Citation: Sani, A-U. (2021). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
ZAMANI ZO MU TAFI: AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET
NA
ABU-UBAIDA SANI
Email: abuubaidasani5@gmail.com ko official@amsoshi.com
Site: www.abu-ubaida.com
WhatsApp: +2348133529736
*** ***
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 Shimfiɗa
Bincike
a game da intanet abu ne da aka daɗe ana
aiwatarwa. Akwai ayyuka da dama da aka gabatar dangane da intanet. Kowanne daga
cikin ayyukan akwai abin da ya fi mayar da hankali zuwa gare shi. Wasu sun
shafi tarihin samuwar intanet ɗin;
wasu dangantakar intanet da rayuwa; wasu matsaloli da ci gaban intanet, wasu
kuwa kafafen da ake samu a kan intanet, da dai makamantansu. A ƙoƙarin wannan bincike na duba al’adar Bahaushe a duniyar intanet, akwai buƙatar bitar wasu muhimman batutuwa. Sun shafi
waiwaye kan tarihin intanet kansa da bibiyar nau’ukan tasirori da yake da shi ga al’adun al’umma. Daga nan ne za a
iya fahimtar irin ci gaba ko koma-baya da yake tattare da shi.
2.1 Bitar Muhimman Batutuwa
Manyan
batutuwan da suka gina ruhin wannan bincike su ne “intanet” da “al’ada.” Yana
da kyau a bi taliyon kalmomin biyu tare da daddagar ma’anoninsu. Daga nan ne za
a iya bin diddigin dangantakar da ke tsakaninsu.
2.1.1 Intanet
Kalmar
intanet baƙuwa ce
a fannin nazarin Hausa (Mukoshy, 2015: 19). Asalin kalmar a Ingilishi ita ce
“internet.” Masana da manazarta da dama sun yi ƙoƙarin ba da ma’anar
intanet. Umar ya bayyana ma’anar intanet da cewa:
Intanet kafa ce wadda ta haɗa bayanai daban-daban, kuma an sauƙaƙa hanyoyin amfani da waɗannan bayanai yadda kowa zai iya miƙa hannayensa a kowane lokaci a ko’ina. (Umar, 2012: 48)
Mukoshy,
(2015) ya nazarci wasu daga cikin ma’anonin intanet da masana da manazarta suka bayar.[1] Daga ƙarshe ya bayyana tasa ma’ana da cewa:
Intanet kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk duniya.
Tana ba da damar sadar da bayanai kowaɗanne iri, kuma zuwa ko’ina a duniya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. (Mukoshy, 2015: 20).
Da
alama Mukoshy ya yi aron hannu ga Umar, (2012) wajen fitar da wannan ma’ana ta
intanet. Duka ma’anonin biyu (Mukoshy da Umar) suna nuna cewa, kowa na da damar
yin amfani da intanet, sannan daga kowane wuri.
Haƙiƙa waɗannan
ma’anoni sun ba da haske kan ma’anar intanet. Duk da haka, akwai muhimmin
al’amari da ya kamata bayani kan intanet ya ƙunsa. Wannan kuwa shi ne nuna bagire ko
farfajiyar wannan kafar sadarwa wanda ta kasance bisa hanyoyin iska waɗanda ba a iya ganin su. Tun a shekarar 2010 Amfani
ya kawo wannan cikin ma’anar da ya bayar inda yake cewa:
Intanet tsari ne da ya haɗa duniya, ta haɗakar layin iska na kwamfutoci waɗanda ke amfani da tsare-tsaren yanar gizo don biya wa biliyoyin masu
amfani buƙatu a faɗin duniya. (Amfani, 2010 a cikin Umar,
2012: 48).
Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni da ma makamantansu, za a tarar da cewa akwai muhimman abubuwan da suka taru suka samar da kafar intanet. Za a iya kallon su a matsayin siffofin intanet. Ko ma wace ma’ana ce ta fi kwanciya ga rayin manazarci, yana da kyau a fahimci cewa:
- Intanet al’amari ne da ya samu a zamanance.
- Intanet
ya kasance al’amari mai faɗi da
ban mamaki. Yana ƙunshe da dukkanin wasu fannoni da ake samu a duniyar
rayuwar yau da kullum.
- Intanet
ba ya gudanuwa sai da taimakon na’urori masu ƙwaƙwalwa (nau’ukan kwamfuta daban-daban).[2]
- Hulɗayyar intanet abu ce wadda ba a gani, amma ana
kallon sakamakonta ta fuskokin kwamfutoci.
- Intanet
na da yaruka daban-daban. Yayin da aka tura saƙo bisa intanet, sai ya fassaru cikin yaren da
intanet ke ganewa. Daga nan kuma sai ya sake fassaruwa zuwa yare ko sigar da
masu neman sakamakon ke iya fahimta.
- Babu wani al’amari na intanet da ke da damar yin kansa. Komai aka gani a duniyar, to an yi shi ne. Duk da haka, ana iya ba wa wani al’amari a duniyar intanet damar maimaita kansa ko sarrafa kansa zuwa wasu sigogi mabambanta.
- Intanet
al’amari ne da ya jawo nesa kusa,[3] ya
mayar da abu mai yawa ya zama kaɗan,[4] ya
mayar da abu kaɗan ya
zama mai yawa,[5]
sannan ya tsuke faɗin
duniya.
- Intanet haɗaka ce ta tsauraran al’amura daban-daban. Sun haɗa da yarukan intanet da gine-ginenta da hanyoyin shigarta da service ko network wanda shi ke ba da damar kai wa gare ta.
Lura da
waɗannan, ba da kammalalliyar
ma’anar intanet da za ta bayyana dukkanin siffofinsa aiki ne ja. Duk da haka,
ta bin sawun zaren tunanin magabata wajen ba da ma’anar intanet, za a iya cewa:
Intanet
fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar
tsauraran al’amura da suka haɗa da
yaruka da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu ke samar da al’amari ko bagire da ke tattare
da al’amura da fannoni tamkar waɗanda ke
duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu
da bankuna tare da sauran halittu kamar mutane da waninsu.
2.1.1.1 Duniyar Intanet Jiya da Yau
An
gudanar da rubuce-rubuce masu tarin yawa dangane da tarihin samuwar intanet da
bunƙasarsa.[6] Kawo
tarihin tiryan-tiryan zai kasance tamkar maimaici ne ga ayyukan baya kawai ba
tare da gabato da sabon al’amari ba. A bisa haka, wannan bincike zai fi mayar
da hankali wajen zaƙulo sauye-sauye da ci gaba da aka samu a harkar
intanet tun bayan ƙirƙirarsa.
Bincike
da dama da suka gabata sun danganta tarihin intanet da yunƙurin wata hukumar tsaro da ke Amurka. Gerf,
(2004: 1360) ya bayyana cewa, a shekarun 1970s ne aka samu hoɓɓasa na kafar intanet ta farko mai suna ARPANET. Wannan
bayani ya yi daidai da wanda Mukoshy, (2015: 21) ya rawaito daga Deitel da
Deitel, (2009). Mukoshy ya yi ƙarin bayani da cewa, kafar intanet ta ARFA ta samu
ne bayan hukumar da aka fi sani da The Advanced Research Project Agency (ARPA)
ta gudanar da taro a shekarar 1969.
Wannan hukumar ta kasance ƙarƙashin Department of Defense in United States.
A binciken da Romualdo & Alessandro (2007: 2) suka gabatar, sun tabbatar da cewa
intanet a wancan lokaci ya shafi haɗaka ta kai tsaye ne daga kwamfuta zuwa kwamfuta. A
farko-farkon al’amarin intanet, akwai manyan matakai huɗu na ci gaba da aka samu. Romualdo &
Alessandro, (2007: 2) sun bayyana su kamar haka:
a. Linear (Sambai)
Wannan shi ne tsarin intanet na farko. Dukkanin kwamfutocin da ke haɗe da intanet ɗin suna kan layi guda ne. Saƙo na tashi daga kwamfuta ta farko zuwa ta biyu sannan ta uku, har ƙarshe. Misali, saƙon da ya tashi daga “A” sai ya je “B”, ya je “C”, ya je “D” sannan ya je “E.” A irin wannan tsari, yayin da aka katse kwamfuta guda daga kan layi, to tamkar an katse sauran ne. Misali, idan aka katse “C”, to “D” da “E” ba za su iya karɓar saƙo ba. Ga misali cikin hoton da ke ƙasa:
Hoto 2.1: Tsarin Intanet Mai Bin Sambai
Madogara: Romualdo & Alessandro, (2007: 3)
b. Ring (Zobe)
Ci gaba da aka samu ya sa aka fito da tsarin intanet Maizobe. A wannan tsari, saƙo na zagayawa ne cikin wani tsari na da’ira. Saƙo daga kowace kwamfuta na iya zuwa sauran kwamfutoci. Duk da haka, idan kwamfutar ba ita ke gefen wadda ta tura saƙo ba a kan intanet, to sai saƙon ya bi cikin kwamfutocin da ke tsakani a cikin jerin kwamfutocin kafin ya isa zuwa kwamfutar da za ta karɓi saƙon. Ga misali cikin hoton da ke ƙasa:
Hoto 2.2: Tsarin Intanet Maizobe
Madogara: Romualdo & Alessandro, (2007: 3)
c. Star (Tauraro)
Bunƙasar al’amuran intanet ya kai ga samun ci gaba zuwa tsarin haɗakar kwamfutoci cikin sigar tauraro. A wannan tsari, babbar kwamfuta da ta haɗa sauran kwamfutoci takan kasance a tsakiya. Saƙon da ya tashi daga gare ta yana isa ga dukkanin sauran kwamfutoci. Idan wata kwamfuta za ta tura saƙo ga ‘yar uwarta, dole sai saƙon ya iso cikin wannan babbar kwamfuta. Daga nan ne saƙon zai iya kaiwa ga kwamfutar da aka aika shi.
Hoto 2.3: Tsarin Intanet Mai Zubin Tauraro
Madogara: Basu, (2019: 1)
d. Mesh (Jigida)
Ci gaba da aka sake samu a sha’anin intanet ya samar da sabon salon haɗakar kwamfutoci. A wannan tsari, kwamfutoci sukan kasance a sarƙe. Kwamfuta guda na da damar isar da saƙo kai tsaye zuwa kwamfutoci biyu ko ma sama da haka. Abin lura a nan shi ne, kwamfuta na da damar isar da saƙo ne kawai ga kwamfutocin da aka riga da aka samar da hanyar isar da saƙo tsakaninsu. Hoton da ke ƙasa na ɗauke da ƙarin bayani dangane da wannan tsari.
Hoto 2.4: Tsarin Intanet Mai Zubin Jigida
Madogara: Keary, (2021: 1)
A zuwa
yau, tsarin intanet ya samu bunƙasa da ya wuce dukkanin waɗannan matakai. A yau, kwamfutoci suna haɗe ne cikin wani tsari mai sarƙaƙiyar gaske. Kowace kwamfuta na iya haɗuwa da ‘yar uwarta tare da tura mata saƙo kai tsaye. Misali, “A” na haɗe da “B” da “C.” “B” na haɗe da “A” da “C.” “C” na haɗe da “A” da “B.” A taƙaice, ba a buƙatar saƙo ya bi ta cikin wata kwamfuta kafin ya kai ga wata.[7]
Akwai nau’ukan sabis ɗin intanet daban-daban. Masana
na samar da rabe-raben intanet ne ta la’akari da faɗin wurin da sabis ɗin intanet ɗin ke kaiwa.[8] Fitattu daga cikin ire-iren
intanet su ne:
1. PAN (Personal Area
Network) – Keɓantaccen Sabis Ɗin Intanet
Wannan shi ne nau’in sabis ɗin intanet da ya shafi wuri
guda kawai. Yawanci ana samar da wannan nau’in sabis ne domin amfanin mutum ɗaya. Sau da dama sabis ɗin ba ya wuce faɗin mita goma (10). Misali, idan
mutum ya tura bidiyo ko hoto daga kwamfuta zuwa wayarsa ko daga waya zuwa
kwamfuta, to ya yi amfani ne da irin wannan nau’in sabis. Haka ma mutum na iya
kunna sabis ɗin
wayarsa na hawa intanet domin ya ba wa kwamfutoci ko wayoyi sabis. Duk ire-iren
waɗannan
ana kiran su da suna PAN.
2. LAN
(Local Area Network) – Sabis Ɗin Ƙaramin
Wuri
Wannan nau’in sabis ne da ya shafi ma’aikatu ko
gidaje ko masana’antu. Za a iya samun ma’aikata mai kwamfutoci kamar guda goma
(10) amma dukkanninsu suna amfani da sabis guda ne. Bayan haka, ƙwaƙwalen kwamfutocin na
iya kasancewa a haɗe wuri guda. Wannan zai sa duk sauyin da aka yi a
kwamfuta guda ya kasance ya shafi sauran kwamfutocin. Bayan haka, akan samu babban ofishi a ma’aikata da ke ɗauke da kwamfutoci da yawa a
ciki. Ana iya tsara yadda dukkannin kwamfutocin za su riƙa tura takardun da za a
gurza (printing) zuwa na’urar gurza takardu (printer) guda. Sabis ɗin da ya haɗa kwamfutocin shi ake kira LAN.
PAN daban-daban ne ke haɗuwa su ba da LAN.
3.
MAN (Metropolitan Area Network) – Sabis
Ɗin
Yanki
Wannan nau’in sabis ne da ke karaɗe wani yanki. Nau’in sabis ɗin da ake samu a manyan
jami’o’i da ke da gine-gine da dama na iya kasancewa MAN. Bayan haka, ana iya
samun wata ma’aikata da ke da gine-gine ko ofisoshi a wurare daban-daban a
cikin gari guda ko garuruwa da ke kusa da juna. Idan haka ta faru, ana iya
amfani da sabis ɗin MAN domin taƙaita adadin kuɗi da ma’aikatar za ta riƙa kashewa ga sabis. PAN
daban-daban ne ke haɗuwea su ba da LAN. Su kuma LAN sai su haɗu su ba da MAN.
4. WAN (Wide Area Network) – Sabis
Na Dogon Zango
Wannan nau’in sabis ne da yake mamaye dogon zango. Yana
kasancewa tsakanin gari da gari ko ma ƙasa da ƙasa. Misali, a Nijeriya
akwai bankuna da babu wata jaha da ba su da cibiya. Akwai nau’ukan sabis-sabis
da dukkannin cibiyoyin da ke jahohin suke amfani da su a tare. Manyan
kamfanonin fassara suna da tsari makamancin wannan. Misali, kamfanonin fassara
da ke da ma’aikata da dama, sukan yi amfani da tsarin sabis guda. Ko a ɓangaren raba fayilolin fassara
za a iya kallon wannan. Idan akwai fayiloli 20, za su kasance a kwamfutocin
dukkannin ma’aikatan. Sannan kowannensu zai riƙa kallon fayil da aka
riga aka yi aiki a kansa.[9] Yayin da PAN suka haɗu suka ba da LAN, su kuma LAN
za su haɗu
su ba da MAN. MAN kuwa su ke haɗuwa su ba da WAN.
Ɓullar kafafen intanet ya samar da wani sabon
al’amari a duniyar intanet. Kafar intanet wani gida ne ko farfajiya ko rumbu da
ake ƙirƙira. A cikinsa ne ake ajiye bayanai iri-iri. Za a
riƙa bin
wasu tsararrun hanyoyi wajen kai wa ga wannan gida tare da ta’ammuli da
kayayyakin da ke cikinsa.[10] Binciken Armstrong, (2019: 1) ya tabbatar da cewa, an ƙirƙiri
kafar intanet na farko ne a shekarar 1991. Daga wannan lokaci aka ci gaba da
samun ɓullowar kafafen intanet da bunƙasarsu. Ya zuwa shekarar 2016, kafafen
intanet sun kai biliyan guda. Giraf da ke ƙasa na ɗauke da ƙarin
bayani.
Giraf 2.1: Adadin Kafafen Intanet a Duniya
Madogara:
Armstrong, (2019: 1)
A giraf
na 2.1 da ke sama, za a ga tarihin samuwar kafafen intanet a taƙaice. A shekarar 1991 kafar intanet guda ɗaya aka samu. A 1992 adadinsu ya kai goma. A wajajen
2016, wannan adadi ya kai biliyan guda. Bayan haka, giraf ɗin ya nuna shekarun da aka samar da wasu muhimman
kafafen intanet. Sun kasance:
a. Yahoo
(Yahu) a shekarar 1994
b. Google
(Gogul) a shekarar 1998
c. Facebook
(Fesbuk) a shekarar 2004
d. YouTube
(Yutub) a shekarar 2005
e. Instagram
(Insitagiram) a shekarar 2010
2.1.1.2 Intanet a Kadadar Hausa da Hausawa
Ɗaya daga cikin manyan tagomashin da Hausa ta samu
shi ne yawan bincike da ake gudanarwa a kanta a matakai daban-daban.[11] Ba a ƙasar Hausa kawai ba, an fara koyar da Hausa a ƙasashen ƙetare/Turai tun a shekarun 1885 (Sani & Umar,
2018: 24). Ɗaukakar
Hausa da yawan al’ummarta sun sa a yau tana da gurbi a duniyar intanet. Akwai
manyan gidajen rediyo a matakin duniya da ke yaɗa labarai cikin harshen Hausa. Bugu da ƙari, sai aka yi dace suna da kafafen intanet. A
nan ma, sukan samar da rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi da suka shafi Hausa
da Hausawa, waɗanda kuma ake rubutawa cikin
harshen Hausa. An kawo misalan waɗannan
kafafe a ƙarƙashin 1.6 da ke babi na ɗaya.
Wani
muhimmin al’amari shi ne, ya zuwa yau, akwai kafafen intanet na Hausa da dama.[12] Waɗannan kafafe suna ɗauke da bayanai game da Hausa da Hausawa. Misali,
babban maƙasudin
kafar intanet ɗin nan ta Hausa mai suna Abincin
Hausawa (https://abinci.com/) shi ne kawo bayanai kan nau’ukan abincin
Hausawa. Abinci kuwa na daga cikin al’adun fasahar hannu (material culture)
(Maikwari, 2020: 31-32). Ita kuwa kafar Amsoshi (https://www.amsoshi.com/), ta kasance gama-gari inda ta ƙunshi ɓangarorin al’ada da adabi da harshe. A
taƙaice, samuwar kafafen intanet na Hausa da suka kai adadi
mai yawa (har kimanin 44) na nuna matsayinta da yaɗurwarta a duniyar intanet.
Bunƙasar
Hausa a duniyar intanet ya kai wani mataki yayin da ta samu shiga cikin jerin
harsunan da ake amfani da su a kafar Fesbuk. “Yanzu haka masu amfani da shafin
da dama suna yi ne ta hanyar amfani da harshen Hausa a matsayin harshen umurni”
(Morison a cikin ‘Yartsakuwa, 2017: 26). Masu amfani da Fesbuk na da damar
mayar da saitin akawun ɗinsu cikin harshen Hausa. Bayan haka, kamfanin Fesbuk na ba da dubban ɗaruruwan rubuce-rubuce da aka yi a kan
Fesbuk domin a fassara su zuwa harshen Hausa. Duk wani rubutu da aka yi kan
Fesbuk cikin wasu harsuna daban, mutum na da damar duba fassarorinsu cikin
harshen Hausa. Idan ya kasance ba a fassara su zuwa Hausa ba a daidai lokacin
da aka duba, injin ɗin Fesbuk zai yi ƙoƙarin fassara su ta hanyar amfani da
ilimin makamantan fassarori da suka gabata.
Hoto 2.5: Tsarin Fesbuk
Cikin Harshen Hausa
Madogara:
Akawun Ɗin Abdulrahman Muhammad Manga na Fesbuk
A hoto na 2.5 da ke sama, za a ga
cewa akawun ɗin Fesbuk ɗin cikin harshen Hausa yake. Dukkanin ɓangarorin akawun ɗin an sanya sunayensu ne cikin harshen
Hausa. Haƙiƙa wannan ci gaba ne sosai ga harshen.
Yayin da aka bincika jerin harsunan da ake iya amfani da su a kan Fesbuk, za a
tarar da cewa ba su kai ɗari da hamsin (150) ba (har ya zuwa ranar 24 ga watan Maris na shekarar
2020). Kada a manta cewa, harsunan duniya ba su gaza dubu bakwai (7,000) ba
(Bunza, 2019: 7). Ko Yoruba da Igbo da ke bi ma Hausa cikin harsunan Nijeriya
ba su da gurbi a Fesbuk.
Bugu da ƙari,
kamfanin Gogul ya daɗe da ba wa Hausa muhimmanci. Yana fitar da dubban ɗaruruwan jimloli da kalmomi a-kai-a-kai
domin fassara. Kamfanin yana da injin ɗin fassara wanda aka fi sani da Google Online
Translator. Daga cikin harsunan da ke kan wannan tsari har da Hausa. Wani ƙalubale
na wannannan injin ɗin fassara shi ne, yana iya kasancewa a ci karo da fassara da ba ingantacciya
ba. Dalili kuwa shi ne, idan ya kasance jimlar da aka bincika ba ta da fassara
a cikin injin ɗin, to injin zai fassara ta. Zai yi fassarar ta hanyar amfani da ilimin
fassarori makamantanta da ke kan injin ɗin. A kullum kamfanin na ƙara
inganta tsarin. A ƙasa an ba da misalin fassara mai inganci
da marar inganci waɗanda aka ɗauko daga injin ɗin fassara na Gogul:
Hoto 2.6: Fassara Mai Inganci Daga Injin Ɗin Fassara na Gogul
Madogara: https://www.google.com/search?q=english+to+hausa
A hoto na 2.6 da ke sama, za a
iya lura da cewa fassarar da injin fassara na Gogul ya bayar tana da inganci. A
ƙasa an kawo misalin fassara mai rauni (duba hoto na 2.7):
Hoto 2.7: Fassara Marar Inganci Daga Injin Fassara na Gogul
Madogara: https://www.google.com/search?q=english+to+hausa
A hoto na 2.7 da ke sama, za a
iya lura da cewa, fassarar da injin ɗin fassara na Gogul ya bayar na da rauni. Ya fassara
“her” wanda ya kasance jinsin mace a matsayin jinsin namiji, wato “shi.”
Ko bayan Gogul, akwai waɗansu injunan fassara a kafafen intanet
waɗanda Hausa ke ɗaya daga cikin harsunan da ke kansu (supported languages). Wasu kuwa ƙamusoshin
fassara ne daga cikin harshen Hausa zuwa wasu harsuna daban, ko kuma daga wasu
harsuna zuwa harshen Hausa. A ƙasa an kawo misalan wasu daga ciki:
1. Bargery
Online Dictionary (Ƙamusun Bargery na Kan Intanet). Adireshinsa shi ne:
http://maguzawa.dyndns.ws/.
2. Hausa
Dictionary (Ƙamusun
Hausa). Adireshinsa shi ne: http://hausadictionary.com/Main_Page.
3. Stars
21 (Taurari 21). Adireshinsa shi ne:
https://www.stars21.com/translator/english_to_hausa.html.
4. Translation
2 (Fassara 2). Adireshinsa shi ne:
https://translation2.paralink.com/English-Hausa-Translator/.
5. Translator
(Mai fassara). Adireshinsa shi ne:
https://imtranslator.net/translation/hausa/to-english/translation/.
A ɓangare guda kuwa, kafar Wikifidiya (Wikipedia)
fitacciya ce a duniyar intanet.[13] Da
wuya a binciki wata kalma a injin nema na Gogul ba tare da an ci karo da zaɓin Wikifidiya ya fito a shafin farko ba.
Rubuce-rubucen wannan kafa ya shafi dukkanin ɓangarorin rayuwa tun daga kan siyasa da zamantakewa
da addini da tarihi har zuwa kiwon lafiya da harsuna da al’ada da dai sauransu.
A yanzu haka, wannan kafa ta fara samar da bayanai cikin harshen Hausa.[14] Babu
makawa wannan kafa za ta taimaka wa harshen matuƙa wajen yaɗuwa da
yayatuwa a duniya.[15] A ƙasa an kawo misalin shafin farko na wannan kafa
cikin hoto.
Hoto 2.8: Kafar Wikifidiya ta Hausa
Madogara: Shafin farko na Wikifidiyan Hausa (https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi)
A hoto
na 2.8 da ke sama, za a iya lura da cewa wannan shafi na Wikifidiya cikin
harshen Hausa yake. A zuwa lokacin da aka ɗauki hoton (ranar 25 ga watan Maris, shekarar 2020),
akwai maƙalu
dubu huɗu da ɗari bakwai da tara (4,709) a kan shafin.
2.1.2 Al’ada
Al’ada
ta shafi rayuwa ce gaba ɗaya.
Duk wani abin da ke gudana a rayuwa yana cikin kadadar al’ada ne. Idan aka yi
la’akari da amfanin al’ada da matsayinta, ba abin mamaki ba ne da ya kasance an
duƙufa
wajen gudanar da rubuce-rubucen ilimi dangane da ita. Maikwari (2020: 40), ya
bayyana cewa: “Masana al’ada da zamantakewar al’umma (Anthropologist) sun
bayyana cewa, an samu ma’anar al’ada tun a ƙarni na sha tara (Ƙ19).”
A
fashin baƙin
kalmar al’ada, za a iya cewa tana amfani ne a muhimman wurare guda biyu. Na
farko shi ne al’amarin da ke faruwa ga mata, wato al’adar zubar jini. Na
biyu kuwa ya shafi duk wani abu da aka saba aiwatarwa musamman bisa wasu
matakai sababbu kuma sanannu. Ma’anar al’ada da Abraham, (1962: 17) ya bayar ta
ƙunshi
dukkanin ɓangarorin biyu. A cewarsa,
al’ada na nufin: “aure da buki da haila (al’adar mata) da magana da ciwon kai
wanda aka saba da yi.” A nan, Abraham ya jero misalai ne na al’ada ba tare da
sanya su cikin bayani yadda za a gane ma’anar kalmar kai tsaye ba.
Ma’anar
da Abraham, (1962: 17) ya bayar na da matuƙar kama da ta Bargery, (1934: 16). Shi ma ya kawo
kalmomi ne a jere ba tare da sanya su cikin bayani ko sharhin da za a gane
ma’anar al’ada kai tsaye ba. A yunƙurinsa na ba da ma’anar kalmar, ya ce: “Tada ko ɗabi’a ko hanya ko haila...” Idan aka lura, shi ma
Bargery bai fita daga kadadar bayyana al’ada a bagirai biyu ba (abin da aka
saba ko kuma al’adar mata).
A cikin
Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero, an ba
da ma’anonin al’ada da ke kama da na Abraham da Bargery. An karkasa ma’anonin ne
zuwa rukunne huɗu masu
cin gashin kansu kamar haka: “(i) hanyar rayuwar al’umma (ii) jinin haila (iii)
wani hali na daban na mutum (iv) magani ko tsafi” Sa’id da wasu (2006:
9). A nan ma ba a yi cikakken bayani ba da zai fitar da ma’anar kalmar fili. A
maimakon haka, an dunƙule ma’anonin ne.
Ba abin
mamaki ba ne don an kira jinin haila da suna al’ada kasancewarsa
sanannen al’amari kuma sababbe. Kusan dukkanin ma’anonin al’ada da masana da
manazarta ke bayarwa, ba sa fita daga farfajiyar sababben al’amari. Misali,
Ibrahim, (1982: iii) ya bayyana ma’anar al’ada da: “Abubuwan da mutum ya saba
yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Ta haka al’ada ta shafi yanayin rayuwar al’umma
da harkokin da take gudanarwa na yau da kullum.” A taƙaice, wannan bayani ya yi ƙarin haske kan ma’anar da Abraham, (1962: 17) ya
bayar, musamman wurin da ya ambaci “aure da buki.” Ga bisa dukkan alamu
kasancewarsu sababbun al’amura masu bin wasu sanannun matakan gudanuwa, shi ne
ya ja hankalinsa wajen bayyana wannan ra’ayi.
A
shekarar 1987, Ɗangambo ya samar da wata ma’anar al’ada wadda ke ɗauke da kalma mai jan hankali (amincewa). A tasa
fahimta, sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa kaɗai ba ta kai matsayin al’ada ba, har sai mafi yawa
daga cikin al’umma sun aminta da ita. Ya ce:
“Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin
jama’a na cikin al’umma suka amince da ita” Ɗangambo, a cikin Maikwari, (2020: 40).
Ma’anar
al’ada da Bunza, (2006) ya bayar tana matuƙar kama da ta Gusau, (2010). Bunza, (2006: 7) ya
ce: ‘’Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar Ɗan’Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa.”
Shi kuwa Gusau, (2010: 2) cewa ya yi: “Al’ada ta ƙunshi dukkan ɓangarorin rayuwar ɗan Adam.” Idan aka duba ma’anonin guda biyu, suna
nuna cewa, al’ada ta shafi rayuwar ɗan’adam
ne gaba ɗayanta. Gusau, (2010) ya ba da
ma’anar al’ada mai faffaɗar
bayani, ya ce:
Al’ada ta ƙunshi tafarki wanda wata
al’umma take rayuwa a cikinsa dangane da yanayin abinci da tufafi da muhalli da
rayuwar aure da haihuwa da mutuwa da wasu hulɗoɗin rayuwa kamar maƙwabtaka da sana’o’i da
kasuwanci da shugabanci da bukukuwa da sauran abubuwa waɗanda suke da alaƙa da haka. Gusau, (2010: 2)
Haƙiƙa wannan ma’ana ta
Gusau ta ba da haske sosai kan kalmar. Ma’anar
har ta ƙyallaro
ire-iren abubuwan da al’ada ta ƙunsa. Sun shafi bayyanannu kamar “abinci da tufafi da muhalli” da kuma ɓoyayyu
da suka shafi “rayuwar aure da haihuwa da mutuwa da wasu hulɗoɗin
rayuwa kamar maƙwabtaka.”[16]
Wani
abin lura shi ne, idan aka ɗauki
ma’anar al’ada a matsayin hanyar gudanar da rayuwa (Bunza, 2006: 7; Gusau,
2010: 2), to ana iya cewa, al’ada ba ta tsaya kan mutane ba kawai. Tana
iya shafar dukkanin halittu, tun
daga waɗanda ake gani har waɗanda ba a gani.[17] A
bisa wannan tunani ne Maikwari, (2020: 42) yake cewa:
Na lura ba mutane kaɗai ne suke da al’adu ba, hatta ma dabbobi da ƙwari kowa da irin tasa hanyar gudanar da rayuwa kuma da yadda yake
aiwatar da tsarin rayuwarsa, kama daga kuka, da nema, da cin abinci da tanadi
ga masu yin tanadi da sadarwa tsakaninsu da wasu da dai makamantansu. (Maikwari, 2020: 42)
Duk da
haka, wannan bincike ya shafi al’adun mutane ne kawai. A mutanen ma, ya taƙaita ne ga nazartar al’adaun Hausawa a cikin
duniyar intanet. Idan aka yi nazarin ma’anonin al’ada da masana suka bayar, za
a iya fahimtar cewa:
i. Al’ada
ta shafi fitattun ɓangarori
guda biyu. Ɓangare
na farko ya danganci al’adar
mata da ake kira haila. Na biyu shi ne wanda ta shafi al’amuran da ake gudanarwa a rayuwa.
ii. Al’ada
ta shafi rayuwar mutum gaba ɗayanta.
iii. Al’ada
ta shafi abin da aka saba gudanarwa.
iv. Al’ada
ta shafi abin da mafi yawan jama’a a cikin al’umma suka aminta da kasancewarsa
ko gudanuwarsa cikin wani fasali na musamman.
v. Al’ada
ta shafi wani sanannen al’amari sababbe.
vi. Al’ada
na bambanta daga wuri zuwa wuri ko daga al’umma zuwa al’umma.
Bayan
la’akari da duka waɗannan,
za a iya cewa, al’ada na nufin tsarin rayuwa ta gaba ɗaya wanda ta haɗa da sanannun sababbun al’amuran da ke gudana yau da
kullu bisa wasu tsararrun ƙa’idoji
da matakai da kuma waɗanda
aka saba da wanzuwarsu kara zube ba tare da ƙa’ida ta
musamman ba.
2.1.3 Tasirin Intanet a Kan Al’ummomi da Al’adunsu
A yau, intanet ya zama wani ɓangare na rayuwar al’umma. A cikin giraf
na 1 da ke ƙarƙashin 2.1.1.1 a babi
na biyu, za a ga cewa a shekarar 1991 ne aka samar da kafar
intanet ta farko. A zuwa shekarar 2017, adadin kafafen intanet sun kai biliyan ɗaya da ɗigo bakwai da shida (biliyan 1.76).
Adadin ya sauka a shekarar 2018 da 2019. A 2019, adadin na kafafen intanet ya
kasance kimanin biliyan ɗaya da ɗigo bakwai da biyu (biliyan 1.72). Adadin na kafafen intanet ya ƙara
yawa a shekarar 2020.[18]
A ɓangare guda kuwa, sama da rabin mutanen
duniya ne ke amfani da intanet. An samu wannan rahoto daga ƙididdigar
da Statista ta yi a farkon shekarar 2020. A yayin rubuta rahoton a kafar
Statista, Clement, (2020: 1) ya bayyana cewa:
Almost 4.54
billion people were active internet users as of January 2020, encompassing 59
percent of the global population.
Fassara
Masu amfani da intanet
ya zuwa watan Janairu na shekarar 2020 sun kai kimanin biliyan 4.54, wanda
hakan ya kai kashi 59 na adadin mutanen duniya.
Giraf 2.2: Adadin Masu Amfani da Intanet a Watan Janairu na Shekarar
2020
Madogara:
Climent, (2020: 1)
Ko bayan adadin mutanen da ke
amfani da intanet, masu cuɗanya da duniyar intanet a kullum abin dubawa ne. Kowace kafa aka ɗauka za a tarar da akwai adadin mutane
da ke ziyarta tare da gudanar da al’amura a kowace rana (wata ta fi wata yawan
maziyarta). A ranar 20 ga watan Fabarairu na shekarar 2020, an nazarci
hada-hadar da ke gudana a duniyar intanet daidai ƙarfe
11:30 na dare. A ƙasa an kawo bayanai game da alƙaluman
hada-hadar duniyar intanet na wannan rana.
Hoto 2.9: Hada-Hadar Yau da Kullum ta Wasu Kafafen Intanet 1
Madogara:
Internet Live Stats, (2020: 1)
A hoto na 2.8 da ke sama, za a
iya lura cewa, sama da mutane biliyan biyar ne suka yi amfani da intanet ranar
20/02/2020. Adadin ya fi yawan rabin mutanen duniya. Wannan na nuni da tarisin
intanet ga rayuwar al’umma. Har ila yau, adadin kafafen intanet masu aiki a
wannan rana sun fi biliyan guda da miliyan dubu ɗari bakwai da hamsin da ɗaya. Za a iya hasashen cewa, wannan
adadi ya fi yawan adadin gidajen da ke duniya.[19]
A ɓangare guda kuwa, saƙonnin imel da aka tura sun zarta biliyan
ɗari biyu da hamsin da uku da miliyan ɗari da goma sha uku. Wannan ma na ƙara
nuni ga yadda intanet ya zama wani ɓangaren rayuwar al’umma.
Hoto 2.10: Hada-Hadar Yau da Kullum ta Wasu Kafafen Intanet 2
Madogara:
Internet Live Stats, (2020: 1)
A hoto na 2.8 da ke sama, za a
iya lura cewa, an aika tambayoyi sama da biliyan shida da miliyan ɗari takwas da hamsin da huɗu a Gogul a ranar 20/02/2020. Kada a
manta da cewa, Gogul ba shi kaɗai ne injin nema a duniyar intanet ba.[20]
A ɓangare guda kuwa, adadin sabbin labarai da aka ɗora a kan bulog-bulog a wannan rana sun
haura miliyan shida da dubu ɗari biyar. Baya ga haka, an ɗora labarai sama da miliyan ɗari bakwai da hamsin da ɗaya a kafar Tuwita.[21]
Hoto 2.11: Hada-Hadar Yau da Kullum ta Wasu Kafafen Intanet 3
Madogara:
Internet Live Stats, (2020: 1)
A cikin hoto na 2.9 da ke sama,
za a ga cewa, an kalli bidiyoyi sama da biliyan bakwai da miliyan ashirin da
uku a Yutub a ranar 20/02/2020. Haka kuma, an ɗora hotuna sama da miliyan tamanin da
biyu a kafar Insitagiram. La’akari da dukkanin waɗannan alƙaluma,
haƙiƙa intanet na da matuƙar
tasiri ga rayuwar al’umma.
Wellman, et al (2002: 6) sun
nazarci ayyukan Barlow, (1995) da Wellman, (2001) da Nie, (2001) da Nie,
Hillygus, & Erbring, (2002) inda suka fitar da nau’ukan tasirin da intanet
ke yi kan al’umma. Sun bayyana su kamar haka:
i. The
Internet decreases community
(Intanet na samar da koma-baya ga al’umma)
ii. The
Internet transforms community
(Intanet na kawo sauye-sauye ga rayuwar al’umma)
iii. The
Internet supplements community
(Intanet na samar da wata al’umma ta daban)
Koma-baya
da intanet ke samarwa ga al’umma ya shafi fannonin rayuwarsu daban-daban.
Misali, al’amuran nishaɗi da ɓata lokaci da intanet ke ƙunshe da su na ɗauke wa mutane hankali da shagaltar da su. A haka ne
al’umma ke auren intanet a maimakon yin amfani da lokutansu wajen aikata
ayyukan da za su taimake su a matsayin ɗaiɗaiku da a matsayin al’umma. Sauye-sauye da intanet
ya zo da su kuwa nau’uka biyu ne. Akwai masu amfani, akwai kuma waɗanda ke mazaunin ƙalubale.[22] A ɓangare guda kuwa, al’umma ta daban da intanet ke
samarwa na nufin al’amura da hulɗayya da
ke wanzuwa a duniyar intanet.
Za a ƙara
fahimtar tasirin intanet yayin da aka nazarci tasirin kafafen sada zumunta ga
zamantakewar yau. A duniyar yau, kafafen sada zumunta sun zama wani ɓangare na rayuwar al’umma. Kusan za a
iya cewa, duniyar mutane ba za ta iya rayuwa ba sai da su. Dalili kuwa shi
ne, rayuwar mutane da dama ta dogara kacokan kan ire-iren waɗannan kafafe. Nan ne cinsu, nan ne shansu![23]
A rahoton da Clement, (2019: 2)
ya fitar, masu amfani da kafar Whatsapp a watanni kaɗan bayan samar da kafar sun kai kimanin
biliyan guda da miliyan ɗari biyar (1,005,000,000). Binciken da Jayasekara, (2015) ya gudanar ya
nuna cewa, ana samun ƙaruwar masu amfani da kafafen sada
zumunta matuƙa. Masana da manazarta da dama sun yi bincike da
rubuce-rubuce game da tasirin kafafen sadarwa a zamantakewa.[24]
Siddiqui & Singh sun bayyana cewa:
Now a day’s
social media has been the important part of one’s life from shopping to
electronic mails, education and business tool. Social media plays a vital role
in transforming people’s life style. Siddiqui & Singh, (2016: 71)
Fassara
A yau, kafafen
sada zumunta sun zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan’adam tun daga kan sayayya da tura saƙonni da ilimi
har zuwa kasuwanci. Kafafen sada zumunta suna taka muhimmiyar rawa dangane da
salon rayuwar mutane.
Lallai wannan batu haka yake,
domin kuwa ko a ƙasar Hausa akwai mutane da dama da suka
raja’a matuƙa kan kafafen na sada zumunta. Akwai muhimman ɓangarorin rayuwa da waɗannan kafafe suka fi shafa. Sun haɗa da:
i. Sada zumunta
ii. Tattaunawa a matakin ɗaiɗaiku ko ƙungiyoyi
iii. Kasuwanci da cinikayya
iv. Ilimi da karantarwa
Tun farko dai waɗannan kafafe an samar da su ne domin
sada zumunta. Misali, Fesbuk da aka samar a wajajen 2004, ya kasance hoɓɓasa ne na ɗalibin Jami’ar Harvard mai suna Mark
Zuckerberg. Ya ƙirƙire ta ne a matsayin kafar sada zumunta
tsakanin ɗaliban makarantar ta Harvard. Sannu a hankali ɗaliban wasu makarantu na
daban suka fara amfana da ita.[25]
A shekarar 2006 ne kuma aka fitar da ita a matsayin kafar sada zumunta da
duniya gaba ɗaya za ta iya amfani da ita (Baruah, 2012: 4; Clement, 2019: 2). A
zuwa yau, Fesbuk ke kan gaba a duk cikin kafafen sada zumunta. Bayan ita, sai
wasu daga cikin fitattun kafafen sada zumunta, su ne:
a. Instagram
b. Twitter
c. Whatsapp
2.2 Bitar Ra’i
Wannan aiki ya ƙunshi
manyan batutuwa guda biyu masu cin gashin kansu, wato “al’ada” da “intanet.”
Al’adar kuma ta Hausawa ce. A bisa wannan dalili, babu wani ra’i da ya fi
dacewa da ya jagoranci wannan ɓangare na binciken face “Bahaushen Ra’i.” Akwai masana da
ke goyon bayan amfani da Bahaushen Ra’i wajen gudanar da bincike. Bunza, (2019)
na ɗaya daga cikinsu inda yake cewa:
Lokaci ya yi da
al’adunmu da tunanin magabatanmu ya yi tasiri ga iliminmu da bincike-binciken
iliminmu. Ban ce ra’o’in Turawa na ilmi na a kan kuskure ba, amma a kowane irin
al’amari gara a kai na hannu gida kafin a dawo a kama na dawa. (Bunza, 2019:
721).
Idan aka yi la’akari da ma’anar
karin magana kamar yadda wasu masana suka bayyana, za mu tarar da cewa sun kai
matsayin hanyar ɗora aiki ko ra’i kai tsaye. Gray, (1987) kamar yadda aka rawaito a cikin
Tambuwal, (2018: 32) ya ce karin magana: “Gajeren zance ne wanda ke cike da
gaskiya da ƙayatarwa.” An dai kuwa san cewa, kafin a tabbatar da wani
ra’ayi a matsayin gaskiya, dole sai an sha gwaji ana samun sakamako marasa cin
karo da juna.
Za a sake gaskata wannan fahimta
yayin da aka yi la’akari da masana da ke kallon karin magana a matsayin:
“...maganganun hikima da fasaha, wadda ta cikin waɗannan zantukan ake fahimtar halaye da ɗabi’un wannan al’umma.” (Kirk-Green,
1966 da Skinner 1980 a cikin Tambuwal, 2018: 31). Da ma dai ta hanyar ra’i ne
ake fahimtar yanayin wani al’amari. John, (1998: 364) ya rawaito Poole da Van
de Ven na cewa: "A good theory is, by definition, a limited and fairly
precise picture.” Fassara: “Ta fannin ma’ana, ingantaccen ra’i
shi ne hoton wani al’amari ko yanayi a taƙaice.” Haƙiƙa karin
maganar Bahaushe na da wannan matsayi na bayyana hoton al’amari a taƙaice.
Ra’ayin Malumfashi da Nahuce,
(2014) ma ya bayyana karin magana a matsayin abin da zai iya ɗaukar ma’anar ra’i. Suna da fahimtar
cewa, karin magana na nuni ga al’ada da salon rayuwar al’ummar da ke amfani da
waɗannan karin maganganu. Idan kuwa haka ne, karan karin maganganun Bahaushe sun
kai tsaikon zama a matsayin ra’i. Idan muka duba ma’anar ra’i wanda Sashen
Ilimin Jarida da Sadarwa ta Jami’ar Fulorida da ke Amurka (College of
Journalism and Communications University of Florida) ta bayar, za mu sake tabbatar
da karin maganganun Bahaushe ra’o’i ne. Sun bayyana ra’i da cewa:
Theory explains
how some aspect of human behavior or performance is organized. It thus enables
us to make predictions about that behavior. (UF College of
Journalism and Communications, (ND)).
Fassara
Ra’i yana bayani
a kan tsari da fasalin ɗabi’ar ɗan’adam ko aikinsa. A bisa haka, yana ba mu damar
yin hasashe dangane da wannan halayyar (ta ɗan’adam).[26]
Ado, (2017: 32) ya kawo fassarar
ma’anar ra’i da Oxford, (1998) ya samar. A wannan fassara, ra’i na nufin:
“Tunani ko jerin tunane-tunane waɗanda aka shawarta cewa su ne ke iya yin bayani kan wani
abu da ya faru ko zai faru.” Wannan ma’ana na ƙara
tabbatar da karin magananganun Bahaushe a matsayin ra’i ko hanyar ɗora bincike. Dalili kuwa shi ne, bai
fita a da’irar ma’anar karin magana da Ɗanyaya, (2007: vii) ya bayar ba. Ya ce: “Karin magana zance ne gajere, mai
faɗakarwa kan zaman duniya.” An dai san cewa, faɗakarwa na ƙunshe
da bayani kan lamura da sakamako mai
kyau ko marar kyau da ka iya biyo bayan aikata wani aiki.
Duk da haka, akwai masana da suke
da fahimtar cewa, karin magana bai kai ya tsaya a mazaunin ra’i ba. A maimakon
haka, sai dai a ɗauke shi a matsayin “hanyar ɗora aiki.”[27],[28]
Wannan bincike ya tafi kan ra’ayi na biyu (karin magana a matsayin hanyar ɗora aiki) bisa waɗannan dalilai:
a. Har yanzu masana harshe da
al’ada da adabin Hausa ba su kai matsaya kan karin maganganu a matsayin ra’i ko
hanyar ɗora aiki ba.
b. Ko ba komai, ra’i ma jagoranci
ne na aiki. Hanya ce da ake ɗora tunanin bincike (alƙiblar
da zaren tunanin bincike zai nufa). A bisa wannan dalili, ko da an kai matsayar
aminta da karin magana a matsayin ra’i, hakan ba zai saɓa da matsayar wannan bincike ba.
An ɗora wannan aiki kan karin maganar
Bahaushe ta: “Zamani Riga” domin jagorancinsa. A tunanin Bahaushe,
zamani tamkar riga ce wato yayi-yayi. “Wato ke nan idan ya zo sai kowa ya ɗauka ya sa a jikinsa?” (Yunusa, 1989:
40). A lokacin yayin abu, sai a yi shi. Bayan yayin ya wuce kuwa, sai a watsar
domin a riƙi sabon yayi. Bahaushe ya ƙara ƙarfafa
wannan fahimta a karin maganarsa da ke cewa: “Lokacin abu a yi shi!” Duk wanda bai taka rawar kiɗan gangar zamani ba, lallai kafin ya
farga an masa fintinkau.[29]
Akwai ayyuka da suka gabata waɗanda karin maganganu ke musu jagoranci a
matsayin ra’o’i ko hanyoyin ɗora aiki. Bunza, (2019: 721) ya yi amfani da “Ba banza ba
ƙuda a warki” a cikin bincikensa mai taken “Ƙwarya a
Farfajiyar Adabi da Al’adun Bahaushe.” An wallafa wannan maƙala
cikin East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature
Vol. 2, Issue 12. Karin maganar ya yi wa binciken nasa jagoranci wajen
binciko dalilan da suka sa ƙwarya ta mamaye adabi da al’adar
Bahaushe. Lallai “ruwa ba ya tsami banza.”
Sani, Buba & Mohammad, (2019: 45) sun yi amfani da karin maganar da
ke cewa: “Mai nema yana tare da samu” yayin gudanar da bincikensu. Binciken na
da taken: “Wanda Ya Tuna Bara...: Biɗa da Tanadi a Tsakanin Hausawa Matasa a Yau.” An buga maƙalar a
cikin Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences, Vol. 1,
Issue 1 & 2. Ra’in ya jagoranci binciken nasu wajen bayyana cewa,
takunkumin tattalin arzikin da ya dabaibaye matasan Hausawa a yau na da alaƙa da
rashin hazaƙarsu wajen fafutukar neman na kai. Ko da ma dai, “Ba a
kama zomo daga zaune.”
Shi kuwa Yahaya, (2020: 7) ya yi
amfani da karin magana ne a matsayin hanyar ɗora aiki. Ya zaɓi karin maganar nan na “Zamani Riga.” A
kansa aka gina bincikensa mai taken: “Damben Hausawa a Zamanance.”[30]
Dangane da wannan hanya ta ɗora aiki, Yahaya ya ce: “Wannan karin magana manufarsa ita ce bayyana yadda
lokaci wato zamani yake shiga cikin ɓangarorin rayuwa ya samar da tsari da zai tafiyar da wani
sha’ani daidai da zamani” (Yahaya, 2020: 7).
Fahimtar Bahaushe ta “Zamani
riga” ta tafi kan cewa, karɓar sauye-sauyen da zamani ya zo da su dole ne domin samun ci gaba mai ɗorewa. A bisa wannan tunani, abin da ya
fi dacewa ga Hausawa shi ne su rungumi intanet a matsayin abin da zamani ya zo
da shi. Da yake ana magana a kan al’adunsu ne, saka rigar zamani zai ba su
damar:
i. Tantancewa da ƙalubalantar
duk wasu bayanan ƙarya dangane da al’adunsu da ke duniyar intanet, da
ii. Samar da ingantattun bayanai
dangane da al’adun Hausawa a duniyar ta intanet.
Wani hanzari ba gudu ba shi ne,
wannan hanyar ɗora aiki kaɗai ba za ta iya biyan buƙatar binciken gaba ɗaya ba. Kamar yadda John, (1998: 364) ya
bayyana, ra’i dole ne ya kasance ya wadatar a fannonin da suka haɗa da: “definitions, domain,
relationships, and predictive claims to answer the natural language questions
of who, what, when, where, how, why, should, could and would.” Ma’ana, dole
ne su wadatar da ɓangarorin: “ma’anoni da bagire da dangantaka da ra’ayoyin da ke samar da
amsoshi kan tambayoyi kamar “wa?” da “me?” da “yaushe?” da “a ina?” da “ta
yaya?” da “me ya dace?” da “me zai yiwu?” da “me za a yi?””
A bisa wannan dalili, za a yi
amfani da wani ra’in na daban wanda zai mayar da hankali kan ɗaya ɓangaren binciken (intanet). Masana da
dama sun tabbatar da cewa, mai bincike na iya amfani da ra’i sama da guda
musamman domin ya samu ra’o’in da suka dace da dukkanin ɓangarorin bincikensa.[31]
Ojua, ya bayyana cewa:
In most social
science and humanity, you should know that no single theory best correctly
explain a social issue. Ecclectic usage of theories is very adequate. (Ojua, 2019:
1).
Fassara
Ya kamata a
fahimci cewa a mafiya yawan fannonin ilimin kimiyyar zamantakewa da na
mu’amala, babu wani ra’i guda ɗaya da yake
bayanin wata matsala yadda ya kamata. Amfani da ra’i sama da guda shi ne ya fi
dacewa.
Ra’in da ke jagorancin ɓangare na biyu na wannan bincike shi ne Pulatoriyya
(Platonism). Da zarar an ambaci wannan ra’i, hankali zai koma kan fitaccen
malamin falsafar nan Plato[32]
(Gerson, 2005: 253). Duk da haka, abin lura shi ne, a farkon lokaci ba a kiran
wanan ra’i da Pulatoriyya. Daga cikin mabiya ra’in da ba su rayu lokacin da aka
sanya masa wannan suna ba akwai Speusippus[33]
da Xenocrates[34] da Antiochus[35]
da Numenius. Wannan ya samar da babbar tambaya cewa: “Shin Plato mabiyin Pulatoriyya
ne?” A bisa haka ne Gerson, (2013: 3) yake cewa:
The question is
only marginally more illuminating if we take it to mean “Would Plato have
agreed with one or another of the historical, systematic representations of his
philosophy?” Naturally, this question, like all questions about counterfactuals
in the history of philosophy, is unanswerable. (Gerson, 2013: 3)
Fassara:
Tambayar ba za
ta kasance mai armashi ba har sai idan tana nufin cewa: “Shin Plato zai yarda
da tarihi ko tsararren wakilci na falsafarsa?” A al’adar duniya, wannan
tambayar ba mai amsuwa ba ce, tamkar dai sauran tambayoyin idan-da[36] a falsafance.
Lura da wannan, binciken nan na
da fahimtar cewa, Pulatoriyya tunani ne da falsafa ta Plato. Duk da haka, ana
iya samun sauye-sauye kan tunani da sigogin ra’in na asali. Hakan na faruwa
kasancewar a kullum akan samu sabbin tunani. Baya ga haka, masu bincike na iya
gyaran fuska ga ra’i domin dacewa da tsarin bincikensu.
Pulatoriyya ya tafi kan cewa,
rayuwa ta ƙunshi gaskiya nau’uka biyu (wanda ake kallo da wanda ba a gani). Wannan tunani ya tsaya a tsakiyar fahimtar
mabiya Ɓoyayyiyar Gaskiya (Incorporealism)
da mabiya Zahiriyya (Realism). ‘Yan falsafa da ke kallon gaskiya a ɓoye take suna da ra’ayin cewa duk wani
abin da ake gani a duniya rayawar zuci ce kawai. Misali, launin fari ko
baƙi ko shuɗi da rigar mutum ke ɗauke da shi, ba zahiri ba ne. A maimakon
haka, rayawa da ƙwaƙalwa ta yi na samuwar launin ne ya sa
har idanu ke kallon sa.
Masu fahimtar Zahiriyya kuwa, sun
tafi kan cewa, babu wani abu ɓoyayya. Duniya ɗungurungum ta taƙaita ne a kan abubuwan da ɗan’adam ke iya kallo. A taƙaice ke
nan, Pulatoriyya ya tsaya ne a tsakaninsu. Ya haɗa tunanin duka biyu. Wannan ne ya sanya
mabiya ra’in suke ɗora ayar tambaya kan Baɗiniyya (sprituality) da rayuwa bayan mutuwa da makamantansu. A wannan
tunani, abubuwan da ido ke iya kallo ko kunne ke iya ji ko jiki ke iya taɓawa su ne kaɗai ke wanzuwa.
A ra’ayin Pulatoriyya, akwai
abubuwan da suna wanzuwa ne a duniyar baɗini. Babban misali a nan shi ne kurwa. Sai dai ko cikin
mabiya Pulatoriyya akan samu muhawarori dangane da ire-iren waɗannan ɓoyayyun gaskiya. Misali, ra’in ya fi
mayar da hankali kan bayanin yadda kurwa take, sama da abubuwan da suka haɗu suka samar da kurwar. Thein, (2018:
57) ya jadda hakan inda yake cewa:
... despite the
very different aim and setting of both dialogues, the problem is much the same:
what exactly is the soul that performs the actions that reach beyond the states
of our visible and tangible body? (Thein, 2018: 57)
Fassara
... duk da
bambancin da ke tsakanin manufa da kuma wurin zama da aka gudanar da waɗannan muhawarori, kanun muhawarar guda ne: Kai
tsaye mece ce wannan kurwar da take da siffofin da suka wuce ganin idonmu ko ji
a jikinmu?
A nan, muhawarorin da marubucin
ke nufi su ne (i) Me kurwa ke yi, kuma me ake iya mata? (ii) Mece ce kurwa? Pulatoriyya
ya fi damuwa da tambaya ta biyun. Kamar yadda yake a tunanin Pulatoriyya, sanin
kurwar (sama) shi zai ba da damar sanin abin da ya samar da ita da kuma
abubuwan da take iya yi da waɗanda ake iya mata (ƙasa).
Wata siffa ta Pulatoriyya ita ce
jaddada cewa: (a) A cikin kowane abu ko lamari akwai abu mai kyau da marar
kyau.[37]
Haka kuma (b) Abu marar kyau shi ke gurɓata mai kyau har daga ƙarshe
ya lalata shi. A dangane da wannan, Thein, (2018: 65) ya rawaito cewa: “The
bad is what destroys and corrupts, and the good is what preserves and benefits.”
Ma’ana: “Abu marar kyau shi ke gurɓatawa da lalatawa. Abu mai kyau kuwa shi ke adanawa da
amfanarwa.” Wani mawaƙi ya gina waƙarsa
kan irin wannan tunani. Ya kira kafafen sada zumunta na intanet da suna “Duniyar Matasa.” Ya ce:
Soshiyal midiya duniyar matasa,
Mu yaɗa alkairi kar mu yaɗa zamba.
(Ɗan’iro
Katsina: Waƙar Soshiyal Midiya Dandalin Matasa)
Akwai masana da suke hasashen
wannan ra’i na da alaƙa da falsafar ‘Yan Ƙwaƙƙwafi
(skeptical philosophers).[38]
Daga cikin ‘Yan Ƙwaƙƙafin farko akwai Arcesilaus[39]
da Carneades[40] da Clitomachus[41]
da kuma Philo wanda ya rayu tsakanin 158 - 84 B.C.E. (Gerson, 2005: 253-254).
Ba abin mamaki ba ne a samu dangantakar ra’in Pulatoriyya da falsafar ‘Yan Ƙwaƙƙwafi.
Dalili kuwa shi ne, gaba ɗaya duniyar falsafa da ma ta tattara kan ra’ayin binciken haƙiƙanin
lamura ne. Sukan yi tambaya da suka haɗa da:
i. Me? (What?)
ii. Me ya sa? (Why?)
iii. Ta yaya? (How?)
iv. A ina? (Where?)
v. Mene ne tabbaci? (How
certain/How sure?)
vi. Shin an kai a tabbatar?
(Right to be sure?)
Za a iya hasashen cewa, ra’in Pulatoriyya
na cike da ire-iren waɗannan tambayoyi. Yayin da Gerson, (ND: 7) yake bayani a kan fitattun
siffofin Pulatoriyya, sai ya ce:
What is most
distinctive about Platonism is that it is resolutely and irreducibly ‘top-down’
rather than ‘bottom-up’. A top-down
approach to philosophical problems rejects and a bottom-up approach accepts the
claim that the most important and puzzling phenomena we encounter in this world
can be explained by seeking the simplest elements out of which these are
composed.
Fassara
Siffar da ta
kasance fitacciya ga Pulatoriyya ita ce dogewarsa kan tsarin “daga sama zuwa ƙasa” a maimakon
“daga ƙasa zuwa sama.”
Tsarin tunkarar matsalolin falsafa na sama zuwa ƙasa ya yi watsi da ikirarin cewa abubuwa mafiya
muhimmanci da ɗaukar hankali da
ake cin karo da su a rayuwar duniya ana iya bayaninsu ta hanyar ƙwanƙwance mafi ƙanƙantar abubuwan da suka taru suka haɗa su. Tsarin tunkarar matsalolin falsafa na ƙasa zuwa sama ya
aminta da wannan zance.
‘Yan Zahiriyya na da fahimtar
cewa, batutuwa irin su ilimi da hankali ba sa wanzuwa sai da ɗan’adam. Kafin a fahimce su, sai an
fahimci ɗan’adam tare da fahimtar mafi ƙanƙantar abubuwa da suka samar da shi,
sannan suka samar da abubuwan da yake cuɗanya da su. Pulatoriyya kuwa yana kallon waɗannan batutuwa (misali ilimi da hankali
da lura da rayuwa da makamantansu) suna wanzuwa ne ta hanyar cin gashin kansu.
Nau’uka ne na gaskiya waɗanda ba a iya gani. Fahimtarsu shi ne zai ba da ƙarin
haske dangane da halittu da ke ɗauke da su.
A hasashe irin na nazari, za a
iya cewa akwai ayyuka da suka gabata waɗanda aka ɗora su kan ra’in Pulatoriyya. Kasancewar babu wanda hannu
ya kai kansa ba hujja ba ce ta rashinsu. Abin la’akari shi ne daɗewar da ra’in ya yi da kuma yawan
mabiyansa tun daga zamanin Plato zuwa yau.
Gerson, (2013) ya yi ƙoƙarin
yin bayani a kan haƙiƙanin abin da ake kira Pulatoriyya.
Wannan ya sa taken aikin nasa ya kasance tambaya “What is Platonism?” Wato
“Mene ne Pulatoriyya?” Ya bibiyi tarihin Pulatoriyya sannan ya zayyana wasu
daga cikin mabiyan ra’in. Daga nan ya mayar da hankali kan nazarin tunanin mabiya ra’in. Aikin nasa na da shafuka talatin. Ya fito cikin
mujalla da aka yi wa suna From Plato to Platonism. Wato “Daga Rayuwar
Plato Zuwa Ra’in Pulatoriyya.”
Pena, (2018) ya rubuta maƙala mai
suna “Platonism as a Philosophical Method,” wato
“Pulatoriyya a Matsayin Ra’in Falsafa.” An wallafa wannan maƙala a
cikin mujallar ƙasarsu Platon (Athens). Sunanta
Athens Journal of Humanities & Arts (Volume 5, Issue 1 – Pages 45-60).
A ciki ya yi ƙoƙarin bayyana ma’anar Pulatoriyya. Daga nan ya mayar da
hankali kan bitar wasu maganganun Plato. Daga shafi na 52 zuwa 55, ya yi ƙoƙarin
danganta falsafar Pulato da babban ɗalibinsa wato Aristotle.[42]
Editocin Encyclopedia Britannica[43] (Augustyn, et al., 2020) sun yi rubutu mai taken: Platonic Criticism (Tarken Pulatoriyya). A ciki sun kawo bayani dogo mai gamsarwa dangane da
ra’in. Wannan ya haɗa da dangantakar ra’in da tunanin addinin Kiristanci da kuma sauran ɓangarorin falsafofi. Sun kuma kawo
fahimtar ra’in a kan duniya da al’muran da ke gudana cikinta (waɗanda ake iya gani da waɗanda ba a iya gani).
Ire-iren waɗannan ayyuka da kai tsaye suke magana a
kan Pulatoriyya, suna ƙara fito da ra’in fili. Bayan haka, suna nuni ga
shahararsa, da cancantarsa wajen jagorancin bincike. Ko ba komai Plato na ɗaya daga cikin manyan fitattun malaman
falsafa na farko. Yana ɗaya daga cikin malaman falsafar da ayyukan da aka gudanar kansu ke da ɗimbin yawa sama da na saura.
A wannan bincike, gurbin Pulatoriyya
a bayyana yake. Binciken zai duba tasirin intanet ne (sama) kan al’adun Hausawa
(ƙasa) tamkar dai yadda Thein, (2018: 57) ya yi bayanin
tsarin tunkarar mas’ala ta Pulatoriyya (daga sama zuwa ƙasa).[44]
Kai tsaye za a fahimci hakan idan aka yi la’akari da cewa:
i. Gaskiya da ake kallo ta shafi
suturarmu da abincinmu da gine-ginenmu da ababen hawanmu da muhallanmu da
wasanninmu da sauran abubuwa makamantan waɗannan.
ii. Gaskiya wanda ba a kallo ta
shafi duniyar intanet. Wannan ya haɗa da al’adunmu da ke ciki, da siyasarmu da muhallanmu da
harkokinmu da tufafinmu da abincinmu da dukkanin sauran abubuwa da ke wanzuwa a
cikin intanet. A taƙaice, a wannan ɓangare an samu duniyoyi guda biyu:
Duniyar Zahiri da Duniyar Intanet.[45]
Yana da kyau a kula da cewa, cuɗanyar da ke tsakanin duniyoyin biyu
(intanet da zahiri) ba ya sa a ce intanet ba duniya ba ce mai zaman kanta.
Misali, Musulmai sun yi imani da cewa, duk abin da ɗan’adam ke aikatawa mala’iku na
rubutawa. Mazaunin mala’iku ba duniyar mutane ba ne, duk da sukan zo. Haka ma
Musulmai sun yi imani da zaman barzahu. Idan aka yi nazarin ƙwaƙƙafi ga
lamarin, sai a tarar da cewa, akwai dangantaka tsakanin rayuwar duniyar mutane
da rayuwar barzahu da kuma rayuwar duniyar sararin samaniya. Dole ne kuma a ɗauki kowace a matsayin rayuwa mai cin
gashin kanta. Dalili shi ne, kowace tana da tsare-tsarenta da yanaye-yanayenta
wanda hakan ya bambanta ta da ‘yar uwarta. A fahimtar wannan bincike, za a iya
bayyana duniyoyi da ake da su kamar haka:
a. Duniyar mutane (duniyar
zahiri)
b. Duniyar intanet
c. Duniyar tunani
d. Duniyar mafarki
e. Duniyar sarari (duniyar sama)
f. Duniyar matattu (barzahu)
g. Duniyar tatsuniya
Wannan bincike na da fahimtar
cewa, duniyar intanet na ɗauke da kyawawan abubuwa da kuma munana. Hakan ya yi daidai da ikirarin Pulatoriyya
kamar yadda Thein, (2018: 65) ya bayyana. Kyawawan al’amura su ne za su iya
amfanarwa. Munana kuwa, za su iya gurɓata kyawawan ko ma su lalata su. Ke nan, idan ba a yi hoɓɓasa ba dangane da al’adun Hausawa a
duniyar intanet, gurɓatattun bayanai da ra’ayoyi marasa kyau na iya lalata al’amarin gaba ɗaya. Zai iya kai matsayin da ba a kallon
komai sai rashin amfanin intanet dangane da al’adun Hausawa. Za a iya yarda da
wannan yayin da aka yi la’akari da wasu kafafen intanet na Hausa da kai tsaye
suka ci karo da addini da al’adun Bahaushe. Babban misali a nan shi ne kafar
intanet ɗin nan da ta shahara wajen kawo hotuna da bidiyoyi da maganganun batsa,
wato Batsa Posts.
2.3 Bitar Ayyuka Masu Dangantaka ta Kai Tsaye da Aikin
Wannan
bincike ya ci karo da ayyuka da dama da ke da dangantaka da shi. Mafi yawansu
an yi su ne cikin wasu harsuna ba Hausa ba. Wannan ɓangare na binciken zai bibiyi ayyukan da suka gabata
waɗanda ke da matuƙar kama da binciken. Hakan zai tabbatar da an
kauce wa maimaita aikin da aka riga da aka gudanar. Bugu da ƙari, nazartar ayyukan zai ba da haske tare da
jagoranci ga wannan bincike. An kawo bitar daki-daki inda aka fara da kundayen
digiri. Daga nan an gangaro kan litattattafai da mujallu da muƙalu.[46]
2.3.1 Kundayen Digiri na Uku
Wannan
bincike bai ci karo da wani kundin digiri na uku da ke da alaƙa da shi na kai tsaye ba. Duk da haka, an ci karo
da kundayen da suka taɓo
batutuwa masu alaƙa da binciken da ake gudanarwa. Sun haɗa da aikin Nadama, (1977). A cikin aikin an kawo
batun zuwan Turawa ƙasar Hausa wanda ya yi sanadiyyar rugujewar daulolin
ƙasar
Hausa da dama. Dangantakar kundin nasa da wannan bincike kawai shi ne
kasancewar dukkanninsu biyu sun taɓo batu
kan sauye-sauyen da ke aukuwa sakamakon sauyin zamani. Akwai kuma kundin Akodu, (1985) inda ya yi magana kan
sauye-sauye da aka samu ga rayuwar Maguzawa a zamanance. ‘Yar alaƙar da
kundin yake da shi da wannan bincike ba ta wuce batun zamananci ba.
Aikin Sallau, (2009) ma na da ‘yar alaƙa da wannan bincike
kasancewar ya taɓo
batun sauye-sauyen da zamani ya samar ga sana’ar wanzanci. Aminu, (2015) kuwa
ya mayar da hankali wajen nazartar nason al’adun Turawa a kan al’adun Hausawa
musamman a lardin Sakkwato. Tarihin zuwan Turawa kuwa ba ya cika ba tare da an
taɓo batun sauye-sauyen
zamani ba. Hakan ne kuma abin da ya alaƙanta shi da binciken da ake gudanarwa.
2.3.2 Kundayen Digiri na Biyu
Aikin Nasir (2009), ya kasance
yunƙuri irinsa na farko a fagen karatun Hausa inda aka samu
gabatar da tatsuniya a zamanance cikin sigar katun (hoto mai motsi). Kundin
nasa na da danganta da wannan aiki kasancewar dukansu biyu sun mayar da hankali
kan Hausa a duniyar zamaninta.
A
shekarar 2009, Almajir ya yi rubutu kan yadda abubuwan zamani suka yi tasiri
kan rayuwar matasa Hausawa. Manya daga cikinsu sun shafi kafafen intanet ne.
Daga ciki kuwa har da Fesbuk da Was’af a matsayin kafafen sadarwa. Akwai kuma
kafafen da ke gurɓata
tarbiyya. Kundin Almajir na da dangantaka da wannan bincike kasancewar dukansu
sun shafi intanet da al’adun Hausawa. Duk da haka, Almajir bai mayar da hankali
kan wakilcin al’adun Hausawa a duniyar intanet ba. Ya fi karkata kan nazarin
yadda duniyar ta intanet ke shafar al’adun Hausawa, musaman matasa.
Mukoshy
(2015), ya ya yi ƙoƙarin tattara wasu muhimman kalmomin kwamfuta
musamman waɗanda suka shafi intanet tare da
samar da fassarorinsu. Kalmomin da ya fassara sun haɗa da na intanet da na kwamfuta da na burauzozi da
makamantansu. A shafi na 108, ya yi kira da cewa: “Ya kamata Hausawa su shiga
cikin sha’anin nazarin fannin kwamfuta, su yi ruwa, su yi tsaki a dukkan ɓangarorinta.” Ya nuna ɓunƙasa da matuƙar alfanu da tagomashin da harkar intanet da
kwamfuta ke da shi a shafuka na 107-108.
Kundin
Mukoshy na da da dangantaka da wannan bincike kasancewar duka sun taɓo duniyar intanet. Bugu da ƙari, duka suna kira da faɗakar da Hausawa kan inganta matsayinsu a wannan
duniya ta intanet. Duk da haka, ayyukan biyu mabambanta ne. Mukoshy ya mayar da
hankali ne kan fassarawa da adana kalmomin fannu da suka shafi intanet da
kwamfuta. Wannan aiki kuwa ya karkata ne kan nazartar al’adun Hausawa a duniyar
intanet da kira ga samar da wakilci nagartacce a duniyar.
Wani aikin da ke da dangantaka da
wannan bincike shi ne na Magaji, (2018). Kundin ya bayyana cewa, hanyoyin
sadarwar zamani sun yi tasiri a kan zumuncin Hausawa. Hanyoyin kuwa sun shafi
kafafen intanet na sadarwa irin su Was’af da Facebook. Sanannen abu ne cewa zumunci
na daga cikin ɓoyayyun al’adun Bahaushe.[47]
Kundin Magaji da wannan bincike suna da dangantaka kasancear dukansu sun taɓo tasirin intanet a kan al’adun Hausawa.
Duk da haka, kundin na Magaji ya taƙaita ne kawai a kan al’adar zumunci. Wannan
bincike kuwa ya shafi al’adun Hausawa mabambanta da ake samu a duniyar intanet.
2.3.3 Kundayen Digiri na Farko
Masana
da dama na da ra’ayin cewa binciken kundayen digiri na farko na da rauni. Duk
da haka, wannan bincike ya ci karo da wasu kundayen digiri na farko da ke da
matuƙar
dangantaka da shi. A bisa haka an yi bitar su duk da raunin da suke da shi. Sun
haɗa da:
Makuwana (2011), ya nazarci yadda
Hausa ta yaɗu a duniyar intanet. Yaɗuwar ta haɗa da kafafen intanet daban-daban da kuma kafafen sada zumunta. Abin da ya
bambanta kundin da wannan bincike shi ne, Makuwana ya mayar da hankali ne kan
nazartar bunkasar Hausa a duniyar intanet. Wannan bincike kuwa zai bibiyi
al’adun Hausawa a duniyar intanet tare da nazarin hanyoyin inganta su.
Ashiru (2012), ya rubuta kundin
digiri na farko wanda ke da matuƙar dangantaka da wannan bincike. A ciki
an nazarci hanyoyi daban-daban da adabin Hausawa ke bunƙasa a
dalilin intanet. Wannan ya haɗa da rubuce-rubucen adabi da ke kan kafafen intanet. Bugu
da ƙari, akan ɗora waƙoƙin Hausa har ma da littattafai da aka
karanta a matsayin odiyo. A taƙaice, kundin ya mayar da hankali kan yaɗuwar adabin Hausawa a intanet tamkar dai
yadda wannan bincike ya duƙufa wajen nazartar al’adun Hausawa a
intanet ɗin. Wannan bincike bai taƙaita ga nazartar adabin Hausa a duniyar
intanet ba kawai.
Aikin
'Yartsakuwa (2017), ya mayar da hankali wajen nazartar sadarwa a kafar intanet
ta Whatsapp. Daga shafi na 15 zuwa na 17, an kawo tarihin intanet. A shafi na
37, an kawo illolin intanet kan al’adun Hausawa. Illolin sun fi shafar gurɓata tarbiyya da ɓata lokaci. Kundin na da alaƙa da wannan bincike musamman la’akari da cewa
dukansu sun mayar da hankali kan al’adun Hausawa da duniyar intanet. Duk da
haka, kundin ‘Yartsakuwa ya fi karkata kan sadarwa a intanet. Bai bibiyi
matsayin al’adun Hausawa a ciki ba. Bai kuma yi nazarin hanyoyin inganta su ba.
2.3.4 Mujallu da Muƙalu
Almajir (2008), ya rubuta maƙala wadda
ta mayar da hankali kan nazartar matsayin Hausawa a duniyar intanet da yadda
ake amfani da ita wajen sadarwa. Sadarwa da Hausa ya shafi kafafen intanet na
sada zumunta daban-daban. Bambancin maƙalar da wannan bincike shi ne, Almajir
ya bibiyi Hausa ne da kuma al’amarin sadarwa cikin Harshen Hausa a duniyar intanet.
Wannan bincike kuwa zai mayar da hankali kan intanet da al’adun Hausawa.
Amfani (2010), ya rubuta kan kalomomin intanet na Hausa. A ciki ya kawo kalmomi da dama da ake amfani da
su a harshen Hausa waɗanda
suka shafi intanet. Haƙiƙa maƙalar ta Amfani na da dangantaka da wannan bincike
kasancewar duk sun taɓo
intanet da kuma Hausawa. Duk da haka suna da bambanci domin binciken nasa ya taƙaita ne a kadadar harshen Hausa. Wannan bincike
kuwa ya fi mayar da hankali kan zawarcin al’adun Hausawa a duniyar intanet.
A
shekarar 2013 an fitar da gagarumin aiki da ya shafi al’ada da zamananci.
Hukumar Raya Tarihi da Al’adu ta Jahar Katsina (Katsina State History and
Culture Bureau) ita ce ta gudanar da gagarumin taron ƙara wa juna sani tare da haɗin guiwar Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina. An
tattara muƙalun da
aka gabatar yayin wannan taro inda aka wallafa su a matsayin babban kundi a
watan Yuni na shekarar 2013. Littafin ya ƙunshi muƙalu da ke da alaƙa da wanna aiki. Daga cikinsu akwai Adamu, (2013)[48]
da Ahmad, (2013)[49]
da Garba, (2013)[50]
da Getso, (2013)[51]
da Guibi, (2013)[52]
da Isah, (2013)[53]
da Kiyawa, (2013)[54]
da Mai’aduwa, (2013)[55]
da Mwami, (2013)[56]
da Shehu, (2013)[57]
da Sulaiman, (2013)[58]
da Umar, (2013).[59]
Mukoshy
da Umar (2014), sun rubuta maƙala da ta mayar da hankali wajen nazartar yadda za a
iya bunƙasa
karatun Hausa ta hanyar amfani da intanet. Sun bayyana yadda intanet ke
taimakawa a harkar ilimi, musamman abin da ya shafi ɗakunan karatu bisa intanet da mujallun da ke kan
intanet da makamantansu. Muƙalar ta Mukoshy da Umar na da dangantaka da wannan
bincike musamman idan aka duba kiran da suka yi cewa: “Muƙalar tana kira ga ɗalibai da manazarta Hausa da su ƙara ƙoƙari wajen amfani da intanet wajen taskace sahihan
bayanai domin bunƙasa bincike da nazarin harshen Hausa” (Mukoshy da
Umar, 2014: 10). Ko da ma dai, manufar wannan bincike shi ne nazartar al’adun
Hausawa cikin duniyar intanet da kuma hanyoyi da matakan da za su iya taimakawa
wajen inganta su. Ayyukan biyu sun
bambanta ta fuskar farfajiya da manufar bincike.
Mukoshy
(2016), ya gudanar da bincike inda ya yi ƙoƙarin bayyana wasu hanyoyin kasuwanci da hada-hada a
duniyar intanet waɗanda za
su iya taimaka wa tattalin arzikin Hausawa. Sun haɗa da kasuwanci a intanet, da biyan kuɗi ta intanet. Maƙalar Mukoshy na da dangantaka da wannan bincike
kasancewar dukansu sun shafi Hausawa da duniyar intanet. Duk da haka, Mukoshy
bai mayar da hankali wajen nazartar al’adun Hausawa da matakan inganta su a
duniyar intanet ba.
Shehu
da Aliyu (2019), sun rubuta maƙala wadda ta mayar da hankali wajen nazartar
illolin wayar salula a kan al’adun Hausawa. Daga ciki har da al’adun da suka
shafi zamantakewar aure. Daga shafin 708
zuwa 710, takardar ta bibiyi yadda shafukan intanet ke gurɓata tarbiyya. Ta fi mayar da hankali a
kan shafukan Fesbuk da Was’ap.
Maƙalar
Shehu da Aliyu na da matuƙar dangantaka da wannan bincike. Dukansu
biyu sun taɓo al’adun Hausawa da kuma intanet. Duk da haka, maƙalar
tasu ba ta mayar da hankali kan nazartar hanyoyin da za a bunƙasa
tare da inganta al’adun Hausawa a duniyar intanet ba.
Shehu
da Rambo (2019), sun rubuta maƙala wadda ta yi ƙoƙarin fito da yadda kafar intanet ta Was’af ke lalata
tarbiyyar Hausawa. A shafi na 359, sun kawo ire-iren saƙonni da ake iya turawa ta kafar Was’af. Sun haɗa da rubutu da sautin magana da kuma bidiyo. Daga
nan sai suka mayar da hankali wajen bayyana hanyoyin da wannan kafar intanet ke
gurɓata tarbiyyar Hausawa. Hakan ne
kuma ya samar da dangantaka tsakanin makalar tasu da wannan bincike. Dukansu
biyu sun shafi intanet da al’adun Hausawa. Duk da haka, Shehu da Rambo ba su
nazarci al’adun Hausawa a duniyar intanet ba. Bayan haka, ba su nazarci
hanyoyin da za a iya bi domin inganta wakilcin al’adun Hausawan a duniyar
intanet ba. Wannan bincike kuwa, hakan ne manufarsa.
2.3.5 Jaridu da Intanet
Adamu (2000), ya yi rubutu cikin
harshen Ingilishi a kan harshe da al’adun Hausawa a duniyar intanet. An buga ta
a cikin jaridar Weekly Trust ta ranar 20 ga watan Nuwamba, shekarar
2020. A ciki ya bibiyi yaɗuwar rubuce-rubuce da al’adun Hausawa da yadda suke a intanet. Kai tsaye
rubutun nasa na da dangantaka da wannan bincike musamman da yake sun taɓo al’adun Hausawa a duniyar intanet.
Abubakar
(2007), ya rubuta maƙala da aka buga a cikin Aminiya ta ranar ɗaya ga watan Maris, shekarar 2007. Ya mayar da
hankali wajen fito da tasirin intanet a ɓangarorin
rayuwar al’umma. Wannan ya haɗa da
kasuwanci da ilimi da sauran ɓangarorin
rayuwa. Rubutun nasa na da dangantaka da wannan bincike kasancewar dukansu biyu
sun shafi hada-hadar duniyar intanet. Duk da haka suna da manufofi mabambanta.
Abubakar ya mayar da hankali ne kan danganta harkokin rayuwa a zamanance da
kuma intanet. Wannan bincike kuwa ya karkata kan zawarcin al’adun Hausawa a
duniyar intanet tare da nazartan hanyoyi da matakan inganta su.
Ko
bayan waɗannan ayyuka da ke da alaƙa ta kusa da binciken, an nazarci wasu ayyukan waɗanda za su iya taimakawa wajen kammaluwarsa cikin
nasara. Ayyukan sun kasance masu dangantaka ta nesa da wannan bincike. Sun
shafi fannonin kwamfuta da intanet da sauran fasahohin zamani masu dangantaka
da waɗannan. Daga cikinsu akwai Aƙibu, (2001) da Adamu, (2004) da Guiɓi, (2006) da Sambo, (2009).
2.4 Hujjar Ci Gaba da Bincike
A
binciken Mukoshy an nazarci ayyukan masana da manazarta, sannan aka fitar da
sakamakon da ke cewa: “Hausa tana da kyakkyawar safiya. Sai dai, matuƙar ana son wannan harshe ya ci gaba da haskakawa,
dole masana su taskace sababbin kalmomi na sha’anin kwamfuta da intanet da kuma
sauran ɓangarorin da ci gaban zamani ya
kawo. Saboda haka Hausawa su shiga a
dama da su a kowane ɓangare
na amfani da kwamfuta da intanet” (Mukoshy, 2015: X). Wannan gagarumar yekuwa
ce da ke da buƙatar
gudummuwar manazarta a wannan fannin. Wani abin lura kuma shi ne, ba a samu
wani aiki da ya nazarci al’adun Hausawa a duniyar intanet ba.
Hatta
ayyukan da suke da makusanciyar dangantaka da wannan bincike (waɗanda aka yi bita a baya), za a tarar da cewa sun
bambanta ta fuskar manufa. Misali, aikin Almajir, (2008) na “Hausa da
Sadarwar Intanet,” bai mayar da hankali kan matakan inganta wakilcin al’adun
Hausawa a duniyar intanet ba. Haka ma Makuwana, (2011) ya fi mayar da hankali
kan nazartar yaɗuwar da Hausa ta yi a duniyar intanet kawai. A taƙaice ke
nan, an samu dalilin ci gaba da wannan bincike kasancewar babu wani aiki da aka
ci karo da shi wanda ya cike gurabun da wannan bincike ke da muradin cikewa.
2.5 Naɗewa
An daɗe ana gudanar da bincike a kan intanet da
dangantakarsa da harshe da kuma al’adun al’umma, ciki har da Hausawa. Hakan ya
biyo bayan ɗumbin tasirin da intanet ɗin ke da shi ga rayuwar al’umma a yau. Binciken
masana da manazarta da suka gabata da dama sun yi kira da a nazarci al’amarin
intanet sosai domin shiga cikin jerin al’ummun da ke cin gajiyarsa. Da alama
manazarta da ɗaliban ilimi sun amsa wannan
kira ganin yadda aka ci karo da ayyuka da dama a wannan fanni. Duk da haka,
akwai gurbin da ba a cike ba wanda ya shafi zawarcin al’adun Hausawa a duniyar
intanet tare da nazarin hanyoyin samar musu wakilci mai inganci.
[1]
Sun haɗa da ma’anonin da suka fito daga Almajir,
(2008) da Muhammad, (2011) da Umar, (2012).
[2]
Yana da kyau a tuna cewa, kwamfuta
na zuwa cikin sigogi da dama. Wayoyin hannu na shiga cikin jerin nau’ukan
kwamfutoci da ake da su.
[3]
Misali, wanda yake zaune a ƙasar
Hausa zai iya yin magana da wanda yake birnin Sin yayin da suke kallon juna.
Zai kuma iya taya shi wani aiki da yake gudanarwa a kan intanet a wannan
lokaci.
[4]
Misali, kafar intanet guda za ta iya
ɗaukar dubban miliyoyin
manyan littattafai waɗanda
idan ɗakin
karatu za a gina domin adana su, abin sai wanda ya gani.
[5] Idan za a ba da wata sanarwa ta
amfani da jarida ko wasiƙa, ana buƙatar buga takardu masu matuƙar
yawa domin rarrabawa ko lilliƙawa a wurare domin amfanin jama’a. Ta hanyar amfani da intanet, rubutu
guda yana biya wannan buƙata ba tare da an yi ta maimaitawa ba.
[6]
Rubuce-rubuce da aka yi kan tarihin
intanet sun haɗa da
Leiner, et al (1997) da Romualdo & Alessandro (2007) da Kleinrock, (2010) da Mukoshy, (2015) da Press,
(2015) da Strickland, (2020).
[7]
Duk da haka, akan yi wannan tsari
musamman yayin da ake buƙatar tara saƙonni da tace su a wani mataki kafin a wuce
da su zuwa sauran kwamfutoci.
[8]
Masana da suka yi aiki game da
nau’ukan intanet sun haɗa da Bourgeois,
(2016) da Dornal, (2021).
[9]
Domin ƙarin bincike game da
nau’ukan haɗakar sabis ɗin intanet, ana iya ziyartar https://www.javatpoint.com/types-of-computer-network ko https://www.router-switch.com/faq/types-of-networks.html ko https://www.belden.com/blogs/network-types ko https://afteracademy.com/blog/What-are-the-different-types-of-network.
[10]
Domin ƙarin bayani dangane da kafafen
intanet, ana iya duba Armstrong,
(2019).
[11]
Domin samun ƙarin bayani dangane da
Hausa da Hausawa ana iya duba Funiss, (1996) da Philip, (2001) da Bunza, (2008)
da Abdullahi, (2008) da Gobir, (2012) da Sani & Umar, (2018) da Gobir &
Sani, (2019) da Bunza, (2019).
[12]
An lissafo kafafen intanet na Hausa guda arba’in da huɗi (44)
a ƙarƙashin
1.6.
[13]
Domin ƙarin bayani a kan wannan
kafa ana iya duba https://wikipedia.org/.
[14]
Shafin farko wanda ake kira “gida”
(home page) na Hausa da ke kan kafar Wikifidiya yana da adireshi kamar haka: https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi.
[15]
Ya rage ga masana da manazarta Hausa
da su shiga a dama da su cikin harkar bunƙasawa da inganta wannan kafa. Koma bayan
haka, kafin a farga, ɓarnar
da za a yi wa Hausa a ilimance ba za ta misaltu ba!
[16]
Yana da kyau a lura cewa, a cikin ɓoyayyun al’adun da ya lissafo ana iya
samun al’amuran al’ada da suka kasance bayyanannu. Misali, alhini da baƙin
ciki yayin mutuwa a ɓoye suke,
amma yanka dabba a bayyane yake.
[17]
Kowace halitta tana da al’amuran da
suka shafi rayuwarta.
[18]
Wannan bincike ya yi ƙoƙarin ɗaukar
rahoton Internet Live Stats na ranar 20 ga watan Fabarairun shekarar 2020.
[19]
Kafar The Conversation ta
wallafa rahoto a ranar 28 ga watan Fabarairun shekarar 2018 mai taken “The
world needs to build more than two billion new homes over the next 80 years”
wato “Akwai buƙatar a gina sababbin gidaje sama da biliyan biyu a
duniya a cikin shekaru 80 masu zuwa.” A cikin rahoton ta nuna cewa, gidajen da ke duniya sun kasance kimanin
biliyan guda da ɗigo biyu (biliyan 1.2).
[20]
An kawo misalan injunan nema na
duniyar intanet a babi na ɗaya ƙarƙashin
1.7 (Farfajiyar Bincike).
[21]
Yana da kyau a tuna cewa, adadin
masu amfani da Fesbuk sun fi na waɗanda
ke amfani da Tuwita nesa ba kusa ba. Wannan na nuna cewa, labaran da ake ɗorawa a Fesbuk ya wuce wannan adadi sosai.
[22]
Sauƙaƙa sadarwa da kasuwanci
da sauran huldayyar al’umma
ci gaba ne da ya samu a sakamakon intanet. A ɓangare guda kuwa, akwai al’amuran da
intanet ya zo da su da suka kasance koma-baya ko cikas ga al’adu da
zamantakewa. Sun haɗa da
satar bayanan sirri da yaɗa
alfasha da mugun aiki da makamantansu.
[23] A shekarar 2019,
kafar intanet ɗin nan
mai suna Sitatista da ke adana bayanai dangane da kafafen intanet ya fitar da ƙididdigar ma’aikatan Fesbuk. Ya bayyana cewa, a shekarar 2018, ma’aikatan sun kai dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya da
biyar (25,105).
[24]
Wasu daga cikin rubuce-rubucen sun haɗa
da na Baruah, (2012) da Korkmaz, Celebe & Yucel, (2014) da OwusuAcheaw
& Larson, (2015) da Siddiqui & Singh, (2016).
[25]
Makarantun da suka fara amfani da
kafar sun haɗa da Columbia da Yale da Stanford (Clement, 2019: 2).
[26] Sai dai yana da kyau a lura cewa,
ra’i na iya fayyace halayya ba na ɗan’adam ba kaɗai, har ma da sauran abubuwa (waɗanda ake gani da waɗanda ba a gani). Ba abin mamaki ba ne da
ma’anar ra’in da suka bayar ta taƙaita kan ɗan’adam kasancewar Sashen na Ilimin Jarida da
Sadarwa ne. Al’amuran sashen kai tsaye sun shafi ‘yan’adam ne.
[27] Dr. Isah Abdullahi Muhammad ya
jaddada wannan batu yayin taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na huɗu da aka gudanar a Tsangayar Fasaha da
Addini Musulunci da ke Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Taron na da taken: “Zamfara
Kingdom: Social and Political Transformation from 14th Century to Date.” An
gudanar da shi daga 24 zuwa 28 ga watan Fabarairu ta shekarar 2020.
[28]
A hirar da aka yi da Sa’idu Umar
Yahaya ta waya ranar 6 ga watan Mayu ta shekarar 2020, ya bayyana cewa: “Ass.
Prof. Abdullahi, I.S.S. na da ra’ayin cewa ba za a kira karin magana ra’i ba. A
maimakon haka, sai dai a ce hanyar ɗora aiki.”
[29]
A nan gangar zamani ba ta nufin
sharholiya. A maimakon haka, tana nufin ci gaba da zamani ke zuwa da shi a
fannin kiwon lafiya da kimiyya da fasaha da ra’ayoyi da al’adu da zamantakewa
da makamantansu.
[30]
An nazarci wannan bincike bayan ya
tsallake matakin jarabawar cikin gida (Internal Defense) a Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
[31]
Masu wannan ra’ayi sun haɗa da Fafowora, B. da ke University of
Ibadan, Nigeria da Mwangi, N. da ke London School of Hygiene and
Tropical Medicine da Laverne A. Davis da ke Grand Canyon University, US
da Ali Nasser Al-Tahitah da ke USIM | Universiti Sains Islam Malaysia da
Wright, D. da ke University of Nevada, Las Vegas da Ojua, T. da ke University
of Calabar, Nigeria da Rehman, U. da ke Aligarh Muslim University India
da Muhanga, M. Sokoine University of Agriculture (SUA) Tanzania da
Ojua, T. da ke University of Calabar, Nigeria. Domin ƙarin
bayani ana iya duba:
https://www.researchgate.net/post/Can_I_use_Two_or_more_theories_to_support_my_research_model
[32]
Plato ɗan asalin Athens ne da ke Girka (Greece).
Ya rayu tsakanin 428/427 BCE - 348/347. Ɗalibi ne ga Socrates sannan malami ga
Aristotle. Domin samun cikakken tarihin Plato, ana iya duba: Meinwald,
C. C. (2020). Plato (Greek Philosopher). In Encyclopedia Britannica. Retrieved
on 17th March 2020 from: https://www.britannica.com/biography/Plato.
[33]
Ya rayu tsakanin 410 – 339 B.C.E.
[34]
Ya rayuwa tsakanin 396 – 313 B.C.E.
[35]
Ya rayu tsakanin 130 – 68 B.C.E.
[36]
Tambayoyin idan-da a nan na nufin
ire-iren tambayoyin da akwai “da” a cikinsu. Misali: “Da a ce rana ta kudu take
fitowa, da duniya za ta fi daɗin
kallo?”
[37]
Thein, (2018: 65) ya kawo misalan da
suka haɗa da
“tsatsa ga ƙarfe”, “ruɓewa ga ice”, “rashin lafiya ga jiki.” Ya bayyana
cewa, waɗannan
duka munanan abubuwa ne da suke tabbatattu a al’adar rayuwa. A fahimtar wannan
bincike ma haka abin yake.
[38] Ko da ma ƙwaƙƙwafi
na ɗaya daga cikin abubuwan
da suka assasa falsafa a doron ƙasa. Mabiyan sun damu da tambayar asalin haƙiƙanin
yadda al’amura
suke da dalilan faruwarsu.
[39]
Ya rayu tsakanin 316 – 251 B.C.E.
[40]
Ya rayu tsakanin 2014 – 129 B.C.E.
[41]
Ya rayu tsakanin 187 – 110 B.C.E.
[42]
Bincike ya tabbatar da Plato na da
bambancin ra’ayi sosai da ɗalibinsa
Aristotle. Don ƙarin bayani ana iya duba Pena, (2018: 52-55).
[43]
Ana iya duba edotocin Encyclopedia
Britanica a cikin wannan kafa: https://www.britannica.com/editor/The-Editors-of-Encyclopaedia-Britannica/4419.
[44]
Saɓanin ta Zahiriyya da suke bin tsarin daga
ƙasa
zuwa sama. Da a Zahiriyya ne, binciken da za a yi zai mayar da hankali ne kan
al’adu da nau’ukan tunani da suke kai ga amfani da
intanet. Yayin da aka ci karo da al’ada a cikin intanet ɗin, za
a yi ƙoƙari ne a binciko abin da ya kai ta, ba wai tasirinta kan al’adar al’umma masu ita a duniyar zahiri ba.
[45] Tamkar dai yadda ake da wasu
duniyoyi da suka haɗa da
duniyar sararin samaniya da duniyar barzahu da kuma lahira.
[46]
Wannan ba shi ne kaɗai
tsarin da ake bi wajen nazartar ayyukan da suka gabata ba. Akwai masana da ke
da ra’ayin cewa ba za a raba ayyukan da aka nazarta zuwa rukunnai ba. A
maimakon haka, za a bi tsarin
shekaru ne (daga mafi daɗewa
zuwa mafi sabunta). Daga cikin
masana masu wannan ra’ayi akwai Fraenkel, (2003) da McCombes, (2020).
[47]
Rubuce-rubuce da dama sun tabbatar
da “tarbiyya” a matsayin ɗaya
daga cikin ɓoyayyun
al’adun Hausawa. Daga cikinsu akwai Tambuwal, (2018: 102) da Maikwari, (2020:
106).
[48] Ya fito da gudummuwar shirye-shiryen
gidan radiyon Muryar Jama’a, Kano wajen kare taɓarɓarewar al’adun Hausawa. Ya fi mayar da hankali kan
shirin ‘Aiki Da Hankali’ da ‘Tamburan Kano.’ Bai taɓo
al’adun Hausawa a cikin duniyar intanet ba.
[49] Ya nazarci
ire-iren tasirin da wayar salula ta samar a kan al’adun Hausawa. Za a iya lura
da cewa, bai mayar da hankali wajen nazartar al’adun Hausawa a duniyar intanet
ba.
[50]
Ya duba yanayin auren zoben Bahaushe
a ƙarni na 21. Ya ɗora gidan Rediyon Rahama 97.3 FM a faifan al’ada. Shi ma
wannan bai taɓo al’adun Hausawa a cikin duniyar intanet ba.
[51] Ya nazarci irin rawar da kafafen yaɗa
labarai ke takawa wajen bunƙasawa ko ruguza al’adun Hausawa. Shi ma wannan bai
taɓo al’adun Hausawa a cikin duniyar intanet ba.
[52]
Ya nazarci rawar da kafafen yaɗa
labarai ke takawa kan al’adun Hausawa. Suna iya bunƙasa su ko su janyo taɓarɓarwarsu.
Shi ma wannan bai taɓo al’adun Hausawa a cikin duniyar intanet ba.
[53]
Ya taƙaita nazarinsa kan
rawar da gidan rediyon Companion FM 104.5 Mhz Katsina ke takawa wajen bunƙasa al’adun
Hausawa
[54]
Aikin ya taƙaita kan nazartar
tasirin finafinai kan tarbiyyar Bahaushe.
[55]
Shi ma wannan nazari ya taƙaita kan
nazartar tasirin finafinai kan tarbiyyar Bahaushe.
[56]
Ya nazarci yadda finafinai ke haifar
da taɓarɓarwar tarbiyyar Hausawa. Ya nuna cewa wannan ya ƙara
ruruta wutar samuwar daba.
[57]
Wannan nazari ya keɓanta
kan duba tasirin wasannin kwaikwayon gidajen rediyo wajen bunƙasa al’adun
Hausawa. Ya fi mayar da hankali kan shirin ‘Duniya Budurwar Wawa’ da ‘Jami’iyar
Jatau Na Albarkawa.’
[58]
Takardar ta nazarci tasirin
finafinai wajen gurɓata tarbiya, musamman abin da ya danganci fyaɗe.
[59]
Marubuciyar ta nazarci wata addu’ar
da ‘yammata ke yi wadda ta yaɗu a cikin wayar salula. Ta nuna cewa, zamananci ya yi
tasiri a kan al’amarin zaɓen mijin aure a yau.








0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.