MAI MARTABA ABDULKADIR II: SARKIN KATSINAN GUSAU NA 16
An haifi Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello Ranar 1-12-1977. Bayan karatun Addinin Musulunci a wajen Malamai daban - daban a garuruwa daban daban ya kuma yi karatun zamani a Township Model Primary School, Gusau da GSSS, Gusau da GDSS Danturai, Gusau da GDSS B/Ruwa, Gusau da Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto da Biomedical College, Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Ahmadu Bello, Shika, Zaria daga shekarar 1985 zuwa shekarar 2013.
A lokacin wannan karatu nasa ya samu takardun shedar gama
karatun Firamare da karatun Karamar Sakandare dana babbar Sakandare da Karatun
Digirin farko a fannin Turanci da kuma Satifiket a fannin Injiniyancin kiyon lafiya.
Yayi aikin kula da rage cutar maleriya a Karamar Hukumar
Mulkin Talata Mafara da Asibitin King Fahd, Gusau da Babbar Asibitin Gusau da
Hukumar Kula da Asibitota/Asibotoci ta Jihar Zamfara da kuma Ma'aikatar Lafiya
ta Jihar Zamfara. Ya na da aure da kuma 'ya'ya.
An nad'a shi sarautar Bunun Gusau a shekarar 2017 matsayin
da yake rike dashi har zuwa ranar Talata 29/07 /2025 da aka tabbatar masa da
sarautar Sarkin Katsinan Gusau sanadiyar rasuwar mahaifinsa, Mai martaba Sarkin
Katsinan Gusau, Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR ranar 25/07 /2025.
Dan Sarkin Katsinan Gusau Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR wato
Sarki na 15 ne, Sarkin Katsinan Gusau Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR d'an K'ogo
/Kogo Bello Bello ne, K'ogo /Kogo Bello d'an Sarkin Katsinan Gusau na 6 Murtala
(1900-1916) ne, Sarki Murtala dan Sarkin Katsinan Gusau na 3 Muhammad Modibbo
(1867-1876) ne, Sarki Muhammadu Modibbo kuma d'an Sarkin Katsinan Gusau na
farko, Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa (1799-1827) ne.
A gefen mahaifiyarsa kuwa d'an Hajiya Jamila Alh. Aliyu ne.
Hajiya Jamila 'ya /d'iya ce ga mashahurin attajirin nan ne da aka yi a Birnin
Gusau, Jihar Zamfara Alhaji Aliyu Dango da aka fi sani da kinayar "Dango
d'an aljanna" ( zamu kawo dalilin kiran sa da wannan kinayar a nan gaba In
Shaa Allah).
Wannan matsayi da
Allah SWT ya bashi ya sa ake yi masa lak'abi da "Sarkin Katsinan Gusau
Abdulkadir II" domin kuwa an yi Sarkin Katsinan Gusau Abdulkadir I d'an
Sarkin Katsinan Gusau Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa wanda ya yi
sarauta daga shekarar 1827 zuwa 1867, kenan shi ne Sarkin Katsinan Gusau na
biyu domin shi ne ya gaji/gadi mahaifinsa Sarkin Katsinan Gusau na farko, Malam
Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa. Allah
ya jaddada masu rahama, amin.
Daga Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ya zuwa
yau anyi Sarakuna 16 a Gusau duk kuwa da yake ba dukan su ne suka fito daga
gidan sarautar Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ba.
Tsarin Sarakunan Gusau /Sarkin Katsinan Gusau :
1. Mal. Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa (1779-1827)
2. Mal. Abdulkadir I(1827-1867)
3. Mal. Muhammadu Modibbo (1867-1876)
4. Mal. Muhammadu Tub'uri (1876-1887)
5. Mal. Muhammadu Gid'e (1887-1900)
6. Mal. Muhammadu Murtala (1900-1916)
7. Mal. Muhammadu Dangidan (1916-1917)
8. Mal. Umaru Malam(1917-1929)
9. Mal. Muhammadu Mai'akwai(1929-1943)
10. Mal. Usman d'an Sama'ila (1943-1945)
11. Marafa Mal. Ibrahim (1945-1948)
12. Mal. Muhammadu S/Kudu(1948-1951)
13. Alh. Sulaimanu S/Kudu (1951-1984)
14. Alh. Muhammadu Kabir Danbaba(1984-2015)
15. Alh. Ibrahim Bello (2015-2025)
16. Alh. Abdulkadir II ( Juli 2025-)
Daga Sarki na 8, Malam Umaru Malam (1917-1929) zuwa Sarki na
13, wato Malam Sulaimanu S/Kudu (1951-1984) sune Sarakunan Gusau wadanda ba
daga gidan sarautar Mal. Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa suka fito ba. Sai a
shekarar 1984 lokacin da aka nad'a Marigayi Mai martaba Alhaji Muhammad Kabir
Danbaba sarauta ta dawo gidan Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ya zuwa
yau.
Allah SWT ya jaddada rahamarsa zuwa ga magabatanmu, ya yiwa
Sarkin Katsinan Gusau na 16, Alh. Abdulkadir Ibrahim Bello II jagora, ya sa mu
wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.
Daga Taskar:
Ho. Ibrahim Muhammad
Danmadamin Birnin Magaji
Jihar Zamfara,
Nijeriya
04/08/2025

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.