Citation: Sani, A-U. (2021). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
ZAMANI ZO MU TAFI: AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET
NA
ABU-UBAIDA SANI
Email: abuubaidasani5@gmail.com ko official@amsoshi.com
Site: www.abu-ubaida.com
WhatsApp: +2348133529736
*** ***
BABI NA UKU
BUNƘASAR AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET
3.0 Shimfiɗa
Abubuwan
amfani na yau da kullum[1] na
tasiri a kan al’adun Hausawa. Al’amura da ke wanzuwa a duniyar intanet na da
kwatankwacin wannan tasirin. Idan aka ɗora
wannan batu kan Pulatoriyya, sai ya kasance cewa, al’adun Hausawa na samun
tasiri iri biyu. Na farko shi ne sauye-sauyen zamani a duniyar zahiri. Na biyu
kuwa sauye-sauye da ake samu a duniyar intanet. Wannan babi na uku ya bibiyi ɓangarorin al’adun Hausawa da intanet ya yi tasiri a
kansu. Wannan tasiri na faruwa ne yayin da ta kasance cewa
mutane (Hausawa) na ta’ammuli da al’amuran da suka shafi ɓangarorin rayuwa daban-daban a intanet. Misali, mata
na iya ɗaukar samfuran abinci daga
intanet domin su dafa ire-irensu lokacin bukukuwa. Haka ma, matasa na iya ɗaukar samfuran suturu da suka ci karo da su a
intanet. A bisa wannan dalili, za a fara duba yaɗuwar al’adun Hausawa a duniyar intanet kafin a
tunkari bayyana amfanin intanet da kuma aibinsa.
3.1 Intanet da Taskace Al’adu
Idan
ana maganar al’adu a jimlace, kafar intanet ta kasance taska ta al’adu. Wannan
ba sabon abu ba ne. Tuni kafafen intanet suka kasance wani bagire da ake
rubuce-rubuce dangane da al’adu. Ko bayan rubuce-rubuce, akwai hotuna da
bidiyoyi dangane da al’adun al’ummomi daban-daban. Wannan ya haɗa da bayyanannu da ɓoyayyun al’adu. A matakin duniya, abubuwan da ake
samu dangane da al’adu a kafafen intanet sun haɗa da:
a. Akan
ci karo da samfuran abinci daban-daban. Sun haɗa da abincin bukukuwa da na otel-otel da abincin yau
da kullum waɗanda ake samu a gidaje.
b. Akan
sanya hotunan tufafi. Akan kuma ci karo da nau’ukan tufafi daban-daban cikin
bidiyoyi a kafafen intanet.
c. Akan
ci karo da gine-gine nau’uka daban-daban. Gine-ginen na kasancewa cikin hotuna
da bidiyoyi.
d. Har
ila yau, a intanet akan ci karo da wasannin gargajiyar al’ummu daban-daban. Su
ma sukan kasance cikin hotuna da bidiyoyi.
e. Bugu
da ƙari,
akan ci karo da bukukuwan al’ummu
mabambanta a kafafen intanet.
f. Nau’ukan
kitso da na aski ma ba a bar su a baya ba. Akwai kafafen intanet da ke kawo
hotuna da bidiyoyinsu.
A taƙaice duk wata al’ada da aka sani ta mutane, akan samu kafafen intanet
da ke kawo su. Wannan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da yawan adadin kafafen intanet na duniya
(sama da biliyan 1.72). Dangane da al’adun Hausawa kuwa, su ma akan samu da
dama a kafafen intanet. An kawo misalai a 3.2 da ke ƙasa.
3.2 Intanet da Al’adun Hausawa
Tuni
hankalin masana da manazarta ya kai kan
tasirin intanet a kan al’adun Hausawa. A wasu lokutan sukan yi rubutu da ke
nuna wannan tasiri kai tsaye. A wasu lokuta kuwa, akan tsinci batun ne yayin da
suke tattauna tasirin zamananci kan al’adun Hausawa. Ko ba komai dai, intanet
na ɗaya daga cikin manyan abubuwan
da zamani ya zo da su, waɗanda
kuma suke da matuƙar tasiri a rayuwar al’umma. Wannan ne ya ja
hankalin Clement, (2020: 1) inda ya nuna cewa tuni intanet ya
zama wani ɓangare na rayuwar al’umma.[2]
Abin
lura a nan shi ne, yawancin ayyukan da aka gudanar a kan wannan batu sun
karkata ne zuwa ga bayyana illolin intanet a kan al’adun Hausawa. Babban misali
a nan shi ne, aikin Shehu da Rambo,
(2019) mai taken: “Shafin Zumunta na Was’af (Whatsapp): Tasirinsa ga Lalacewar
Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa.” Kai tsaye sun dubi yadda wannan shafi ke kai wa ga
taɓarɓarewar al’adun al’ummar Hausawa musamman tarbiyya.
Wannan bincike kuwa zai riƙa bugin jaki yana bugun taiki. Babban burinsa shi ne
nazartar tasirin intanet ɗin a
kan al’adun Hausawa. Wannan tasiri na iya kasancewa mai kyau ko marar kyau.
Domin jin daɗin
tattauna batun (bunƙasar al’adun Hausawa a duniyar intanet), ba za a yi
wa al’adun kaɗar ‘ya’yan kaɗanya ba. Maikwari, (2020: 29) ya bayyana cewa:
“Masana da dama sun raba al’adun Hausawa zuwa gida biyu.” Kason biyu su ne (i)
Bayyananniyar al’ada (fasahar hannu) da (ii) Ɓoyayyiyar al’ada (fasahar baka). Za a yi amfani
da wannan rabo yayin tattauna yaɗuwar
al’adun Hausawa a duniyar intanet.
3.2.1 Intanet da Bayyanannun Al’adun Hausawa (Fasahar Hannu)
Bayyanannun al’adu sun shafi dukkanin al’adun da
idanu ke iya kallon su. Sun haɗa da
wasannin gargajiya da abinci da gine-gine da sana’o’i da suturu da magunguna da bukukuwa da dazuka
da koguna. Za a ɗauki waɗannan al’adu dalla-dalla domin zawarcinsu a duniyar
intanet.
3.2.1.1 Intanet da Wasannin Hausawa
Wasa
dai na nufin duk wata magana da aka furta ko wani aiki da aka aikata da nufin
raha da nishaɗi.
Ƙamusun
Ingilishi na kamfanin Google ya ba da ma’anar wasa da cewa: “an activity
that one engages in for amusement or fun.”[3] Abin
da yake nufi shi ne “duk wani abin da mutum ke aikatawa domin samun nishaɗi.” Yayin da aka ce wasannin gargajiya
kuwa, ana nufin wasannin Hausawa da suka kasance sanannu. Bayan haka, sun kasance na Hausa tsura ba waɗanda aka kwaikwaya daga baƙin al’ummu ba. Daga cikinsu akwai waɗanda suke da takamaimai wuri da lokacin aiwatarwa,
wasu kuma har da sanannun kayan aiki da ake amfani da su yayin gudanar da
wasannin. Daga cikin wasannin gargajiya na Hausawa akwai na
furuci, wato waɗanda
suka shafi magana. Sannan akwai wasannin kurma, wato waɗanda aikatawa ake yi ba tare da
wani furuci ba.
Wannan bincike ya ci karo da wasannin Hausawa
daban-daban a duniyar intanet. Sun kasance ta fuskoki mabambanta. Daga ciki
akwai:
i. Rubuce-rubuce dangane da wasannin Hausawa
ii. Hotounan wasannin Hausawa
iii. Bidiyoyin wasannin Hausawa.
Hoto 3.1: ‘Yara Mata na Gudanar da Tashe
Madogara: Arewa24,
(2018) Tashe Ep 5
Hoto na 3.1 da ke sama ya kasance na wasan tashe. A ciki za a ga ‘yara mata sun shafe fuskarsu da farin alli. An ɗauko wannan hoto daga bidiyon da aka ɗora a kafar intanet ta Yutub. Haƙiƙa wannan wata hanya ce ta adana wasannin Hausawa na gargajiya tare da koyar da yadda ake yin su ga masu kallo.
Hoto 3.2: Wasan Langa
Madogara: Abubakar, da Ladan, (2019: 1)
A hoto na 3.2 da ke sama, za a iya kallon matasa na
wasar langa. Wannan daɗaɗɗen wasan Hausawa ne. Haƙiƙa ire-iren waɗannan
na taimakawa wajen adana al’adun wasanni da yanzu haka suka dusashe, har suna ƙoƙarin ɓacewa
gaba ɗaya.
3.2.1.2 Intanet da Abincin Hausawa
Bai zama laifi ba, idan aka faɗi cewa kalmar abinci ba ararriyar kalma ba ce daga
kowane harshe. Dalilan faɗin haka
sun haɗa da kasancewar abinci ɗaya daga cikin abubuwa na farko da ɗan’adam zai fara cuɗanya da shi yayin da ya zo duniya. Wannan na nuna
cewa, dole ne ya samar wa kansa sunan da yake ambaton wannan abu da shi. Baya
ga haka, kalmar abinci ta fi kama da haɗaka na
kalmomi guda biyu, wato abu da kuma ci. Za ta iya yuwuwa Hausawa sun fara
ambaton sunan abinci ne da furucin: “abin da za a ci” ko “abin da ake ci.”
Sannu a hankali har aka gajarce shi zuwa abinci. Ohio Department of Taxation (ODT) sun ba da
ma’anar abinci a shekarar 2004 a
matsayin duk wani abu da: “... mutane ke haɗiyewa ko taunawa sannan ana cin su ne domin ɗanɗanonsu
ko amfaninsu a jiki.”[4]
Ma’anar ta ODT ta yi kama da ma’anar da aka samar a kafar Rumbun Ilimi inda
suka ce abinci: “shi ne dukkan abin da za a ci sannan kuma ya bai wa jiki
sinadaran da yake buƙata domin samun ƙarfi” (Rumbun Ilimi, ND: 1).
Wannan
bincike ya ci karo da kafar intanet wanda aka gina ta sukutum a kan abincin Hausawa. Duka ƙumshiyar kafar ya karkata ne kan abinci. Hakan ne
ma ya sanya sunan kafar ya kasance abinci (https://abinci.com/). Kafar na matuƙar ƙoƙari wajen ɗora
hotunan abincin Hausawa tare da taƙaitaccen tsokaci game da yadda ake sarrafa su. A
hoto na 3.3 da ke ƙasa an kawo misali:
Hoto 3.3: Hoton Masa a Matsayin Abincin Hausawa
Madogara: Abincin
Hausawa, (2015: 1).
Masa sanannen nau’in abinci ne a ƙasar Hausa. A cikin hoto na 3.3 da ke sama, za a
iya lura cewa da akwai tasirin zamani kan wannan nau’in abinci. Na farko dai ƙullin masar kanta ta shinkafa ce a maimakon gero.
Zainab,[5] (2020)
ta bayyana cewa, da wuya a iya hasashen lokacin da Bahaushe ya fara masar
shinkafa “domin kuwa daɗaɗɗen al’amari ne.” Bayan haka, tanderun masar ya
kasance na dalma a maimakon na ƙasa/laka da ake da shi a gargajiyance. Na uku, da
cokalin silba ake amfani wajen juya masar a maimakon kalaba ko tsintsiya.[6] Koma
dai yaya abin yake, tuni wannan nau’in masa ya nashe cikin gargajiyar Bahaushe.
3.2.1.3 Intanet da Gine-Ginen Hausawa
Gini na ɗaya
daga cikin muhimman bayyanannun al’adu. A wannan ɓangare ma, Hausa ta samu tagomashi. Akwai kafafen
intanet daban-daban da suke ɗauke da
hotuna da bidiyoyin gine-ginen Hausawa. A duba misali a hoto na 3.4 da ke ƙasa:
Hoto 3.4: Hoton Fadar Katagum (Azare)
Madogara: Azare Online, (2020: 1)
A zuwa lokacin da aka bincika kafar intanet ta Azare
Online, hoton Katagum (Azare) ne ke matsayin babban hoton shafin farko
(home page picture). Kafar intanet ta Amsoshi ta kawo kwatankwacin wannan
hoton. Sai dai ita fadar Sakkwato da Katsina da Kano ta kawo.[7] Za a
iya lura da cewa, ginin fadar na zamani ne. Ma’ana ba tun ginin gargajiya aka
adana ba. Ba makawa hakan na da nasaba da kasancewar a da babu wadatuwar
kafafen intanet na Hausa.[8] Bayan
gine-ginen zamani na Hausawa, akan ci karo kuma da na gargajiya. A duba misali
da hoton da ke ƙasa:
Hoto 3.5: Hoton Ginin Hausawa na Gargajiya
Madogara: Dan Zubair, (2017: 1)
A hoto na 3.5 da ke sama, za a ga cewa gini ne na gargajiya.
An kuma ƙawata
shi sosai da yake ginin sarauta ne. Haƙiƙa ana da ire-iren waɗannan gine-ginen tarihi zai kasance mai amfani a nan
gaba. A 3.5b da ke ƙasa ma za a iya kallon ginin gargajiya:
Hoto 3.5b: Ginin Hausa Na Gargajiya
Madogara: Yusuf, (2017: 1)
3.2.1.4 Intanet da Sana’o’in Hausawa
“A san mutum a san sana’arsa” in ji Hausawa. “Sana’a”
ba Bahaushiyar kalma ba ce. An aro ta ne daga Larabci. A larabci tana nufin
“aiki.” Sallau, (edita) (ND) na da ra’ayin cewa “Bayan tafiya ta yi
tafiya sai ma’anar kalmar a wurin Bahaushe ta ƙara faɗaɗa har ta ƙunshi duk wani aiki da za a yi don gudanar da wani
abu da za a musanya a tsakanin ɗaiɗaikun al’umma ko rukunin jama’a.” Sana’a kuwa in ji
Newman, (1977:
177) ita ce “abin da mutum yake yi don sabawa kamar gini.” Akwai bayanai sosai
game da sano’o’in Hausawa daban-daban a duniyar intanet. A kafar intanet mai
suna Al’ummar Hausawa, Musa, (2019: 1) ya rubuta maƙala mai taken: “Sana’ar Kiyo a Ƙasar Hausa.” A ciki ya sanya hoton kaza da ‘yan
tsakinta. A duba hoto na 3.6 da ke ƙasa:
Hoto 3.6: Kaza da ‘Yan Tsakinta
Madogara: Musa, (2019: 1)
A tarihin tattalin arziki da sana’o’in Bahaushe,
kiwo na da gurbi na musamman. Har ila yau, kiwon kaji sanannen al’amari ne a
gidajen Bahaushe. A inda aka fito, da wuya a samu wani gidan Bahaushe da ba a
kiwon kaji. Akwai sanannen kirarin nan da ake yi wa kiwon kaji cewa: “’Yar ƙaramar dukiya da babbar riba.”
3.2.1.5 Intanet da Suturun Hausawa
“Sutura ita ce mutum” in ji Hausawa. Jaridar Leadership 29 ga watan
Afirilu, shekarar 2019 ta samar da fassarar wani rubutu da aka yi cikin harshen
Ingilishi mai taken “Sociology of Writing.” A ciki an nuna yadda sutura
ta kasance wata shaida da za a iya gane mutane da ita. A fahimtar marubutan,
shi tufafi “wani abu ne wanda al’umma ta samar da shi, kuma me ɗauke da ma’anar da ke daidaita yanayin mu’amala,
ciki kuwa har da samar da yanayin da ake kallon abu a matsayin ado”[9]
Wannan bincike ya ci karo da tufafin Hausawa a
duniyar intanet. Sun fi yawa a kafar intanet ɗin nan mai suna Hausa Weddings[10] (Auratayyar
Hausawa). Dalili kuwa shi ne, kafar ta shahara ne wajen ɗaukar hotuna da bidiyoyin auratayyar Hausawa tare da
ɗora su duniyar intanet. A ƙasa an kawo misalin suturun Hausawa wanda aka ɗauko a intanet:
Hoto 3.7: Hoton Hausawa Cikin Ado Bisa Dawaki
Madogara: Shehu da Sani (2020: 1)
A hoto
na 3.7 da ke sama, za a ga cewa Hausawa ne cikin ado bisa dawakai. Su ma
dawakan an caɓa musu ado. Haƙiƙa wannan yayata al’adu ne na Hausawa.
Dalili kuwa shi ne, al’ummomi daga wasu yankuna na duniya na iya kallon wannan
hoto ta kafafen intanet. Idan aka duba hoto da ke ƙasa
kuwa (3.7b), za a ga Hausawa maza cikin tufafin Hausawa.
Hoto 3.7b: Hausawa Cikin Tufafin Gargajiya
Madogara: Wikiwand, (ND: 1)
3.2.1.6 Intanet da Magungunan Hausawa
Magani daɗaɗɗen
al’amari ne. Hasashen farkon samuwar magani ga wata al’umma daidai yake da
hasashen farkon samuwar cuta ga al’ummar. Farkon samuwar cuta ga al’umma kuwa
daidai yake da farkon kasantuwarsu a raye. Dalili shi ne, hasashe ya nuna ba a
taɓa wani lokaci da ɗan’adam ba ya tare da cuta ba. Ko da babu cutar
rashin lafiya, akwai ta zuciya wadda kuwa ba a samun kwanciyar hankali har sai
an cimma muradin zuci.
Bargery, (1933: 743) ya ce: “Magani yana nufin
riga-kafi da kariyar cuta.” Dangane da
cuta kuwa, Gobir, (2012) ya tabbatar da cewa ta haɗa da ta jiki da ta zuciya. Ya kawo hakan cikin
ma’anar magani da ya bayar. Ya ce: “Hanya ce ta kawar da, ko kwantar da, duk
wata cuta ta jiki ko ta zuciya, ko neman ɗaukaka,
ko kariya daga makaru da jifa da sihiri ko siddabaru.” Gobir, (2012: 224).[11][12]
Hoto 3.8: Magungunan
Gargajiya
Madogara: Adamu, (2020: 1)
A
hoto na 3.8 da ke sama, za a iya kallon magungunan gargajiya nau’uka
daban-daban. A ciki akwai sassaƙe da ciyayi da jijiyoyi da gari da kuma sassan
dabbobi. Haƙiƙa wannan ma wani mataki ne na yayata al’adun Hausawa.
3.2.1.7 Intanet da Bukukuwan Hausawa
Buki na ɗaya
daga cikin al’adun Bahaushe masu jan hankali.
“Buki dai wani taro ne da Hausawa kan yi domin nuna farin ciki a kan
faruwar abin murna, ko domin gudanar da wani muhimmin abu da ya shafi
rayuwarsu” Shehu, a cikin Maikwari, (2020: 45).[13] Akwai
kafar intanet sukutum wanda aka gina kan auratayyar Hausawa. Wannan kafa na da
suna Hausa Weddings, wato Auratayyar Hausawa. A ciki, akan samu
hotuna da bidiyoyi na auratayyar Hausawa daban-daban. A ƙasa an kawo hoton shafin farko na wannan kafa:
Hoto 3.9: Kafar Intanet Takamaimai Kan Auratayyar Hausawa
Madogara: Shafin farko na Hausa Weddings: https://hausaweddings.com/
Hoto na 3.9 da ke sama ya kasance na shafin farko na
kafar Hausa Weddings. A tsakiyar hoton za a iya lura da tambarin kafar.
Tambarin ya kasance hannun mace da aka caɓa wa
ado. Da zarar an kalla, abu na farko da zai zo ga zuciyar mai kallon shi ne
“amarya.”[14]
Idan aka yi amfani da ire-iren waɗannan
kafafe ta hanyoyi da suka dace, lallai za su taimaka wajen haɓaka Hausa da yayata ta, tare da kundace al’adunta.
3.2.2 Intanet da Ɓoyayyun Al’adun Hausawa (Fasahar Baka)
Rukuni na biyu a rabe-raben al’adu ya shafi “ɓoyayyun al’adu.” Maikwari, (2020: 45) ya bayyana
ma’anar ɓoyayyun al’adu da cewa:
Ɓoyayyar al’ada
ita ce nau’in al’ada da ta shafi abubuwan da ba a iya gani ko taɓawa, a maimakon haka, sai dai ƙwaƙwalwa ta fahimce
su kawai. Waɗannan abubuwa
sun shafi halaye da ɗabi’u al’umma
kawai (Maikwari, 2020: 45)
A taƙaice ke nan, ɓoyayyiyar
al’ada ta shafi sababbiyar amintacciyar hanyar gudanar da rayuwa wadda ba
bayyananniya ba. Duk al’amuran da suka shafi tunani da basira da ladabi da
biyayya da zamantakewa suna ƙarƙashin ɓoyayyiyar
al’ada ne. Wannan nau’in al’ada ma ba a bar shi a baya ba wajen shiga duniyar
intanet. Akan samu al’amuran da suka shafi zamantakewa da tarihin Hausawa. Kai
tsaye kafar intanet ɗin nan
mai suna Tsangayar Adabin Hausa ta buga a shafinta na farko cewa: “Tsangayar Da Ta
Himmatu Wajen Kulawa Da Killacewa Da Taskace Abubuwan Da Suka Shafi Adabi Da
Zamantakewar Al'ummar Hausawa.”[15]
A ɓangare guda kuwa, kafafen intanet da dama na ƙoƙari wajen kawo tarihin
Hausa da Hausawa. Babban misali a nan shi ne kafar intanet mai suna Rumbun
Ilimi (https://www.rumbunilimi.com.ng/tarihi.html).
A ƙasa (hoto na 3.10)
an kawo misali:
Hoto 3.10: Tarihin Hausa da Hausawa a Kafar Intanet
Madogara:
Shafin tarihi a kan Rumbun Ilimi: https://www.rumbunilimi.com.ng/tarihi.html
A hoto
na 3.10 da ke sama, za a iya ganin cewa illahirin ƙumshiyar shafin da aka ɗauko ya karkata ne kan tarihi. An rarraba tarihin
zuwa rukunnai kamar haka:
i. Tarihin
masarautu
ii. Tarihin
dauloli
iii. Tarihin
ƙasashe
iv. Tarihin
shahararrun mutane
3.3 Amfanin Intanet ga Hausa da Hausawa
Kafafen
intanet na da matuƙar amfani wajen haɓaka harshe da yayata shi. A babi na ɗaya, ƙarƙashin 1.1 (Dalilin Bincike), an nuna yadda al’amuran duniya a yau ba sa haɓaka har sai an haɗa da intanet. Masana da dama sun yi rubuce-rubuce
dangane da tasirin intanet da zamananci a kan al’adun Hausawa. Daga ciki akwai
aikin Almajir, (2009) da Muhammad, (2011) da Magaji, (2018) da Shehu da Aliyu,
(2019) da Shehu da Rambo, (2019) da
Usman da Bunza, (2020).
Abin
lura a nan shi ne, mafi yawansu sun karkata ne kan fito da ire-iren illolin da
intanet da zamananci ke da shi ga al’adun Hausawa. Duk da haka, akwai aikin da
ya yi ƙoƙari matuƙa inda ya bugi jaki ya bugi taiki. Wannan aiki shi
ne na ‘Yartsakuwa, (2017). Aikin ya yi ƙoƙari matuƙa wajen zayyano amfani da kuma aibin kafafen intanet
tsakanin shafi na 35-37. Wannan bincike ya nazarci ayyukan magabatan. Sakamakon
ya nuna cewa, amfanin intanet ga Hausa da Hausawa sun haɗa da:
1. Samun Ilimi a Sauƙaƙe
Ɗaya daga cikin manyan alfanun intanet shi ne samun
ilimi har gida. Ta hanyar amfani da intanet, mutum zai karanta nau’ukan
rubuce-rubuce da dama yayin da yake kwance a ɗakinsa. Haka kuma, zai iya sauraron odiyo ko ya
kalli bidiyoyi. Haƙiƙa wannan janyo nesa kusa ne tare da sauƙaƙawa. Misali, a shekarar 2020 da aka samu yaɗuwar cutar korona, ƙasashen duniya da dama sun komar da tsarin
karatunsu kacokan zuwa kan intanet. Jami’o’in ƙasar Hausa ba su da wannan tsarin. Ko ba komai,
Bahaushe ya ce: “Ba a
fafe gora ranar tafiya.”
Intanet
kafa ce ta neman ilimi. Akwai makarantu da dama da suka kasance saman intanet. Ɗalibai za su yi rigista da irin waɗannan makarantu daga duk wuraren da suke a faɗin duniya. Za su riƙa ɗaukar
darusa ta intanet, su rubuta jinga ta intanet su kuma yi jarabawa ta intanet.
Daga cikin irin waɗannan makarantu
akwai:
a. Arizona
State University–ASU Online
b. Boston
University. (Boston, Massachusetts)
c. Indiana
University–IU Online.
d. Northeastern
University
e. Penn
State World Campus. (State College, Pennsylvania)
f. UMass
Online. (Amherst, Massachusetts)
g. University
of Florida Distance Learning. (Gainesville, Florida)
Hausawa
na iya morar wannan dama ta hanyar yin karatu a ƙasashen ƙetare ta kafar intanet. Baya ga haka, a yanzu haka
akwai kafafen intanet na Hausa da suke ƙoƙarin samar da makarantu ta kafar intanet. Daga cikin
masu wannan hoɓɓasa akwai masu gudanar da kafar
Bakandamiya (https://bakandamiya.com/). Akwai kuma masu kafar Wikihausa waɗanda tuni suka fara koyar da kwasakwasai da suka haɗa da na koyan kwamfuta da girke-girke da sauran ɓangarorin ilimi da dama.[16] Bugu
da ƙari,
jami’ar Nijeriyar[17] nan
wanda ke gudanar da harkokin karatunta ta kafar intanet ta sanya Hausa cikin
jerin kwasa-kwasai da take koyarwa.[18]
2. Sauƙaƙawa
Sauƙaƙawa a nan bai taƙaita a kan sauƙin da mai karatu ke samu ba kaɗai. Yana nufin (i) Sauƙin da marubuci ke samu, inda yana iya ɗora rubuce-rubucensa bisa intanet. Wannan hanya ta
fi sauƙi inda
ba zai kashe kuɗin buga
littafi mai yawa ba. (ii) Gwamnatoci da cibiyoyin ilimi na samun sauƙin ɗaukar
nauyin ɗakunan karatu. Bayan
littattafan da ake tarawa da kundaye da sauran abubuwan karatu, akwai kuma abin
da ake kira e-library,[19] wato ɗakin karatun intanet. Ɗakunan karatu na tara dubban ɗaruruwan littattafai a kan intanet. Da a ce sai an
samo kwafinsu, lallai akwai buƙatar kuɗaɗe masu yawa da kuma gine-gine masu yawa inda za a
ajiye su.
3. Bunƙasa Hausa
Kamar
yadda ake bunƙasa
Hausa ta hanyar rubuce-rubuce a duniyar zahiri, haka ma abin yake a duniyar
intanet. Wani abu mai jan hankali shi ne, sau da dama rubutu bisa intanet ya fi
yi wa matasa sauƙi a kan rubutu ta amfani da takarda da alƙalami. A haka ana samar da rubuce-rubuce da dama
a duniyar intanet. Ya rage ga masu kishin Hausa da su dage wajen bunƙasa al’amarin domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
4. Yayata Hausa
Idan
mutum ya ci gaba da rubutu domin amfanin Hausawa, to haɓaka ta kawai yake yi. Idan kuwa ya kasance cewa waɗanda ba Hausawa ba na amfana da rubutun, to a nan
yana yayata ta ke nan. Babbar hanyar yayata Hausa cikin sauƙi a yau shi ne ta amfani da intanet. Wanda ke
zaune a ƙasar
Hausa na iya yin rubuce-rubuce da za su zaga duniya. Hakan kuwa na ƙara wa harshen sanuwa tare da ɗaga darajarsa cikin jerin harsunan duniya. Ba
makawa, yayatuwar Hausa na daga cikin abin da ya fifita ta tare da ɗaga darajarta sama da tsaranta a yau. Duk da haka,
“idan kana da kyau, sai ka ƙara da wanka.”
5. Samar da Kafafen Sada Zumunta
Haƙiƙa wata babbatar gudummuwar da intanet ke bayarwa a
yau ita ce samar da kafafen sada zumunta. Zumunci ya dawo ana iya sadar da shi
alhali ana kwance cikin ɗaki.
Wannan ya kasance saɓanin da
(kafin samuwar intanet) wanda sai an tashi takanas domin ziyara. A yau, akwai
kafafen sada zumunta barkatai a duniyar intanet.
6. Yaɗa Labarai
Intane wuri ne na samun labaran abubuwan da ke wakana a duniya. Da
yawa daga cikin jaridu da gidajen rediyo da na tibi suna ɗora labaransu a kafafe daban-daban na intanet. Wasu
labaran kan kasance a rubuce, waɗansu
kuwa na magana, wani lokaci har da na bidiyo. Daga cikinsu akwai na Hausa,
misali:
a. BBC
Hausa
b. VOA Hausa
c. Aminiya
d. Arewa24
7. Samar da Muhimman Bayanai
Akwai
kafafen Intanet daban-daban da suke adana muhimman bayanai game da ɓangarorin rayuwa mabanbanta. Wannan ya haɗa da harshe da kimiyya da fasaha da kiwon lafiya da
sauransu. A irin waɗannan
kafafe, akan samu muhimman bayanai cikin ƙanƙanin lokaci kuma ba tare da wata wahala ba. Kafafen
Intanet na Hausa da ke adana bayanan ilimi sun haɗa da:
i. Amsoshi
(www.amsoshi.com)
ii. Bakandamiya
(www.bakandamiya.com)
iii. Hausa
(www.Hausa.wordpress.com)
iv. Hausa
Dictionary (www.Hausadictionary.com)
v. Kano
Online (www.kanoonline.com)
vi. Makarantar
Hausa (www.makarantarhausa.com)
vii. Teach
Yourself Hausa (www.teachyourselHausa.com)[20]
8. Samar da Kafafen Kasuwanci
Intanet
babbar hanya ce ta cinikayya. Akwai masana’antu da dama a ƙasar
Hausa da kuma
musamman ƙasashen waje da ke amfani da
kafafen intanet a matsayin farfajiyar kasuwanci. Sukan tallata hajarsu a
kafafen na intanet. sannan cinikayyar na kasancewa a intanet. Wani lokaci har
akan biya kuɗin kaya kafin a turo wa mai saya da kayan. Wani lokaci
kuwa, sai an turo kaya ga mai saya kafin ya biya kuɗin. Daga cikin kamfanoni
masu cinikayya ta kafafen Intanet akwai:
Wasu
Kafafen Intanet na Kasuwanci a Nijeriya
a. Dealdey Ltd
(https://dealdey.com.cutestat.com/)
b. Jumia
(https://www.jumia.com.ng/)
c. Kara
(https://www.kara.com.ng/)
d. Konga (https://www.konga.com/)
e. Parktel Online
(https://parktelonline.com/)
f. Slot (https://slot.ng/)
Wasu
Kafafen Intanet na Kasuwanci a Ƙasashen Waje
a. 6pm (https://www.6pm.com/)
b. AllSaints
(https://www.allsaints.com/)
c. Amazon
(https://www.amazon.com/)
d. Ann Taylor
(https://www.anntaylor.com/)
e. ASOS (https://www.asos.com/)
f. Barnes & Noble
(https://www.barnesandnoble.com/)
g. Ray-ban
(https://www.ray-ban.com/usa)
h. Urban Outfitters
(https://www.urbanoutfitters.com/)
i. Yoox (https://www.yoox.com/us)[21]
9. Adana Tarihi
Tuni
duniyar intanet ta kasance tamkar wani rumbun adana bayanai. Rubuce-rubuce da
hotuna da bidiyo da odiyo na iya kasancewa a kafafen intanet na din-din-din.[22]
Saboda haka, garaɓasa ce
ga Hausa da Hausawa a matsayin wata ma’adana ta al’adunsu. Idan aka yi amfani
da wannan garaɓasa ta hanyar da ta dace,
lallai abin zai kasance sai dai a ce san barka.
10. Samun Abin Masarufi
“A
cikin ƙira ake
ɗaɗi.” Kafafen intanet na iya kasancewa harƙallar da ke samar da abin masarufi ga masu
gudanarwa. Babbar hanyar samun kuɗi ta
intanet ita ce talla. Masu gudanar da kafafen intanet na karɓar talla daga kamfanonin cikin gida da na waje. Idan
aka ci sa’a mutanen da ke hawa kafar intanet na da yawa, mai karɓar tallar zai caɓa.
11. Hana Yawon Banza
Yawon
banza yana ɗaya daga cikin halayen da
Bahaushe ba ya so. Wannan ne ya sanya Bahaushen ke da hanyoyin rage yawon
banza. A da, yakan yi amfani da tatsuniyoyi domin hana yara fita yawo. A nan,
samuwar intanet ta rage yawon banza. Dalili kuwa shi ne, matasa da dama sun fi
buƙatar su
zauna a gida sannan su yi hira da duk wanda suke buƙata ta hanyar amfani da intanet. A yanzu da aka
samu ci gaba, kallace-kallacen finafinai duk sun koma kan intanet ta amfani da
wayoyi. Wannan ya sake taimakawa wajen hana matasa tafiya gidajen kallon
talabijin musamman da dare.
12. Bayyana Muradun Siyasa da Tallata ‘Yan Takara
Intanet
ya kasance kafa da ‘yan siyasa ke bayyana manufofinsu. Haka kuma, mutane da
dama na amfani da kafafen intanet domin tallata ‘yan takara. A duk lokacin da
zaɓe ya kusanto a ƙasar Hausa, kafafen intanet musamman na sada zumunta
cika suke yi taf da zantukan siyasa na kamfe. Zaɓuɓɓuka da
dama da suka wakana, intanet ya taka rawar gani wajen sadar da manufofin ‘yan
siyasa zuwa ga talakawa.
13. Isar da Saƙo Cikin
Sauri da Sauƙi
Intanet
yana taka rawar gani wajen bazuwar saƙo cikin gaggawa. Gwamnatoci da cibiyoyin ilimi ko na kiwon lafiya na amfani da kafafen intanet domin isar da
saƙo.
Misali, idan akwai wata sanarwa da Jami’ar Usumanu Danfodiyo, Sakkwato ke son
isarwa ga ɗalibai, sau da dama takan yi
amfani da kafar intanet nata domin isar da shi. Wani babban misali shi ne, tun
a farko-farkon shekarar 2020 Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) take amfani da
kafafen intanet domin isar da saƙonni da suka shafi ɓarkewar annobar Koronabaros da aka samu.
14. Bincike da Nazari
Tuni
kafafen intanet suka zama wani gulbi da ake kamfatar ilimi daga cikinsu.
Manazarta a fannoni daban-daban kan nemi bayanai a kan intanet. Masu binciken sun
haɗa da ɗalibai da aka ba su jinga a aji, ko ɗalibai masu ƙoƙarin rubuta kundin digiri, ko kuma yayin rubuta
takardun da za a gabatar a wuraren tarukan ƙara wa juna sani. Babban misali shi ne, fiye da
rabin bayanan da wannan bincike ya samu, ya same su ne a kafafen intanet.
Wannan ne dalilin da ya ja hankalin Abubakar Muhammad Tsangarwa har ya buɗe kafar Rumbun Ilimi. Ya bayyana dalilin da
ya sa shi buɗe kafar da cewa: “Tallafa wa
masu bincike ta kafar Intanet wajen samun haƙiƙanin bayanai game da al'adun Hausa.”
3.4 Aibin Intanet ga Hausa da Hausawa
Duk da ɗimbin amfanin intanen ga Hausa da Hausawa da aka
bayyana a ƙarƙashin 3.3 da ke sama, yana kuma da tarin aibi. A ƙasa an kawo wasu daga cikin aibin intanet ga
Hausa da al’adun Hausawa:
1. Rage Zumuntar Sawu
A lamba
ta 5 da ke ƙarƙashin 3.3 a babi na uku, an bayyana samuwar
kafafen sada zumunta. A zahirin gaskiya, abin ya kasance hanjin jimina, wato
akwai na ci akwai na zubarwa. Samuwar kafafen sada zumunta na da alfanu a ɓangare guda. A ɗaya ɓangaren
kuwa, yana da babbar illa. Daga ciki akwai ɓata lokaci da cin karo da hotuna da bidiyoyi da
labaran batsa da dai makamantansu. Haka kuma, kafafen na taimakawa wajen rage
zumuncin sawu a tsakanin al’umma. Kasancewar koyaushe ana da damar gaisawa ta
kafafen, zumuncin sawu sai ya rage tasiri.
2. Bayanan Ƙarya
A ƙarƙashen lamba ta 3 na 3.3 an bayyana yayata Hausa a
matsayin ɗaya daga cikin amfanin kafafen
intanet ga Hausa da Hausawa. A ɓangare
guda, wannan na kasancewa aibi. Yana zama aibi ne yayin da aka yi rashin sa’ar
cewar bayanan da aka samar a kafafen intanet ba sahihai ba ne. A irin wannan
lokaci, waɗanda za su karanta daga wata
uwa duniya na iya zaton haƙiƙanin yadda al’adun
Hausa suke ke nan. A taƙaice, “a garin
gyaran gira an rasa ido.” A
lamba ta 14 da ke ƙarƙashin 3.3, an kawo batun nazari da bincike. A wannan
ɓangare ma akan samu matsala
yayin da ya kasance an dogara da bayanan da aka samu a kafafen intanet. Idan ya
kasance an ci karo da bayanan ƙarya, haƙiƙa ba za a samu sakamako mai inganci ba a binciken da
ake gudanarwa. Ƙasar Hausa ba za ta manta ba da lokacin da aka
yayata zancen ƙarya
game da cewa shugaban ƙasar Nijeriya zai aure wata. Wannan ya faru a
wajajen 2019. Jaridu da dama sun rawaito wannan jita-jita. Ciki har da Rashin,
(2019) da Kaina, (2019).
3. Lalata Tarbiyya
Intanet
yana ɓata tarbiyya matuƙa. Akwai kafafe da dama a bisa intanet waɗanda ke sanya hotuna da bidiyoyi da rubuce-rubuce na
batsa. Cikin waɗannan
kafafe an fara samun na Hausa. Babban misali a wannan gaɓa shi ne kafar intanet ɗin nan mai suna Batsa Post. Wani bincike da
aka gabatar a shekarar 2013 ya yi nuni da cewa, kafafen ilmantarwa na intanet
sun fi kafafen shiririta da kusan kashi saba’in (70%) cikin ɗari. Duk da haka, matasa sun fi ziyartar waɗannan kafafen shiririta. Shehu da Aliyu, (2019) sun
bayyana cewa:
Wayar salula na daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye rayuwar
ma’aurata a ƙasar Hausa a yau... idan
miji ba ya nan sai mace ta riƙa kiran samarinta na
waje su riƙa hira tamkar saurayi da
budurwa. A wani lokacin kuma, sukan riƙa musayar saƙonni ba tare da sanin
mijin ba. Shehu da Aliyu, (2019: 707).
A taƙaice ke nan, intanet ya zama sanadiyyar gurɓacewar tarbiyya. Matsalar har ta kai ga ma’aurata
inda matar aure ke musayar saƙonni da mazaje a waje. Haka shi me a ɓangaren namiji, wa ya ce duk matan da yake mu’amala
da su a kafafen intanet ba matan aure ba ne? Ko da babu matar auren a cikinsu,
hakan ya ci karo da al’ada da addinin Bahaushe a yau. Ɗan’iro ya
kawo irin wannan batu cikin waƙarsa inda yake cewa:
6. Abin takaici ma har
da ma amare,
Su samu ƙato catin suke a tare,
Su kama yin soyayya ƙwarai a tare,
Har ma ta ce masa honi
su canza yare,
Da iggiyar aure ukku
kanta ɗaure,
Shi miji gwangwani kun ga bai sani ba.
(Ɗan’iro Katsina: Waƙar Soshiyal Midiya Dandalin Matasa)
A cikin
wannan baiti, yana nuna cewa har amare sukan yi musayar saƙonni ta kafafen sada zumunta da wasu mazaje.
Sannan har abin kan kai ga kalaman soyayya. Irin waɗannan mata ba su damu da auren da ke kansu ba. A
ire-iren waɗannan lokuta, shi mijin sam bai
san wainar da ake toyawa ba.
4. Farfaganda
Bayanan
ƙarya na
da bambanci da bayanai marasa inganci. Bayanan ƙarya a nan sun fi shafar farfaganda. Da ma dai ƙarya na nufin rusasshen zance marar asali ko
tushe da ake furtawa ko rubutawa da nufin mai sauraro ko karanta ya aminta.
Kafafen intanet, musamman kafafen sada zumunta sun kasance wuraren yaɗa farfaganda da labaran ƙarya. Akan baza jita-jita marar tushe a intanet.
Irin waɗannan jita-jitan sun haɗa da masu ta da hankali tare da harzuƙa al’umma domin su tayar da zaune-tsaye a samu
hargitsi da tashin-tashina. Misali, akan sanya labarai masu jan hankali da
niyyar jawo hankalin mutane su shiga wata kafar intanet. Sai bayan an shiga ne
ake tarar da cewa labarin na bogi ne. Haƙiƙa wannan aibi ne na kafafen intanet.
Da ma dai, ƙarya na daga cikin ɓoyayyun al’adu da suka ci karo da al’ada da addinin Bahaushe. Dangane da haka ne Shehu da Aliyu, (2019: 790-710) ke cewa: “Al’adar Hausawa da addininsu duk sun yi haramci a kan aikata ƙarya. Wannan ya sa idan mutum ya zama maƙaryaci bai da ƙima da mutunci a idon jama’a.” Dangane da farfaganda a kafen sada zumunta, Ɗan’ido na cewa:
A yaɗa alkairi kar a yaɗa zamba,
A nan ake mai da kaɗan ta zamma babba,
A nan ake haddasa ƙi a rai da gaba,
A nan ake tarbiyyar da
ban faɗi ba,
A nan ake wargaza
tarbiyyar su baba,
Duk a nan midiya in ba
kus sani ba.[23]
(Ɗan’iro Katsina: Waƙar Soshiyal Midiya
Dandalin Matasa)
5. Ta’addanci
A duk lokacin da mutane (musamman
yara) ke kallon ayyukan ta’addanci, zuciyarsu tana ƙara
bushewa ne da ƙeƙashewa. Sannu a hankali tausayin da suke
ji zai riƙa raguwa. Za a kai gacin da kwata-kwata nau’ukan
ta’addancin ba sa wani tasiri irin na sanya tausayi ko jin ƙai a
zukatansu.
A ɓangare guda kuwa, yana koya wa yara
hanyoyin aikata rashin gaskiya daban-daban. Daga cikin nau’ukan abubuwan da ke ƙunshe a
kafafen sada zumunta waɗanda kuma ke da alaƙa da ta’addanci akwai:
i. Hotuna da bidiyoyi da labarai
a kan makamai da yadda ake sarrafa su.
ii. Hotuna da bidiyoyi na makamai
da yadda ake safarar su.
iii. Hotuna da bidiyoyi da
labaran kashe-kashe.
iv. Hotuna da bidiyoyi da labarai
game da ayyukan ta’addanci da aka aikata irin su fashi da makami da sata da
garkuwa da mutane da makamantansu.
A ƙasa an
kawo ‘yan misalai waɗanda aka tattaro daga kafafen sada zumunta.
Hoto 3.11: Bindigogi da
Alburusai a Fesbuk
Madogara: An ɗauko wannan hoto
ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.
A hoto na 3.11 da ke sama, za a
ga hoton bindigogi da kuma alburusai. A ƙasar Hausa an saba ganin yadda yara ke
kwaikwayon wasa da bindigogi waɗanda suke haɗawa da kara ko ‘yan itatuwa. Masu wayo daga cikinsu suna
amfani da fayif da ƙaramin katako ko falanki da ashana domin
yin bindigar wasa wadda take ƙara. Duka waɗanan na faruwa ne sakamakon
kallace-kallacen hotuna da bidiyoyin nau’ukan bindigogin da kuma yadda ake
sarrafa su. A bisa wannan dalilai, kai tsaye ire-iren hotunan nan na da
tasiri a kan tarbiyya da falsafar yara masu tasowa.
Hoto 3.12: Bidiyon ‘Yan
Bindiga na Shirin Kai Hari
Madogara: An ɗauko wannan
bidiyo ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.
An sanya wannan bidiyo ne da
sunan ‘yan bindigar Jahar Zamfara ne ke shirin kai hari. Sai dai bincike ya
nuna cewa, labarin ba gaskiya ba ne. Hasali ma, ba a Nijeriya aka ɗauki wannan bidiyo ba.
6. Zamba da Damfara
A lamba
ta 10 da ke ƙarƙashin 3.3 an kawo “Samun Abin Masarufi” a matsayin amfanin intanet ga Hausa da al’adun
Hausawa. A ɓangare guda kuwa, akan samu
masu bin haramtattun hanyoyi domin samun kuɗi ta amfani da intanet. Wannan ya haɗa da tura wa mutane saƙonnin damfara. Ta wannan hanya sukan nemi samun
bayanan sirri kan mutane ko su buƙaci da a tura musu kuɗaɗe.
Bayan nan akwai hanyar datsar akawun-akawun na mutane (hacking) domin a musu
sata.
7. Ɓata Lokaci
A lamba
ta 11 da ke ƙarƙashin 3.3 an kawo “Hana Yawon Banza” a matsayin ɗaya
daga cikin amfanin intanet ga Hausa da al’adun Hausawa. Tuni ‘yammata da samari
suka auri kafafen sada zumunta a yau. Kusan kullum matasa na ɓata tsawon awanni a kan intanet. Da a ce za su yi
amfani da wannan lokaci wajen aikata wani aikin ƙwarai, lallai “da ba gizo ba in ji ƙoƙi.” A nan
za a iya cewa samar da kafafen sada zumunta da aka ambata a ƙarƙashin lamba ta 5 da ke 3.3 ba amfani kaɗai gare shi ba. Bayan amfaninsa a gefe guda, a ɗaya gefen ya tattare da aibi.
8. Gurɓatar Kyawawan
Al’adu
Gurɓatar al’adun Hausawa na faruwa ne yayin da Hausawa
suka ɗauki baƙin al’adu a
kafafen intanet. Intanet kafa ce da ke yaɗa
al’adun baƙin
al’ummu. Hausawa kan ɗauki
al’adun wasu al’ummu musamman Turawa da Indiyawa da Larabawa. Mafiya yawan waɗannan al’adu sun ci karo da na Hausawa. Gurɓatatun al’adu da ake ɗauka a intanet sun fi shafar halayya da tufafi. Tasirin
intanet kan al’adun Hausawa ya ja hankalin manazarta da marubuta da dama. Daga
cikin ciken rubuce-rubucen da suka fito da bayanai game da wannan batu akwai
Almajir, (2009) da Magaji, (2018) da Shehu da Rambo, (2019) da Shehu da Aliyu,
(2019).
3.5 Naɗewa
Haƙiƙa al’adun Hausawa sun kai wani matsayi na bunƙasa a duniyar intanet. Kusan babu wani ɓangaren al’adun Hausawa da ba a cin karo da shi a
cikin kafafen intanet. Abin tambaya a nan shi ne: (i) Shin Hausawa ne mamallaka
waɗannan kafafen intanet da ke
nuna al’adun Hausawa? (ii) Idan Hausawa ne ko ba Hausawa ba, shin suna da
ilimin harshe da al’ada da adabin Hausa? (iii) Shin al’adun Hausawa da ake cin
karo da su a duniyar intanet na haƙiƙa ne ba gurɓatattu
ba? Domin amsa waɗannan
tambayoyi, akwai buƙatar nazartar “nasarori da ƙalubalen kafafen intanet na Hausa.” Hakan ne zai ba da damar fahimtar inda aka kwana
tare da hasashen gobe.
[1]
Misali ababen hawa da tufafi da
kwamfutoci da gine-gine.
[2]
A duba Clement, (2020: 1) a 1.1
(Dalilin Bincike) da ke babi na ɗaya na
wannan bincike.
[3] A duba: https://www.google.com/search?q=game+meaning&oq=game+meaning&aqs=chrome..69i57j0i512l9.3156j1j4&sourceid=chrome&ie=UTF-8.
[4]
“... ingestion or chewing by humans and are consumed for their taste or
nutritional value.”
[5]
An yi hira da ita ranar 13 ga watan
Maris, shekarar 2020. Tana da kimanin shekara 75 da duniya. Bayan haka, ta yi
sana’o’i da jaura daban-daban, ciki har da masar sayarwa.
[6]
Bunza, (2021) ya tabbatar wa wannan
bincike cewa Bahaushe ya fara amfani da tsintsiya ne wajen juya masa. Daga baya
ne ya koma amfani da kalaba.
[7]
Domin kallon hoton fadar Sakkwato,
ana iya duba Bunza, (2020: 1).
[8]
Idan ba a ɗauki matakai da suka dace ba, abu mai sauƙi ne
tarihi ya maimaita kansa. Idan kuwa aka mayar da hankali wajen samar da
kyakkyawan wakilcin Hausa da Hausawa a duniyar intanet, tarihi cikin
rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi zai kasance a adane har Mahadi.
[10]
Domin nazartar wannan kafar intanet,
ana iya bin: https://hausaweddings.com/.
[11]
Ko kafin wannan ma’ana da kuma
bayanta, masana da dama sun bayyana ma’anar magani. Daga cikinsu akwai Tukur,
(1988: 134) da Bunza, (1995: 135) da Sarkin Gulbi, (2014: 5).
[12] Domin ƙarin bayani kan
magunguna ana iya duba Bunza, (1990) da Abubakar, (1997), Mahmud, (1997) da
Adamu, (1998) da Gobir, (2002) da Bunza, (2004) da Bunza, (2005) da Ayad,
(2008) da Sallau, (2010) da Sarkin Gulbi, (2014) da Gobir & Sani, (2017) da
Gobir & Sani, (2018)2.
[13]
Wannan ma’ana ta Shehu na da matuƙar
kama da ma’anar buki wanda Gusau ya bayar. Ya ce: “Buki ana yin sa don a nuna
irin farin cikin da ake da shi ga wani abin farin ciki da ya faru, ko don
tunawa da wani abu muhimmi ko don zagayowar wata rana. Biki ko bukukuwa suna
daga cikin fitattun al’adun Hausawa waɗanda suka sami asali tun daga kaka da kakanni.”
Gusau, (2012: 26). Domin ƙarin bayani a kan bukukuwa ana iya duba Ibrahim,
(1981) da Abu, (1985) da Ibrahim, (1985) da Muhammad, (1998) da Gwarjo da
wasu, (2005) da Rambo, (2007) da Abdullahi, (2008) da Funtuwa da Gusau,
(2010) da Guau, (2012) da Bunza, (2013) da Hassan, (2013) da Gada, (2014).
[14] Da zarar an ga amarya kuwa, abin da zai zo zuciya shi ne “bukin aure.” Babajo, (2001: 12) ya rawaito Alhasan na cewa: “Aure alaƙa ce ta halaccin zaman tare tsakanin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali da mutunci da ɗaukaka da kiwon iyaye.” Domin ƙarin bayani kan auratayyar Hausawa ana iya duba Ibrahim, (1985) da Rambo, (2007) da Faruk, (2011).
[15]
A duba shafin farko na Tsangayar
Adabin Hausa: http://tsangayaradabi.blogspot.com/.
[16]
Adreshin kafar Wikihausa shi ne: https://wikihausa.com.ng/.
[17]
National Open University of Nigeria
[18]
An samu wannan bayani a hirar da aka
yi da Dr. Yahaya Idiris a ofishinsa da ke Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usumanu Danfodiyo, Sakkwato.
[19]
A nan sakamakon ya yi canjaras da
tunani irin na Pulatoriyya. Ɗakunan karatun intanet ba a kallon su (duk da ma
ana iya kallon littattafai da sauran kayan karatun yayin da aka Hausa intanet).
A wuraren da suka ci gaba, idan aka ce ɗakin karatu na da littattafai miliyan goma, wataƙila
miliyan bakwai duka a kan intanet suke. Da za a zo a lissafa, za a yi mamakin
ina miliyan bakwai ɗin
suka shiga. Lallai kuwa suna duniyar intanet.
[20]
An jero su ne bisa tsarin abajada.
An bibiyi kowace kafa domin nazartar ƙumshiyarta. Dukkanin kafafen da aka
zayyana, an zaɓe su
ne ta la’akari da nagartan ƙumshiyarsu.
[21]
An samo waɗannan bayanai ta hanyar duba sunayensu a
intanet tare da shiga cikinsu domin tabbatarwa
[22]
Ana iya samun salwantar bayanai
yayin da aka samu wata matsala ta musamman. Duk da haka, akwai hanyoyi da ake
bi domin tabbatar da adanuwar bayanai na din-din-din.
[23] Sallau, (2021) ya labarta yadda
jami’an ‘yan sanda suka yi ikirarin cewa su ne suka ƙwato waɗansu
mutane da masu garkuwa da mutane suka sace. Wannan labari ya bazu a duniya
alhali a haƙiƙanin gaskiya mutanen ne suka samu nasarar kuɓucewa da kansu, ba
tare da taimakon kowi jami’in tsaro ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.