AJAMI A SAUƘAƘE
Daga
Farfesa Abdallah
Uba Adamu
(A duba shafinsa
na Facebook domin samun rubuce-rubuce masu kama da wannan)
Ba fitacce ba ne. Ban jin da yawa sun san shi, illa waɗanda yake mu’amala da su. Ni kai na ban san shi ba sai ta hanyar sadarwar zamani lokacin da ya lalubo ne domin sanar da irin yunƙurin da yake yi wanda ya yi daidai da nawa. Hasali, tun da na fara wannan yunƙurin, babu wanda ya taɓa nuna sha’awar karɓa daga waje na domin ci gaba da shi, sai yanzu. Kuma yunƙurin sa ya wuce nawa fiye da misali. Idan za a ce ni ne na ƙyasta ashanar yunƙurin, to shi ya ruruta wutar.
Sunan sa Abdullahi Abba Ɗalhatu.
A yanzu ya na ƙasar Brazil yana digiri na uku a fannin fasaha da ƙere-ƙere a
University of São
Paulo. Yau shekara guda kenan (dalilin wannan rubutun) da fara magana da shi,
wanda shi ya fara turo min da bayanin gabatarwa da kuma abin da yake tafe da
shi. Ban taɓa haɗuwa da abin da ya birge ni
a ƴan
shekarun nan, kamar abin da Abdullahi ya ke yi ba. Ya gama faranta min a
rayuwar boko, domin ya karɓi
fitilar da nake ƙoƙarin haskawa, ya ƙara haskenta – da kuɗin
sa, gumin sa, lokacin sa, basirar sa, kuma, kamar ni, ba a fannin sa – fiye da yadda nake zato.
Alhamdulillah. Ga tushen.
Tun 1996, a lokacin ina Tsangayar
Ilimi ta Jami’ar Bayero (Faculty of Education) na ke da tunanin yadda za a
canja aƙalar
ilimintar da Almajirain tsangayu a ƙasar Hausa. Waɗanda suka san ni da jimawa, sun da da wannan.
Na yi mu’amala da ƙungiyoyi sa kai da dama a kan wannan, taƙamaimai
Amurkawa ta USAID. Kullum damuwar ita ce “akwai yara fiye da miliyar shida wadanda ba sa zuwa
makaranta a Arewacin Najeriya.”
A duk lokacin da ake wannan maganar, ana maganar ‘Almajirai’
ne. Kullum a matsayin jahilai ake ganin su saboda ba sa makarantun boko. Kuma
tun kafin akai ga matsalar tsaro, jaridun mutanen kudancin Najeriya suka
dodontar da Almajirai da nuni da cewa ai daga cikin su ne a ke samun ƴan
boko haram. Sai da rigingimun ta’addanci
suka yi tsamari sannan aka juya akalar rashin zaman lafiya daga Almajirai zuwa
makiyaya.
Babbar manufata a wancan lokacin
(kuma har yanzu), ita ce gusar da tunanin cewa duk Almajiri jahili ne saboda bai yi karatun boko ba.
Yaron da zai ɗauki Ƙur’ani mai tsarki wanda babu
wani littafi kamar sa a duk halitta, ya rubuce shi, ya karance shi, sannan in
hali ya yi, ya haddace shi, sannan a kira shi jahili? Tabbas masu cewa
Almajirai jahilai ne, SU ne jahilan, saboda ba su san cewa tun 1349 aka kafa tushen ilimin Almajarai a ƙasar
Hausa ba. A lokacin mutanen su zigidir suke yawo a daji, ba gidaje, ba birane,
ba kasuwanni, ba cinikayya, sai ka ce dabbobi.
Ƙalubalen shi ne, ta ƙaƙa za a
juyar da akalar ilimi da basirar da Allah Ya bawa Almajirai ta yadda za ta dace
da zamani? Amsa ta ita ce, “Ajamancin
Ilimi” (Ajamization of
Knowledge). Da na fara tuntuɓar
mutane a kan wannan maudu’in, dariya waɗan
su suka yi – domin ba su ga dangantakar Ajami da ilimi ba. Wani ma – wanda ya
zama babban mutum daga baya – cewa ya yi da ni “yo kai da ka dame mu da wani
Ajami, meye amfanin sa?” Kaɗan
ne suka hango inda na nufa, kamar su Fatuhu Mustapha da Nasiru Wada Khalil, waɗanda suka zama malamai na a
fannin saboda tari da zurfin ilimin da suke da shi.
Kai, har a wani gagarumin taro a
Arewa House da aka yi a Maris 2003 tare manyan shehunanan malamai na lokacin na
yi kokarin jawo hankali a kan abun, aka banzantar da ni. Na jawo hankali da
rubutun da John Philips ya yi, mai suna “Spurious Arabic: Hausa and Colonial
Nigeria”, amma ko a jikin su. Philips ya nuna muhimmacin Ajami a tarihin ƙasar
Hausa. Ganin yadda aka banzantar da maganar – daga Malaman jami’a, zuwa Malaman addini da kuma jami’an gwamnati – sai na fara tunanin ko ni ne na yi batan hanya ne? Koma
in haƙura
ne?
Wata rana yawon neman kuɗin Laraba ya kai ni
Akwanga, a jihar Nasarawa. Na tsaya a wani gidan mai a wajen gari domin shan
man mota. Bayan mai zubawar ya gama, na biya shi. Zan shiga motar kenan, sai na
ga yana rubuta lissafin cinikin da aka yi a lokacin a wani littafin rubutu. Na
tsaya ina gani, sai na lura da Ajami ya ke rubutawa. Na rufe motar na hau
tattaunawa da shi. Ya nuna min sauran abubuwan – rubutu, saƙonni,
d.s. –duk da Ajami
yake yi. Sai wani haske ya fito min.
Tunda akwai Ajamawa kamar wannan,
to Ajami na nan a raye. Mu ne dai ƴan boko da ƴan zamani muke ƙyamar sa. Dalili? Ni a
nawa ganin, ba a son Almajirai su fahimci duniyar zamani kada su fara neman cin
gumin rayuwar su ma. Mun fi so mu bar su a wanke-wanke, aikace-aikace da kuma
leburanci, muna ta bautar da su, da sunan ai mu ƴan takarda ne, mun san abin da duniyar ta
ke ci. Wannan ba zata sabu ba, bindiga a ruwa. A lokacin na dawo gadangadan
zuwa binciken Ajami.
A take a nan Akwanga, na fitar da
tunanin Ajamization of Knowledge. Na dawo Kano, na shiga bincike. Kamar yadda
na ce, jagorori na – waɗanda
abin ya ba su mamaki ganin yadda na hikikaice – su ne Nasiru Wada Khalil da
Fatuhu Mustapha. Sai kuma Muhammad Auwal Ɗankumbotso.
Ba nan ne wurin bayar da
sakamakon duk binciken da na yi ba. Amma matakin farko shi ne gabatar da
Bakandamiyar Lacca (Inaugural Lecture). Na zama farfesa a 1997, saboda haka na ɗauki kusan shekaru biyar
ina nazari kafin in gabatar da laccar a ranar Afrilu 24, 2004. Amma mai ya biyo
baya – shiru ka ke ji kamar an aiki bawa garin su!
Gwiwa ta dai ba ta yi sanyi ba. A
tsaka-tsakin lokacin daga 2004, ilimi da mallakar kwamfuta ta yawaita. Sai na
canza akalar maudu’in – samar da haraffin Ajami a kwamfuta. Ta hanyar samun
haruffan boko a ka yawaitar da ilimi a Turai a 1440 wanda Johannes Gutenberg ya
yi. A nan, na san akwai haraffun Larabci a kwamfuta, amma duk Hafs ne. Ni, a
waje na, rubutun Larabcin Bahaushe Warsu ne. Saboda haka, in dai zaka yi wa
Bahaushe rubutu, ya karɓa
da hannu biyu, to Warsantar da shi.
A cikin binciken da na yi, na yi
karo da Mamoun Sakkal, Balaraben Amurka, kuma mai sana’ar ƙera
haruffan kwamfuta (font designer) a Seattle, jihar Washington da ke Amurka.
Muka fara magana a kan yadda zai ƙirƙiro min haruffan Warsh na Hausa. Na aika
masa da littattafai masu rubutun Warsu daga Kano. Bayan kusan shekaru tara ana
ta kai-wa-da-kawowa, ya ce a biya shi $50,000 (dala dubu hamsin). Na ce da shi,
“bissalam.” Wane ni?, inji kiyashi a
jirgi.
Da Allah (SWT) Ya ga zuciyar ta,
da farar niyyar ta, sai kawai Ya kai ni ga wani dandazon Kiristocin SIL
International, a Dallas, Texas, Amurka waɗanda
suka sadaukar da rayuwar su a kan nemo hanyar da za su Kiristantar da mutane ta
hanyar buga Bibul da harsunan mutanen. Hausawa, saboda taurin kan su wajen
kafewa akan addinin Musulunci, sai suka zama abin yunƙurawa na farko. SIL suka ɗauki nauyin wata mace mai
suna Becca Hirsbrunner Spalinger ta je Jami’ar Reading a Ingila inda ta yi
karatun digiri na biyu a fannin MATD (Masters in Art Typeface and Design) a
2015. Project ɗinta
shi ne ƙirkiro
da harafin Warsu da abin na kira ‘Gardanci’, watau Warsh font. Ta kira
shi, Alƙalami.
Ta samu samfuran rubutun Gardanci ne daga littaftafan da a ka sayo mata wajen
Ajamawan da ke sayar da Littattafai a Kasuwar Kurmi (Kano, Najeriya).
Da ta gama, ta gabatar da shi ga
SIL wanda su kuma suka sake shi cikin dajin duniya da niyyar a yi amfani da shi
wajen rubuta Bibul da Hausa Warsu. Dalilin yin haka kuwa shi ne la’akari da
cewa ba yadda za a yi a sa Hausawa Musulmi su karɓi
wani rubutu ba na Ƙur’ani
ba, in ba da Warsu aka yi shi ba. Warsu shi ne na su – a duk duniya ba bu wata al’umma da ke da salon rubutun Warsu irin na Hausawa.
Pakistan (Urdu), Iran (Farsi), Malaysia (Jawi) da wurare da dama na amfani su
ma da Ajami – amma da
Hafs. Shi ya sa rubutun Ajamin su ya ke kamar na Larabawa.
Nan da nan na sakko da shi
Alkalamin. Na koyawa Abdalla Sani Shu’aibu, hazikin matashi da ke cikin ofishin
Visually Ethnographic Networks a Kano. A cikin ƙanƙanin lokacin ya laƙance shi. A karon farko
na Ajamanci, sai muka hau juyar da duk wani littafin Hausa da Larabci na tarin
Kano zuwa Hausa rubutun Warsu. Waɗannan
sun haɗa da Taqyidl
Akbar, Kano Ta Dabo Ci Gari, Labarin Tarihin Kano (Kano Chronicle), Waƙar
Bagauda, da sauran su. Nan ba da jimawa ba, zan ɗora
su duk a Internet domin amfanin kowa, amma duk sadaukarwa ne ga Almajirai. Su
san tarihin su.
Ana wannan gaɓar ne, sai Abdullahi Abba Ɗalhatu
daga Brazil ya lalubo ni. Ashe ya ga yunƙurin da muke yi, shi ma sai ya bazama.
Basirar sa ta fi ta mu, nesa ba kusa ba, domin shi ya iya Larabcin, Ajamancin,
sannan kuma maƙirƙirin manhjar kwamfuta ne (programmer). Abin da ya fara yi sai
ya kafa ƙungiya
Akadamiya. A ƙarƙashin wannan sai ya ɗauko
Ƙur’ani fassarar Hausa ta
Sheikh Abubakar Gumi ya Ajamantar da fassarar da Hausar Warsu – shafi fiye da 700. Ya yi
amfani ne da Harafin Alƙalami da muka kuɓutar
da shi daga SIL.
Ganin wannan baiwar ta sa, sai ni
da amini na Salisu Ɗanyaro muka ce ya ƙirƙiro mana keken rubutun Ajamin Warsu a
wayar hannu, ko nawa ne za mu biya shi. Wannan ma sadaukarwa ce ga Almajirai,
saboda su samu hanyar isar da saƙonni ga ƴan uwan su, abokai da iyayen su. A yanzu
dai Abdullahi na kan yin hakan.
Bayan wannan, akwai sanannen
littafi Mu Koyi Ajami da Larabci na Na’ibi Suleiman Wali da Halliru Binji wanda
Gaskiya Corporation Zariya suka buga. Shi ma ni da Abdalla Sani Shuaibu mun
surantar da shi da Alkalami font saboda zamanantar da shi. To amma matsalar ita
ce samun iznin acibilistar da shi ga jama’a, wanda sai da iznin masu kamfanin.
Mun fara tuntubar su, amma ba mu kai ga ko’ina ba. Kwatsam sai Abdullahi ya
rubuta nasa littafin mai suna “Koyon Ajami da Boko”. Kuma ya ce kyauta ne ga
duk al-acibilisti. Nan da da jimawa ba za a saka shi inda kowa zai samu.
Ana cikin jira sai ya ƙirƙiro da
wata dabara ta juya Hausar boko zuwa Hausar Ajami Warsu ta hanyar gidan yana a
intanet. Za ka rubuta sakon ka da Hausar boko, manhajar sai ta Ajamantar da
shi. Abin gwanin ban sha’awa.
Yi tunanin mutumin da ya iya boko, amma zai aika sako ga wanda bai iya ba.
Wannan hanyar -- ta farko a adabin Hausa -- ita ce hanyar muhawara mai sauki a
gare su! Waya dai ta zama ruwan dare yanzu – har Almajirai ma na da ita! A yanzu shima wannan yana kan gwaji. Da zarar
duk mun kammala komai da komai, za a sanar. Ga dai hoton misali na maƙala a ƙarshen
wannan dogon rubutun!
Ajamanci shi ne kaɗai hanyar da za mu yi
amfani da ita wajen wayar da kan mutanen mu da ake iƙirarin jahilai ne saboda
ba su san boko ba. Yaya za ka ce kana koyar da yaƙi da jahilci ga mutumin da ke hanyar zama
farfesa, kawai saboda ba salon rubutun ku ɗaya
ba, kuma ba ka da niyyar bin nasa salon don ilmintar da shi, sai naka domin daɗa duhuntar da kuma daƙile
shi?
A duk wannan yunƙurin
tun daga 1996 har yanzu, ban nemi tallafin gwamnati ba. Kuma bana nema. Amma
mai gwamnati za ta yi ta faranta min? Misali, duk rubutacciyar sanarwa a
Asibitoci ko kasuwanni, a yi du da Ajami. Ko Turawan mulkin mallaka sun girmama
wannan basirar –
sunayen Unguwannin mu a Kano duk da Ajami aka rubuta su. Mace ta zo antenatal
ga fastoci na wayar wa, amma duk da boko, kuma ba ta iya bokon ba. Yi su da
Ajami ka sha mamaki.
Duk sunayen ofisoshin gwamnati a
suranta su da Ajamin Warsu. Ban ce a cire bokon ba, amma a gefe, ko kuma ƙasa, a
suranta su da Ajami. Haka a ke yi a Ethiopia da Amharic. Sunayen manyan tituna
da sunayen garuruwan da ke ƙarkashin mallakar Kano, a rubuta su da Ajami.
Mai kuma jama’ar gari za su yi?
Duk mai shago, ko supermarket, ko Plaza, ko Mall, kuma mai kishi, ya rubuta
sunan wurin da Ajamin Warsu. Duk wani katin sanar da daurin aure, a yi shi da
Ajamin Warsu. In an yi haka, an biya ni.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.