Ticker

6/recent/ticker-posts

Kanal Daudu Suleiman

Kanal Daudu Suleiman

ALLAH SWT YA GAFARTAWA KANAL DAUDU SULEIMAN, AMIN.

Ɗan Malam Suleiman, Suleiman ɗan Galadiman Kano Abdulkadir, Galadima Abdulkadir ɗan Sarkin Kano Abbas, Sarkin Kano Abbas ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo, an haifi Kanal Daudu Suleiman a shekarar 1942.

Ya shiga aikin Soja har ya kai muƙamin Kanal kafin ya yi ritaya. Bayan ritayarsa ne ya shiga harkokin siyasa a Jamhuriya ta biyu har ma ya nemi Jam'iyyar NPN ta tsayar dashi takarar Gwamnan Jihar Kano duk da yake haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

Ya daina harkokin siyasa ya shiga sabgar noma gadan-gadan har a wannan lokaci da Allah ya karb'i abinsa a ranar Asabar, 09/08 /2025 ya na da shekaru 83 a duniya.

Ya bar matar aure ɗaya Hajiya Gaji yar Galadiman Kano Alhaji Ahmad Tijjani Hashim ɗan Turaki Hashim ɗan Sarkin Kano Abbas ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo.

Ya bar 'ya'ya 8, 3 maza, 5 mata da ƙanwarsa Hajiya Sabuwa matar Marigayi Babban Jojin Nijeriya Dahiru Musdapher /Dahiru Mustapha da kuma sauran danginsa.

Dakta Mamman Shata Katsina ya yi masa waka mai amshi "Kanal Daudu Suleimanu".

Allah SWT ya jiƙan sa da rahama shi da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

9/08/2025.

Post a Comment

0 Comments