Ticker

6/recent/ticker-posts

Rubutun Ajami a Kasar Hausa

Rubutun Ajami

RUBUTUN AJAMI A ƘASAR HAUSA

Daga

Malam Muhammad Cisse

Rubutun Ajami na nufi amfani da haruffan Larabci wajen rubuta harsunan da ba Larabci ba, musamman a yammacin Afirka. Hanya ce ta rubuta harsuna kamar Hausa, Fulfulde, Wolof, a daular Songhai da Mandéhi da sauran su ta hanyar amfani da harrufan Larabci. Al'adar ta samo asali ne tare da yaduwar Musulunci da kuma tasirin Larabci a yankin.

A kasar Hausa rubutun ajami, wani nau'in salon rubutu ne da Bahaushe ya samar daga harrufan Larabci. Wannan salon rubutu yana ɗaya daga cikin daɗaɗɗun hanyoyin rubutu da aka yi amfani da ita a Ƙasar Hausa. Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), sun ce rubutun ya haura sama da shekaru ɗari da hamsin, ana amfani da wannan hanya ta rubutun ajami a Ƙasar Hausa kafin zuwan rubutun boko. Mashahuran malaman Musulunci na ƙarni na goma sha tara kamar irin su Shehu Ɗanfodiyo da almajiransa, sun yi amfani da wannan salon rubutu wajen rubuta littattafai da waƙoƙi.

Farfesa Bunza (2002), ya cewa, “ajami na nufin rubutun harshen Hausa cikin harufan Larabci”.

Masana fannin Hausa sun yi rubuce-rubuce masu yawa, kowa da nasa ra’ayin. Farfesa Bunza (2002), yana ganin cewa rubutun ajami ya wanzu a Ƙasar Hausa tun kafin zuwan Musulunci, ta in da ya kafa hujjoji da zuwan Bayajidda, da kuma dangantakar cinikayya da ta masarauta da ta wanzu tsakanin Ƙasar Hausa da kuma Ƙasashen Larabawa.

Shi kuwa Ɗanmasanin Kano, Alhaji (Dr.) Yusuf Maitama Sule, ya bayyana cewa Wali Ɗanmasani na Katsina shi ne ya ƙirƙiro da rubutun ajami na Hausa. A wannan ra'ayi nasa ana lissafa shekarun rubutun ajami da kusan shekaru ɗari bakwai kenan.

Sai dai, wani abu da ya fito fili shi ne cewa yaɗuwar addinin Musulunci a Ƙasar Hausa ya taimaka gaya wajen shaharar wannan salo na rubutu. Sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban rubutu a cikin harshen Hausa.

Bayan da Turawan mulkin mallaka suka yi mulkin mallaka, sun yi amfani da rubutun Hausa da haruffan boko, kuma rubutun Ajami ya ragu sosai. Wasu al'ummomi masu adawa da mulkin mallaka sun ci gaba da amfani da Ajami. Farfadowar Musulunci a karni na 19 ya haifar da guguwar rubuce-rubucen Ajami.

Kwanannan an gano rubuce-rubucen Hausa da yawa, kwatankwacin irin Rubutun Timbuktu da aka rubuta a cikin rubutun Ajami, kuma wasu daga cikinsu suna bayanin ilmin taurari da kalanda.

Post a Comment

0 Comments