Wannan ɗaya ne daga tsarabar da muke kawo muku daga Ummu Amatulqahhar Kitchen.
Alkaki ɗaya ne daga cikin abinci nau'in soyawa wanda yake da tsohon tarihi a tsakanin Hausawa. Yana da daɗi matuƙa sannan yana da daraja. Na ce yana da daraja ne saboda abinci ne nau'in girma wanda ko a bukukuwa, ba koyaushe ake samun alkaki ba. Idan aka yi alkaki lokacin biki kuwa, lallai hakan zai ƙara masa armashi.
Yayin da za ki yi alkaki, za ki tanadi kayan haɗi kamar haka:
a. Alkama
b. Mangyaɗa ko butter (ko duka biyu)
c. Ruwan tsamiya ko nono (kindirmo)
d. Sugar (ruwan sugar da aka dafa)
Ga yadda ake alkaki dalla-dalla
1) Da farko za ki gyara alkamarki, ki bushe ki cire duk wani
datti da yake ciki, sai ki barza shi, kar ya yi laushi sosai kuma kar ya yi
guda-guda sosai, kamar dai biski.
2) (Za ki jiƙa tsamiya ki barshi ya kwana ko ya yi
kamar awa hudu yadda zai jiƙu sosai).
3) Daga nan sai ki kawo Ruwan tsamiyar nan ki tata ki saka a
kan alkamar da aka barza, za ki saka ba da yawa ba daidai, sai ki saka ruwa ma
daidai (Ruwan tsamiyar yafi normal ruwa yawa).
3) Idan ba ki da tsamiya ana yi da nono, maimakon ruwan
tsamiyan da za ki saka sai ki saka nono (kindirmo) ki kwaɓa da shi da ruwa.
4) Za ki saka mangyaɗa
kadan, misali idan alkamar gwangwani hudu ne sai ki saka mangyaɗa ludayi ɗaya.
4) Sannan za ki iya amfani da butter maimaikon mangyaɗa.
5) Za ki saka yis ki kwaɓa
tare da shi (wasu suna sakawa wasu ba sa sakawa).
5) Za ki hade su ki kwaɓa
gaba ɗaya, kar ya yi
tauri kuma kar ya yi laushi sosai tsaka-tsakiya.
6) Daga nan sai ki rufe ki barshi ya kwana, (za ki kwaɓa da dare ki bari ya
kwana).
7) Da safe za ki saka masa ruwan kanwa kadan ki hade shi
sosai.
8) Daga nan sai ki saka a turmi ki daka shi yadda zai zama
ya kama jikinsa, ko ki yi amfani da hanunki ki buga shi sosai.
9) Daga nan sai ki dinga gutsura kina mulmulawa kina fitar
da shape din alkaki din.
10) Bayan kin gama sai ki soya shi. (Ba a saka masa wuta
sosai, sabida in kika saka wuta sosai cikin ba zai soyu ba).
11) Bayan kin soya kina fitarwa sai ki saka a cikin ruwan
sugar da kika dafa wato scrub.
12) Za ki bari ya kama jikinsa iya yadda kike so sai ki
fitar da shi.
Shikenan kin kammala alkaki dinki.
Ga nan ƙarin bayani cikin hotuna:
Hoton alkama kafin a ɓarza ta.
Hoton alkama bayan an haɗa shi, ya kwana, sannan an daka/buga shi da safe.
Matakin naɗawa na farko: Misalin yadda za a gutsuri curin domin naɗawa
Mataki na biyu: Yadda za a mulmula shi domin ya yi tsayi
Mataki na uku: Za a kalmasa sannan a ɗora ɗaya a kan ɗaya
Mataki na huɗu: Za a kalmasa ɗaya ya hau kan ɗaya
1 Comments
Na ji dadin wannan bayani na yadda ake alkaki
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.