a yi lalama a yi sulhu, ga abin da yake ceawa:
‘Yan sanda hadda soja zana kirawoku,
Da ma ‘yan sakan wajenmu zaku ji sunanku,
D.S.S da Civil Defence ku zo a mazauninku,
Da duk ‘yan bangarmu sai ku sake salon taku,
Rigima ce ta cikin gida aradu ta doso ku,
Da ganganci zaka tai ka rusa mahaifarka.
(Fulbe: Rarara)
Mawaƙin yana ganin duk waɗannan rukunin
jami’an tsaro na gwamnati da masu zaman kansu, yayin tunkarar wannan matsala ta
tsaro a sanya natsuwa da hankali da ƙwarewa da lalama a magance matsalar ta
hanyar sulhu a wasu a wasu lokuta, ba kowa ne lokaci ya dace a yi amfani da
ƙarfin tuwo ko ƙarfin iko na makami ba, saboda rikici ne na ‘yan cikin gida
tsakanin Bahaushe da Bafullatani, idan ba a bi a hankali ba, za a yi ta ƙara
kwaɓa abin.
Illar Rashin Tsaro
Matuƙar babu wadataccen tsaro a yanki ko a
ƙasa tabbatar akwai babbar barazana, domin kuwa rashin tsaro ba ƙaramar illa
yake yi wa al’umma ta fuskar zaman lafiya da lumana da tattalin arziƙi da
mutunci da cigaba mai ɗorewa a ƙasa ba. Kuma matuƙar aka yi riƙon sakainar
kashi da lamarin tsaro, tabbas sai ya shafi kowa. Mun ga haka a cikin wasu
baitoci kamar haka:
Ba shiyar da za ka je ka ji lumui a zaune,
Boko Haram ake kiran mahara a can gabas ne,
Bandits masu garkuwa da mutane a nan ne,
Bambancinsu ba yawa duk ga kashe mutane,
Bindiga har bamabamai duk sun zo Arewa,
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Idan aka kalli wannan baiti mawaƙin yana
ishara ne da yadda matsalar tsaro ta mamaye duk yankunan da ke arewacin
Nijeriya. Wato babu inda ake zaune lafiya ƙalau ko dai akwai matsalar masu
tayar da ƙayar baya na Boko Haram da suka yi sansani a Arewa maso gabas, wato
musamman a jihar Borno. Ko kuma Ɓarayi ‘yan fashin daji da suka yi sansani a
Arewa maso yamma, musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da
sauransu.
A wani baitin ya ƙara bayyana yadda illar ta
cigaba da faɗaɗa, kuma take shafar kowa. Misali
Kai yau rayuwar mutum tamkar ran kiyashi,
Kan hanya da ƙauyuka har a gida a bishi,
Kidnapping da garkuwa da mutum ɗan uwanshi
Kuɗin fansa shi hankali nan zai ƙara tashi
Kui! Fyaɗe akai da mata wayyo! Arewa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Tabbas wannan mummunan yanayi da rashin tsaro
ya haifar da babbar barazana da illa ga duk al’ummar yankin arewa da ma ƙasa
baki ɗaya.
Ga ƙarin wasu misalan da suka ƙara fito da illar rashin tsaro ƙarara a
wasu baitoci:
In
mun lura yau abin nan ya shafi kowa,
In
police kake a yau an kashe polisawa,
In
ma soja ne da dama mun gan su gawa,
In
mulki Sarakuna an yi ta karkashewa,
In
ma ba ruwanka to babu wurin fakewa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Wani ƙarin misalin shi ne:
Ba wani janibin da bai koka rashin tsaro ba,
Ba wani ɗan Arewa bai kwana da fargaba ba,
Bambancin da ma muke so su ba su rarrabe ba,
Babu ruwansu ‘yan ta’adda ba su san da shi
ba,
Bakirisce kaza musulmi suka karkashewa.
(Tsaro a Arewacin Nijeriya: Bello Shehu
Alkanci)
Tabbas za a yarda da abin da mawaƙin ya
ambata a waɗannan baitoci dangane da yadda wannan yanayi na rashin tsaro ya
shafi kowane ɓangare da rukunin mutane a arewa. Jami’an tsaro daga kowane
ɓangare babu wanda ba a kashe ba, haka ‘Yan siyasa da Attajirai da Malamai da
Sarakuna, ballantana talakawa da kullum ne sai an kashe ko an yi wa matansu da
‘ya’yansu fyaɗe, ko an kama su an ajiye su tamkar bayi ana azabtar da su da
kowane irin nau’i na uƙuba.
Kammalawa
A cikin wannan takarda bayan an yi shimfiɗa
da kallon adabi da waƙa, an kawo batu a kan abin da ake kira tsaro da bayanansa
dangane da fahimtar masana da ƙamusu har ma da mawaƙa. Sannan an kalli abin da
ake kira rashin tsaro, sannan an kalli wasu hanyoyi da za a bi a samar da tsaro
tare da inganta shi daga wasu baitocin waƙoƙi, wato waƙar ‘Tsaro a Arewacin
Nijeriya’ ta Bello Shehu Alkanci. Waƙar da ta zama ta farko a cikin waƙoƙin
da aka gabatar kan gasar matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya daga Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo Sakkwato a Shekarar 2021. Sai kuma waƙar Fulbe Ta
Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara). Ita ce waƙar da ya yi a shekarar nan
(2024) kan jan hankali ga Fulani da Hausawa a zauna lafiya. A ƙarshe an kawo
misalan illar da rashin tsaro yake kawo wa arewacin Nijeriya.
Shawarwari
Wannan takarda ta kalli hanyoyin samar da
tsaro da inganta shi, sannan tana ba da shawara ga rukunin al’ummu kamar haka:
® Gwamnati ta yi adalci, ta
yi gaskiya a cikin kowane lamari, idan ta yi haka za a magance matsalar tsaro.
® Fulani da Hausawa, kowa ya
ji tsoron Allah a fitar da son zuciya da mugun tunani na jin kai ko fifiko ko
ƙabilanci, babu wanda ya fi wani ga Allah sai wanda ya fi biyayya da tsoran
Allah.
® Iyaye su tarbiyanci
‘ya’yansu da kyakkyawar tarbiyya su ciyar da su da halal su guji sakin ‘ya’ya
sakaka.
® Jami’an tsaro su yi aikinsu
bisa ga tsoran Allah da adalci da amana.
® Sarakunan gargajiya su yi
jagoranci na gari su haɗa kan al’umma da gaskiya.
® Malamai su faɗakar da
wa’azantar bisa gaskiya da yaɗa kalamai masu kyau cikin tafarkin tsafta.
® Jama’a su so juna, su zauna
da zuciya ɗaya, su yi addu’a. Idan aka bi waɗannan shawarwari za a samu.
Manazarta
Al Fakhuri, H.
(1971). Al Jadid Fil Adabil Arabiy. Lebanon: Darul Kitabul Labnaniy
Bunguɗu, U.M. (2019). Waƙa
Zancen Hikima Sabon Tsari. (Ed), Zaria: Ahmad Bello University Press Ltd.
CNHN (2006). Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Kano.
Ɗangambo, A. (2008). Ɗaurayar
Gadon Feɗe waƙa (Sabon Tsari). Kano:KDG Publishers)
Ɗangambo, A. (2011) Rabe-raben
Adabin Hausa Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa(Sabon Tsari).Kano:KDG
Publishers.
Garba, S.A (2022) Matakan
tabbatar da Tsaro A Gwamnatance. Ta Sambo Journal of Language, Literature And
Culture.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran
Nazarin Waƙar Baka. Kano:Fisbas Media Services.
Gusau, S.M. (2015). Mazhabobin
Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and
Publishing Ltd.
Horaby, A.S (2010). Oxford
Advance learners Dictionary, International Edition Oxford:Oxford University
Press.
Junaidu, I. Da Yar’aduwa,
T. (2007) Adabin Hausa A Kammale. Ibadan: Spectrum Books Ltd.
Malumfashi, I. (2019).
(ed) Labarin Hausa A Rubuce 1927-2018. Zaria: Ahmad
Bello University Press And Publishers.
Manna, M.A. (1981). Addalil:
Mu’jam Inkilzy-Arabiy, Arabic-English Dictionary Aɗɗaba’ul Awwal. Libya;
Almansha’atu al Sha’abiyya.
Muhammad, S.S.
(2019). Matakan Rubutacciyar Waƙar Hausa. Zaria: Ahmad Bello
University Press.
Sarbi, S.A. (2007). Nazarin
Waƙen Hausa. Kano: Samarib Publishers.
Sarkin Sudan, (2024). Matsalar
Tsaro A Arewacin Nijeriya. (ed). Sokoto: UDUS Press
Limited
Yahya, Y.I (1984). Hausa
A Rubuce. Zariya: NNPC
Yunusa, A. (2023). Matakan Tsaro A wasu Waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa Tubali. International Conference on Ibrahim Narambaɗa Tubali. Kano: Bayero University Press.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.