Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamani Zo Mu Tafi: Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet (Babi Na Huɗu)

Citation: Sani, A-U. (2021). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

ZAMANI ZO MU TAFI: AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET

NA

ABU-UBAIDA SANI
Email: abuubaidasani5@gmail.com ko official@amsoshi.com
Site: www.abu-ubaida.com
WhatsApp: +2348133529736

*** ***

BABI NA HUƊU
NASARORI DA ƘALUBALEN KAFAFEN INTANET NA HAUSA

4.0 Shimfiɗa

Nazartar nasarori da ƙalubalen kafafen intanet na Hausa na da amfani a duniyar karatun Hausa a yau. Hakan ne zai ba da damar sanin inda aka kwana domin kyakkyawan tanadin gyaran gobe.  Wannan babi na huɗu ya karkata kan nazarin matsayin kafafen intanet na Hausa a yau. Kamar yadda aka bayyana a babi na ɗaya ƙarƙashin 1.6 (Farfajiyar Bincike), wannan bincike ya zaƙulu kafafen intanet na Hausa guda arbain da uku (43). A cikinsu, za a mayar da hankali kan guda talatin da ɗaya (31) kamar yadda Krejcie & Morgan, (1970) suka zayyana a jadawalin zaɓen samfuri. A ƙarshen wannan babi, ana sa ran fahimtar matsayin kafafen intanet na Hausa a yau. Wannan ya haɗa da ci gabansu da kuma naƙasunsu.

4.1 Kafafen Intanet na Hausa

Ya zuwa watan Maris na shekarar 2020, adadin kafafen intanet na Hausa fitattun sun kasance kimanin 43. Yana da kyau a tuna cewa, ya zuwa 2019, kafafen intanet da ke duniya gaba ɗaya sun kasance kimanin biliyan 1.72.[1] Harsunan duniya kuwa sun kasance kimanin dubu bakwai (7,000) kamar yadda aka bayyana a babi na biyu ƙarƙashin 2.1.1.2.

Idan aka raba adadin kafafen intanet na duniya (biliyan 1.72) a waɗannan harsuna (7,000), adadin zai kasance wajajen miliyan ashirin da huɗu da ɗigo hamsin da bakwai (miliyan 24.27). A taƙaice, kason kafafen intanet na Hausa bai wuce wajajen 0.00000000025% ba. Sai dai wani abin lura shi ne, a adadin kafafen intanet na duniya har da na kafafen yaɗa labarai. Su kuwa kafafen intanet na Hausa, ba a sanya da kafafen yaɗa labarai ba. Baya ga haka, za ta iya yiwuwa akwai ƙananan kafafen intanet na Hausa waɗanda wannan bincike bai kai gare su ba (saboda rashin bunƙasarsu wanda ya sa injunan nema ba sa iya gano su).

A taƙaice, idan aka yi laakari da yawan kafafen intanet da ke duniya, to Hausa ba ta da kafafe na a-zo-a-gani! Duk da haka, tana kan gaba-gaba a cikin tsaranta harsunan Afirka, musamman na Nijeriya da Nijar. Kamar yadda aka nuna a babi na biyu ƙarƙashin 2.1.1.2, Hausa ce kaɗai daga cikin manyan harsunan Nijeriya ta samu shiga cikin Fesbuk. Bayan haka, tana da gindin zama a Wikifidiya.

Dangane da masu gudanar da kafafen intanet na Hausa, mafi yawa ba masu ilimin harshe da al’adun Hausawa ba ne. Wannan bincike kafafe biyu kacal ya ci karo da su waɗanda suka kasance masu gudanar da su sun karanci Hausa a matakin digiri. Kafafen su ne Amsoshi[2] da Makarantar Hausa.[3] Misali, shahararrun kafafen intanet ɗin nan guda biyu Hausa Online da Karin Magana, ba Bahaushe ba ne ke gudanar da su.[4] A shafin farko na kafar Hausa Online, ya wallafa hotonsa ɗauke da bayani kamar haka:

Hoto 4.1: Hoton Mr. Uwe Seibert Tare da Tsokaci

Hoton Mr. Uwe Seibert Tare da Tsokaci

Madogara: Seibert, (2017: 1)

Seibert ya nuna cewa, ya buɗe kafar intanet na Hausa tun wajajen shekarar 2006.[5] Yayin da yake magana game da dalilin da ya sa ya rage ɗora rubuce-rubuce, sai ya ce: “... there are now more better elearning websites and smartphone apps than when I started Hausa online.” Ma’ana: “Yanzu an samu wadatar kafafen intanet da manhajojin wayoyi masu ilimantarwa sama da lokacin da na buɗe Hausa Online.

Wannan maganar tasa na nuna cewa, har zuwa wajajen 2006 babu wadatar kafafen intanet na Hausa. Wannan ya yi daidai da abin da Chamo, (2020)[6] ya labarta cewa: “Lokacin da nake ƙasar waje, mutane da dama sun tambaye ni cewa: Me ya sa babu rubuce-rubucen Hausa a kan intanet?””

An samu damar zantawa da masu gudanar da kafafen intanet na Hausa da dama.[7] Duka waɗanda aka yi hira da su, babban muradinsu na buɗe kafafen intanet na Hausa shi ne domin bunƙasa Hausa a duniyar intanet.[8] Bashir Ahmed, wanda shi ne ke da kafar intanet ta Hutu Dole, ya bayyana dalilin buɗe wannan kafa da cewa: “Habbaka[9] Al'adun Hausa, Adabin Hausa, samar da bayai[10] a zamanance ga Hausawa.” Shi kuwa, Lawan Ɗalha, dogon jawabi ya yi inda yake cewa:

Dalilan da suka sa muka bude[11] Bakandamiya dai kamar guda biyu zuwa uku.[12] Na farko mun fahimci cewa litattafan ilimi, wato literature, musamman a fannin kimiyya da fasaha sun yi karanci[13] cikin harshen Hausa. Saboda haka, sai muka ga za mu yi amfani da taskar Bakandamiya don baiwa[14] mutane dama suke rubuce-rubuce har da bidiyoyi wajen karantarwa da kuma yin muhawara akan[15] kimiyya da fasaha don dalibai[16] su fahimta.

Abu na biyu, muna tunanin taskar zai[17] zama wurin tattara abubuwan tarihi ne na al’adun Hausawa da ma Arewacin Nigeria. Don haka muna dora[18] sautuka (wakoki[19] da wa’azuka[20] da makamantansu) da hotuna na tarihi tare da bayanai yadda duk wanda ya ci karo da su zai fahimci wani abu akai.[21]

Na uku shi ne, muna ganin akasarin al’ummar dake[22] amfani da harshen Hausa, mu’amalarsu bata[23] da yawa da na’urorin zamani kasancewar yawanci na Turanci ne. Don haka, muna ganin samar da wata kafa ta Intanet kuma cikin harshen Hausa zai kara[24] baiwa[25] masu amfani da harshen dama su fahimci kuma su ci moriyar kafafen na zamani la’alla ta bangaren[26] ilmantuwa ko kuwa kasuwancin zamani.

Dangane da bunƙasar kafafen intanet na Hausa kuwa, ana iya cewa ba yabo ba fallasa. Ya zuwa yau (2020) kusan kafafen sun taɓa dukkanin ɓangarori na rayuwa. Ɓangarorin da kafafen intanet na Hausa suka taɓa sun haɗa da:

i. Ƙamusu

ii. Labarai

iii. Sadar da Zumunta

iv. Kimiyya da Fasaha

v. Ilimi

vi. Adabi

vii. Cinikayya

4.1.1 Ƙamusu

Ƙamusu matattara ce ta kalmomi da ma’anoninsu. Ƙamusu na da matuƙar amfani ga bunƙasar harshe da ci gabansa na baki ɗaya. Tuni Hausa ta yi wa sauran harsuna sa’o’inta zarra a wannan ɓangare. A rumbun manhajojin wayoyi mai suna Play Store, akwai manhajojin ƙamusushin Hausa masu yawa. Suna kasancewa cikin tsari na musamman, misali ɗaya daga cikin:

i. Ƙamusun kalmomin Hausa da bayanan Ingilishi

ii. Ƙamusun kalmomin Hausa da bayanan Hausa

iii. Ƙamusun kalmomin Hausa zuwa kalmomin Ingilishi

iv. Ƙamusun kalmomin Ingilishi zuwa kalmomin Hausa

Daga cikinsu akwai waɗanda ba a iya amfani da su sai da data. Ma’ana dai, ko da an sauke su kan waya ko kwamfuta, to dole sai an kunna data kafin a iya amfani da su. Wasu daga cikinsu kuwa, da zarar an sauke su kan kwamfuta ko waya, to ana iya amfani da su ko da babu data. Kaso na uku su ne waɗanda ba a sauke su kan kwamfuta ko waya. A maimakon haka, ana yin amfani da data ne kawai a duba su a kan intanet. An kawo misali a ƙasa cikin hoto:

Hoto 4.2: Ƙamusun Hausa na Kan Intanet

Ƙamusun Hausa na Kan Intanet

Madogara: Shafin Farko na Hausa Dictionary: http://hausadictionary.com/Main_Page

A hoto na 4.2 da ke sama, za a ga ƙamusu ne na Hausa wanda ake amfani da shi a kan intanet. Kamar yadda ake gani cikin hoton, an ba da damar bincika kalma kai tsaye a gurbin da aka rubuta Bincika <> Search. Da zarar mutum ya rubuta kalma a wannan wuri, to ƙamusun zai buɗo da bayananta nan take. Bayan haka, an yi wani tsari na abajada. Yayin da mai nema ya latsa ɗaya daga cikin abajadan, ƙamusun zai gabato masa dukkanin kalmomi da suka fara da wannan harafi. Wani babban misali bayan wannan shi ne Bargery Online Dictionary.

4.1.2 Labarai

Akwai kafafen intanet na Hausa da suka shahara a ɓangaren yaɗa labarai. Yana da kyau a fahimci cewa, a nan ba a nufin jaridu da gidajen rediyo ko talabijin da ke da kafafen intanet. Ana nufin kafafen intanet masu zaman kansu da ba su jingina jikin kowane kafar yaɗa labarai ba. Sukan samar da rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyin al’amuran da ke faruwa a ƙasar Hausa. Wasu lokutan har sukan taɓo labaran ƙasashen ƙetare. Babban misali dangane da wannan shi ne kafar intanet mai suna Jaridar Hausa. A shafinta na farko, ta wallafa rubutu kamar kamar haka:

Jaridar Hausa jarida ce da za ta dinga kawo muku abubuwa da ke faruwa a kowanne lungu na saƙo na duniya, sannan kuma ta baku[27] cikakken bayani a kan ainahin abin dake[28] wakana cikin harshen Hausa (Shafin Farko na Jaridar Hausa: https://jaridarhausa.com/).

Hoto 4.3: Wani Ɓangaren Shafin Farko na Jaridar Hausa

Wani Ɓangaren Shafin Farko na Jaridar Hausa

Madogara: Shafin Farko na Jaridar Hausa: https://jaridarhausa.com/

Wani babban misalin kafar intanet mai kawo labarai shi ne kafar Hutu Dole. Ita ma wannan kafa ta shahara a ɓangaren kawo labaran yau da kullum. A ƙasa an kawo hoton rukunnenta (categories):

Hoto 4.4: Rukunnai (Categories) na Kafar Hutu Dole

Rukunnai (Categories) na Kafar Hutu Dole

Madogara: Shafin Farko na Hutu Dole: https://hutudole.com/

Shafin hutudole.com ɗaya ne daga cikin shafukan yanar gizo da ke wallafa labarai da harshen Hausa...” Hutu Dole, (2018: 1). Idan aka yi la’akari da hoto na 4.4 da ke sama, za a lura da cewa shafin ɗungurungum ya karkata ne kan labarai. Sauran rukunnai da ke cikin hoton sun danganci bayanai ne a kan shafi. Misali, TUNTUƁI HUTUDOLE da DANGANE DA HUTUDOLE.

4.1.3 Sadar da Zumunta

Sadar da zumunta ta intanet wani abu ne da ya mamaye duniyar yau. Galadanci da wasu (1990: 8) sun bayyana ma’anar sadarwa kamar haka: “... a taƙaice,  ita ce sanya wani ya fahimci abin da kake so ya ji, ko ya yi  ko ya sadu da abin da kake so ya karɓa.” Ya zuwa yau, an samu kafafen intanet na Hausa da ke ba da damar sada zumunta tsakanin al’umma. Babban misali a nan shi ne kafar Kano Online. A duba hoto da ke ƙasa:

Hoto 4.5: Sada Zumunta ta Kafar Kano Online

Sada Zumunta ta Kafar Kano Online

Madogara: Shafin tattaunawa mai taken kacici-kacici a kan kafar Kano Online: http://kanoonline.com/smf/index.php?topic=2739.0;prev_next=next#new

Idan aka duba hoto na 4.5 da ke sama, za a tarar da misali na tattaunawa a kafar Kano Online. Kafar na ba da damar tattaunawa tsakanin al’umma a zaure ko kuma a keɓance (group or private chats). Ko bayan wannan kafa, akwai kafar intanet mai suna Bakandamiya. Ita ma na da tsarin da ke ba wa mutane damar sadar da zumunta a tsakaninsu. Haƙiƙa wannan wani ci gaba ne da ya samu. Idan an yi amfani da shi yadda ya kamata, lallai Hausa ce ke da tagomashin.

4.1.4 Kimiyya da Fasaha

A duniyar yau, kimiyya da fasaha na kan gaba. Mutuncin ƙasa da ƙarfin tattalin arzikinta sun dogara ne kan ƙarfin kimiyya da fasaharta. Akwai kafafen intanet da dama da ke tsakuro labarai da sharhi ko fashin baƙi da faɗakarwa dangane da kimiyya da fasaha. Daga cikinsu akwai amsoshi.com da managarciya.com da hutudole.com. Duk da haka, manufofin kafafen bai mayar da hankali kan kimiyya da fasaha ɗungurungum ba. Cikin sa’a sai aka samu ɓullar kafafen intanet waɗanda suka mayar da hankali kan wannan ɓangare. A duba hoto da ke ƙasa:

Hoto 4.6: Kafar Intanet Kan Kimiyya da Fasaha (Jakadan Fasaha)

Kafar Intanet Kan Kimiyya da Fasaha (Jakadan Fasaha)

Madogara: Shafin Farko na Jakadan Fasaha: https://www.jakadanfasaha.com/

Idan aka duba hoto na 4.6 da ke sama, za a tarar da cewa kafar ta raja’a ne kan kimmiya da fasaha baki ɗaya. Ko daga sunanta ma ana iya fahimtar hakan (Jakadan Fasaha). Kafa ce da ta shahara wajen kawo bayanai kan na’urori irin su kwamfutoci da wayoyi da makamantansu. Bayan haka, tana kawo bayanai game da duniyar intanet. Wannan ya shafi amfani da intanet, da kare kai daga damfarar intanet da makamantansu.

4.1.5 Makaranta

A matakin duniya, an daɗe da samun makarantu kan intanet. Hausa ta fara cin gajiyar wannan fasaha bayan samuwar kafafen intanet irin su Makarantar Hausa da Pen Profile da Teach Yourself Hausa. Makarantar Hausa tana da tsari ne na karanta mafi yawan abubuwan da ke kan kafar a kyauta. Duk da haka, akwai ‘yan kaɗan waɗanda sai an biya ake karantawa. Bayan haka, makarantar ba ta samar da darrusa kai tsaye domin ɗalibanta ba. A maimakon haka, ta kasance ne tamkar sauran kafafen intanet masu ɗora bayanai da ke ilimantarwa. A hoton da ke ƙasa an kawo shafin farko na kafar:

Hoto 4.7: Shafin Farko na Kafar Makarantar Hausa

Shafin Farko na Kafar Makarantar Hausa

Madogara: Shafin Farko na Makarantar Hausa: https://makarantarhausa.com/akawun

Kafar Teach Yourself Hausa ita ma shahararriya ce. Tana ɗauke da rubuce-rubuce da hotuna da ke ba da damar koyon Hausa. Kafar ta fi amfanar waɗanda ba Hausawa ba. An samar da ita cikin tsarin Ingilishi da Hausa. Babayan haka, bayananta na da saukin fahimta. Sannan kafar na ba da hurumin aika gyara ga duk wanda ya gani. A duba hoton da ke ƙasa:

Hoto 4.8: Kafar Teach Yourself Hausa

Kafar Teach Yourself Hausa

Madogara: Shafin Farko na Teach Yourself Hausa: http://www.teachyourselfhausa.com/

Kafar Pen Profile ita ce ke da tsarin makaranta kai tsaye. Tana da tsari na kwasa-kwasai da ɗalibta. Ɗalibai na yin rigista sannan su karanta kwasa-kwasai. Akwai kuma tsari na ba da jinga da jarabawa. Duk wannan na faruwa ne a duniyar intanet.

4.1.6 Adabi

Abu ne mai matuƙar muhimmanci a ce adabin wata al’umma na da gindin zama a duniyar intanet. “Adabi fage ne babba da ake iya hango kowane abu da ya shafi rayuwar Bahaushe” (Bunza da Atuwo, 2015: i). A wannan ɓangare ma, ba a bar Hausawa a baya ba. Tuni an samu kafafen da suka yi fice wajen ɗora abubuwan da suka shafi adabin Hausawa. Kafar Hausa Top na ɗaya daga cikin waɗanda suka fi saura shahara a wannan fanni. A duba hoto da ke ƙasa:

Hoto 4.9: Hoton Rukunnen Kafar Hausa Top

Hoton Rukunnen Kafar Hausa Top

Madogara: Shafin Farko na Hausa Top: http://www.hausatop.com/

Idan aka duba hoto na 4.9 da ke sama, za a tarar gaba ɗaya rukunnen  an rubuta su ne cikin harshen Ingilishi. Duk da haka, kafar ta Hausa ce. Ta shara wajen kawo waƙoƙin Hausa cikin sautukan odiyo da bidiyoyi. Sun wallafa a shafin cewa:

HausaTop.Com is the Most Visited Online Platform that Delivers Hot Fresh Northern Nigerian Music, Video, Entertainment Gist & News Content on a daily Basis to Nigerians Home and Abroad. Hausa Top, (2020: 1)

Fassara:

HausaTop.Com ta kasance kafar da aka fi ziyarta wacce take kawo zafafan sabbin waƙoƙin Arewacin Nijeriya da bidiyoyi da wasanni da labarai a kowace rana. Tana samar da su domin yan Nijeriya a cikin gida da kuma ƙasashen waje.

4.1.7 Kasuwanci

An daɗe ana cinikayya a duniyar intanet. Idan aka bi fahimtar Pulatoriyya, ana iya cewa, yadda duniyar zahiri take da kasuwanni, haka duniyar intanet ma. Tun da kuwa zamani riga ce, bai dace a bar Hausa a baya ba dangane da cinikayya a duniyar intanet. Irin wannan nau’in cinikayya ya shafi duba abin da ake buƙata tare da tura kuɗin ta intanet. Daga nan za a ba wa mutum damar samun abin da ya saya (misali rubutu, odiyo, bidiyo da sauransu). Idan na kawowa ne kuma, za a kawo zuwa adireshin da mai saye ya zayyana (kamar mota, tufafi da sauransu). Hausa ta fara shiga wannan tsari. A duba misali da ke ƙasa:

Hoto 4.10: Kasuwanci a Duniyar Intanet

Kasuwanci a Duniyar Intanet

Madogara: Shafin sayar da littattafai na Wikihausa: https://www.wikihausa.com.ng/littattafai/

A hoto na 4.10 da ke sama, za a iya kallon littattafan sayarwa, kowanne da farashinsa. Masu saye na iya yin odar littattafan kai tsaye daga wannan kafa ta Wiki Hausa. Haƙiƙa wannan nauin ci gaba na buƙatar saka hannun masana da mahukunta domin haɓaka shi. Hanya ce ta sauƙaƙa rayuwa.

4.2 Ƙalubalen Bunƙasar Kafafen Intanet na Hausa

A ƙarƙashin 4.1 an bayyana cewa, ɗaya daga cikin manyan matsaloli ko ƙalubalen kafafen intanet na Hausa shi ne masu gudanarwar. An bayyana cewa, kafafen intanet biyu ne kacal masu gudanar da su suka karanci Hausa a matakin digiri. A bisa wannan ana samun ƙalubale nau’uka uku:

i. Saɓa wa al’adu

ii. Kurakuran rubutu barkatai

iii. Rashin ingancin bayanai[29]

4.2.1 Saɓa wa Al’adu

Akwai kafafen intanet na Hausa da kai tsaye suke saɓa wa al’ada da addinin Hausawa. Mafi shahara a cikinsu ita ce Batsa Post. Kamar yadda sunan ya nuna (batsa), wannan kafa babu abin da take yi face kawo rubuce rubuce da hotuna da kuma bidiyoyin batsa. Babban maƙasudin wannan kafa shi ne nuna tsiraici cikin hotuna da bidiyoyi. Kafar na ƙoƙarin kalato hotunan tsiraici na matan Hausawa. Haka abin yake dangane da bidiyoyi.

Babu makawa kafar ta Hausa ce. Hatta rukunne da ɓangarorin kafar duka cikin harshen Hausa aka rubuta su.[30] Duk da haka, kai tsaye za a iya gane cewa ba Hausawa ba ne ke gudanar da shafin. Dalilan da aka dogara da su domin yanke wannan hukunci su ne:

a. Kusan babu wata jimla da aka rubuta ta daidai ba tare da tafka kurkuren rubutu ba (karya ƙaidojin rubutu).

b. Karin harshen bai yi kama da na Bahaushen asali ba. Akwai wurare da ana iya kallon karin harshen mai koyo (L2) kai tsaye.

Hoto 4.11: Samfurin Rubutu Daga Kafar Batsa Post

Samfurin Rubutu Daga Kafar Batsa Post

Madogara: https://www.batsapost.com/category/news-labarai/

An ɗauko hoto na 4.11 kai tsaye daga kafar intanet ta Batsa Post. Duk da rubutun ba shi da yawa, akwai kurakurai sosai da za a iya kallo daga ciki. Waɗannan kurakurai sun haɗa da:

a. An rubuta “taunawa” a maimakon “tona wa.”

b. An rubuta “kamashi” a maimakon “kama shi.”

c. An rubuta “akace” a maimakon “aka ce.”

d. An rubuta “dauki” a maimakon “ɗauki.”

e. An rubuta “vidiyan” a maimakon “bidiyon.”

Ko bayan wannan, wurare da dama daga cikin kafar na nuna cewa ba Hausawa ba ne ke gudanar da shafin. Akwai wuraren da ƙarara za a iya fahimtar cewa inji ne ke musu fassarar rubuce-rubuce da suke ɗorawa. Misali, a inda suke ƙoƙarin rubuta manufar shafin, sai suka sanya:

Hoto 4.12: Misalin Fassarar Inji a Kan Kafar Batsa Post

Misalin Fassarar Inji a Kan Kafar Batsa Post

Madogara: Shafin farko na Batsa Post: https://www.batsapost.com

A hoto na 4.12 da ke sama, za a tarar kai tsaye salon fassarar inji ne. Ya kasance:

i. An fara rubutun da Hausa, sai aka ci gaba da Ingilishi. Daga ƙarshe kuma aka ƙarƙare da Hausa.[31]

ii. An rubuta “ba’a” a maimakon “ba a.”

iii. An rubuta “fada” a maimakon “faɗa.”

Bayan wannan shafi, akwai shafuka da dama da ke ɗora hotuna da suka ci karo da al’adun Hausawa. Nau’ukan hotunan yawanci na mata ne cikin shigar da ta ci karo da addini da al’adar Bahaushe. Mafi akasarin hotunan sun shafi:

1. Hoton matan Hausawa ‘yan fim (jaruman finafinan Hausa)

2. Hoton matayen ƙetare ‘yan fim da ‘yan tallata haja.[32]

3. Hoton sauran mata na Hausawa ko mataye daga ƙasashen ƙetare.[33]

4.2.2 Kurakuran Rubutu Barkatai

Ɗan’adam tara yake bai cika goma ba!” Haka kuma: “Yin daidai sai Allah!” Duk da haka, kurakuran da ake samu a kan wasu kafafen intanet na Hausa sun yi yawa sosai. Hakan na faruwa ne sakamakon masu gudanar da su ba su da ilimin rubutun Hausa. A ƙarƙashin 4.1, an kawo misalan amsoshi da wasu masu gudanar da kafen intanet suka bayar dangane da abin da ya ja hankalinsu wajen buɗe kafafen. Za a tarar da cewa a cikin kowace amsa akwai matsalar ƙa’idojin rubutu barkatai. Matsalar ta fi shafar haɗawa da rabawa da kuma rashin amfani da baƙaƙe masu ƙugiya. Ko bayan wannan, akwai misalan saɓa ƙa’idojin rubutu a kafafen intanet na Hausa daban-daban. Ga ‘yan misalai a ƙasa:

Dan Allah kira ga mafi yawancin ku yan uwan mu mawakan Hausa Hip Hop ma su tasowa, ku daina turancin da ba daidai ba ne ko ku rage inya zama dole ku yi turancin da ba daidai ba ne a wakar ku, kuna bada Arewa da ma jihar Kano ne, domin babu anfanin ka yi yaran da ba ka iya ba daidai a waka bayan ga na ka yaran na asali wanda ka kware a kai. San nan sama da kashi 70% na wannan turancin da su ke yi ba daidai ba ne, gashi kuma sama da kashi 80% na ma su sauraron wakokin ku ba sosai su ke jin turancin nan ba, kunga asara biyu kenan, ka yi waka amma kai kan ka ba ka san abun da kake fada ba a ciki, kuma ga sakon ka bai kai ga wadan da su ya kamata ya kaiwa ba (Dabo, 2019: 1).

i. Dukkanin tsawon rubutun a matsayin jimla guda aka rattabo shi. Ya dace a raba shi zuwa jimloli da dama.

ii. Ba a sanya baƙaƙe masu ƙugiya a wuraren da suka dace ba.

iii. An haɗe kalmomi a wuraren da ba su dace a haɗe ba.

iv. An rabe kalmomi a wuraren ba su dace a rabe ba (kamar gajeruwar mallaka).

A shafin Qalubale ma an samu misali kwatankwacin wannan. Ga yadda rubutun ya kasance:

Shidai wannan matashi yasamu nasarar kammala tattakinsa lafiya ya kuma isa kano tangaram inda kai tsaye yawuche ofishin ABBA KABIR YUSUF dake a nasarawa shikadai batare da yan tarba ko rakiya ba inda ya,isa office din amma ko ruwa ba,abashi ba, hasalima bai samu ganin kowa ba chikin jagororin kwankwasiyar inda aka shaida masa wai sunyi tafiya zuwa ABUJA (Ahmed, 2020: 1).

Idan aka yi la’akari da rubutun da ke sama, za a tarar da cewa:

a. Duk yawansa an rubuta shi ne a matsayin jimla guda.

b. Akwai wuraren da aka haɗe rubutu alhali ya dace a rabe su.

c. An yi amfani da “ch” a matsayin “c” misali “yawuche” a maimakon “ya wuce.”

Ko bayan waɗannan misalai, akwai wasu masu tarin yawa. Kusan duk wata kafar intanet ta Hausa da aka ɗauka sai an ci karo da ire-iren waɗannan misalai na kurakuren rubutu.[34] Kafafen da suka yi zarra dangane da bin ƙa’idojin rubutu guda biyu ne. Na farko akwai kafar Amsoshi (https://www.amsoshi.com/). Kafa ta biyu ita ce Makarantar Hausa (https://makarantarhausa.com/).

4.2.3 Ƙarya

Bayanan ƙarya sun yawaita a kan intanet. A ƙarƙashin 1.1 (Dalilin Bincike) da ke babi na ɗaya an kawo bayani mai alaƙa da wannan. A shekarar 2017, fitaccen Ɗangaladiman Farfesan, Abdullahi, I. S. S. A ɓangaren al’ada ya yi tir da cin karo da bayanai marasa inganci dangane da Maguzawa da Maguzanci a intanet. Idan dai marasa ilimin Hausa suka ci gaba da jagorantar kafafen intanet na Hausa, babu makawa waɗannan kurakurai ba za su kau ba.

Babban misali a wannan ɓangare shi ne, masu gudanar da kafafen intanet ba su karanci al’adun Bahaushe ba. A bisa wannan dalili, babu yadda za a yi bayanai da za su kawo dangane da al’adu su kasance na zahiri. Ilimin al’adu fage ne mai zaman kansa. Ana neman sa tamkar yadda ake neman sauran ilimummuka. Ana nazarin sa tamkar yadda ake nazarin sauran ilimummuka. Ke nan, ba abu ne da za a yi wa hawan ƙawara ba. Haka abin yake ga adabi da harshen Hausa. Yayin da aka samu marasa ilimin abin su ne ke jagorancin sa a duniyar intanet, to “a garin neman ƙiba za a samo rama.”

4.3 Dalilan Koma-Bayan Kafafen Intanet na Hausa

Akwai dalilai da dama da suke mazaunin ƙalubale ga bunƙasar kafafen intanet na Hausa. A ƙasa an kawo bayanansu dalla-dalla:

4.3.1 Muhalli

Harkar intanet abu ne mai buƙatar muhalli na musamman. Akwai buƙatar wutar lantarki mai ɗorewa. Ɗaukewar wuta abu ne mai kawo cikas ga harkar. A ɓangare guda kuwa, akwai buƙatar sabis na intanet mai nagarta. A wuraren da suka ci gaba, waɗannan duka ba matsaloli ba ne. Wuta tana da tabbas. Haka ma akwai sabis na intanet mai ƙarfin gaske. A ƙasar Hausa kuwa, ana iya faɗin abin da jakin dawa ya faɗa wa na gida: “Allah wadai naka ya lalace!”

4.3.2  Ƙarancin Tallafi da Ƙarfafa Guiwa

A ƙasashen da suka ci gaba, tallafa wa masu hoɓɓasar ƙirƙiro wata fasaha abu ne sababbe. Wannan ne ma dalilin da ya saka kafafe da dama suke sanya madannin ba da tallafi (donate) a kafafen nasu. Madannin na ba wa masu raayi damar tura tallafinsu zuwa ga kafafen intanet ɗin. Yayin da aka bincika, za a ci karo da ire-iren waɗannan madanne a kafafen intanet manya da ƙanana. A cikinsu har da shahararriyar kafar nan wato Wikifidiya.  A ƙasa an kawo misalin hoton tambarin neman tallafi:

Hoto 4.13: Hoton Tamfarin Neman Tallafi

Hoton Tamfarin Neman Tallafi

Madogara: Binciken “Donate Botton PNG” a Rumbun Hotunan Gogul

Dangane da ƙasar Hausa, abin ba haka yake ba. Ba a damu da tallafa wa fasahohi masu tasowa ba. Hasali ma, masu gudanar da kafofin sukan sha suka da tsangwama. Sau da dama, akan samu alummar da ke kallon ɓata lokaci kawai masu wannan hoɓɓasa suke yi.

Lawal Ɗalha (mai gudanar da kafar Bakandamiya) ya bayyana wannan ƙorafi inda ya ce: “Babbar matsala ta ƙarshe ita ce matuƙar ba a samu hanyar shigowar kuɗi mai ɗorewa ba da zai taimaka wajen gudanar da taskar, mai yiwuwa nan gaba mu kasa iya riƙe ta.” Dangane da ƙarfafa guiwa kuwa, Bashir Ahmed (Maigudanar da kafar Hutu Dole) cewa ya yi: “... Rashin masu sharhi waɗanda za su yi sharhi a kan al'amuran yau da kullun, kamar yanda ake samu a shafukan jaridun Turanci.”

4.3.3 Yanayin Intanet

Yanayin intanet kansa na tasiri ga bunƙasar harkokin intanet na Hausa. Intanet wani al’amari ne mai sarƙaƙiya tare da cakwakiya. Yana buƙatar ilimi na musamman. Yana tafiya da yaruka na daban. Yayin gudanar da al’amuran intanet, akwai buƙatar samun ilimin waɗannan yaruka. Fitattu daga ciki su ne:

a. HTML (Hypertext Markup Language)[35]

b. PHP (Personal Home Page Tools)[36]

c. CSS (Cascading Style Sheets)[37]

d. Javascript[38]

Rashin samun ilimin waɗannan yarukan intanet koma baya ne ga gudanar da harkokin kafafen intanet. Sun kasance tamkar tubalan ginin kafafen intanet. Idan babu su, kafafen intanet ba za su iya wanzuwa ba kamar yadda ake kallon su. Akwai dalilai da ke sa Hausawa ƙasa a guiwa a wannan ɓangare na koyon yarukan intanet. Sun haɗa da:

i. Babu wadatattun masu ilimin da za su koyar da yarukan intanet da kwamfuta.

ii. Babu wadatattun santoci da makarantun koyar da yarukan intanet da kwamfuta.

iii. Yawancin Hausawa ba su da ra’ayi a wannan ɓangaren ilimi.

iv. Koyon yarukan kwamfuta da intanet na buƙatar biyan kuɗin horaswa.

v. Yawancin waɗanda ke da ra’ayin koyon ba su da damar biyan kuɗin horaswar da ake buƙata.

A ɓangare guda kuwa, harkar gudanar da kafafen intanet abu ne mai buƙatar lokaci. Da farko akwai buƙatar lokacin koyon yaruka kamar yadda aka ambata a sama. A duba a da b da c da ke ƙarƙashin 4.2.3. Samun wannan lokaci ba ƙaramin ƙalubale ne ba. Da a ce akwai tallafi ga masu wannan hoɓɓasa, haƙiƙa gudanar da kafafen zai zo da sauƙi. Dalili shi ne, tallafin zai ishe su biyan buƙatun rayuwar yau da kullum. Ke nan za su duƙufa kain da nain wajen aiki ba kama ƙafar yaro, tun da ba sa tunanin rashin ruwan ciki wanda da shi ake jan na rijiya.

4.3.4 Ƙin Karɓar Sauye-Sauyen Rayuwa

Ɗan’adam na da halin ƙin karɓar sauye-sauye a rayuwa. Wannan ne ma ya sa ake da ra’in “resistance to change” da “cultural lag” (ƙin karɓar sauyi da liƙe wa alada). Waɗannan ra’o’i suna nuna cewa, ɗan’adam na jin shakku da wasi-wasi game da duk wani sauyi da aka gabato masa da shi a rayuwa. Zuciyarsa za ta raya masa cewa, tsohuwar hanyar da yake bi ita ce daidai. Zai kuma ji cewa, sabuwar hanyar na iya kasancewa cike da ƙalubale da wahalhalu, sannan ba za ta ɓulle ba.

Mutum na karɓar sauyi a rayuwa yayin da ya yi amfani da abin da ake ce wa “overcoming resistance to change” (yaƙar ɗabi’ar ƙin karɓar sauyi). Sau da dama yayin da mutum ya karɓi sabon al’amari, zai yi mamakin kasancewar har ya fi tafarkin da yake bi da. Bayan haka, zai yi mamakin yadda zai saba da shi a hankali. Wato koma bayan yadda da yake tunanin ba zai iya sabo da shi ba.[39] Masu ƙoƙarin samar da kafafen intanet na Hausa na fuskantar wannan ƙalubale. Hirar da wannan bincike ya yi da wasu masu kafafen intanet na Hausa na nuna cewa:

i. Ba sa samun goyon bayan da ya kamata yayin da suka tunkari cibiyoyi ko sasukan nazarin Hausa.[40]

ii. Ba sa samun goyon bayan da ya kamata yayin da suka tuntuɓi masana harshen Hausa.[41]

iii. Ba a samun goyon baya daga ɗaliban Hausa kamar yadda ya kamata.[42]

Cikin sauƙi, abin da ya kamata shi ne a bi maganar Bahaushe da ke cewa: “Zamani riga.” Ya jaddada wannan batu in da ya ce: “Zamani abokin tafiya.”

4.3.5 Rashin Ingantattun Injunan Gyara Rubutun Hausa

Rashin ingantattun injunan gyara rubutun Hausa ya kasance ƙalubale ga ci gabanta a duniyar intanet. Idan aka ɗauki harshen Ingilishi, za a tarar da cewa yana da injunan gyaran rubutu. Yayin da mutum ya rubuta kuskure, injin gyaran rubutu zai iya nuna masa akwai kuskure. Babban misali a nan shi ne Microsoft Word. Da zarar mutum ya rubuta kalma ba daidai ba, to za a ga jan layi ya bayyana a ƙasan kalmar. Idan kuwa jimla ce aka rubuta ba daidai ba, za a ga layi ruwan bula a ƙasan jimlar baki ɗayanta.

A kan kafafen intanet ma (har da kafafen sada zumunta) akwai injunan da ke iya gyara rubutu. Babban misali a nan shi ne injin ɗin Grammarly. Ya kasance inji da ake iya setawa a kan kwamfuta ko waya. Da zarar mutum ya rubuta kuskure, wannan inji zai zaƙulo kuskuren sannan ya nuna wa mai rubutun zaɓuɓɓukan gyara. Wani lokaci kuma yakan gyara rubutun kai tsaye ba tare da jiran mai rubutun ya yanke hukunci ko ɗaukar wani mataki ba.

Hoto 4.14: Injin Gyaran Rubutu na Grammarly

Injin Gyaran Rubutu na Grammarly

Madogara: Rubutu a Gimel Bayan an Sauke Grammarly Kan Kwamfuta

A hoto na 4.14 da ke sama, za a ga cewa dukkanin kalmomin da ke cikin saƙon da aka rubuta an ja musu layi ban da guda biyu (“of” da “for”). Wannan ya faru ne sakamakon an rubuta su bisa kuskure. Haka wannan injin gyara na Grammarly ke taimaka wa marubuta wajen nuna musu kurakuren da ke cikin rubuce-rubucensu na Ingilishi.

Dangane da Hausa, ba haka abin yake ba. A maimakon gyara, sai dai ma injunan su riƙa rikita mai rubutu. Wani lokaci har sukan ɓata masa rubutun. Misali, idan mutum na rubutu a kan Microsoft Word, idan ya rubuta wata kalma mai kama da ta Ingilishi, injin ɗin na iya sauya tsarin abajadan zuwa kalmar Ingilishi da ke kama da ita. Misali:

a. “bara” (begging) na iya sauyawa zuwa “bar a”

b. “boko” (formal education) na iya sauyawa zuwa “book”

c. “buga” (hit) na iya sauyawa zuwa “bugs”

d. “daya”  (one) na iya sauyawa zuwa “days”

e. “ita ce” (she is the one) na iya sauyawa zuwa “it ace”

f. “waje” (place) na iya sauyawa zuwa “wake”

g. “yamma” (east) na iya sauyawa zuwa “gamma”

h. “yawo” (momvement) na iya sauyawa zuwa “yawl”

Wannan matsala na haddasa yawaitar matsalolin kurakuran da suka shafi ƙaidojin rubutu. Yakan kasance aiki biyu mutum zai yi. Na farko gyara kurakuran da ya tafka da kansa. Na biyu kuma gyara kurakuran da suka samu sakamakon sauya masa rubutun da inji ya yi. Mafi yawan rubuce-rubucen Hausa a duniyar intanet cike suke da kurakuren da suka shafi ƙaidojin rubutu.[43]

Ba wannan ba ne kaɗai dalilin samun yawaitar kurakuran da suka shafi ƙaidojin rubutu a kafafen intanet na Hausa. Akan same su yayin da masu gudanar da kafa ba su naƙalci ƙaidojin rubutun Hausar ba. A taƙaice ke nan, zai kasance suna rubuta Hausar kamar yadda tsammaninsu ya raya musu. Babu wata doka da ta hana buɗe kafar intanet ga wanda bai ƙware ga harshe da al’adar al’umma ba. A bisa haka, ya rage ga masana da manazarta Hausa da su yi hoɓɓasar samar da ingantattun kafafen intanet. Hakan ne zai yaƙi wannan matsala ta karya ƙaidojin rubutun Hausa a duniyar intanet.

4.3.6 Baƙaƙe Masu Ƙugiya

Hausa tana da baƙaƙe na musamman. An fi saninsu da “baƙaƙe masu ƙuniya. Sun kasance kamar haka: /Ƙ/, /ƙ/, /Ɗ/, /ɗ/, /Ɓ/, /ɓ/.  Rubutun Hausa babu su tamkar miya ce da ba ta da gishiri. Kasancewar sanya su na da wahala, yawancin kafafen intanet suna amfani ne da makamantansu. Haka ma sauran na’urori kamar a wayar salula da sauran kafafen intanet da ke ba da damar rubutu. Misali:

a. /K/ a maimakon /Ƙ/

b. /k/ a maimakon /ƙ/

c. /D/ a maimakon /Ɗ/

d. /d/ a maimakon /ɗ/

e. /B/ a maimakon /Ɓ/

f. /b/ a maimakon /ɓ/

A wasu lokuta kuwa, akan ɗan yi musu kwaskwarima. Wannan bincike ya ci karo da rubuce-rubuce da dama a kafafen intanet inda aka yi wa baƙaƙe kwaskwarima da nufin su wakilci baƙaƙe masu ƙugiya. A ƙasa an kawo misali:

i. /K’/ a maimakon /Ƙ/

ii. /k’/ a maimakon /ƙ/

iii. /’D/ a maimakon /Ɗ/

iv. /d’/ a maimakon /ɗ/

v. /’B/ a maimakon /Ɓ/

vi. /’b/ a maimakon /ɓ/

Duk da akan yi amfani da wannan dabara sosai, ba ta wadatar ba. Daga baya ne aka samu salailan rubutu (fonts styles) da ke ɗauke da baƙaƙen Hausa masu ƙugiya rubutun da aka fi sani da Rabi’at da kuma Abdalla.[44] Daga baya an ci gaba da samun manhajojin baƙaƙe masu ƙugiya. A shekarar 2019 ne kuma kamfanin Microsoft ya fitar da baƙaƙen Hausa masu ƙugiya waɗanda za a iya amfani da su a kan kowace kwamfuta.

4.3.8 Rashin Ilimin Amfani da Kafafen Intanet Daga Ɓangaren Hausawa

Hausawa da dama na da matsalar rashin ilimin yadda za su yi ta’ammuli da kafafen intanet. Wannan ya haɗa da (i) Yadda ake hawa kafen intanet ɗin da (ii) Yadda ake binciko bayani ko bidiyo ko odiyo da ake buƙata. Lawal Ɗalha (mai gudanar da kafar Bakandamiya) ya bayyana wannan ƙorafi inda ya ce: “Akasarin mutanenmu (Hausawa), musamman waɗanda ba su yi makaranta mai zurfi ba, ba sa fahimtar yadda za su yi amfani da taskar cikin sauƙi.”

4.4 Naɗewa

Ya zuwa yau, manyan kafafen intanet da ake da su na Hausa sun kai arba’in da uku (43). Wannan adadi mai yawa ne idan aka kwatanta da da takwarorinta harsunan Nijeriya da Nijar. Duk da haka, yawan kafafen bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da adadin kafafen intanet a duniya waɗanda sun haura biliyan guda da ɗigo bakwai. Kafafen intanet na Hausa na fuskantar ƙalubale daban-daban. Waɗannan ƙalubale sun shafi yanayin duniyar intanet da yanayin ƙasar Hausa da yanayin Hausar kanta. A ɓangare guda kuwa, sun shafi halayyar Hausawa na ƙarancin ilimin amfani da kafafen intanet da kuma rashin ba da gudummuwa da kuma ƙarfafa guiwa ga masu gudanar da kafafen intanet ɗin.



[1] A duba Giraf 2.1 da ke babi na biyu.

[5] An yi la’akari da maganarsa da ke cewa: “I have started this blog more than 11 years ago.” Ma’ana: “Na buɗe wannan kafa sama da shekaru 11 da suka wuce.” Ya yi wannan maganar ne a shekarar 2017. Shekara 11 kafin 2017 zai kasance 2006.

[6] An yi hira da shi ranar 2 ga watan Maris, shekarar 2020. Shi ke jagorantar kafar intanet ta Hausa mai suna wikihausa.

[7] Akwai masu kafafen intanet da suka ɓoye adireshi da lambobinsu. Samun tuntuɓar ire-irensu ya ci tura.

[8] A rataye an kawo ƙididdiyar adadin mutanen da ke ziyartar wasu daga cikin kafafen intanet na Hausa.

[9] Haka!

[10] Haka!

[11] Haka!

[12] Haka!

[13] Haka!

[14] Haka!

[15] Haka!

[16] Haka!

[17] Haka!

[18] Haka!

[19] Haka!

[20] Haka!

[21] Haka!

[22] Haka!

[23] Haka!

[24] Haka!

[25] Haka!

[26] Haka!

[27] Haka!

[28] Haka!

[29] Wannan ya shafi ɓangaren tarihi da sauran bayanai da suka shafi al’adu da adabi da harshen Hausa.

[30] Akwai ɓangarori kaɗan da aka bar su cikin harshen Ingilishi. Hakan na iya kasancewa sakamakon kasa samun takamaiman fassarorinsu.

[31] Wannan salo ne na fassarar inji. Inji na fassara iya wurin da ya sani (ta hanyar amfani makamantan fassarori da aka ɗora masa). Sauran ɓangarorin da bai sani ba kuma, yakan bar su haka nan ba da fassara ba.

[32] Yawanci matan da ke tallata haja suna shiga da ta ci karo da al’adun Hausawa. Misali, waɗanda ke tallata rigar mama, akan ɗauke su hoto ba tare da tufafi ba. Daga su sai rigar mama da suke tallatawa.

[33] Yana da kyau a fahimci cewa, an ƙi kawo misalan hotunan ne domin kare martabar al’ada da addinin Bahaushe (kasancewar sun saɓa musu). Idan aka ce za a kawo misalan hotunan, to tamkar “mai dokar barci ne ya ɓuge da gyangyaɗi.”

[34] An kawo jerin kafafen intanet na Hausa guda arba’in da uku (43) a ƙarƙshin 1.6 da ke babi na ɗaya.

[35] Yaren gina kafafen intanet

[36] Yaren daidaita ginin kafafen intanet domin ba shi tsari mai kyau

[37] Yarin ba wa kafafen intanet umarnin aikata wasu ayyuka

[38] Yaren harhaɗa ɓangarorin kafafen intanet da ba su umarni

[39] Har ya zuwa shekarar 2020, mutane da dama suna amfani ne da samfurin Microsoft Office 2007. Sun ƙi karɓar sababbi da aka samar waɗanda an bunƙasa su sama da na 2007. Wasu da suka karɓi sauyi kwana-kwanan nan, sun nuna farin ciki da gamsuwa. Kamar haka abin yake a sauran ɓangarorin rayuwa. Wannan ne ya sa Bahaushe ke cewa: “Sai an gwada akan san na ƙwarai.

[40] A ƙasashen da suka ci gaba, kusan abu ne da ya zama tilas kowane sashe a jami’a ya kasance yana da kafar intanet (za a iya tabbatar da hakan yayin da aka bincika duniyar intanet). Dangane da sasukan nazarin Hausa, ba haka abin yake ba. Har ya zuwa 2020, wannan bincike bai ci karo da ko da sashen koyar da Hausa a Nijeriya ko Nijar da ke da kafar intanet tasa ta kansa ba! Wai “wata miyar sai a maƙwabta!.

[41] An yi hira da Bunza, (2019) bayan ya dawo daga taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa wanda aka gudanar a Folan. Ya bayyana cewa mallakar kafar intanet dole ne ga malami a ƙasashen da suka ci gaba. Wannan abu ba haka yake ba a ƙasar Hausa. Dangane da abin da wannan bincike ya gano, masana Hausa masu kafar intanet ba su da yawa.

[42] Ɗaliban Hausa sun fi ƙwarewa a kafen sada zumunta kamar su Fesbuk da Was’af. Sukan ɓata lokaci matuƙa a ire-iren waɗannan shafuka. Da a ce za su mayar da hankali wajen bibiyar shafukan intanet na Hausa, to “da ba kwaɗo ba inji gaya.”

[43] An tabbatar da haka bayan an nazarci kafafen intanet na Hausa guda 39, tamkar dai yadda aka bayyana a ƙarƙashin 1.7 (Hanyoyin Gudanar da Bincike) da ke babi na ɗaya.

[44] Fasfesa Abdalla Uba Adamu ya cancanci yabo matuƙa a wannan fanni. Ya taka muhimmiyar rawa a duniyar intanet ta Hausa. Shi ya samar da waɗannan salailan rubutu a sauƙaƙe a karon farko. Ya zuwa shekarar 2019, ana amfani da salon rubutun Abdalla ne domin rubuta baƙaƙe masu ƙugiya a mafi yawan rubuce-rubucen Hausa.  Salon rubutun Rabi’at shi ke bi masa.

Post a Comment

0 Comments